← Book details Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 95 OF 152

Sashe 95

Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A b’angaren Khadija kuwa,abubuwa da dama ne suka had’e mata!
Kenan har yanzu Imam bai yi bincike ya goge zarginta ba!bai yi nadamar abunda ya aikata mata ba?
Sannan ko kewarta
ma bai yi ba duk tsawon waennan shekarun bai nemeta ba, bai nemi ta dawo garesa ba maimakon hakan ma yana so ne ya ƙarasa yanke duk wata alaƙar da suke da ita da shi,y’ar cikinta ma ya raba ta da ita kenan yanzu.!
Abu na uku kuma ta san tana da gaskiya akan sharrin da Lawal ya yi mata, amma kuma har ga Allah idan akwai Al’amari mafi k’ololuwar tozarci da Muni da masifar tashin hankalin da ba ta son
tunawa a rayuwar shine wannan al’aamarin,ita kanta ita kad’ai idan ta tuno ji takeyi kamar ta binne kanta tsabar tashin hankali, ba don k’arfin addu’a ba da tuni ta zauce tsabar yadda abun yake addabar ta a ko da yaushe idan ta tuna,
A yadda Imam ya zama wani irin mugun mutum ta san zai yi mata terere ne kamar yadda mai makarantar su Yahansun ta ce yace “kowa sai ya ji kansu shi da ita,har Yahanasu”.A ganinta idan ba ta samu damar shak’uwa da Yahanasu ta bata tarbiyya da kulawar da ta kamata ba to bai kamata ta bada gudunmawa wajen goga mata bak’in fenti ba!Yahanasu mace ce, aure za ta yi, ta san muddin ta bawa Imam k’ofa ya tozartata tabbas abun sai ya shafi rayuwar y’arta.
Mommy Uwa ce ta gari kuma za ta iya rantsuwa a kan soyayyarta ta gaskiya ga Yahanasu shiysa ta zab’i ta bisu ta addu’a, dama rayuwa ba a yi ta dan ka samu komai yadda ka ke so ba!…tsakaninta da lawal Allah ne kad’ai zai Isar mata dan ya cuceta ta koina,Imam kuma ya tarwatsa ta gaba d’ayanta!….

kaico!da rashin sa’ar Miji na gari wanda zai tsaya mata ya bugi k’irji ya yi shaidar ta ya kareta a gaban kowa,asalima shi harin rayuwarta da duk wani sauran farin ciki da darajarta yake yi…
ko maganar tozarcin da wannan rana ta k’unsa ba ta so ta tuna ballanta a yi mata terere a bainar jama a a gaban y’arta.
Dan haka ta zab’i ta bi y’arta da fatan alkhairi kawai tare da addu’ar samun Miji na gari dan tabbas duk macen da ta yi rashin sa’ar Mijin kwarai a rayuwa to ta yi babban rashi…..
………shiyasa tun jiya Hankalinta yake a tashe, take addu’ar Allah ya kawo abunda zai tarwatsa maganar auren Jidda da Yusuf dan tabbas Yusuf bai dace da Jidda ba, mutumin da ba a san silar arzik’in sa ba ta ya za a d’auki y’a a basa saboda Allah…………..

Sallamar su Manubiya ce ta katsewa Mama dogon tunanin da ta lula!
A hankali ta sauk’e wata nannuyar ajiyar zuciya ta shiga goge hawayen da ita kanta sai yanzu ta san suna zubo mata.Sai da ta gama goge fuskarta tukunna ta d’ago ta kallesu tana mai amsa sallamar tasu.

Cikin tsananin mutuwar jiki Manu ta k’arasa inda take suka gaisa da Mama da Aisha da Anty Umma,ta gaida Ammi wadda daga ita har Siyama suka yi mamakin ganinta a parlourn nasu tukunna tace musu “Ina su Inna”
Aisha ce ta mik’e tace”mu je wajen nasu”
Daga haka ta yi gaba suka bi bayanta.

Su biyu kawai suka tarar a cikin d’akin,Jidda ta rame a cikin kwana d’aya tak! ta fita a haiyyacinta..
Suna zaune Inna ta na yi mata nasiha a haka su Manu suka shigo suka tarar da su.
A gefen gadon suka zazzauna suka sakata a tsakiya kowa idanunta ya cicciko.
Bayan gaishe gaishe Inna ta yi sauri ta mik’e ta ce”ga ta, Manu, Aisha ku yi mata fad’a kuma. Baba yace ana d’aurawa za a wuce a kaita gidanta.”
Siyama ce ta iya cewa”Inna kuma babu abunda za a yi?”
Murmushin da ya ki fi kuka ciwo Jidda ta yi ta rik’o hannunta tace”ba komai Siyama,Allah ya sa hakan ne ya fi alkhairi”
Siyama na shirin yin magana suka had’a ido da anty Umma wadda shigowarta kenan dan haka ta yi saurin d’aura yatsanta a kan labb’anta alamun ta yi shiru kafin ta kalli Manubiya tace”Manu d’an zo”
Suna fita ita da Inna suka ce mata “tunda har Jiddan ta yi shiru, ta hak’ura itama, to kawai a ci gaba da kwantar mata da hankalli,kar wadda tace wani abun da zai d’aga mata hankali a cikinku.
Baba ya riga ya yi nisa ba zai ji kiran kowa ba, ga Ammi Chan a parlour har ita aka had’u aka dinga bashi hak’uri d’azu amma ya k’i hak’ura!!
dan haka kawai mu zuba mishi ido.Zab’in Allah muke nema a ko da yaushe..dan haka ba a san meye a k’asa ba, a dai ci gaba da addu’a kawai…”

Da “to” kawai Manubiya ta amsa su, daga haka ta nufi d’akin da ke opposite na Jiddahn dan ta san watak’il shine na Inna, tana shiga ta mayar da k’ofar da rufe dan har ga Allah ba ta son had’a idanu da Jidda ba za ta iyaba, gaba ɗaya ta kasa yarda da ‘wai Jidda za ta auri Yusuf amma ba abunda za ta iya yi a kai.’
Waya ta d’auko ta kira Yashjub….a tunaninta har yanzu za ta ji fushi a muryarsa amma sai ta ji sa wasai kamar ba ta yi masa laifi jiya ba har yana tambayarta akwai abunda take so ya siyo ya taho mata da shi?yana hanya Daddy ya d’an kirasa zai je ya dawo.”
“A’a”kawai tace.
Daganan ta tambayesa ya suka yi da Baba,komai ya gaya mata daga haka shima yace “su yi ta addu’a, zai kirata anjima, yana shiga office d’in Daddy yanzun”
Sallama suka yi ta ajjiye wayar tana tunani barkatai a cikin ranta.

K’arfe 10:30am guri ya cika taff da jama’a dan Yusuf da kaka mallan sun yi gayya ba laifi,cikin gida kuwa kowa hankalinsa a tashe yake, suma su Ya Nafi’u hankali a tashe dan yanzu suka dawo daga kai gado, shiyasa suka kuma tabbatarwa eh fa Jidda Yusuf za ta aura…kaff wajen daga y’an gaiyyar sod’i da suka ga anata sauk’e kulolin abinci da lemuka da snacks da kajii sai Yusuf da kaka mallan ne kawai suke farin ciki dan hatta Baba hankalinsa ba a kwance yake ba, ba a son ranshi zai aurawa Jidda wanda ranta ba ya so ba musamman ma yanzu da Baban Al’Ameen ya zo ya ja sa gefe ya basa hak’uri, sannan ya ce masa
”a shirye yake su ɗaura auren Al’Ameen da Jidda a yanzu.Ya yarda da Al’ameen har ma da ita kanta Jiddan, amman indai har zargin su yake yi kamar yadda labari ya iske masa to tabbas babu wanda ya fi chanchanta Jiddan ta aura idan ba Al’ameen d’in ba.”
“Ya je ya sake tunani,da shi da wakilin Al’ameen suna nan babu inda za su je,fatan Allah ya sa su ji alkhairi.”

Tun daga nan jikin Baba ya yi sanyi, tun ba ma da Baban Al’ameen yace”ya yarda da har ita kanta Jiddan” ba!
A take a lokacin ya ga rashin adalcinsa ga Jidda…..tabbas ya biyewa dokin zuciya ya yanke d’anyen hukuncin da har abada zai dinga damunsa dan ya san zuwa yanzu kam ba zai yiu ya chanja d’aurin auren nan daga kan Yusuf ya koma kan Al’ameen ba….

BULAMA ✍️
0903 441 3252
*MANNUBIYA*
*Book 2*
*page 33*

“Na gaya miki dama,ni ne Mijinki…in da ace ba ki tsaya b’ata mana lokaci ba da tuni abubuwa da dama basu faru ba!.
Allah ya bamu zaman lafiya Jidderty”
Yusuf yana gama turawa Jidda message kamar haka, ya juya ya nufi cikin masallacin, yana zuba wani faffad’an murmushi..yana ji kamar an yi masa bushara ne da Gidan Aljannah.

A gefen Baba ya nemi guri ya zauna, idaunsa a kan Baban Al’ameen wanda tun d’azu ya ke ankare da shi!! yana sane da shi ya san so yake a fasa auren a bawa d’ansa. har ga Allah bai yi niyyar yi wa Baban Al’ameen ko Al’ameen d’in wani abun ba amma abunda mutumin yake ta yi tun d’azu ya sa ya k’ullacesu, kuma sai ya nuna musu waye Yusuf!
Bari a gama d’aura masa aure da Jidda a kaita gidansa lafiya, Wallahi sai ya b’atar da su.

Ana shirin fara d’aurin auren.
Sojoji da y’an sanda masu fararen kaya sun fi mota ashirin, suka danno kai cikin layin…a dai-dai wannan lokacin.

Sojoji uku da ss guda d’aya ne suka shigo cikin masallacin suka ce “kowa ya fito!”cikin dakakkiyar murya,aikuwa tashi d’aya waje ya hautsine….
cike da fargaba jama’ar suka fara kiciniyar fita ana hayaniya da tambayar “mai ya faru”
Baba ne ya juya da niyyar cewa Yusuf
“mu je, mu ji mai ya faru, a samu abun ya lafa sai a dawo a d’aura”..amma kamar walk’iya da ikon Allah sai ya ga babu Yusuf babu mai kama da shi, bayan yanzunnan suka gama magana da shi.

A b’angaren Yusuf kuwa, tunda ya ga Sojoji hankalinsa ya yi masifar tashi! tsoro ya rufesa, in banda dukan uku uku babu abunda k’irjinsa yakeyi. dukda kuwa ya san cewa fuskarsa ba sananniya bace ba a cikin yaran black snake kuma shi bai yi abun da har ya zamto wanted ak nemansa ba amma hakan bai hanasa tunanin watak’il shi aka zo nemeba, dan yanzunnan ya ga message d’in Abokinsa ta inda yake sanar masa ”an zo kama Black snake a airport, ya yi yunk’urin guduwa an harbesa ya mutu, sannan an bud’e wayarsa an fara binciken neman Yaransa!!
dan haka a duk inda yake kawai ya gudu!! kafin a samu komai ya lafa.”
Yana gama karanta message d’in ko numfashi bai ja ba ya ga Sojoji sun shigo, shiyasa ana fara hayaniya ya sulale ya bi ta k’ofar liman da sauri ya fice, amma yana fita ya ci karo da wasu a ta gaban k’ofar saboda dama zobe su ka yiwa masallacin….tashi d’aya suka damk’esa dan an raba musu hotonsa shiysa suka yi saurin shaidasa.
Chapter 95 · 0% Book details