Sashe 100
Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
‘Ya jiki?’suka yi mata, ita kuma ta gaida Inna daga haka ta shiga kallonsu ɗaya bayan ɗaya idanuwanta suna masu begen son ganin fuskar Yashjub..ta samu ta ga halin da yake ciki, su koka tare, su rarrashi juna tare, amma sai ta ga babu shi babu mai kama da shi…
Siyama ta tambaya, Siyaman tace mata”ita ma yanzu suka shigo,ba ta gansa ba”
Dan haka ta juya ta fara laluben wayarta still hawaye suna sintiri a kan fuskarta sun k’i tsayawa ko na second d’aya.
Kallonsu Hajiya Mama wadda ta gama cewa Najeeb ‘ya je ya Kira Doctor ta yi,sannan tace”me kike so Manu?”
Ta yi mata tambayar cike da tausayawa don yadda take hawaye jikinta har yana karkarwa dole ta bawa kowa tausayi!
A hankali Inna ta matso ta ruk’o hannunta da niyyar yin rarrashinta aikuwa kamar jira take yi tashi d’aya ta fashe da wani irin kuka ta fad’a jikin Inna ta k’ank’ameta.
Duk dauriyar Hajiya Mama sai da ta yi hawaye….duk kalar kunya da kawaici irin na Manubiya kalli yadda take kuka a gabansu ita da Inna akan cikin jikinta ya zube ai kuwa tab’uwa ta kai tab’uwa, kuma ta sake tabbatarwa ba ita ta zubar da cikin da kanta ba, zubar mata da shi aka yi, tabbas Mommy ta zalinci baiwar Allah nan amma ba ta Isa ta ci bulus ba wallahi……wani irin tausayin manubiyan ne ya lullub’eta, a ranta ta aiyyana ‘a hakan ma Manubiyan ba ta ji abunda Likita ya ce ba,’
tashi d’aya ta shiga addu’a ‘Allah ya sa kar maganarsa ta tabbata, Allah ya sa Manubiya za ta haihu’
shiyasa ma ba ta gayawa ko su Inna ba, kuma za ta cewa su Ummi suma su b’oye gudun ma kar baki ya yi yawa a zancen aje ya tabbata, inshaaAllah Manubiya sai ta haihu, babu abunda ya samu mahaifarta.!!!
Kuka sosai Manubiya take yi kamar ranta zai fita, dan zuwa yanzu ta kasa b’oye kawaicin ta…
shigowar Najeeb da Likita ne ya tsagaita hak’urin da su Hajiya Mama suke ta bata, suka d’an matsa gefe domin ya yi aikinsa.
A karon farko ya tabbatar musu jininta yayi mugun hawa, sannan tana buƙatar hutu sosai sosai, dan haka ya ce ‘bari ya yi mata allurar bacci.’
Cikin kuka ta shiga cewa
“A’a ka fara jira Ya Yash ya zo tukunna sai ka yi min,ina son ganinsa.”
Kallonsu Likitan ya yi, zai yi magana Najeeb yace”ka barta tukunna, bari in kira sa.”
Cike da kwarin guiwa kanshi tsaye ya shiga gwada numbobin Yashjub, amma duka hud’un da ya ke amfani da su a kashe!
Gashi kowa ya tsura masa ido yana jira…shi abun ma mamaki ya basa ‘Anya kuwa Yashjub ne ya aikata haka?’
Manubiya ba lafiya tana asibiti, ba ya wajen, sannan ya kashe gaba d’aya wayoyinsa!gaskiya to akwai matsala kenan..definately..
A hankali ya d’ago ya kallesu cikin in ina yace”wayoyinsa ba sa tafiya, bari in je gidansa in duba”
Shiruuu Manubiya ta yi, hawayen idanunta suka k’afe, ta shiga wani irin rikitaccen yanayi…dama ta san Ya Yash sai ya shiga tashin hankali, amma ba ta yi tunanin zai yi watsi da ita ba! ko a wanne Hali yake a ciki ta yi tunanin zai taushi zuciyarsa ya zo gareta!
to ko dai bai san ta yi b’ari ba? Inaa ya sani ta san shine mutum na farko da su Hajiya Mama za su fara kira.
Tana wannan tunanin Likita ya kamo hannunta, ta cikin cannula ya juye mata ruwan allurar bacci, wanda tun kafin ya gama zarewa bacci ya yi awon gaba da ita.
Ba ta dad’e da yin baccin ba Daddy ya zo, dan haka bayan sun gaisa da su Inna suka fita shi da Hajiya Mama.
A garden d’in da ke cikin asibitin suka nemi guri suka zauna.
Cikin fahimtarwa ba tare da b’oye b’oye ba Hajiya Mama tace “Manubiya ta yi b’ari, kuma Likita ya tabbatar mana magani ta yi ta sha akai akai shiyasa ta yi ɓari wanda ƙarfin maganin ya janyo watak’ila ma ba lallai ta haihu a gaba ba.
Na san ka shiga ka ga halin da Yarinyar nan take ciki, kuma ka san ko da wasa ba ita ta yi yunk’urin zubar da cikin nan ba, dan haka inaso ka gaya mini me lissafinka ya baka a halin da ake ciki yanzu?.”
Shiruu ya yi, ya fi minti ashirin…duk su biyun sun yi shiru babu mai cewa komai, kafin ya d’ago ya kalli Hajiya Mama yace”ina riba ga su Yasira idan sun zubar mata da ciki?”
Lumshe idanuwanta ta yi ta bud’e tace”mashaaAllah Imam, na gode Allah da soyayyar ƴaƴanka ta daina rufe maka idanu daga ganin gaskiya.
Ina so ka san cewa su Yasira ba su da riba dan sun zubar da cikin Manu, amma Khadijah fa?”
A mugun zuciye ya mik’e yana wani irin huci, tashi d’aya idanuwansa suka kad’a suka yi jazir, cikin fushi yace”yanzu ne komai ya baiyyana, ya bada ma’ana”
Ya fad’i hakan yana mai juyawa had’i da shirin barin wajen….da sauri Hajiya Mama ta mik’e itama ta ruk’o sa, cikin hikima tace”Imam idan ba ka iya kama b’arawo ba fa shi sai ya kama ka. Yanzu ka gaya mini hujja d’aya da zaka nuna ka kamasu da laifi?”
Bata jira ya bata amsa ba ita ta ce
“Babu!.
Kuma idan ka yi haka to kamar ka sake dulmiyar da y’ay’anka mata ka saka su a halaka ne, mazan kuma har abada ba za su tab’a yafe maka ba, ka ga ta raba ka da su kenan har abada.”
Cikin rashin fahimta yace”Hajiya Mama ni ne Uba, ni zan fad’a a ji, da ni da ke duk mun san ita ce do we really need to prove anything to them? (Ta ina kasa musu gaskiya a faifai su ganta muraran ya zama dolenmu?)”
Girgiza kai ta yi kafin tace”dad’ina da kai kenan, idan zuciyarka ta motsa Imam ba ka ji ba ka gani!
Wallahi d’azu da na fahimci abunda Khadija ta saka yaran nan suka yi sai da na yi hawaye, Imam su Yasira y’ay’anka ne jininka ne kai ya kamata ka tashi ka tsaya ka gyara tarbiyyar su da lissafinsu da aka lalata,yanzu idan ka kori uwarsu kana tunanin za su rabu da ita ne?
Za ka sha mamaki idan suka kwashe kayansu suka yi maka yaji suka koma gabanta gaba d’aya, tunda bakinsu d’aya, kalli fa abunda ta tura su suka aikata, meye kake tunanin ba za su iya yi mata ko su aikata dominta ba?..kaga daga nan kuma sai abunda Hali ya yi, hakanan za ta lalata maka zuri’a! Allah kad’ai ya san abunda Hali zai yi.
Su kuma mazan ba za su tab’a yafe maka ba, cewa za su yi ka kori uwarsu saboda kawai ba ka sonta.
Abunda ya kamata mu yi yanzu shine
mu nutsu mu karance su, sai mu san abun yi, saboda wallahi Imam akwai abubuwa da dama da bamu sani a kan Khadijah ba, kuma idan muka ce za mu yanke hukunci cikin fushi tou kuwa za mu kwafsa, dan indai har Khadija za ta iya kashe d’an cikin Yash to akwai wasu abubuwa da yawa game da ita wanda mu ba mu sani ba.
Sannan yanzu idan aka yi hayaniya, ta tafi, to fa ba za mu tab’a sani ba, sannan a fannin ƴaƴanka nan ma zai zamana bamu bamu samu mun gyara abunda ta b’ata ba wanda na tabbata Wallahi ko gidan miji ba su Isa su iya zama da wannan mugun halin ba…daga karshe su yi muguwar rayuwa!Imam yaran nan amana ne Ubangiji ya baka, kuma zai tambayeka ranar gobe k’iyama fa!…ka nutsu ka yi abunda nace sai ka ga an dace”
A hankali ya koma ya zauna ya dafe kansa da Hannu bibbiyu, kafin ya d’ago ya kalli Hajiya Mama yace “Mamaa ba zan iya ci gaba da zama a inuwa d’aya da matar nan ba, ta yi mini abubuwa da dama ta cuce ni da yawa,Hatta lamarin Khadija ba ni da tantama itace wallahi….”
Tiryan tiryan ya zaiyyano mata yadda mallan lawal ya kirasa, da kuma yadda ya mutu kafin ya samu ganinsa, sannan ya ɗaura da cewa ”ya yi hacking wayarta amma yana ga kamar ta gane, dan ta ma chanja wayar da layi, ta kashe wanchan,wanda haka ya ke sake nuni da tabbas ba ta da gaskiya.”
Waje Hajiya Mama ta nema itama ta zauna, ta kamo hannun Imam wanda zuwa yanzu yake kuka kamar k’aramin Yaro, cikin tsananin rashin jin dad’i tace”ka yi hak’uri Imam,da ni da mahaifinka mu muka tilasta maka aurenta,ka yi hak’uri ka yafe mana, mun had’aka da…..”
Da sauri yace”ba laifinku bane Mama,na san ba ku yi tunanin za ta zama haka ba ai,saboda da ba hakan take ba,na san tana da masifar kishi amma sam ban yi tunanin zata zamo haka ba.”
Ajiyar zuciya Hajiya Mama ta sauk’e kafin tace”kaga ire iren abunda na ke gaya maka ko?kaga lamarin Khadija ma har da sa hannunta sannan recent mutuwar lawal ma muna zargin itace..Ni tunda na ga abunda ta aikata a Yash na san ta yi abubuwa da dama waenda bamu sani ba, shiysa ka ji na ce maka mu bi komai a sannu, mu bincike ta kafin mu san abunyi idan ba haka ba ba za mu ci ribar al’amarin ba…..”