← Book details Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 105 OF 152

Sashe 105

Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ganin ta fara ihu kuma ta k’i mutuwa ne yasanya kawai ya rarumo pillow ya danna mata..Ba dan su Daddy sun shigo da wuri ba da tuni Kausar ta bak’onci lahira.

Da farko duk yadda Daddy ya so ya janyesa su samu su ture pillow d’in
kasawa sukayi daga shi har Mommy, saboda Yash gaba d’aya k’arfinsa ya saka ya danne pillow d’in, bashi da wani burin da ya wuce ya ga ta daina motsi!
Dan haka Daddy ya daddage ya kifa masa wani rikitaccen mari wanda ya taimaka aka samu Yash ya d’an dawo cikin haiyyacinsa, tukunna da sauri Daddy ya turesa Mommy ta d’auke pillow d’in ta yi sauri ta rufawa Kausar blanket

Ganin Yash d’in yana k’ok’arin sake yin kan Kausar d’in ne yasa Daddy ya rik’esa ya
tsayar da shi ya daka masa tsawa yace”one more hit! Yash, ko sau ɗaya tak ne idan ka ƙara bugunta to za ta mutu ne,
kuma ka yarda da ni idan nace maka ‘mutuwartata za ta addabeka ne daga nan har ƙarshen rayuwarka!’…
muddin ka kasheta Its going to hunt you for the rest of your life.
Dan haka ka nutsu!!!!”
Ya fad’i hakan cikin tsawa sannan ya girgiza sa.”

Sai a sannan Yash ya d’an kalli Daddy, jikinsa yana wani irin karkarwa fuskarsa da idanunsa sun yi jaaa….
Kawai kuma tashi d’aya sai ya fashe da kuka ya rungume Daddy….

Babu abunda ya fi d’agawa Mommy hankali kamar yadda gaba d’aya pillown ya b’aci da jini kacha kacha!
Ga kausar d’in ta ma k’i motsi fuskarta kacha-kacha! Koina jini.
Dan haka a gigice ta juyo kan Yash za ta kai masa duka, Daddy ya yi saurin juyawa ya rik’eta.

Tsakiyarsu Yash ya shiga!
ransa a mugun b’ace idanunsa suna zubar da hawaye ya fara magana cikin b’acin rai”Ka barta ta dake ni Daddy!ai ba yau ta fara taking sides ba.
Ki kasheni kawai idan ma za ki iya, tunda abunda ya rage kenan!
Kinsan me ta yi?”bai jira jin amsarta ba yace”Tricking d’ina ta yi na aikata Zina! da aurena!
Amman na san dukda haka still bayanta za ki bi….
Dan haka ki dakeni!
Ki kasheni!..
Gara ma ki kashenin
Dan muddin ba ta riga ta mutu yanzun ba
Tou idona idonta kasheta zan yi sai dai duk abunda zai faru ya faru!
So inma kasheni za ki yi gara ki kasheni  tun kafin in kashe y’ar da kike fifitawa sama da mu ƴqƴan da kika Haifa a cikin cikinki
Musamman ma ‘Ni’.…”

Dakyar Mommy ta samu ta yi lissafi mai kyau ta danne zuciyarta…a gigice ta juya ta fita kiran Yasmeen…

BULAMA ✍️
0903 441 3252
*MANNUBIYA*
*Book 2*
*page 35*

Kallonsa kawai Daddy yake yi, yana nazartarsa. Tashi d’aya ya fahimci tabbas dagaske gadar zare Kausar ta haɗa masa…shakka babu tricking ɗin nasa ta yi.
tunda
ya haifi Yashjub bai tab’a ganin tsoro firgici da tsananin
tashin hankali k’arara a tare dashi kamar na yau ba.

Ahankali ya rik’e sa yace”Mu je sama ka huta,ka kwantar da hankalinka ka ji ko?ka sasssauta zuciyarka, ka bi komai a sannu”
..
Shiruu ya yi yak’i motsi,
dan baima san me Daddyn yake cewa ba, sam ba ya fahimtarsa tsabar tashin hankali…

“Mu je Yash”
Daddy ya sake cewa.
Sai a lokacin tukunna ya bar kallon k’ofar da Mommy ta bi ta fita ta fice daga d’akin…runtse idanunsa ya yi..ya d’an jima a hakan, kafin ya bud’e, bai yarda ya kalli Daddy ba ya fice
da sauri….

Yana fita ya ga makullin motarsa a inda ya yar d’azun, tashi d’aya ya sa hannu ya d’auka tare da wayarsa kawai ya fice gaba d’aya, ko bi ta kan Daddy bai sake yi ba.
Yana fita ya shige motarsa, alokaci guda ya kunna ya fice daga gidan…..
…
Test din HIV ya fara zuwa akayi masa, dukda ya san dole ya sake komawa a yi wani nan sati shidda amma dole ya haɗa aka yi masa har da shi a cikin jerin tesatesan da ya lissafa yace duk a yi masa su bayan nahiv ɗin.
cikon ikon Allah komai ya fito negative, still sai da aka yi masa allurai ya sha magunguna tukunna ya bar asibitin.

Direct Bristol ya wuce, yana zuwa ya kama d’aki, dan ba ma ya so ya je inda wani zai nemo shi…….Idan ya rufe idanunsa fuskar Manubiya kawai yake gani…”innalilla wa inna ilaihirrajiun” yake ta ambata a cikin ransa…idan ya b’oye mata ya ha’inceta, amma kuma bai san ta Ina zai iya kallonta ya gaya mata wannan mummunan al’amari ba, ya san tabbas wannan shine al’amari mafi ƙololuwar tashin hankali da zuciya da kanta za su iya ɗauka kuma su jura…
Kaɗan ya rage bai mutu ba! A lokacin da Abbakar ya shirga masa zantukan nan, ba dan su Najeeb sun wayar masa da kai ba ya san tsaf ciwon zuciya zai iya yin ajalinsa shiyasa ya ma kasa iya hasaso halin da Manubiya za ta shiga idan ya gaya mata abunda ya faru tsakaninsa da Kausar, bayaga hakan ma bai ma san ta Ina zai fara had’a ido da ita ba, balle ya yi mata bayani, wani irin tsananin tausayinta da kunyarta kawai yake ji….
Wayarsa ce ta d’auki k’ara, a karo na hud’u. dan haka ya d’ago da niyyar kashe wayar gaba d’aya amma sai yaga ‘Honey’ a kan screen d’in yana yawo….
Wasu zafafan hawaye ne suka shiga bin fuskarsa, hannunsa ya fara karkarwa, k’irjinsa ya shiga dukan uku uku….
Har ta katse bai d’auka ba, haka ta sake kira ta katse bai ɗauka ɗin ba, daga k’arshe ta turo masa message”Baby Ina wuni, hope you are fine..d’azu ka kira Ina barci, yanzu na farka..ba ka d’aukan wayar!ina fatan kana lafiya, i need you, i want to see you (ina buƙatarka, ina so in ganka) plss.”
Yana gama karantawa ya yi jifa da wayar ya mik’e ya fad’a toilet, ya sakarwa kansa ruwan sanyi yana wani Irin huci, kansa yana juyawa fiye da misali…

Ya fi awa d’aya a cikin band’akin, da kyar ya yi wanka ya yi alwallah ya fito yana istighfari….jallabiyarsa ta riga ta jike tana band’akin shiyasa sai da ya jira ya yi order aka kawo masa, tukunna ya mik’e ya tada ik’ama bayan ya shirya…yana ta istighfari dan bai tashi tuna bai yi sallar Magrib da isha ba sai da ya gama wanka ya fara alwallah, saboda bai tab’a kaiwa war haka bai yi ba, shiyasa ya manta…..

Yana idar da sallar ya tashi ya fara jero nafilfili,ko da ya gama ma karatun Al’kur’ani ya zauna yayi, sai wajajen 1 na dare tukunna ya d’an samu zuciyarsa ta fara yin sanyi…

Wayarsa ya d’auka…
Ya danna dial a number Manu ya kashe, ya fi sau shidda!!
kafin daga baya kawai ya rufe ido ya danna, ya runtse idanuwansa, zuciyarsa tana wani kalar mahaukacin bugawa.

“Assalam alaikom”
Ya jiyo muryarta mai dad’in sauraro da kwantar da hankali.

A hankali ya lumshe idanunsa, hawaye suka shiga zirara, kafin ya ce”ameen wa alaiki assalam,ba ki yi barci ba har yanzu?”
A hankali

Cikin firgice tace”Ya Yash kaima kuka kake yi? har yanzu?.”
Bata jira ya bata amsa ba ta ɗaura da cewa
“killace kanka da k’aurace mini ba shine zai yi mana maganin damuwar mu ba.
Na kasa nutsuwa, hankalina a tashe! ban yi tunanin za ka gujemini a irin wannan lokacin da nake matuk’ar buk’atarka ba Ya Yash.”

Kuka sosai ta ji ya saka, kafin ya kashe wayar,yana kashewa ya yi switch off d’inta gaba d’aya.
Ta kira sa ya fi sau ashirin amma switch off, dan haka hankalita ya sake tashi!ta fara wasu Irin hawaye masu zafi…

Ta shiga tashin hankali da firgici matuk’a a lokacin da aka ce cikin jikinta ya fita, amma dama ita 50%na damuwarta Yashjub ne…da farko ta d’auka fushi ya yi da ita bayan damuwar da yake a ciki, shiyasa ya k’i zuwa gareta, amma yanzu da suka yi waya tashi d’aya ta fahimci tsananin damuwa da tashin hankali ne suka sanya shi ya killace kansa ya k’i zuwa wajenta…ta san Yashjub yana sonta, yana son cikin jikinta amma ba ta yi tunanin abun zai kai ga haka don wanda ya basu ya amsa ba…..

Bayan ya gama waya da Manubiya da kamar awa d’aya da rabi lokacin ya san ta hak’ura ta daina gwada layukansa ya kunna d’ayar wayarsa ya kira Yahanasu, bai damu da dare ko kuma kar ya tasheta a barci ba haka nan ya yi ta kira yana sake kira har sai da ta d’auka cikin magagin bacci a d’an rikice tace”Assalam alaikom”
“Yash Ina ka tafi ne an je har gidanka ba ka nan, kuma ba ka d’aukar waya?”

“Yaha ki taimakeni ki yiwa Manubiya bayanin abunda ya faru, ba zan iya ba, ba kuma zan iya b’oye mata ba..sannan mun riga mun yiwa juna alk’awarin babu b’oye b’oye a tsakaninmu…kuma na san ko yaya mutum ya kai ga iya b’oye sirri dole sai an samu ta inda zai ɗan fita, idan ta ji a wani wajen za ta karaya sannan ba za ta sake yarda da ni ba…ki yi mata bayani ki
Ba ta hak’uri, ki fahimtar da ita a madadina, Ina son ganinta amma ba zan iya fuskantar ta ba kunya nake ji sanan a dame nake, kuma tsoro nake ji………”

A hankali Yaha ta share hawayenta tace”slow down Yash….!”
Kafin ta mik’e ta zauna tana mai kunna bedside lamp tace”maganar b’oye mata kam dama bai taso ba, dan na san ko da gangan sai an samu masu gaya mata!Tunda abu ne wanda kowa ya sani…
Chapter 105 · 0% Book details