Sashe 149
Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Har wani irin huci kuwa Mommy take yi tsabar b’acin rai!!!
Enough is enough fa!! wallahi zata yi fito na fito da mutanen nan inyaso komai ta fanjama fanjam!!!
Ba ta kai ga bud’e bakinta ta yi magana ba suka ji knocking…
Ko da Mommy ta lek’a da
kyar ta iya gane Yassir!! dan sanye yake da kayan sanyi ga hula ta rufe masa kai, goshi da kunnuwa sannan ya sanya bak’in gilas…
da sauri ta sa Hannu ta bud’e masa ya shigo….
Wani Irin sanyi Yassir ya ji a ransa sakamokon idanu biyu da ya yi
da Kausar…saboda dama zuwa ya yi akan ya d’auki Yusra su je ta je ta fito
masa da Kausar ɗin saboda shi an hana masu gadi barinsa ya shiga gidan sannan yana ta kiran wayarta ba ta d’auka.
Mommy tana shirin yin magana ya sa Hannu ya rik’o hannun Kausar yace mata “Mommy d’an bamu mintina goma za mu je mu dawo”
“To” kawai ta ce masa, ta bisa da kallo tana jin wani irin yanayi….
Har ya juya zai fita, sai kuma kawai ya dawo ya sa Hannu ya rungume Mommyn sosai a jikinsa tukunna ya cikata, ya ja Kausar suka fice suka bar Mommy a nan tsaye kamar gunki.
Sosai k’irjin Kausar yake dukan uku uku, dan a yadda ta shirya komai ta tsara komai bai kamata ace ta ga Yassir free har yanzu ba!!!
A ranta tace
“Ko dai ya fahimci abunda na yi ne?”
dan kayan sanyi ne a jikinsa ga bak’in glass amma she can tell’ransa a masifar b’ace yake’!.
Sai da ya zaunar da ita a seat ɗin gaba na motar, tukunna ya zagaya ya shiga ya zauna ya kunna motar ya saka lock ya bata wuta!!!!
..
Wani irin uban gudu yake tsulawa, wanda tun daga nan Kausar ta fara dana sanin biyosan da ta yi….gashi tace masa”Yassir”
Daga fitowarsu zuwa yanzu ya fi sau talatin amma ko kallonta bai yi ba!
Sai da ta ga sun d’auki hanyar barin Kano tukunna ta fashe da kuka, cikin kukan tace”Yassir baka da hankali ne?ina zaka kaini??”
Ba tare da ya kalleta yace
“Zuwa ga mutuwarki!!”
Sosai ta firgita, gashi ta fara hango wani mahaukacin k’aton rami kuma shi ta ga Yassir ɗin ya durfafa, dan haka jikinta yana wani irin karkarwa ta sa Hannu ta zare key d’in, da sauri shi kuma ya taka burki kafin ta Ida cirewa….
Cikin kuka sosai tace”Baka da hankali ne?”
Sai kuma ta juya ta fara k’ok’arin bud’e k’ofa domin ta samu ta fita amma inna sam sai ta gagara….
Komawa ya yi kawai ya kwanta a jikin seat d’in da yake a kai, har ta k’araci bige bigen ta…ganin bafa za ta iya escaping bane ya sanya ta juyo garesa ta fara yi masa magiya…
Ahankali ya juya ya fuskanceta sannan ya Zuba mata ido ta cikin glass d’in, ya ɗan jima a hakan kafin ya furzar da huci yace
“Kausar, su grenade sun tura mini duk wasu chat d’inki da su, saboda suna so in san who is behind it all…..
kamar yadda kika so, an saki videos d’ina a wajen hukuma, yanzu haka nemana ake yi dead or alive(a mace ko a raye)…
sannan satin nan da ya shige! A gidan Abokina, muka yi raping wata y’ar minista to death! wanda mu kanmu bamuyi tunanin fyaɗen zai kaita har ga mutuwa ba! Shiyasa da muka ga ta mutu sai muka b’oye gawar, muka saka ta a fridge…
kwatsam! kuma yau da aka zo arresting d’ina sai aka ga gawar!!.
Ba su samu sun kama ni ba! shi kuma Abokin nawa ba ya nan…
Da kyar da mugun kyar na samu na iya guduwa, amma kuma sai da na gudu d’in tukunna na ga guduwar tawa ma ai ba ta da wani amfani tunda na san dole sai an nemo ni, kuma hukuncina kisa ne!!!
Bani da mai bani shelter yanzu kam..saboda Abokina da yake bani hatta abinci da kayan sakawa da motar hawa shima ta kansa yake yi kuma laifukana sun fi k’arfinsa!
bani da gatan da wani zai tsaya mini ko ya kare ni, ko kuma ya taimaka mini in gudu….”
Kin yi betrayin d’ina Kausar kin ci amanata, kin tarwatsa mini trust, sannan kin tarwatsa duk wani hope ɗin da ya taallaƙa sannan ya ƙunshi burukana!!…
Idan wani yace mini zaki bada kud’i sabida a kamani a kashe ni Wallahi Kausar tsaf zan kashe mutumin saboda abune wanda na yarda sannan na tabbatr ba za ki yi ba! amma kwararan shaidun da na gani su suka tabbatar mini da tabbas kin ci amanartawa kin yi betraying d’ina sannan a lokaci guda na fahimci kuma na gane cewa ‘ashe yaudarata kike yi kina using d’ina tun usuli, kuma
ba nine zab’in ranki ba…..’
Amma dukda haka inaso ki san cewa da sanki na rayu kuma da son ki zan mutu kuma wallahi babu wanda zan barwa ke a doron k’asa…ni yanzu tawa ta riga ta k’are! da a kan a kamani a yi hanging d’ina ko a fille mini kai gara ni in kashe kaina da kaina!! amma Kausar kamar yadda na fad’a miki ‘ba zan barwa kowa ke ba! ke d’in tawa ce ni kad’ai! dan haka you are coming along with me, tare za mu mutu!!”
Wani irin zabura Kausar ta yi, ta sake fashewa da kuka, sannan ta manne a jikin marfin motar ta shiga magiya da basa hak’uri bil hakk’i da gaskiya……
Fincikota kawai ya yi, ya fara k’ok’arin k’arb’ar key d’in daga Hannunta, amma sai ta hana, dan haka ya sa k’arfi ya lankwasa hannun nata wanda hakan da ya yi ya janyo Hannun ya k’arya ya bada k’arar k’asss!!! Alokaci guda itama ta saki wata razananniyar k’ara!!!!
Key d’in kawai ya d’auka, a fili yace mata”ke da zaki mutu ma Kausar menene na ihu dan hannunki ya karye???”
Daga haka ya zura ya kunna ya bawa motar wuta ya nufi d’urmemen ramin da ke a gabansu da wani kalar mahaukacin gudu….
…
Kausar kira take”Yassir!! Yassir!!!Yasssir!!!!!”
Da masifar ƙarfi! Amma inaaa! sam bai saurareta ba, sai da suka kusan fad’awa cikin ramin tukunna ya juyo ya kalleta yace mata “I love you!” Daga haka ya take gudu da k’afarsa sosai! ya saki sitiyarin ya d’aga hannuwansu duka biyu sama yana kallonta yana murmushi ita kuma tana ihu tana kuka tun k’arfinta..a haka suka fad’a cikin ramin….
Sai da motar tasu ta yi galantoyi ta bubbugu sau wajen biyar tukunna ta Isa k’asa, tana fad’awa kuwa ta kama da wuta……..
•••••
in banda dukan uku uku babu abunda k’irjin kowannensu yake yi tsabar zullumi….da Ya Musbah suka fara had’uwa a bakin gate shi da Ya Nafi’u da Aisha waenda suma duk Gwaggo Suwaiba ce ta kirasu…Manubiya cikin zumud’i ta fara kokarin fita domin ta je ta sanar da su amma sai Yash yace mata ta tsaya tukunna surprises ne kar ta gayawa kowa…hakanan ta ja bakinta ya yi shiru tana jin farinciki kamar zai fasata…haka
Suka nufi ciki gaba d’ayansu.
Daddy a waje ya tsaya shi da Yashjub sai da Baba ya zo tukunna ya shigar da su parlourn bak’i, Yayinda su Ummi suka nufi ciki gaba d’ayansu….Hajiya mama ta na shiga sukayi ido biyu da Mama wanda hakan ya sanya duk su biyu suka k’ame a yadda suke kowacce ta kasa motsi.
Kuka Mama ta saka a take ta durkushe a wajen tana jin wani kalar nauyin Hajiya Mama yana lullub’eta…k’arasawa inda take Yahanasu ta yi tana zuwa ta durk’usa itama, cikin kuka Mama tace”sai da kika yi abunda na hanaki ko?”
Dai dai nan Daddy Yashjub da Baba suka shigo dan suna ce masa Yahanasu ce ta kawosu gashi gashi yace to su shiga cikin suga menene surprise d’in…….
A hankali Yahanasu ta girgiza kai tace”kamar yadda na gaya miki basuyi tunanin kinada rai ba, kuma Daddy bashi da wani burin da ya wuce ya had’u dake a halin yanzu..d’azun nan ya gama fad’in haka a gabana a gaban kowa shiyasa na kawo su…..”
Shi dai Daddy zuwa yanzu hatta tsokar datake a jikinsa karkarwa take yi…bai riga ya ga wadda Yahansu take magana da ita ba amma dukkan bayananta suna nuni ne da Khadijarsa ce……
Tashi d’aya numfashinsa ya d’auke jinsa ya d’auke a daidai lokacin da Hajiya Mama ta k’arasa ta mik’ar da ita tsaye tace”Khadija!!!”
Sai kuma ta rungumeta ta sa kuka…
Kallonsu Yashjub ya ke yi saboda saɓanin Yahansu shi tun yana Yaro da aka ce ta rasu bai sake sakata a idanunsa ba, shiyasa bai ganeta ba.. ammafa tashi ɗaya tunda ya ganta ya ji wata kalar k’auna da son matar suna shigar sa bana wasa ba….
Yana jin Hajiya Mama kuma tace”Khadija”, sai
ya tabbatar tabbas ita d’ince, dan haka ya taka izuwa gareta idanunsa suna zubda hawaye!
Yana zuwa wajen, Hajiya mama ta matsa, shi kuma ya tsaya a gaban Mama idanunsa suna fidda ruwan hawaye…duk yadda ya so ya yi magana sai ya ji ya kasa, dan haka kawai sai ya rungumeta ya fashe da wani irin kuka wanda hakan ya sanya gaba d’aya suma su Manubiya suka saka kuka…..
cikin k’ok’arin zaro shi daga jikinta take ɗan tapping bayansa alamun rarrashi tana mamakin kalar so da tausayinsa da take ji suna shigarta a take a lokacin sannan kuma da suka yi ido biyu ita da shi sai taga Yash d’in kamanninsa d’aya da ita…
Hajiya Mama ce ta share hawayenta tukunna ta ce ”ki rungumi d’anki Khadija!
d’an da makircin Mace ya sanya ba ki san ke ce mahaifiyarsa ba”
A rikice ta juya tana kallon Hajiya Mama! Wadda hakan ya sanya Hajiya maman
Jinjina mata kai sannan tace”tabbas! kece mahaifiyar Yashjub ta asali…
makirci! rashin tsoron Allah! da son zuciya ne suka sanya Larai da Khadija suka musanya miki shi da Yahanasu..amma yanzu komai ya zo k’arshe. ranakun kuka, bak’in ciki, k’umbiya-k’umbiya da munafurci duk sun k’are a zuri’ar Imam kura….”
gaba d’aya parlourn a tare sukace “inshaaAllah” kowa yana sheshek’ar kuka banda Mama da Daddy waenda suka yi mutuwar tsaye tun d’azu…