← Book details Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 69 OF 152

Sashe 69

Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ko da labarin ya je mata ba ta yi komai ba, dan zuwa yanzu tama kasa kuka, amma fa sai da ta yi kwana uku bata runtsa ba..sai da Yasmeen ta yi mata prescribing magani tukunna aka samu ta yi bacci..gabad’ayan su tausayi Kausar d’in ta ke basu dan ta zama wata shiru shiru kamar ba Kausar ba, wani zubin har sai ka zo ka na yi mata magana amma ba ma ta sani ba, ko kuma kawai ta zuba maka ido ta yi ta kallon ka har ka gama baza ta iya cewa komai ba.
Lamarin ta ba k’aramin sake d’agawa Mommy hankali yayi ba, gashi ita ta ma kasa rarraashin ta dan batasan mai za ta ce mata wannan karon ba!
Ita tace ta yi hak’uri kar ta yi komai zata nema musu mafita, amman sai da Manubiya ta basu mamaki
saida ta shigo gidan yashjub..amma ba komai!dan wallahi ko da ace za ta bada ranta ne fansa to wallahi gara ta bayar ɗin akan dai ta bari kud’iranta ya tafi a banza,tura ta kai bango! Dan haka komenene zai faru a hanyar cimma manufarta sai dai ya faru bata damu ba! dan sai ta cimma manufarta.
Hankalinsu bai sake tashi ba sai da suka ga su Manubiya sun yi fiye da sati biyu amma shiru ba su ma da niyyar dawowa…dukda Mommy ba ta kasance mai yawan laulayi ba amma sai ga ta a asibiti wannan karon jininta ya hau matuk’a, matar da ko a ciki ba ta laulayi iyaka ciwon nak’uda kawai ta sani.Sai da suka shafe sati d’aya cur ba su zauna ba sunata jerawa Yash da Manubiya kiranye amma ko kyallin dawowarsu ba su hango ba,ganin Mommy tana shirin susucewa ne ya sa Baba larai nemo musu sabon solution ta inda ta kawo shawarar kawai su yi wa Manubiya ajiya a ciki sannan su cire mata Yash d’in a rai kwata kwata ta yadda duk nacin sa ba za ta tab’a bashi kanta ba. A ganinta wannan kad’ai ce mafita dan ta san maganar kunce jini da tayi zuwa yanzu har sati uku ba lalle ya yi musu yadda suke so ba…
Dan tsabar bala’i a jeji Mommy da Baba Larai suka je suka binne abunda suka yi,a ranar suka yi wa Daddy k’arya suka ce masa an yi musu rasuwa a k’auye suka je suka kwana washegari da yamma suka dawo sunata murna su ala dole sun yiwa Manubiya ajiya a ciki sannan sun saka mata tsanar Yash a rai.
A tunanin su, tunda sun yi hakan to su Manubiyan bai fi su k’ara sati d’aya ba daga haka su dawo, amman sai suka ji shiru har fiye da wata biyu, hakan ya sa Mommy ta sake d’aga hankalinta dan a ganinta indai har abubuwan da suka yi suna aiki ai Yash da Manubiya bai kamata ace sun yi zaman su a chan shiruu kamar haka ba, cike da bata tabbaci Baba larai tace”ta kwantar da hankalinta, watak’il har yanzu jinin da aka kunce mata tun farko bai daidaita ba, wataƙil yana on and off ne saboda ita dai bata karya abun da ta yi ba dan haka watak’il sunachan sunata yawon neman magani ne amman ba dai honeymoon ba.”

A b’angaren Yassir kuwa yana nan zargin Kausar ya dasu a ransa fiye da ko yaushe, dan ya lura Yashjub yana tafiya ta fara rashin lafiya….sai dai kuma Maganin da take sha na saka bacci ba kad’an ba ya ke taimaka masa, dan in ta sha ta kwanta haka zai shige d’akin nata ya yi ta bidirin sa wani lokacin ta nuna masa bata so amma sai ya yi ta ƙarfi wani lokacin kuma kawai ta rabu da shi dan ta san ba hak’ura zai yin ba ita kuwa bata da k’arfin hana sa ko yin fad’a da shi a wannan lokacin tunda ko ta gwada ɗin ma ba riba…rannan kad’an ya rage Yasmeen ba ta kama sa ba tsabar yadda yake zirya ba d’aga k’afa sam, amma ko a jikinsa bai damu ba..yana sonta kuma hakan yana taimakawa wajen kawar masa da damuwar da yake a ciki saboda kamar yadda damuwa ta yi wa Kausar d’in yawa hakanan shima damuwa ta yi masa k’ad’abaibai!!
Shi babban tashin hankalinsa a wannan lokacin shine ‘Yashjub yana chan yana hutawa tare da kyakykyawar matarsa, shi kuma yanannan duk wani plan d’in da ya had’a sai ya tarwatse’
dan hatta a tafiyar nan da Yashjub d’in ya yi sau uku yana k’ok’arin yashe sa amman ya kasa!
Har company d’in sa ya je amman komai thumbprint ne bayan thumbprint d’in kuma hadda password
Sannan ga zargin sa a kan Kausar ga Munirat da ta fara k’ular da shi da nacin ta….

Ba zai yiu Yashjub ya fi sa komai ba sannan ya fi sa kwanciyar hankali ba…shiyasa kawai ya gama deciding rufe chapter Yashjub da wurwuri dan ya gaji da nad’ar takaici…tunda yayi yayi ya kasa to zai b’arar kawai kowa ma ya rasa…
Wallahi ko sunansa ba ya so ya ji an ambata, Allah Allah ya ke ya ga babu shi a doron k’asa, ba don ya san ba zai taɓa iya sake jurar ganinsa a doron ƙasa na tsahon ɗan lokaci ba to da zai so ace ya fara tura masa bak’in cikin da watak’il ma shi ne zai zamo ajalin sa dan tabbas idan akace Yashjub ya mutu da takaici bak’in ciki da kuma tashin hankali abun zai fi yi masa dad’i fiye da komai.…tsabar yadda Yassir ya kwallafa rai da son ganin bayan Yashjub har wata y’ar rama ya yi…..

Today.(yau)

Daddy, Yash ɗin ya gayawa time na landing d’insu,
Ya so ace driver d’insa aka turo masa amma suna fitowa sukayi ido biyu da Yassir.

Sai da Yassir ya ji numfashin sa ya d’auke na y’an dak’ik’u tukunna ya dawo da kyar, sakamokon hango Manu da yayi..ta yi wani irin fari ta yi fresh ta k’ara kyau
Har kamar ba ita ba!.
Da kyar ya d’auke idanuwansa daga kanta ya maida akan Yash yace ‘’Wlcm”
Sai kuma ya yi musu jam’i yace
“Ya hanya?”

“Alhamdulillah”
suka ce, daganan suka nufi motar da ya faka, Yashjub yana mamakin yadda ya ga jikin Yassir d’in yayi wani irin sanyi kamar mara lafiya..

Sosai Jeep d’in ta cika taff da kaya dan sun yo tsaraba ga kuma kayyakin su da suka tafi da su sannan ga kayan wajen su hajiya mama….Ana gama lode kayayyakin a cikin motar suka shiga, ya ja motar suka yi gaba.

Har suka d’au hanyar gidan Daddy Yassir ya kasa magana,
wani irin kishi da zafi da takaicin Yashjub yake ji ta koina, ji yakeyi kamar ya juya ya shak’e sa, kokuma ya cika sitiyarin kowa ma ya mutu!
Amma da ya tuna ya kusan kawo k’arshen Yash d’in sai ya yayyafawa zuciyarsa ruwan sanyi dan ya riga ya gama had’a plan d’insa Allah Allah kawai yake ayi ayi lokaci ya cika, bayason ganin sa baya son jin ko da muryarsa ce! Ya kag’u ya rufe babin Yashjub ya fad’a wata sabuwa, dan a yadda Manubiya take yi masa d’innan ya san zai d’an sha fama da ita kafin ta yarda ta auresa bayan mutuwar Yashjub…..

“Ya na ga ka d’au hanyar gida?”
Muryar Yashjub ta katse masa lissafin sa
Sai da ya d’an d’au lokaci tukunna ya juya ya kalle sa ya ce
‘’Mommy ce tace in kai ku chan, ku huta. Zuwa gobe sai su Yasira su je gaba d’aya a tayata gyaran gida, dan ta san ba za ta iya ita kad’ai ba’’

Ba Manubiya ba hatta Yashjub sai da ya ji gaban sa ya yanke ya fad’i..shiruu kawai ya yi a ransa yace
“Allah ya rufa asiri”
Daga nan motar ta d’au shiru tsit kawai akeji ta koina har suka k’arasa bakin mansion d’in aka bud’e musu suka shiga, ba wanda ya sake cewa komai.

Tun kafin motar ta tsaya ya ga sun fito gaba d’ayansu
Har Kausar Ummi da Munirat..shine ya fara fitowa tukunna ya bud’ewa Manubiya gidan baya itama ta fito..kallon Kausar take yi tana mamakin kwalliyarta ta cikin glass d’in shiyasa ma ta kasa fitowa har sai da ya buɗe ɗin…
Gashi kayan jikinta k’anana, ga hula ta d’aura a kanta amma ba ta cusa gashinta a ciki ba instead ta fito da shi duka yana reto gefe da gefe da baya ko k’aramin ribbom ba ta mak’ala ba, ga wani irin high makeup da ta yi kamar wadda za ta je gasar saurauniyar kyau!
Ko ba a fad’a mata ba ta san saboda Mijinta ne ta yi wannan kwalliyar da shigar shiyasa ta kasa hana kanta jin kishi, dama tun d’azu a jirgi take jin amai da ciwon Kai ga kuma zazzab’i, yanzun kuma ganin Kausar ya sake b’ata mata rai shiyasa gaba d’aya ta shiga jinta wani iri sosai sosai.
Ahankali yake nazartar ta kafin yace”muje mana”
Ya fad’i hakan yana k’ok’arin ruk’o hannunta, gudun magana yasa ta d’an janye da style ta d’aga masa Kai alamun ‘to’
daga nan suka nufi inda dandazon su Mommy suke a tsatstsaye.

Ba abunda ya fi d’agawa Mommy hankali irin farin da ta ga Manubiya ta yi, dan har wani d’aukar ido ta ga tanayi!
Ta san sun yi mata ajiya a ciki
amma sai ta kasa hana kanta zargin ‘ko dai cikine da ita’!!
Har Manubiyan ta k’arasa inda take tsaye, ta d’urkusa a gabanta ta na gaida ita ba ma ta sani ba saida Baba larai ta d’an zungureta tukunna ta dawo cikin haiyyacinta,
Ahankali ta dafa kan Manubiya ta ce “lafiya y’ar albarka ya hanya?”
“Alhamdulillah”kawai Manubiya tace, daga nan ta gaida Baba larai itama ta amsa mata da kulawa kafin ta mik’e ta nufi Ummi tana shirin durk’usawa Ummin ta rik’eta tace
“Sannu ya hanya”
cikin tsananin ganin girman matar Manubiya tace “Alhamdulillah” daga nan ta gaida ita sai kuma suka hau murna da hugging juna ita da su Yahanasu yayinda Yashjub yake chan suna gaisawa da su Mommy, Baba larai tana tsokanarshi wai ‘ya yi k’iba.’
Chapter 69 · 0% Book details