Sashe 91
Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sai da Yusra ta ji Siyama ta shige ciki ta rufo k’ofa tukunna ta juya ta nufi su Yasira waenda suka tsura mata ido tana wani irin murmushi….tana zuwa ta zaiyyane musu abunda kunnuwanta suka jiye mata Manubiya da Siyama suna cewa…ji suka yi kamar an yi musu bishara da gidan aljannah!Tabbas Allah ya na son su,saboda dama neman hanyar da za su bi su nunawa Yash kamar Manu ce ta zubar da cikin da kanta suke yi, yanzu kuwa Yasira tana jin wannan batun tashi d’aya ta san abunda ya kamata ta yi, dan haka ta cewa su Yusran gobe duk runtsi su yi ta kwak’umarta har sai sun ga password d’in wayarta, daga nan kuma sai su nemi number a wayar tata,saboda ita gobe za ta fita office…Yadira tana da kwakwalwa shiyasa tashi d’aya tace mata d’azu dai da yake ta kira ta ga number 090443 ne farkon number k’arshen kuma ba ta gani sosai ba
”Ba damuwa,Allah ya sa ba ta yi deleting history d’in ba idan muka d’au wayar time d’in kawai za mu duba na san lokutan da ya kikkirata ai”
Cewar Yasira.
Cikin tarar numfashinta Yusra tace”ko ta goge ma ni na san inda zan shiga in dubo,Allah ya kaimu goben da rai da lafiya.”
Baba larai suka kira suka sanar mata sannan suka d’aura da cewa”Sun fara zuba abubuwan da ta basu a duk abincin gidan,sannan ba za su samu matsala wajen jefa mata tablet d’in a ruwa ta sha ba saboda lucky for them ba ta shan bottle water ko na dispencer iyaka ruwan borehole kawai take iya tara a cup ta sha sakamokon laulayin ciki shiysa cikin sauƙi d’azu tana ajjiye cup d’in kafin ta je ta dawo suka jefe mata kwayar ba tare da su manubiyan sun farga ba daga ita har Siyama,to dai da ta dawo ta d’an yi sip biyu daga nan ta ajjiye maybe taste d’in ne ta ji ya chanja mata, shiysa suka yanke shawarar su dinga raba kwayar gida uku saboda kar ta gane….
to dai a halin yanzu sun zuba mata a gorar ruwanta na borehole uku da ta tara ta saka a fridge akan za ta dinga sha…”
Murna a wajen Baba larai abun ba a cewa komai..ji take kamar ta zuba ruwa a k’asa ta sha…sai da ta gama shi musu albarka kafin tace”amma Yasira cctv fa?”
Dariya ta yi tace kar ki damu Baaba, ba zai tab’a ganewa ba, saboda sai da muka shige jikin fridge d’in sosai tukunna muka saka kuma ƙofar fridge ɗin ta karemu sannan ba direction d’in wajen ma cctvn take kallo ba…sannan na cup ɗin shima ɗazu da za mu jefa ba mu yi a yadda cctvn za ta ganmu ba”
murmushi baba larai ta yi tace”MashaaAllah, Alhamdulillah,Allah ya ci gaba da taimakon mu”
daga haka ta mik’awa Mommy,itama duk da tashin hankali da fargabar Daddy da take ciki, sai da ta yi farin ciki matu’uka, ta yi ta sanya musu albarka, daga k’arshe suka yi sallama suna masu hango silver lining(alamun nasara)…
A b’angaren Najeeb da Siyama kam a ranar kusan kwana suka yi suna waya…da kyar ta samu ya yi mata sallama suka katse kiran, nan da nan bacci ya yi awon gaba da ita ,yayinda shi kuma ya duk’ufa Nafila…Tabbas ya manta rabon da ya shiga farin ciki kwatankwacin wannan..shiysa ya kwana sallah yana godewa Ubangiji, sannan yana rok’onsa ya tabbatar da aurensa da Siyama!…
Ya Musbah kuwa da ya yi alk’awarin zuwa, ko alamar sa babu, kuma bai yi waya ba,har cikin dare sai da Ya Nafi’u ya gawada kiransa amma bai d’auka ba, saboda Ya Nafi’un ya lura har da takaicinsa ne suka tarar wa Baba ya birkice musu lokaci guda haka…shi kam zuwa yanzu ya daina jin haushin Ya Musbah dan maimakon yaji haushin nasa ma shi kam tausayinsa yake ji, kuma inshaaAllah zai taimakesa ya fitar da shi daga kaidin Baraka..shiysa ya shirya zuwa gidan nasa gobe da sassafe dan shi da Yashjub dama sun riga sun san gidan…zai je ya samesa su fara ceto rayuwar Jidda wadda take shirin fad’awa halaka a gobe, daganan zai san abunda zai yi dan abun na Baraka ya zama abun tsoro.
BULAMA ✍️
0903 441 3252
*MANNUBIYA*
*Book 2*
*page 32*
A zaune ta same shi yana aiki a computer…zafi sosai take ji sakamokon zazzab’in da ya fara sauka daga jikinta, dan haka ta nufi bathroom domin ta samu ta sake yin wanka bayan wanda ta yi ba da jimawa ba.
Sai da ta sauya kaya tukunna ta fito, lokacin shi kuma ya gama aikin yana zaune ya miƙe ƙafafunsa akan gado…kallon ta yake yi yana mamakin yadda ta shiga ta yi wankan ta fito da wayarta rik’e kyam! A hannunta…da sauri ya kawar da zargi a cikin ransa ya mik’a mata Hannu alamun ta zo garesa..
Sai da gabanta ya yanke ya fad’i!…Ta san Yashjub ya yi k’ok’ari, sai dai ita kuma laulayin ciki ya zo mata har da k’in son kasancewa da shi, dan babu abunda ta ji ta tsana kamar yace zai nemi wani abun daga gareta.
Murmushin yak’e ta yi ta nufesa, tana zuwa ya gyara zama ya d’aura ta a kan cinyarsa, cikin muryar bege yace”yanzu dai ai jikin da sauk’i ko?”
Sunkuyar da kanta ta d’an yi k’asa, kafin ta girgiza kai alamun”a’a”.
Ya ji babu dad’i tabbas, dan yana lura da yadda ko Hannunta ba ta so ya rik’e a cikin kwana biyun nan..amma sai ya dake still,yace”haba mana!a ji da ni gaskiya ko in yi miki kuka..”
Daga haka bai bata ikon yin magana ba ma ya fara kissing d’inta cike da shauk’i….
Wani irin kuka ya ji ta fashe masa da shi, cikin kukan ta shiga k’ok’arin kwatar kanta.
Dakatawa ya yi, ya d’an cikata, sannan ya zuba mata rinannun idanunsa yana kallonta kafin da mamaki yace”Abunda na yi yanzun ne ya sanya ki yin kuka har haka?”.
Kasa magana ta yi dan ba ma ta san me za ta ce ba, kafin ta mik’e da sauri ta zagaya d’aya b’angaren gadon ta kwanta, ta juya masa baya, still tana sheshshek’ar kuka..
Ya fi mintuna ashirin a haka, ya k’ame kawai a yadda ta barsa, dan ya ma kasa motsi. kafin da kyar ya samu ya kwanta rigingine yana kalllon sama zuciyarsa tana wani irin tafarfasa ga wani irin ciwon ciki da ya turnik’e shi tashi d’aya.
Tashin hankalin zarginta da yake shirin dasuwa a cikin zuciyarsa sam bai sa ya yi tunanin ‘watak’il cikin jikinta ne ya zo da laulayin hakan’ ba, bayaaga haka shi bai ma tab’a sanin masu ciki suna gudun mazajensu ba sai ma son kasancewa a tare da su da ya san anayi….shiyasa gaba d’aya zuciyarsa ta jagule, ransa ya b’aci matuk’a, hankalinsa kuma ya tashi!! dan ya lura ba ta fara basa wannan attitude d’in ba sai da aka fara kiranta a waya….
Gaba d’aya kwakwalwarsa ta yi zafi, haka ma zuciyarsa tunani kala kala ya shiga yi….
ganin zuciyarsa ta na shirin tarwatsewa ne ya sa kawai ya mik’e ya fad’a bathroom ya kama ruwa ya yo alwallah ya zo ya ɗau niyyar nafila…..
Sai da ta ji shigewarsa bathroom tukunna ta sauk’e ajiyar zuciya ta yi addu’o’i ta shiga karatun Al’Qurani a cikin ranta, da haka wani bacci mai d’an karen dad’i ya yi awon gaba da ita…..
Sai da ya tashe ta sallar Asubah, tukunna ya juya ya fice ya nufi masallaci…ta lura da yadda ransa yake a d’an b’ace, dan haka ta shirya idan ya dawo za ta yi masa bayani ta basa hak’uri, ta san zai fahimceta.
Tana idar da azkar Yahanasu ta kira ta tace”tun jiya cikin dare ta so ta kirata,da kyar ta iya bari asubah ta yi…kamar yadda su Yash suka samu identity d’in mutum biyu su kuma sun samu na mutum biyar har an fara nemansu wataƙila Allah bai yi su Yash d’in za su ga wannan footage d’in ba.
yanzu tana ganin su gayawa Yash d’in ne, su k’ara musu haske su had’a k’arfi da k’arfe? ko kuma su yi nasu a daban?”
Ajiyar zuciyaManubiya ta sauk’e, ta yi hamdala a fili tana mai jin dad’in good news d’in tukunna tace” Adda Yaha mu yi namu a daban kawai, inaso in taimaka nima, Ina kwad’ayin ganin farin cikin da zai wanzu a fuskar Ya Yash a ranar da muka kama mai laifi sannan idan ya ga muma mun bada tamu gudummawar, mun taimaka.
Na ji suma suna maganar da shi da sir Najeeb, and a ta b’angaren nasu suma akwai haske,wanda inda ace sun maƙale sun kasa yin gaba ne to da sai mu k’ara musu haske da namu bayanan, amma tunda suna tafiya suma kawai muma mu yi namun, idan mun riga su yin nasara Alhamdulillah idan sun rugamu hakan ma Alhamdulillah kawai ni dai inaso in taimaka in bada gudummawa ne.”
Murmushi Yahansu ta yi kafin tace”shikenan Manu,duk yadda kika ce”.
“Yauwa.
akwai kud’in da na ajjiye zan baki na case d’in, yaushe za ki karb’a? cash ne”
Murmushi Yaha ta yi tace”ai kawai ki barshi…”
Da sauri Manu tace”Ina so in yi taimaka ta ko ina ne fa Adda Yaha,pls kar ki ce A’a”
“Tam shikenan”Yahansu tace kafin tace”yana Ina?”.
Dai dai nan Yash ya k’araso bakin k’ofar d’akin.
Tarr ya ji muryar Manubiya tana cewa”ya fita sallah, ai shiyasa ma na samu damar yin wayar, jiya ma na ga misscall, na san watak’il a kan maganar ne shiyasa ban d’auka ba saboda muna tare da shi…”
Da sauri ya juya ya bar wajen dan ba ma ya so kunnuwansa su sake jiyo masa wani bala’i da tashin hankalin..har dishi-dishi yake gani, da kyar ya k’arasa kan sofa na corridor ya zauna,
yana wani irin haki kamar wanda ya yi y’ar tsere…
Manubiya ta san akwai Gwaggwo mai aiki, kuma har ta fara jiyo k’amshin girki, amma hakan bai hanata mik’ewa ta d’an kimtsa domin ta je ta had’awa Mijinta breakfast ba, dukda kuwa morning sickness d’in da ya fara rufar mata mai zafiii.