Sashe 17
Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ingijetan da Mommy ta yi ne ya sanya ta kasa ci gaba da magana, cikin tsananin fushi Mommy ta fara magana…tana hawaye take cewa’’kar ki soma tab’ani, ki bar ni kawai in mutu Larai tunda kin kasa yi min maganin matsalata.
Abu d’aya tak! Zuwa biyu amma ya gagareki wanda hakan ya sanya na fara tunanin ‘anya ma kuwa kina yi min aikin nan tsakani da Allah?.’
In ba ki ci! In ba ki sha! In baki sutura da wajen zama amma ace wai ki kasa mi……’’
Yadda Mommyn ta ga Baaba Larai ta kafeta da manyan idanunwanta waenda suka yi jazir suka cicciko da kwallah ne ya sanya ta kasa ci gaba da magana, dan haka kawai sai ta juya mata baya ta sake rushewa da wani irin kuka.
Baaba Larai ta so yin fushi da Mommy itama, ta so mayar mata da martani daga nan in yaso su yi kacha kacha ma amman kuma sai ta kasa, saboda ta san zafin rashin nasarar da suke ta fuskanta ne ya tunzura ta ga furta mata hakan, dan ko ita kanta daurewa kawai takeyi amman abun ya fara bata tsoro kuma ta fara gajiya….ba wai iyaka kai kud’in Yash da suka kasa hanawa ba, hatta su Hajiya Mama sai da suka so su hana su zuwa amma kalli tsulum kawai sai ganin su sukayi…..
Tana cikin wannan tunanin Mommy ta juyo tana kallonta tana goge hawayenta kafin ahankali cikin sheshshek’a ta ce ’’yi hak’uri dan Allah’’ sai kuma ta sake rushewa da wani kukan.
Wani irin tausayin Mommy ne ya lullub’e Baaba Larai tashi guda..tun suna Yara ita kanta ta san abunda yake saka Mommy kuka ba k’arami bane, shiyasa yanzun da ta ga tana kuka ta sake tausaya mata ta tausaya musu ta kuma yi wa kanta alk’awarin ‘inshaaAllah ba za su kwashi kashin su a hannun ba….’
Ahankali ta sa Hannu ta janyota zuwa jikinta ta rungume sannan ta shiga bubbuga bayanta alamun rarrashi.
Kamar zuga Mommy ake haka ta shiga rera kuka kamar jira takeyi, cikin kukan ta fara magana tana cewa ’’Larai na gaji, kuma na sadaƙar, dan na san tunda har aka kai kud’i aka saka rana kuma Matar nan (Hajiya Mama) ta riga ta zo, to kamar an yi auren Yash ne an gama…shikenan mun yi failling, mun faɗi, mun ci tura, mun faɗi warwas a ƙasa Larai.
Sannan ga zuwan Matar nan, bana son ta a cikin gidana, mutuwa zan yi Larai, bana son ganinsu a cikin gidana! Zuciyata za ta buga…
Ban san da wanne zan ji ba, abun ya yi yawa, duka ta ko’ina ban san wanne zan tare ba…..’’
Ganin yadda take magana saboda zafin zuciya da baƙin ciki ne ya sanya Baaba Larai ta zaro ta daga jikinta cikin sigar rarrashi ta ce ’’ban san mai zan ce miki ki sake yarda da ni wannan karon ba, amma inaso ki yarda da ni sannan ki ɗora dukkan amincewa da hope ɗinki a kaina! inshaaAllah ba zan sake baki kunya ba, ni na san mai zan yi wannan karon, ba za mu faɗi ba inshaaAllah, ba za ayi auren ba, ba nan da kwanaki tara masu zuwa ba, ba kuma a har abada ba!.
Ba za a taɓa yin auren nan ba.
Sannan itama Hajiya Mama inshaaAllah sai sun koma inda suka fito, da yardar Allah, dan ba zan zuba miki ido in barki a hakaba, ba zan iya ba y’ar uwata…..sannan ba zan zuba ido ina gani ake ci miki kashi a cikin gidan ki ba! sanann ga shi daga zuwanta na lura so take ta yi wa mutane handsfree a gaban idon kowa’’…
•••••••
Gyara sosai Manubiya take sha, dan a cikin kwana d’aya da aka yi mata sau biyu safe da rana kawai har ta fara chanzawa….in banda ƙamshi ba abunda yake tashi daga jikinta, fatarta har ta fara sumul sumul da yellow ta na d’aukar ido.
Yanzun ma na uku aka yi aka gama, dan Mama ta ce ba su da lokaci dan haka a dinga yi
akai-akai tunda ba su fara da wuri ba…
Ana gama gyaran jikin ta fad’a wanka tana fitowa kuma ta sake zama a kan kujerar tsugunno ba dan ta so ba sai dan yadda ta ga Mama ta dage akan sai fa ta sake zaman, a cewarta ‘’d’azu tana sane da ita ba ta zauna sosai ba ta fake da cin abinci’’…
dariya duk suka yi, har Manubiyan wadda take Allah Allah ta yi ta shirya dan ta san daga yanzun zuwa ko wanne lokaci zai iya zuwa saboda ce mata yayi da yamma…dama Jidda ta tambaya mata su Baba sun bata go ahead, amma sun ce ta tafi da d’an rakiya shiyasa tun d’azu ta cewa Muhsin ya shirya.
Sai da ta kusan sakawa Mama kuka tukunna ta yarda ta ce shikenan ta tashi tana ta yi mata tsiya tana ce mata’’raguwa’’daga haka Maman ta yi musu sallama ta tafi dan tana so ta je itama ta d’an huta.
Manubiya ta na tashi ta nufi wardrobe, ta zaro kayan da za ta zata saka tukunna ta zauna ta shiga shiri…mai gyaran jikin tana gama shirin tafiya dai-dai itama ta gama shirin ta kenan, kiran Yashjub kuma ya shigo wayarta, duk a lokaci guda.
Dama wayar tana Hannunta yau kam babu wani maganar jan aji dan ita kanta kawai gani ta yi ta d’auka ta kara a kunnenta…..shiruuu ta ji ya yi da farko kafin chan ta ji ya ce ‘’Ina k’ofar gida.’’
Da kyar ta iya cewa ‘’tam’’
daga haka ta kashe ta k’arasa wajen Inna ta d’an durk’usa ta gaya mata, kafin ta mik’e ta d’auki mayafi me kyau da girma da kauri sosai ta d’aura akan doguwar riga y’ar kantin dake a jikinta.
Har za ta fita, sai kuma ta dawo ta k’ara turare har da d’an lipstick pink ta d’an goga sannan ta gyara zaman hularta….ta na juyawa suka had’a ido da inna dan haka gaba d’aya duk sai kunya ta rufeta, da sauri ta juya da niyyar cewa Jidda Ina Muhsin yayi amma sai suka had’a ido da shi ya d’ago labule, dan haka ta yi gaba bayan ta ce musu ‘’sai sun dawo‘’
suka fita ita da Muhsin da mai gyaran jikin….
Suna fita ta yi mata sallama,
Matar ta wuce, ita kuma ita da Muhsin suka tsaya kallon dalleliyar motar da ke fake a gaban su.
BULAMA ✍️
0903 441 3252
*MANNUBIYA*
*Book 2*
*page 10*
Suna fita ta yi mata sallama
ta wuce, ita kuma ita da Muhsin suka tsaya kallon dalleliyar motar da ke fake a gaban su.
Dukda ba ta riga ta ga na cikin ba dan motar tinted glass gareta amma tashi d’aya Jikinta ya bata shine.
A b’angaren Yash kuwa tunda ya zo ya yi parking a k’ofar gidan yake sake k’arewa gidan kallo yana sak’e-sak’e a ranshi…tun ranar farko da suka zo shi da Najeeb yake tunanin ta yadda zai siya musu gida su yarda su karb’a dan ya san tabbas da wuya su amince da hakan, amman dai zai gwada ya gani saboda har ga Allah daga arean har gidan basu kwanta mishi ba..
A take tashi d’aya tausayinta da k’imarta suka mamaye shi,
a ranshi yace “yanzu a nan ta girma ta yi wayo amma kalli yadda abun duniya da kwad’ayi sam ba su rufe mata idanu ba.’’
Yana wannan tunanin ya ganta sun fito su uku, sun yi wa d’ayar Matar sallama ta wuce, ita kuma sun tsaya ita da
Muhsin.
Murmushi ya yi, kafin ya d’ago wayarsa ya shiga kiranta, so yake ya ga yadda za ta yi shiyasa ya k’i fitowa balle ma taga inda yake…
Tana d’auka kamar d’azu ya ce ’’ki shigo mana” kawai.
Shiruu ta d’an yi sai da ta ji ya sake cewa ’’Come in pls’’
tukunna ta sauk’e ajiyar zuciya kafin ta kashe wayar suka nufi motar ita da Muhsin.
Su na zuwa ta bud’ewa Muhsin gidan gaba, sai da ya shige ya zauna ta rufe masa tukunna ta nufi baya ta sa Hannu a kan handle d’in….
Dariya ce sosai ta ke tasowa Yash wanda yake zaune a gidan baya, dama ya san hakan za ta yi tun lokacin da ya ga sun fito ita da Muhsin…
A take ya hau Ɗoki da zullumin son ganin yadda za ta yi idan ta shigo gidan bayan suka yi ido biyu da shi, yana cikin wannan tunanin ya ga ta d’aura Hannunta a kan handle d’in dan haka ya yi saurin matsawa ya bud’e mata tun kafin ta murd’a.
Ta d’an yi mamakin ganin yadda k’ofar ta bud’u tun kafin ta murd’a, amma sai ta yi tunanin maybe Yash d’in ne ya bud’e mata ta gaba inda yake zaune.
K’amshin mayatacccen turarenshi da sanyin ac ne suka fara yi mata sallama, har ga Allah sam ba ta lura da shi a ciki a zaune ba, dan motar da d’an duhu, sai da ta d’an sunkuya ta shiga ta zauna ta
mayar da k’ofar ta rufe tukunna ta d’an zabura ta d’ago ta kalleshi sakamokon kamshinsa wanda ta ji ya k’aru sosai a cikin hancinta da kuma alamun mutum da ta ji a zaune a gefen ta.
Suna had’a ido ya yi mata gwalo, yana mai jin ƙamshin da take yi yana shirin zautar da shi, da kyar k’asa-k’asa ta yadda ya tabbatar ita kad’ai ce za ta ji ya ce ’’an guje min kuma anzo an taddani…
A clear reminder to you wifey
‘destiny will forever bring us together,’
(Ki ɗauki hakan a matsayin tunatarwa Matas, a ko da yaushe ƙaddara za ta ci gaba da haɗa mu, har abada)..
Har abada muna manne da juna, InshaaAllah’.’’
Shiruu Manubiya ta yi dan ita ta ma kasa magana, sam tunaninta bai sa ta tuna da hannunshi ba sai da suka yi ido biyu da shi ta kalli hannun tukunna ta tuna ‘ba fa zai iya tuk’in ba.’
A hankali ta d’ago ta d’an kalleshi kafin ta ce ’’Ina wuni’’