← Book details Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 103 OF 152

Sashe 103

Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gani yayi ta tsaya tana kallonsa, dan haka ya ajjiye cup d’in ya zuba mata dogayen idanuwansa kafin yace
“Lafiya dai ko gwaggwo?
Akwai matsala ne!?”

Da sauri ta yi firgigit kafin tace”laa a’a ba komai”sai kuma ta juya ta fice ranta duk ba dad’i…ba ta so ta taso da case kuma a zo a yi bincike
aga ba komai ta je ta shiga masifa,
amman haka kawai
ta ji ba ta yadda da Kausar ba!
Ta gama had’a coffee d’in kenan Kausar d’in ta ce mata”ta je sama ta d’auko mata wayarta a sama a parlournta”

Ta so ta lab’e amma sai ta yi gaba kawai amma da ta dawo
tabbas taga kamar an tab’a flas d’in coffee ɗin, dukda
ba ta ga Kausar ta zuba wani abun ba, cake ma ta tarar da ita tana ci dan lokacin da ta dawo sai da ta d’an lab’e,amma kwata kwata
ita dai bata yarda da coffee d’inba, kuma abunda ya sake saka mata zargin Kausar d’in yadda ta dinga cewa “ta d’auka ta kai masa” “ta d’auka ta kai masa”bayan ta dawo d’in.
Gashi ta ga ta ci uban kwalliya,
dukda doguwar rigar abaya mai bottons ce a jikinta amma ta fahimci kamar k’ananan kaya ne ata ciki  saboda har cinyarta sai da ta hango a waje
d’azun da ta zauna tana cin cake, sannan ta gyara gashinta,
ta sha jambaki
ga uban k’amshi tanayi…

Kuma har waje ta biyota,
sai da ta ga ta shigo nan ɗin tukunna ta tsaya a wajen ta
fara wasa da flowers, tana sinsinawa kamar irin dama abunda ta fito yi kenan……..

Yadda Yashjub ya ga gwaggon ta yi ne yasa ya ɗanji a jikinshi watak’il akwai  abunda take so ta gaya masa amma tana jin tsoro…tashi d’aya lissafinsa ya basa ko dai akan case d’in Manu ne, tunda ai tare suke a gidan har da ita, shi fita yake yi dan haka dole ita ta ga wani abun…..ko kuma maybe taana so ta yi masa basaja ta kare kanta ne.!
Yana wannan tunanin yana sipping coffee d’in ahankali ahankali, kafin ya d’auko maganin ciwon kai daga aljihunsa ya b’alle ya sha, ya d’an had’a da cake kad’an daga haka yayi gyatsa yai hamdala ya fara k’ok’arin mik’ewa dan ya ji har an shiga sallah.

Yana mikewa ya ji kansa ya wani irin sarawa, wanda har sai da hakan ya kaishi ga kaiwa k’asa ya durk’usa a nan bakin kujerar.
Jiri ya fara yi, mai had’e da wani yanayi na daban da ya shiga tashi d’aya, abun har abun tsoro!
“Innalillahi wa inna ilaihirrajiun”ya shiga maimaitawa, dan tashi d’aya gabansa ya fara fad’uwa saboda zai iya cewa bai tab’a tsintar kansa a irin haka tashi d’aya ba!

“Ya subahanaAllah”
Ya furta a fili… ga Manu a asibiti, yanzu ya zai yi kenan, a ransa yace
“da na sani ban sha ruwan zafin nan ba, na san duk shine sila,
amman kuma tou jirin na menene??”
Ya yiwa kansa tambayar ba tare da ya san me bashi amsa ba.

Ganin abun fa gaba yakeyi,
yasanya yayi sauri ya lalubo makullin motarsa….ya san Manubiya ba ta da lafiya amma yana buk’atar kasancewa tare da ita, ta hakan ne kad’ai zai iya tseratar da kansa daga fad’awa halaka….saboda wannan abunda ya ke ji ɗinnan mai matuƙar haɗari ne babba.

Dukda baya jin zai iya yin tuk’i
a halin da yake ciki, ga kuma
jiri, amma gara ya gwada…kar ya je ya yi abunda zai binne kan shi da ransa.

Da k’arfi ya mik’e tsaye…dan zuwa yanzu ya fara ganin dishi-dishi.

Yana mik’ewa ya ji an fara knocking…Addua ya fara yi akan Allah ya sa ba gwaggwo bace ta dawo, dan ba gwaggwo ba ko Iya ce
Indai mace ce to fa akwai matsala muddin suka kasance waje d’aya a tashin hankalin nan da bala’in nan da yake a ciki.

Jin bai yi magana ba, ya sa Kausar ta shigo a hankali ta mayar da k’ofar ta d’an tura ta
barta a bude ba tare da ta saka key ba.

Da farko dishi-dishi ya fara ganinta, sai da ta matso daff da shi tukunna ya fahimci ashe Kausar ce….tunda yake a rayuwarsa Kausar bata tab’a burgesa irin na yau ba…sanye
take da wata arniyar gown ta roba iya guiwa
Fitted
Red
ga stones a jiki sai walwali sukeyi,ta rambad’a jan jambaki,
tasha kwalli!gashi ta gyara gashinta ta yi parking ta yi styling gaban da jel jelar
kuma tana reto a tsakiyar bayanta, sannan ga wani uban k’amshi da take zubawa.

Dakyar ya iya cewa”Kausar.”
Lumsassun idanunsa suna sake lumshewa.
Wata sabuwar k’aunarsa ce ta lullub’e Kausar a take, a hankali ta matso ta sa hannunta a daidai saitin zuciyarsa tana shafawa kafin tace”Dukda kai da Daddy kunce a baka space amma na kasa yin hakan Ya Yash, zuwa na yi in ganka, in ga halinda kake ciki, dan halin da na ganka ɗazu a ciki ya kasa fita daga kaina.”
Ta k’arashe maganar cikin wata shuumar murya,
sannan cikin shagwab’a da turo Baki, kafin a hankali ta d’an matso jikinsa.

Karkarwa jikinsa ya fara yi, dan haka ya tureta da dukkannin ragowar k’arfin da yake a jikin sa,cikin fushi yace mata
“Stay away!!!”
Ya daka mata tsawa.

Daga nan ya fara takawa
da niyyar fita amma sai ƙofofin suka juye masa, parlourn ma gaba d’aya
ya fara juyawa a kwakwalwarsa…ya ma kasa gane wacce ce k’ofar fita!.

Dasauri ta sake zagayowa
ta tsaya a gabansa tace”me ya sameka?In kira doctor ne?”

Tunani yayi tabbas idan doctor ya zo to maybe ya bashi magani,
dan zuwa yanzu ya san ba zai iya driving zuwa inda Manubiya take ba , dan haka da sauri yace
“Yes pls ki kira harda Yasmeen”.ya fad’i hakan a hankali.

Dan sake matsowa jikinsa ta yi tace”Okay mu je in kaika
Bedroom sai in kirasa”
Daga haka ta matso sosai
batayi wata wata ba ta yi hugging d’insa.

Wasu tagwayen ajiyar zuciya ta ji yana sauk’ewa a jere jere, kafin ya d’ago hannuwansa
gaba d’aya biyun ya rungume ta da dukkannin ragowar k’arfin sa.

Wani irin farin ciki ne ya lullub’e Kausar, tashi d’aya hawaye suka fara ambaliya a fuskarta
tsabar farin ciki…a hankali ba don ta na so ba tace”Let me go,
In kira doctor pls Ya Yashhh”
Ta fad’i maganar cikin sigar da ta sanya Yash ya sake rungumeta tsam a jikinsa…..
Shi dai daganan jin sa ganinsa da komai nasa suka d’auke
D’iff!!!
Ba shi ya farkaba sai……

Daddy ya yi tunanin zai ga Yashjub a masallaci amman shiru..
Dukdda ya san yana cikin damuwa amma ya kamata ace ya je Masjid ai….

Akwai maganganun da yake so su yi, yana so ya samu ya d’an kwantar masa da hankali tun d’azun, amma sai ya hak’ura ya bari akan idan sun had’u a dinner sai su yi, dan ya san maybe sai ya huta ya yi dinner tukunna zai wuce asibitin.

Shiruuu nan ma har aka fara dinner babu Yash babu alamun shi, kuma wani abun mamakin babu Kausar.
Tunani ya yi akan ‘ko dai ya wuce gidansa ne, sai kuma ya tuna ai yanzunma kafin ya shigo Sai da ya ga motarsa.

Yassir kasa zama dinner d’in ma yayi saboda tashin hankali da kishi….ya yarda da Kausar
amman idan ya tuna za ta kwanta da waninsa a gado ɗaya ba komai jikinta a ƙarƙashin bargo ɗaya gaba d’aya sai ya ji hankalinsa ya tashi ya gaza
sukuni..babu damar ya yi magana yanzu sai tace bai yarda da ita ba!sannan hakan shine kad’ai mafitarsu dan basu da
mafita sama da wannan ɗin…shiyasa kawai ya ke ta ƙoƙarin daurewa

Kai kawo ya dinga yi,
har sai da 40 minutes d’in da suka riga suka tsara ya cika, tukunna ya sauk’o k’asan lokacin ana tsakiyar cin abinci,
shi a tunaninsa ma an gama…

Tunda aka zauna dinner Mommy da Baba larai suka sha jinin jikinsu, dan kallar kallon tsanar da Daddy yake jifan mommy da shi sai da ya saka su a al’ajabi.

Da kyar Yassir ya dake ya gaida Daddy, daga haka ya juya ya ja kujera ya zauna ya fara zuba abinci a ransa yana
adduar Allah yasa wani ya yi masa maganarta, dan idan ya yi da kansa to ya b’ata komai.

Yassira ce tace
“Am Yassir Kausar tana sama ne?”

Kallon ta yayi yana jin wani sanyi a ransa, a zahiri kuma sai ya sake tamke fuska kawai ya d’auke kai.

Mommy ce tace mishi “ba tambayar ka takeyi ba?”
Dan itama shirun na Kausar d’in ya d’an dameta, saboda missing dinner ba aladar Kausar baceba, babu abunda ta tsana irin ta kwanta bacci da empty stomach.

Ajiyar zuciya ya sauk’e ya ajjiye spoon d’in
tukunna yace
“Mommy pls..kar ki yi mini maganarta, ku rabu da ni kawai.
Ni da na san ma kuna nan da ba zan sak’k’o ba…”
Daga haka ya ci gaba da chin abincin sa.

“Hmm”kawai junior yace, daga haka ya d’auke kai bai ce komai ba.

Ajjiye spoon d’in sa Daddy ya yi, daga nan ya gyara zama
ya yi gyaran murya ya kalli Yassir yace
“Kai!
Ina Yashjub?”

Ahankali ya d’ago ya kalli Daddy yace
“Yana side d’insa”

“Okay ni kuma ka raina ni ko?”
Mommy ta fad’a.

Kamar irin an dameshin nan ya ajjiye cokalin gaba d’aya, ya ture abincin sannan yace”Mommy Kausar ta tafi side d’in Yashjub dubo sa tun d’azu kafin magrib!”
Sai kuma ya yi shiruuu kamar mai tunanin wani abun kafin ya kalli Daddy yace
“Wanda ya ci ace ta dawo zuwa yanzu….
Allah dai ya sa lafiya”
Sai kuma ya mik’e da sauri ya fita, ya nufi side d’in Yashjub.
Gaba d’ayansu mik’ewa suka yi suma, suka bi bayanshi har Yahanasu.
  ……..
Tun a bakin corridor din da zai sadaka da babban parlourn gidan suka tsinci doguwar rigar abayar Kausar…
Da k’arfi k’irjin Daddy ya buga! dan haka suka tura k’ofar suka shige.
A tsaye suka tarar da Yassir a parlour ya k’urawa rigar Kausar ido wadda ke nan a yashe a tsakar parlourn.
Daddy yana gani tun kafin ragowar mutanen wajen su gani ya juya ya kalli Yadira da su Yusra yace musu
“Ku fita!”
Chapter 103 · 0% Book details