Sashe 144
Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ba k’aramin mamakin ganin Aslam M T ya yi ba (Abokinsa da suka yi karatu tare a Uk)
Abunda bai sani ba kuwa wajen taff!! cike yake da Abokansa dan Kausar diary d’insa ta tsinta a d’akin Mommy dan haka ta turawa kusan kaff friends d’insa da invitation na ranar sunan!!!
Yana fitowa Aslam ya yi murmushi yana kallonsa ya ce ”Yash, ya akayi ka yi aure?”
D’an guntun murmushin da ya fi kuka ciwo Yashjub ya yi, kafin ya d’aura kwayar idanunsa a kan matar da ke gefen Aslam d’in yana rik’e da hannunta yace”kai ya akayi ka yi auren?!”
Duk dariya suka yi har ita Hudan..dai-dai nan wasu friends d’insu su biyu suma suka k’araso wajen, d’ayan yana cewa “da ikon Allah Yash da Aslam sun rigani yin aure gaskiya ku nema mini mata”
Dariya d’ayan ya yi kafin yace”ai Yash matansa har biyu amaryar ce ma ta haihu!!”
Ai kuwa nan suka tusa shi a gaba da shaƙiyanci har Aslam wanda duk suka yi mamakin magana da walwalar sa dan hakan sam ba d’abiarsa bace ba kowa ya shaida…sun d’an jima a wajen suna ta tsokanar Yash, kafin suka yi masa murna suka nufi cikin hall d’in gaba d’ayansu..
Shi dai Yash bai so shiga ba sam, amma haka nan suka tilasta masa, gashi ba zai yiu ya yi musu bayani ba, ga tashin hankalin da yake a ciki ! shiyasa ya ji kamar ya d’aga Hannu ya d’aura a ka ya yi ta kurma uban ihu….
Sai da ya shiga cikin ma tukunna ya had’u da ragowar friends d’insa, hakanan aka had’u aka yi ta murna kowa yana cewa Yash ya kyauta da ya had’a musu wannan reunion d’in dan sun dad’e basu had’u ba.
…
Hannu bibbiyu su Mommy suka amshi Manubiya kamar za su goyata, daga su har Kausar d’in…ita dai Yassira binsu take yi da ido amma wallahi tsaf sai ta tona musu asiri saboda ta gaji gashi zargin Mommyn ma ita takeyi da rufe musu Baki dan kwata kwata ta gagara yin maganar Ya’isha a kowa.
Bayan sun shiga ne Yash ya nuna musu Manu, wadda ke zaune a chan gefe yace musu “ga wife d’insa chan!”
Huda dama she’s uncomfortable a tsakaninsu shiyasa ta cewa Aslam ‘bari ta je wajenta….’
Mommy d’ayan Abokin nasa ya hango, dan haka suka je suka gaida ita suka dawo suka ci gaba da tsokanar Yash wanda shi ya k’i yarda ko kallonta ma ya yi….hakanan itama Kausar ya k’i amincewa su je wajenta ko jaririn ma ya k’i basu fuskar su d’auka saboda shi har yau bai ko kalli fuskar Yaron ba, hud’uba ma Junior ne ya yi masa…su Daddy kuma basuce komai ba, har yanzu!
wanda hakan ya sake fusata Kausar, ta san duk dan Manubiya ne hakan take faruwa da ita, shiyasa da ta tuna a yau zata kawo k’arshenta sai kawai ta basar ta d’an ji sanyi a cikin ranta.
Manubiya tana zaune Huda ta zo ta zaune a kusa da ita, suka gaisa tace mata”sunanta Huda Matar Abokin Mijinta Aslam”
Itama Manu ta ce mata sunanta Manubiya, daga nan suka sake gaisawa suka zauna tare suna kallon masu rawar k’oroson da aka d’auko suke ta chasewa…
Ita dai Huda har ga Allah kwata kwata Kausar ba ta yi mata ba..ta wani zauna a kan kujerar alfarmar ta had’e rai kana ganinta ka san bata da mutunci, gashi ita da Manubiyan sam babu had’i! shiyasa take ta tunanin dalilin da yasanya Yash ya auri Kausar bayan Allah ya basa Manu a matsayin mata……
Suna zaune aka kira Hudan a waya, akwai kid’a sosai ta san ba za ta ji ba, shiyasa ta mik’e ta cewa Manubiya ‘bari ta amsa call ta dawo’ daga haka ta fita……ba ta yi mintuna uku da fitan ba ta dawo, ta inda suka shigo kusan a tare ita da Kausar wadda ta shigo ita kuma ta k’ofar kusa da wajen zamanta…tun kafin Hudan ta fita ta ga Kausar d’in ta mik’e ta fita, kuma bata ga lokacin da ta fita da jaririn a Hannunta ba amma tabbas da ta ganta a waje tare da Yaron ta ganta! ita da wata maid a wani dogon lungu! inda ita kuma Hudan ta je ne domin ta amsa waya a lungun…bata ma iya yin wayar a wajen ba ta chanja guri, saboda duk wanda ya gansu tashi ɗaya zai fahimci basu da gaskiya! kuma ba sa so a gansu a wajen ba sa so a ga abunda su ke yi, sannan tabbas indai har ba gizo idanunta suka yi mata ba sannan abunda ta gani dai dai ne to kamar a buhu fa ta ga suna shirin saka Yaron!
Noo it can’t be! Ba zai you ba!
Dan babu uwar da zata saka jaririn d’anta a cikin buhu! Gaskiya babu ita!
Amma kuma what are they up to?me su ke ƙullawa??”
Hudan ta ƙarashe saƙe saƙen nata cikin yiwa kanta tambayar, kanta yana sake d’aurewa…..
Ita kam Manu al’amarin Yash, damuwa, alhini da kuma halin da take a ciki ne suka sanyata a gaba!
Ta ma kasa magana, ga kuma ciwon cikin period d’in da take yi, sannan gashi ta ji kamar har ta fara b’ata jikinta tsabar yadda pad d’in jikinta ya jik’e!
Ba ta k’aunar chanjin pad a unguwa Idan ta fita, amma ya zame mata dole!
Allah ya so ta dama ta taho da pad d’inta, dan haka a gaban idanun Huda ta bud’e jakarta ta d’auka bak’ar ledar mai zip da ta sako pad d’in a ciki, ta ɗauka ta mayar ta rufe tukunna ta bata tace “ta rik’e mata jakar dan Allah, bari ta je yanzu za ta dawo….”
Ba ta dad’e da fita ba itama ta dawo…tana zama baba ya kirata suka yi magana, sai da ta kashe tukunna ta cewa Huda “jibi sadakar arba’in d’in Mahaifiyarta”
Sosai Huda ta tausaya mata, nan ta yi mata gaisuwa tanata bata Baki…
Kwatsam y’an sanda da sojoji tare da masu gadin event centre d’in suka danno kai cikin hall d’in gadan-gadan wanda hakan ya tada hankalin kowa matuk’a…gasu kuma rik’e da jaririn da ake sunansa wanda jama’ar wajen kaff basu ga lokacin da aka fita da shi ba a tunannin kowa Yaron yana chan a cikin gadonsa ne.
Mik’ewa tsaye suma su Manu suka yi, ita da Huda, dan mutane sun fara hayaniya da guje-guje kowa ya nufi k’ofa…
Da gudu Kausar ta je ta karb’e Jaririn daga Hannunsu ta fashe da wani irin kuka…
babban sojan da aka zo da shi ne ya d’auki mike ya yi harbi sama yace kowa ya zauna, wanda hakan ne ya nutsar da mutanen wajen…maid d’in da suka kama da Yaron ya saka aka kawo masa gaban hall d’in itama..dalla dalla yayi musu bayani akan cewa”satar sark’a aka yi wa hajiyarsu (matar da suke gadin ta), to kuma suna shirin shigowa ne suka kama wannan maid d’in da jaririn zata fita da shi a buhu…tace musu sakata aka yi aka bata mak’udan kud’ade, dan haka kowa ya zauna za ta nuna wadda ta turota!!”
Ko da wasa sam Manubiya ba ta yi tunanin ita maid ɗin zata nuna ba…a cikin zuciyarta tanata alhinin rashin imani irin na masu satar Yara….
Kawai tana k’ok’arin zama kwatsam tana d’agowa taga maid d’in ta yi pointing saitin ta!!
A rikice ta juya ta kalli gefe da gefenta amma babu kowa ita d’ince dai….Bata Ida fita daga shock ba mutumin ya nufota gadan-gadan har da ankwarsa……
Aslam ne kad’ai ya rage zuwa wannan lokacin a cikin Abokan Yash bai tafi ba, dan ragowar k’uluwa suka yi da attitude d’in Yash d’in kawai suka yi masa sallama da barka suka wuce abunsu, saboda ya k’i dariya ya k’i basu baby su gani kuma ya k’i tsayawa a yi hoto, sannan gaba d’ayansa a rikice yake kana ganinsa…shiyasa kawai suka basa sarari ta hanyar tafiya……..
Da sauri Aslam ya nufi sojojin da Manu, dan ya lura Yash bashi da niyyar yin komai!!!
Kawai ya tsaya ne ya k’ame….
Yana zuwa ya warce ankwar ya yar yacewa sojan ”Atleast ka yi bincike sosai mana, dan kawai ta fad’i abu shikenan sai mu hau kai mu yarda?ka san wacece wannan d’in da kake shirin arresting?”
Da gudu Kausar ta yo kan Manubiya tana kuka wai zata daketa, da kyar aka rik’eta aka hanata tab’ata, su Mommy suka janyeta aka fita da ita tana cewa”Allah ya isan Yaronta da ta saka mata a cikin buhu, wallahi Allah sai ya yi musu hisabi, muguwa!! azzaluma, saboda ita bata haihu ba shine zata kashe mata nata!!!”
Ita dai Manu uffan ba ta ce da su ba , dan tunda sojan nan ya nufota da ankwa har kawo yanzu kawai ta k’ame a wajen ta kasa motsi ta kasa cewa komai!!
babu wanda ya fi bata mamaki kamar Yashjub wanda kawai ya tsaya ya kafe su da idanuwa ya gagara cewa komai!!!
Shi kuwa Yash bak’in cikin Kausar ne ya ke jin kamar zai kashesa, bayan jama’ar da ta tattaro ta nunawa duniya d’an nasa ne shine hakan bai yi mata ba sai da ta had’a da wannan makircin!?
Ga kuma Mommy wadda wata zuciyar take ingizasa da kawai ya had’ata da sojoji tunda gasu gatanan, watak’il ya san idan ya yi hakan zai ji sauk’in azabtuwar da zuciyarsa takeyi!!…
Gashi shaid’an sai sake hasko
masa moment d’in Manu da Abbakar na d’azu yake yi a kwakwalwa da Idanunsa.
Tsabar bala’in da yake a ciki kasa ma motsi ya yi…ga dai Manu da Aslam yana kallo amma kwata kwata ya gaza tab’uka komai, ya kasa Isa garesu ko yatsarsa kasa d’agawa ya yi..