← Book details Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 142 OF 152

Sashe 142

Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da mamaki Yahanasu ta kalleta kafin tace”Mama pls mana, dan Allah ki bari in…..”
Cikin tarar numfashinta tace”Yahanasu ki yi mini alfarma guda d’aya a matsayina na mahaifiyarki kar ki gayawa kowa kin ganni, inaso ace Daddy ya nemo ni ya maidani cikin zuri’arsa da kansa kamar yadda ya yi mini yankan k’auna da kansa…shekaru kusan talatin Yahanasu amma ace har ke da kanki kin fahimci sharri aka yi mini ta ya zan yarda Daddy da kansa bai fahimci hakan ba, sannan meyasa bai neme ni ba???.
Ni dai kawai inaso ya kasance ya nemo ni
ya mayar da ni da kansa da hannunsa Akan ace kece kika mayarda ni ba tare da yarda da amincewarsaba, kuma inajin tsoron had’uwa ta da shi, ban san ya zata kasance ba, kince abunda mai makarantaar ku ta fad’a sharrin su Mommy ne ko?
To na ji na yarda amma kuma wat if ya yi mini kamar yadda suka ce zai yi d’in?
dan na san zai iya aikata hakan Yahansu mutumin da ya kashe ni zai iya aikata fiye da abunda suka k’aga suka fad’a suka ce ya ce zai yi.”

Ciki girgiza kai Yaha tace
“Na tabbata idan na yi masa bayani zai fahimta zai yarda.
Kumafa Mama shi a tunaninsa kin rasu ne, muma a da duk hakan muka d’auka, ki bari a yi masa bayani”

“Yahanasu inda ace ya damu, to ya kamata ace zuwa yanzu ya fahimci gaskiya kamar yadda kema kika fahimta”

Yahansu zata yi magana Mama ta katseta ta hanyar cewa”dan Allah kar ki yi min jayayya, bana son musu daga gareki, ki yi yadda nace hakan shine farin cikina.
Na fi so ya fahimta da kansa ya nemoni da kansa, hakan shine kad’ai zai goge mini abunda ya faru.

Sannan bamuda tabbacin zai karb’eni Yahansu idan aka yi rashin sa’a ya tozartani Ina riba?
Ba zan so a ci mini mutunci a b’atamin suna ba, dan haka na rok’ek’i da girman Allah kar kiyi komai kar kice komai, alfarmar mutunci da darajata a idanunki ki bari mu yi addu’a ya yi yadda nakeso d’in ko na samu peace of mind da sauk’in radadin da nakeji a cikin zuciyata!”.

Da kyar Mama ta samu ta sanya Yahanasu ta yarda kuma ta hak’ura akan ‘ba zata gayawa kowa ba, har sai Daddy ya huce ya nemo maman da kansa ya fahimci komai…’
ba dan Yahansu ta so ba ta yarda da hakan, amma InshaaAllah ba za ta yi k’asa a guiwa ba har sai ta nuna masa hanya, shi kuma ya gane gaskiya ya nemi sanin inda take da kannasa kamar yadda Maman takeso.

Washegari Jidda suka zo ita da Al’ameen, nan kuwa komai ya dawowa su Manubiya sabo fil…..sun ci kuka kamar ransu zai fita, Jidda da Siyama masu d’auke da juna biyu wata uku uku kam sai da aka dangana da kwantar da su a asibiti tsabar kuka da damuwa….

A ranar ne kuma Gwaggo Suwaiba ta tashi tafiya, babu yadda basuyi da ita ba amma furr tace musu “ita tafiya zata yi..”
Wanda hakan sam bai yiwa kowa dad’i ba, dan kai tsaye hakan rashin kyautawa ne…hakanan su Ya Nafi’u suka kaisu tasha ita da Hadiza suka kama hanya, gidan ya rage daga Manubiya sai su Jidda abun tausayi , dan ma Anty Umma tana tare da su saboda Siyama ba ta wani dad’e ba aka sallamota daga asibitin ta dawo gidansu manu ɗin, Mama kuma ita take tare da Jidda a asibiti itakam sai da ta yi sati biyu a kwance, dama cikin nata ya zo da laulayi sosai tun usulinsa.

Yahansu har asibitin take zuwa ta duba Jidda su tattauna da Mama, amma har yau bata samu ta yi convincing maman ba, ganin fa bazata tab’a yarda ba ne ya sanya ta mayar da hankalinta ga tunanin ta yadda za ta bawa Daddy ko da clue ne a samu ya fara binciken nata, dan maman ta sanyata ta yi mata alk’awarin ba zata tab’a cewa kowa komai ba.

Sosai mama ta ji dad’in ganin kamal a matsayin wanda Yahanasun zata aura, dan shima ya je ya duba Jidda kuma ya je ya yi gaisuwa.

Sai da aka yi kwana ashirin da rasuwar Inna tukunna su Manubiya suka koma gidajensu, anty Umma ma ta koma gida, gidan ya rage daga mai sunan Baba sai Baba Muhsin da Ya Musbah dan Bararka tunda ta fita da gudu har yau ba’a ganta ba, cigiya har a gidan radio mahaifiyarta ta bayar amma shiru…shi ya Nafi’u ma ya d’auka da mahaifiyartata ta ji labarin zata yiwa mutane hauka, amma sai suka ga ta big’e da bada hak’urin abunda Barakar ta yi, sannan ta roƙi ‘dan Allah a yafe mata, a tayata addu’ar nasarar samun ganin ta……..’
….

Bayan kwanaki goma..

Yau kwanakin Inna talatin da rasuwa, su Manubiya kuma goma da komawar su gidajen mazajensu…Jidda ma a nan Nigeria Al’Ameen ya barta ya tafi dan saura kwana sittin ya kammala abunda ya je yi ɗin, kuma exams ne da shi Masu zafi a gabansa, shiyasa tace masa ‘tana son zama a nan’
su Ammi ma suka ce ‘ya barta a nan ɗin’
saboda jikin nata ya yi tsanani sosai….

Ya siya mata gida mai kyau a Na’ibawa, ya zuba kaya ya yi komai, amma dai a Hannun Ammi ya barta for now, saboda kusan kullum sai an k’ara mata ruwa..sosai kuwa Ammi da Mama suke kula da ita dan abunda suke yi mata ko Inna iyakacin abunda zata yi mata kenan.

Siyama ma ta koma gidanta, lafiya k’alau itakam bata wannan fitinannen Laulayi kamar na Jiddah.

A b’angaren Manubiya kuwa gaba d’aya ta gagara gane kan Yash!!
Tun ranar da Inna ta rasu shikenan ya chanja gaba d’aya. kuma ba wai ita kad’ai ba kowa yake yiwa hakan….haka kurum sai dai ya yi shiruu ya zauna ya tusa Mutane a gaba babu um babu um’um ya yi ta kallon kowa..amma iyaka idanuwansa kad’ai idan aka kalla tashi d’aya za’a fahimci yana cikin masifa da tashin hankali…
Hatta office ma da Najeeb ya zo zai yi masa handing over cewa Najeeb ɗin ya yi ‘ya cigaba kawai ba zai iyaba……..’.

Shima da so ya yi ya chanjawa Manubiya gida, amma sai Hajiya mama ta ce ”kawai ya zo Mansion d’in Daddy su zauna a side d’insa na da, dan tabbas yanayinsa yana mugun bawa har su su Hajiya maman tsoro, gashi an yi tambayar duniya yace mus ”he’s fine!! Babu abunda ya ke damunsa!”

Mommy kuwa har yau bata cire rai ba……Ya’isha dai ta tafi dahirr! ta ma cire rai….….amma tsohon yace mata
“ta kwantar da hankalinta, indai hular Manu aka d’auko
akayi aikin da ita to fa ta zuba ido zuwa ko wanne lokaci
labarin rasuwar Manu zai iya riskarta!!
watak’il inna itama ta saka hular ne shiyasa abun ya shafeta kuma shiyasa aka samu jinkirin mutuwar Manubiyan amma tabbas tana hanya itama….Su Yasira kuwa zuwa yanzu sun dawo daga rakiyar Mommy…babu Ya’isha babu labarinta zuwa yanzu kuma idan suka yi mata maganar Ya’ishan ma fad’a take rufe su dashi…dukda sun san itama tana cikin masifa amma sam wannan ba abunda za su yi shiru bane ba dan haka Yasira ta shirya akan zata je ta samu Daddy tace masa ‘ba fa su ga Ya’isha ba, kuma Mommy ko maganar ba ta so ayi!!!’
Ta san ko da matsalar ganin da take fama da shi aka barta ya isheta(dan zuwa yanzu kwata kwata idonta na dama ba ya aiki na hagun shima ya tab’u sosai)amma fa ba zata iya cigaba da yin shiru ba wallahi, dan wannan al’amarin serious case ne.

A lokacin da Yasira suke maganar za su je su samu Daddy ita da Yusra Mommyn tana jinsu…
Shiyasa hankalinta ya sake tashi matuk’a, dama masifar rashin gani da tsohon ya ke ta amshe kuɗaɗenta ana ta yin magani amma a banza ta isheta, ga Manubiya da ranta har yanzu Yash ma haka…a halin da take ciki dai yanzu ta ajjiye komai a gefe, dan ita babbar damuwarta itace a samu ta fara gani tarr tukunna sai a yi komai, su Yasiran kuma ta san ta rufe musu Baki a kan case d’in Ya’isha to amma kuma gashi yanzu kwatsam! Suna shirin jik’a mata aiki,…
Har fa su Yasmeen ta hana zuwa gidan, duk dan kar a tambayi Ya’isha, a lamarin waya kuwa da suka ji ta shiru tace musu ‘bata da lafiya ne’…
ita kanta sai yanzu ta san tanada matsala fa! dan Bata san me zata ce game da Ya’isha ba a gaba, sabida ba zai yiu ta yita b’oye b’oye har abada ba.

A b’angaren Abbakar shima tunda aka yi rasuwar kusan kullum sai ya je musu gaisuwa da daddare lokacin da ya tabbatar ba zai had’u da Yash ba!.
Ita dai Manu gaisawa kawai suke yi, daga haka ta wuce d’aki, dan abu da Abbakar sam ba ta so…to yanzu kuma ya isheta a waya yanason taimakon ta, ta yi blocking d’insa amma a banza a rana sai ya kirata sau bakwai da different layuka ga uban messages, dan ma Allah ya taimaketa Yash bai tab’a gani ba saboda shima he’s
not himself (baya cikin haiyyacinsa) kwana biyun nan duk sai a hankali kawai. …
Ta san watak’il akan rashin lafiyar mahaifiyarsa ne wanda ya k’i ci ya k’i cinyewa (saboda ta ji anata maganar ciwon nata) Abbakar ɗin yake ta nemanta,
amma ita har ga Allah tsoron d’aukar wayarsa ma take yi, Shiyasa jiya da ta je gida ta tura Muhsin gidansu ya karb’o mata accnt numbersa ta tura masa dubu d’ari amma kuma dukda haka Abbakar bai bar kiranta da tura mata sak’onni ba.
Chapter 142 · 0% Book details