Sashe 5
Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tabɗijam!! Ai kuwa in dai har hakan ne to aiki ya ganta! Dan
dole ta tashi ta d’au mataki saboda al’amarin na Yassir ya fara zama wani abun daban…ba ta riga ta tabbatar ba amma muddin ta gama tabbatarwa shi ne to fa ba za ta zauna ta zuba masa ido
tana gani yake wasa da rayuwar Yashjub ba, shirmen nasa ya yi yawa……
A hankali tana Jin kanta yana wani irin mahaukacin sarawa
ta nemi guri ta kwanta, ta lumshe idanunta, a take hawaye suka shiga sintiri akan farar fuskarta…
Har ga Allah ba ta san yadda za ta yi da Yassir wanda ya zame mata k’adangaren bakin tulu ba, gashi ba ta Isa ta yi wani abun ko ta tunkare shi da maganar ba tunda ta lura abunda ya ke expecting daga gareta kenan.
Tashi d’aya ciwon Kan nata ya sake hauhawa, in banda sarawa ba abunda kanta yake yi, shiyasa ta yi shiruu ta kwanta kawai ta lumshe idanuwanta……….
Ba ta dad’e da gama waya da su ba suka dawo gaba d’ayansu, kafin kowa ya shiga inda take Yassir ya shiga shiyasa su Yasira suka wuce d’akunansu kawai.
Ya yi mamakin ganinta a kwance, hankalinta kwance!
Amman dai fuskarta ta kumbura ta yi jaa wanda hakan ya ke nuni da kuka ta yi.
Ƙarasawa ya yi inda take ya d’an zauna a gefen gadon a hankali ya ce ‘’Kausar’’
Da kyar ta samu ta danne Zuciyarta wadda ta ke yunk’uro mata……..
…A da, da farko ta san tana son Yassir, da Yashjub ya dawo gaba d’aya sai ta ji Yassir ya fita a ranta, dan tashi daya k’aunar Yashjub ta ci k’arfin komai a zuciyarta!
A yanzu kuwa a halinda ake ciki tabbas ta tsani Yassir, tsana ba ta wasa ba!
Dan ya yi mata kane-kane ya tare gaba ya tare baya ya hana ta sakat sannan wannan zargin da ta fara akansa yasanya ta sake jin tsanar sa ta nunku a zuciyarta, kuma indai har zargin ya tabbata to ba ta jin akwai wanda za ta tsana sama da Yassir a kaff fad’in duniyar nan…
Da kyar! Ta taushi zuciyarta,
ta d’an bud’e idanunta kad’an.
Suna had’a ido da shi ta yi murmushi, a hankali ta d’an miƙe daga kwancen ta jingina a bakin gadon ta ce “Baby!’’.
Wani sanyi ne ya ratsa zuciyar Yassir, har sai da ta kai shi ga sauk’e wata sassanyar ajiyar zuciyar, kafin ya sake matsawa kusa da ita ya ruk’o Hannunta
ahankali yana kallon cikin idanunta saboda ƙoƙarin ya fahimci yanayin da za ta shiga
ya ce “ban gan ki a asibiti ba, maiyasa??’’
K’ura masa idanu itama ta yi,
kafin da kyar ta samu ta iya cewa
“I’ve better things to do(ina da abubuwan da su ka fiye mini zuwa asibitin mahimmanci),
bayaga hakan ai ba kai ne ka yi hatsarin ba,
Bare har in damu kai na.’’
Wani kalar murmushi ta ga ya yi kafin ya ce ’’kalamanki suna nufin kin san Yashjub ya yi accident,
amma ba ki damu ma ki je ki duba shi ba, ko??’’
Wani k’ululun bak’in ciki Kausar ta had’iye, tana jin wani kalar takaici yana sake lullub’e ta…ji take kamar ta yi tsalle ta damk’i wuyansa har sai ta ga ya daina numfashi tukunna ta cikashi.
Zuwa yanzu ta gama tabbatarwa Yassir ne ya kwance tayoyin motar Yashjub musamman ma da ta tuna
yadda a jiyan ya ƙi barinta ta kwana a d’akinshi, dama tun jiyan taketa sak’e-sak’e a ranta game da hakan
tana so ta fahimci what he is up to(me ya ke shiryawa)….
‘’Don’t you care about him
(Shin Ba ki damu da shi bane)??’’
Ya sake jeho mata tambayar
still yana kallon cikin idanunta.
‘Wato saboda ya na so ya fahimci ko tana son Yashjub shiyasa ya yi wannan haukar kenan??’
Kausar ta yi wa kanta tambayar ba tare da ta san wa zai bata amsa ba, kafin da kyar ta ce ’’kamar yadda na gama gaya maka yanzunnan Yassir ‘Ina da abubuwan da su ka fiye mini zuwa asibitin mahimmanci’
Misali; bacci, hutawa…
Duk sun fiye mini in kwashi jiki in tafi dubashi”
Ta fad’a mishi hakan tana
mai kawar da kanta gefe, a ranta ta na aiyyana
’dole ta yi k’ok’ari ta danne kanta, ta yi tunani mai kyau, da taku mai kyau, dan in dai ta bari Yassir ya fahimci wani abun tou daga ita har Yashjub rayuwar su tana cikin hatsari, dan ta lura Yassir ya haukace’
Matsowa kusa da ita ya yi sosai ya sa Hannu ya kamo fuskarta ya juyo da ita saitin tasa daff da shi tukunna ya ce
‘’Mai yasa to ki ka yi kuka?
Yadda idanunki da fuskanki su ka yi ɗinnan ya tabbatar min da kuka kika yi.’’
Lumshe idanun nata ta yi ta bud’e
tukunna ta ce ’’ba ni da lafiya’’
Murmushi ya yi tukunna ya ce
‘’Kausar! Allah dai ya sa ba ƙarya ki ke yi min ba, umm???…… ‘’
A hankali tace ‘’na ce maka bani da lafiya, shiyasa ka ganni haka, me ye ne yake damunka haka wai?
Akwai matsala ne?’’
ta yi mishi tambayar idanunta suna ciccikowa da hawaye.
Zuciya da abinda take so, dan tashi d’aya sai tausayinta ya lullub’e shi, dan haka duk sai jikinsa yayi sanyi, a take yahau inda-inda.
A hankali ta lumshe idanunta ta bawa siraran hawayen nata damar zubowa, suka shiga sintiri, wanda hakan ya sake yin tasiri ba kad’an ba a zuciyar Yassir….dama tunda ya shigo ya ganta hankali kwance ya d’an sak’k’o, da kuma ta ce ba ta damu ba sai ya kawar da zarginsa a kanta, dama kawai ya yi mata tambayoyin ne saboda yanaso ya tabbatar ta yanda zai kawar da duk wasu zarginsa a kanta, kuma inshaaAllah daga yau ya kawar ɗin, inshaaAllah ba zai sake d’aura ayar tambaya a kanta ba…..
Yana wannan tunanin ya
jawota zuwa jikinsu a hankali, ya shiga rarrashinta, a chan k’asan ransa ya ce ’’Alhamdulillah’’
dan ba k’aramin dad’i ya ji ba da ya fahimta kuma ya tabbatar da ‘Kausar d’insa ba ta son wanin sa’..
Amman fa dukda haka ba wai zai bar Yashjub bane, dan ko ba komai ya san in dai Yash ya na da rai to babu shi babu walwala, saboda har ga Allah jin sa yake yi kamar a tsakiyar kansa, ko yanzun ma da kyar ya ke ta rarrashin kansa yake tausar zuciyarsa wadda take ta faman tunzura shi akan ya je
ya ce ‘zai kwana ya kula dashi’
daganan ya samu ya k’arasa abunda ya soma…..
Kawai dai ya san indai hakan
ta faru tou kamar ya baiyyana kanshi ne, saboda shi zai fara zama suspect tunda shi ya kwana da shi….shi kuma ya riga ya san ba zai iya danne zuciyarshi daga yi masa kwab d’aya ba dan indai suka kad’ance daga shi sai Yashjub tou tsaf zai iya danna masa pillow a cikin baccin sa………..
Shiyasa ya taushi zuciyarsa ya hak’ura ya bari akan gara ya sake sabon plan ta yadda ba za’a kama shi dumu-dumu ba..
••••••
Tun kwana biyu da suka wuce Baba ya fara tantama akan ‘anya kuwa Baraka tana gidan Musbahu’
duba da yadda kullum yake tare da mai sunan Baba tun safe har dare, shiyasa yau yana zuwa shi kuma ya tambayesa…
Cikin nutsuwa da fahimtarwa suka yi wa Baba bayanin abunda ya faru akan batun Baraka dalla-dalla, sannan suka ce ‘ya yi hak’uri akan k’in gaya masan da suka yi, dama suna so ya d’an huta sanann abubuwa su d’an yi sanyi ne tukunna, dan ba sa so hankalinsa ya tashi sosai a lokaci guda.’
Shiruu kawai ya yi da farko kafin daga baya ya ce ‘Allah ya rufa asiri’’
daga haka ya ja Bakinsa ya yi shiru yana kallon su Muhsin suna koya wa Inna rik’e abu dan jikin nata Alhamdulillah anata samun ci gaba a cikin kwanakin da ba su kai sati d’aya ba.
Suna nan zaune gaba d’ayansu,Ya Nafi’u ya kira Ya Musbah ya ce masa “yanzu sir Najeeb ya kira shi yake sanar masa’Yashjub ya yi accident, yana asibiti, driver d’insa ma har ya rasu.’’
Tunda suka ji Ya Musbah ya yi salati dama gaba d’ayan su suka juyo suna kallonsa, ai kuwa yana ajjiye wayar suka hau tambayar sa ’’me ya faru?”
Abunda Ya Nafi’un ya gaya masa shima ya fad’a musu idanunsa a kan Manubiya, ai kuwa hankalinta ba k’aramin tashi ya yi ba a take!!
Sanna ga mamakin su kawai sai suka ga ta fashe musu da kuka…..
Murmushi kawai Baba ya yi
yana mai jin wani kalar kwanciyar hankali da nutsuwa su na ratsashi
dama yanayin yanda suke waya akai-akai ya fahimci kamar itama tana son Yash d’in
yau kam ya tabbatar, shiyasa ya ji zuciyarsa ta yi k’al! Ko ba komai ya san zai kai Manu gidan wanda itama take tsananin so.
..
Cikin d’an k’ankanin lokaci suka yanke akan ‘Manubiya, Ya Musbah, Muhsin da Jidda! Su fara yin gaba, su je su dubo shi, su yi masa ya jiki’
Dan haka aka fara shiri domin su samu su je ɗin da wuri, shi kuma Baba ya ce ‘’idan Aisha ta zo kamar yadda Nafi’u ya ce, sai ta zauna da Inna, shi kuma sai ya taho da mai sunan baba idan ya farka dan tun d’azu da suka shigo ya fara bacci.
Dan haka in ya tashi sai su taho su uku har da Ya Nafi’un wanda yace yana gama abunda yake yi za su zo.
In ya so sai su dawo gaba d’ayansu a tare’.”
Ya ƙarashe faiyyace musu hakan, yana mai zaro kud’i daga aljihunsa ya mik’awa Jidda ya ce ’’gashi su siyawa Yashjub d’in su ayaba da lemo a hanya’’.
Jikin Manubiya har karkarwa yakeyi, tun kafin kowa ya shirya ita har ta shirya ta karb’i
address da room number da sir Najeeb ya turo a wajen Ya Musbah, ta zura hijabinta, ta d’au jakarta da wayarta ta tsaya musu a bakin k’ofa.