← Book details Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 106 OF 152

Sashe 106

Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ka kwantar da hankalinka, InshaaAllah Manubiya za ta fahimceka.
na ji dad’i matuk’a da ka ce ba za ka b’oye mata ba, saboda b’oye b’oye babu abunda yake janyowa sai b’arna, sannan mai gaskiya yana tare da Allah ba zai tab’a tab’ewa ba.!
InshaaAllah gobe da safen zan shirye in je in sameta,ka kwantar da hankalinka, Kausar za ta girbi abunda ta shuka Allah yana tare da kai…”
A hankali yace”inshaaAllah”
yana jin zuciyarsa tana wani irin tafarfasa…
Sai da ta sake kwantar masa da hankali tace”ya yi ta sallah da nafilfili, idan ya kasa bacci..
komai zai yi daidai inshaaAllah sannan idan ya samu hali gobe da safe ya kira Daddy saboda hankalinsa a mugun tashe yake…….”
Tukunna
Daga haka suka yi sallama, yana mai jin sassaucin abunda yake ji kafin su yi magana….
Tabbas Yahanasu tana daga cikin manya manyana kyautar da Ubangiji ya sako cikin rayuwarsa, tana tsaya masa akan komai, tana son farincikin sa sannan ta yarda da shi d’ari bisa d’ari!kalli yanzu ita bata ma da buƙatar ya yi mata bayanin kansa tashi d’aya ta san sharrin Kausar ne….Addu’a ya fara yi a cikin ransa Allah Ubangiji ya sa Manubiya ma ta kawar da kishi, a samu Yahansu tana yi mata bayani itama ta aminta da shi ta yafe komai……..

A b’angaren Kausar kuwa har chan cikin dare ba ta farfad’o ba.
Yasmeen ta yi mata duk abunda ya kamata, ta yi dressing mata ciwukan fuskarta amma duk wanda ya ganta a wannan lokacin in ba cikakken sani ya yi mata ba tou ba lalle ya shaidata ba, dan fuskarta ta kumbura ta yi sutu-sutu ga ciwuka ta koina kamar ba ita ba.

In banda zubar hawaye babu abunda Mommy take yi…da kyar su Yasira suka lallab’ata aka bar Kausar a gida
dan Yasmeen tace musu”she’s fine, kuma idan aka kaita asibiti a haka case ne sannan in akayi bincike aka gano to Yashjub zai iya shiga matsala.”
Dakyar Mommy ta yadda
amma da cewa ta yi “a kaita asibitin a haka! Inyaso ya shiga matsalar shi ya sani, ita ba damuwar ta bace ba.”
Dan ba kad’an ba ta ji mugun mugun zafin halin da Kausar d’in ta ke ciki, ba kad’an ba
dukda ta san wataƙil dagaske Yash d’in yake gadar zare Kausar ta haɗa masa har ya kai ga kwanciya da ita amma sam ita ba wannan ne a gabanta ba! Bata ga dalilin da zai sanya ya illata mata Yarinya haka nan ba, wannan ai rashin imani ne!Yarinya y’ar amana!yanzu inda za a tashi uwarta a nuna mata Kausar a sume hakanan da fuskarta a haka
ai batasan da wanne ido zata kalletaba ranar gobe k’iyama.

Da Mommy da Yassir sun fi kowa tashin hankali a cikin d’akin, sai Yadira wadda yanayin Kausar d’in ya fara bata tsoro itama ta fashe da kuka junior yake ta faman rarrashinta.

Yassir har ya fara shirye-shiryen appointment dan yace “tana bud’e ido za su bar k’asar!”
Saboda tabbas yadda kumatunta da gefen idanunta suka fashe ya san sai an yi wani abun a wajen…dukda ba shi da enough kud’i amma zai
ranta a wajen Abokansa, domin a samu a
je a yi mata aiki kafin ya samu ta warke tukunna ya dawo ta kan Yash dan bai ma san ta Ina zai fara ba!
Tabbas ya bashi mamaki dan sam bai yi tunanin zai
Illata masa Kausar har haka ba…dukda ya san ƙarshen yash ɗin ya zo kenan! dan yanzu Manubiya da Daddy za su juya masa baya saboda ya gama shiryawa da kansa zai tura mata message ya gaya mata komai!amma dole Yashjub ya fuskanci hukuncin abunda ya yi wa Kausar wallahi,dole!…

Ummi ce kawai babu a d’akin sai Daddy amma kaff gaba d’ayansu suna d’akin.
Junior kawai kallon Yassir yake yi…a yadda ya d’aga hankalinsa tabbas ya tonawa kansa asiri ne a idanun Junior, saboda bai kamata ace ba ya fushi da Kausar a yanzu ba, bayan abunda idanunsa suka gane masa awannin da suka shuɗe.

Suna tsattsaye wasun su a zazzaune a kanta, ta d’an fara motsi ,kafin a hankali ta dawo cikin haiyyacin ta!
Sai dai ba ta bud’e ido ba…
Ta san ta daku dan fuskarta in ba da kyar ba sai ta had’a da plastic surgery
amman kuma ba ta jin akwai ranar da ta tab’a tsintar kanta cikin tsananin farin ciki Irin wagga rana!…dan ta riga ta san nan da 10 days inshaaAllah burin ta zai cika
ko da balai ko ta wanne Hali!
Batajin alamun ciwo ko wani abun a mararta kuma dama ta san Yashjub bai sameta a wajen ba dan haka tana da yak’inin cikin ta yana nan daram!. Yo ai ko ya fita sai ta sake yin wani ta lik’awa Yash!yadda aka kamasu d’innan shine mafi girman abunda za ta riƙa ta yi amfani da shi a matsayin makaminta…
Ta ji dad’i matuk’a gameda yadda plan d’insu ya tafi daidai babu targard’a.
Sannan bata wani damu da Manubiya ba, dan ba Manubiya ba ko auren irinta uku ne da Yash wuyarta ta auresa Wallahi sai ta yi waje da ita!.

Mommy dake daff da kanta ce ta d’an matso tace “Kausar”.
Ahankali ta d’an fara k’ok’arin bud’e idanunta…
Duk matsowa sukayi sai da ta d’an bud’e idon guda d’aya saboda d’ayan ba zai bud’u ba!
Tukunna gaba d’ayansu suka ce
“Alhamdulillah”.

Da sauri Yassir ya je ta wajen kanta ya d’ago kanta ya d’aura a kan cinyarsa
Yace “Yasmeen d’an sake duba ta!idan babu emergency
Inaga yanzu za mu fara shirin wucewa kawai!na san dole flight d’inmu ta Abuja zai tashi”
sam bai damu da yadda fuskarta ta kumbura kamannin ta suka sauya ba, shi dai kawai ya san Kausar d’insa ce, dan haka yanason ta a ko wanne irin yanayi.

Ajiyar zuciya Munirat ta sauk’e tanajin yadda zuciyarta take tafarfasa..a hankali
tace “Allah ya k’ara sauk’i”
Daga haka ta juya ta fita da sauri.

Ba wanda ma ya san ta fita ko ya jita dan tun d’azun ma ba wanda ya kula ta babu wanda
ya damu da existence d’inta a cikin d’akin.

A b’angaren Munirat d’in itama ba wajen su ta zo ba, dan in banda gaba harara da bak’ak’en maganganu babu abunda yake shiga tsakaninta da su Kausar d’in…Yassir ta biyo lokacin da taga sun kinkimo Kausar an kaita d’akinta ya fito ya fad’a d’akinsa shine ta tsaya akan idan ya fito su yi magana, amma ko da ya fito sai ya d’auke kai kawai ya afka side d’in Kausar ya wani tamke fuska dan karma ta kula sa..itan ma ta yi alk’awarin fita daga harkarsa kwanakin baya amma babu yadda ta iya ne saboda yanzu haka maganar da take so su yi d’in tanada matuƙar mahimmanci shiysa ta tsaya ta yi ta jiran fitowarsa, jin shiru shine itama ta shiga side d’in Kausar d’in….
A yadda taga yake d’innan ta san ba zai saurareta ba shine ta hak’ura ta tsara akan zata nemo numbersa kawai ta tura masa message tunda ta san zai gani….
Sarai ya lura da ita!tana fita ya yi tsaki ya ci gaba da dudduba Kausar yana tambayarta Ina ne yake yi mata ciwo…

Ba abunda ya fi d’aurewa su Mommy Kai kamar yadda sam Yassir bai wani damu ko ya nuna jin haushi a kan abunda ya faru tsakanin Kausar da Yash ba, shi ta lafiyar ta ma yake yi..
Ko da ya yi fushi ya fita d’azun suna zuwa suka tarar da shi a d’akin Kausar d’in yana safa da marwa…sun san dole zai tausaya mata amma
kuma sam babu alamun kishi ko wani jin haushi a tare da shi,
ko irin kishin da ya nuna a d’akin Yashjub sam ba su ga alamarshi a tare da shi yanzun ba…dukda tace masa dole Yashjub ya yi mata amma ya kamata ya ci gaba da jin haushi ko da d’an k’ank’ani ne, kamar yadda ya nuna a wajen dinner ɗazu da ta tafi side d’in Yash d’in da k’afarta.

Gyaran murya Mommy ta yi kafin tace”Yassir ka bar batun tafiya tukunna, yanzu a ji da abunda ya faru..indai ba so kake Daddynku ya fusata da kai ba, to ka ja bakinka ka yi shiru ka koma gefe tun kafin a huce a kanka.”
Zai yi magana Junior yace”kana fara batun fita da ita waje ma na san tsaf zai saka question mark akan yadda sam ba ka yi kishin komai ba!”
Ya fad’i hakan idanunwansa cikin na Yassir wanda ya juyo ya zuba masa nashi shima….lumshe idonta guda d’aya Kausar ta yi dama so take ta yiwa Yassir sign ya gane ya dena abubuwan da yake yi ɗin tun kafin ya tona musu asiri…Aikuwa gashi har an fara magana…
Shima Yassir d’in sai yanzu ya d’au haske dan haka ya ce “okay Mommy”kawai..daga haka ya mik’e, sai da ya yiwa junior wani kallo tukunna ya sa kai ya fice saboda ya ji haushi da mamakin yadda d’an uwa kuma Abokin nasa ya so kunce masa zani a kasuwa! Ya san Junior ya sanshi ciki da waje, duk abunda ya yi yana ganewa, ya san wannan d’inma ya gano sa tunda gashi har yana shirin yi masa b’aramb’atama a bainar Nasi, amma ba komai za su had’u ne, zai yi maganin sa dan ya lura Junior ɗin ya fahimci komai kuma ya san yadda yake ji da yashjub, dan haka dole ya rufe masa baki da wurwuri tun kafin ya janyo musu ruwa.

Washegari da sassafe Yahanasu ta tashi ta shirya, tana shirin tana fargaba…ba dan Yash ya zab’eta ne kuma ta ji tausayinsa jiya ba wallahi da ba ta ga dalilin da zai sanya ta zamo itace wadda za ta gayawa Manubiya wanna mummunan al’amari ba.

Ummi ce ta yi breakfast, suka shirya ita da Yahanasu suka nufi asibitin
, akan ‘za su chanji Hajiya Mama da Siyama…’

A d’akin suka tarar da Yashjub ga mamakinsu…lokacin Najeeb har ya je ya d’auki Siyama da Hajiya Mama ya tafi zai maida su gida.
Chapter 106 · 0% Book details