← Book details Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 53 OF 152

Sashe 53

Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Jidda kam itama tana cikin matsala, gashi ita tata matsalar ma bata isa ta tattauna ta da kowa ba dan kunya takeji..dukda ta ji Mama tana cewa Inna”jikin Al’ameen d’in Alhamdulillah, ulcer da hawan jini su ke damunsa but yanzu ya ji sauk’i anma sallamosa”
Amma hakan bai hanata shiga cikin matsananciyar damuwa ba, iyakar abunda take so, ta kuma san zai kwantar mata da hankali uwa uba ta ke da buƙata a wannan lokacin shine ta samu ta ga ya jikinsa, su shirya sannan su yi aurensu….ta san babu wanda zai fahimceta shiyasa ta rik’e damuwarta iya ita d’aya take ta fama….har ramewa ta yi tashi d’aya duk ta yi zuru zuru.
•••
A b’angaren Manubiya kuwa
Yashjub ya zame mata abun mamaki….tun tana fushi tana jin haushi har ta daina, dan ita gani takeyi ma kamar he’s possessed….shiyasa ta zubawa sarautar Allah ido amman fa a cikin kwana ukun da suka wuce ta gane Allah d’aya ne! Ga wahala ga azaba shi kuma Yashjub bai san maganar kauda kai ko kawaici a wanga harka ba….ita kam gaba d’aya komai ya fita kanta gashi sun ƙi su yi bak’o
ko guda d’aya, ballantana ta samu ta huta. kullum sai ta kira su Jidda amma an hanasu zuwa har y’ar rama ta yi shi kuwa Yash sai kace wanda yayi watanni da yin auren dan ya murmure abunsa ya yi haske sosai ya k’ara kyau.

Yau dai Allah ya d’aura Manubiya akan Inna ta yarda akan su Jidda su zo su kawo mata ragowar takardunta da aka manta ba a had’o da su ba.

Har da su Ya Musbah za a zo amman Manubiya bata saniba…Ya Musbah da Baba har ma da Ya Nafi’u ne suka
harhad’a kud’i suka yi mata
gara, kuma sunyi k’ok’ari sosai. Shine za su zo su kawowa a yau.

Tun safe taketa faman zumud’i dan ma Yash ya ce “kar ta damu ya riga ya yo order” ne, amma da tuni ta shiga kitchen….bata ma riga ta fara shiga kitchen ɗin ba saboda ya ce “sai sun dawo daga honey moon ɗinsu tukunna sai ta fara girki”,
Ummi ce take ta faman yi musu aike breakfast lunch har dinner.

Suna zaune ta ji k’arar doorbell, dan haka ta mik’e da sauri ta nufi k’ofa, da mayafinta a Hannu.

murmushi yayi ya bi ta da kallo, yana mamakin zumud’in da takeyi, ya san kuma har da murnar freedom d’in da zata d’an samu na wunin yau takeyi.

Tana bud’ewa ta ja ta tsaya, ta yi turuss! sakamokon ido biyu da sukayi da Yassira ita da muk’arrabanta a bayanta, har da Kausar.

Kallo d’aya Kausar ta yi wa Manubiya ta d’auke kai da sauri, sakamokon bugawa da ta ji k’irjinta ya yi!
Tun ba ma da ta yi tunanin
‘Yanzu fa a haka taketa yawo a gaban Yashjub, kwalliyar ma gaba ɗayanta saboda shi ta yi.’.

A b’angaren Manubiya kuwa, ba wata kwalliya ta yi ba sakamokon gajiya da ciwon jikin da take fama da shi..ita batama da energy d’in yin kwalliyar. Sanye take da red lace mai adon duwatsun silver, d’inkin riga da skirt wanda ya d’an kamata ba laifi kuma ya fito da asalin surar jikinta…dan mayafin ma a Hannu ta riƙesa dama ganin kuma ba su Ya Nafi’un bane ya sa bata yi yunƙurin rufawan ba ma…
babu komai a fuskarta sai d’an ragowar jan jambakin da ana gani an san sid’ewa akayi, jewelries kuwa iyaka y’an kunne ne kawai a kunnenta sai agogo a Hannunta..
Kayan ba k’aramin karb’ar ta ya yi ba kuma ya haskata sosai,
sannan yanayin simple d’aurin da ta yi shima sai ya sake fito da asalin kyawun fuskarta, ga kuma kyallin amarci, shiyasa ta sake fitowa ta yi wani irin azababben kyau….

Da kyar ta iya danne takaicin abunda sukayi mata ranar da aka je d’aukota, dan tana ganinsu komai ya dawo mata sabo, a take ta shiga k’ok’arin yakice abun a cikin ranta…dan a ganinta fad’a da gaba da su bashi da amfani tunda su dolen ta ne itan ma kuma dolen su ce!sannan in dai har tana son Yash ya zama dole ta so su.
Ta ji zafi kwarai amman tunda shine na farko, gara kawai ta manta ta yafe, but zatayi k’ok’ari wajen ganin ba su maimaita cin kashin su a kanta a karo na biyu.

Murmushi ta yi a hankali da niyyar welcoming d’insu warmly ta ji Ya’isha tace
“Yassira ki bangaje ta mana ki wuce!”

Dariya Yusra ta yi kafin tace
‘’ki yi mata uzuri, kin san a gidan tsoho dogon soro ake antayawa…sannan kin san
babu k’ofa ba door bell
shiyasa take tunanin shin ya kamata ta barmu mu shige musu parlour kai tsaye ko kuwa?…tunda ba ta san ya ake shiga gida mara soro ba.”

Lumshe idanu kawai Manubiya ta yi, tama kasa magana, ta tsaya kawai waje d’aya nan rike da k’ofar.

Tsaki Ya’isha ta yi kafin ta taho gadan-gadan zata bangajetan ta shige, daidai Yash ya k’araso wajen yana cewa”Baby ya kuka tsaya a waje, su shigo man.. “

Da sauri Ya’isha ta ja ta tsaya,
sai kuma ta koma gefe ta had’e rai ta tamke fuska.

Kallon su ya yi d’aya bayan d’aya kafin yace “Ina Yahanasu?”.

Sai da Yassira ta d’an fesar da iska tukunna tace”May be tana hanya”

Shiruu ya yi kamar zai ce wani abun, sai kuma kawai ya yi shiru.
Sam bai yi tunanin suna da audacity d’in (ƙarfin halin) da za su zo inda yake kwana kusa ba bayan abunda su ka aikata,sannan har da wata Kausar,ba ya so ya yi musu wani abun a gaban Manubiya..kamar yadda Daddy ya fad’a, shiyasa yake k’ok’ari wajen ganin bai bada k’ofar da Manubiya za ta ga wani abu na sab’ani tsakaninsa da y’an uwansa ba.

Dakyar ya danne zuciyar da ya ke ji tana taso masa, dan yana ganin fuskokinsu komai ya dawo masa sabo.
A hankali yace “baby mu je” yayi maganar yana rik’o Hannun Manu, kafin ya kalli Yassira yace mata “bismillah”
Daga haka ya ja hannun Manu…
kamar wata Yarinya haka ta juya ta bisa suka
nufi cikin parlourn wanda hakan yasa Kausar ta ji kamar ta kurma uban ihu!..dama sai da ta cewa Yasira “ba za ta zo ba!kar ta zo ta ga tashin hankali”
amman suka tilasta mata a cewarsu “ba za su bar Manu ta sake ta shak’i iska a cikin gidan dai dai da na kwana d’aya ba, sun dinga zuwa kenan daga yau har zuwa lokacin da zata koma mansion d’insu da zama su samu su fitar da ita daga rayuwarsu gaba d’aya.”

A kan one seater Manubiya ta zauna, dan taga suna da yawa sannan bata buk’atar zama kusa da d’aya daga cikinsu.

Tana jira taga shima ya zauna a d’ayar one seater d’in kawai taga ya nemi guri ya zauna a kusa da ita kamar
zai shige cikin jikinta dan kujerar ta yi musu kad’an sosai.

Ahankali su Kausar suka k’araso cikin parlourn duk suka nemi guri suka zazzauna, Kausar ta sunkuyar da kanta k’asa sosai kamar zai karye.

Tun d’azu Yash ya lura da yanayin Manubiya kuma bashi da tantama a zuwan su ne kafin ya k’arasa k’ofar akayi mata wani abun,
Wataƙilan Kausar ce ta harare ta ko ta fad’i wani abun….
Yana wannan tunanin ya ji sun fara gaida shi cike da mutuntawa, jimullah ya yi musu yace “lafiya”
Daganan ya koma ya fara kallonsu one by one yana jira ya ji sun gaida Manubiya amman sai ya ji shiru…

Minti d’aya ya ware musu,
yana cika kuwa ya gyara zama ya ce “ba za ku gaisa da matar gidan ba?”.

Ba iyaka su ba ita kanta Manubiya sai da ta ji wani iri,
dan ba ta yi tunanin zai iya ce musu hakan ba.

Ganin yadda ya tamke fuska kamar bai tab’a dariya bane
ya sanya Yusra cewa “Ina wuni”
Ta fad’i hakan ba tare da ta kalli Manubiyan ba, dakyar Yadira ma ta gaida ita.

Ahankali Manubiya tace
“Lafiya Alhamdulillah” kanta a k’asa ba tare da ta d’ago ba…
daga haka parlourn ya d’auki shiruuu kamar babu halittar mutane a ciki, kafin Yashjub ya mik’e tsaye kawai ya wuce sama bayan ya cewa Yassira “ta biyosa”.

Suna hawa, a nan parlourn saman ya ja burki ya tsaya ya juyo ya ce “Kun zo
Gidana! kuma na gode, amma ba zan d’auki iskanci ba!
dan haka na baku 3 minutes ku tattara ku tafi, duk lokacin da kuka san abunda ya kamata u guys are free to come back (za ku iya dawowa)”.

Kamar za ta fashe da kuka tace”Ya Yash ni ce zan gaida ita??” ta yi masa tambayar tana mai nuna kanta da yatsa.
Chapter 53 · 0% Book details