Sashe 140
Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read
A rikice ta afka ta tura k’ofar ta mayar ta rufe, cikin tsananin tashin hankali tana ganin dishi-dishi tace masa “Mun wayi gari
babu Ya’isha, ka taimaka mini ka san yadda ka yi y’ata ta dawo!!.
Ina son y’ata, ita kad’ai ce ba ta tab’a yi mini jayayya ba wallahi!.
sannan in har su Yasira suka ganta haka to sun san ni ce!! sun san me ya faru! tunda a gabnsu aka fara maganar jiya, dan haka na san wallahi ba za su tab’a yafe mini ba!!! dan girman Allah ka yi wani abun….”
“Biyo ni”
Kawai yace, daga haka ya nufi cikin gidan….
Wajen Birin jiya suka je, kamar jiyan suna zuwa birin ya matsa musu shi kuma tsohon ya saka hannu ya d’aga dutsen ya turasa gefe!
tun kafin ya d’auko babyn robar ya kwab’e fuska ya ce “too ikon Allah, mai ya faru kenan?”
Da sauri Mommy ta matso tace”ya akayi?
mai ya faru?
Ba dai aikin ne ya lalace gaba d’aya ba dai ko??”
Ta yi masa tambayar a gigice
Girgiza kai yayi, ya sa Hannu ya d’auko Babyn robar yana kallo tukunna yace
“gaskiya kun yi kuskure, amma bansan ta Ina ba! Saboda yadda y’ar tsanar nan ta yi bak’i, kalli kinga fuskarta, “
Ya yi magaar yana nuna mata ƴar tsanar ta hanyar kai
Mata ita saitin fuskarta tukunna ya ɗaura da cewa “to hakan yana nuni ne da aiki ya ci kuma ya kama sannan yana kan yi, kuskuren ne ban fahimci ta ina kuka yi ba!
Saboda tunda har abun ya shafi Ya’isha tou tabbas akwai wani abu da kuka yi ba daidai ba.”
Sai kuma ya kalleta yace”ke fa??lafiya kike jin ki dai ko??”
Jinjina masa Kai ta yi da farko sai kuma tace”idanuwana dai suna ta yi mini dishi-dishi tun d’azu!!!!”
Jinjina kai ya yi, ya sauk’e ajiyar zuciya tukunna yace
“dama na yi zaton hakan a kema ɗin, idanunki ne kenan za su tab’u”
sai kuma ya mayar da gabaki d’aya hankalinsa gareta yace”idan kinaso za a iya karyawa, tunda kinga aiki dai gashi ya ci ya kama amma bai kammalu ba, dan inda ace ya kammalu to da ƴar tsanar za ta ƙone ne daga nan to shine ba za a taɓa iya karyawa ba. Dan haka yanzu muna da damar karyawa amma fa idan aka karya ɗin
Na farko
ba za a sake iya yiwa ita Manubiya irinshi ya kamata ba, sannan abu na biyu
babu tabbacin Ya’isha za ta tashi!”.
Kuka ta fashe dashi sannan tace”kamar ya zaka ce mini Ya’isha ba za ta tashi ba!!
idan fa Yarinyar nan ba ta tashi ba wallahi na san duk su Yasira sai sun fahimci komai, kuma ba za su tab’a yafe mini ba, k’arshentama su tona mini asiri…”
Cikin tarar numfashinta ya ce ”ai
dama sai da na gaya miki aikin yana buk’atar taka tsantsan, kuma yanada haɗari….”
Cikin yi mata nuni da babyn robar a karo na biyu, yace”dan ci kam aiki ya ci kuma kun ce hularta ce sannan ba a samu matsala ta ko ina ba dan haka tabbas ya ci kuma ya kama Manubiyan dan ga zahiri nan nima na gani….amma kuma halin da Ya’isha ta shiga yana nuni ne da aiki ya riga ya fara tab’arb’arewa kenan…..kuma a yanzu tunda har bai kammalu ba to zan san yadda zan yi, zan gwada in sha Allahu zamu iya warwaresa….wanda idan an warware ɗin ta you Ya’isha ta tashi ta you kuma ta tafi kenan har abada, amma tabbas Manubiya kam za ta tashi ita wannan a rubuce yake tunda ga ƴar tsanar nan har yanzu bata ƙone ba…..”
Cikin tarar numfashinsa tace”to mu bari mana sai an kaita (manubiya) inyaso sai mu warware a tare!”
Girgiza Kai yayi yace”sam ba haka abun yake ba..kuma ni yanzu mintuna uku ne ma
suka ragemini, suna cika za ki ga y’ar tsanar nan ta kama da wuta! (idan har ta kama da wuta ba a fara kwanceta ba to aiki ya riga ya ci kuma ya kammalu kenan..an gama komai baza a taɓa iya warwarewa ba)saboda daga nan abun ya fita daga hannuna kenan!!..
dan haka ki yanke hukunci da wurwuri, kin riga kin lalata komai da ke da y’arki, dan haka iyaka bayanin nan da na gama yi miki shine kawai taimakon da zan iya yi miki a halin yanzu….”
Shiruu ta yi kafin tace”idanuwan nawa da na fara ganin dishi dishi dasu a haka za su dauwwama?”
Shiruu ya d’anyi kafin yace”akwai taimakon da zan baki, tunda ke kinga abun da alamun shafarki ya yi kawai ba wai ya rikito gaba ɗaya a kanki kamar Ya’ishan ba ne, dan haka inshaaAllah in na yi miki maganin za a dace”
Cikin sake jeho masa wata tambayar tace”tashin Ya’isha k’ila wak’ala ne ko?”
Jinjina kai ya yi yace”Bari ki ji ba zan b’oye miki ba Ya’isha ba ma na jin tanada rai a halin yanzu, dan haka ba zan iya yin komai a kai ba, saboda kun damalmala komai ne, gashi kuma bamusan ma ta ina matsalar take ba taƙameme…ga dai aiki ya yi kuma yana ci wanda hakan yake nuni da ya kama har Manubiyan da aka yi wa tabbas…to shafar Ya’isha da aikin ya yi ne matsalar, shiyasa abun zai fi k’arfina!”
A hankali Mommy ta lumshe idanuwanta hawaye suka zubo cikin d’acin zuciya tace”ka bar shi kar ka karya!!!”
Ta ji tsananin zafin mutuwar Ya’isha tabbas, amma da ta tuna abunda ya ke faruwa da Manubiya a halin yanzu sai ta d’an ji sanyi, ko banza ta san kwalliya ta biya kud’in sabulu!!!!….
Ba ta dad’e da gama rufe bakinta ba Babyn robar ta kama da wuta, tana jin tsohon yana cewa
“Aiki ya kammalu kenan, yanzu kam ba zai yiu a taɓa iya warwarewa ba, sannan a halinda ake ciki shi kansa bai san ranar da numfashin Manubiya zai komo mata ba, aiki ba a hannunsa yake ba ba zai iya yin komai ba tunda sun riga sun damalmala masa komai!!”
Itadai Mommy ta ji sanyi a ranta, tunda ba a warware ba to ta san duk bala’i ko nan da shekara nawa ne Manubiya ba ta Isa ta fito ba!.
Da shi da ita suka yanke shawarar ‘gara su binne Ya’isha, maganar ta tsaya a iyaka su biyu kawai. dan idan wani ya sani tofa akwai matsala….
Inyaso
Mommyn sai ta cewa ƴan uwan Ƴa’ishan ta aike ta k’auye ne, kafin su kuma (ita da tsohon) su san abun yi.
Sannan shi kuma ya yi mata alƙawarin inshaaAllah kafin a nemo abunda za a ce ya samu Ya’ishan har a samu zancenta ya gushe, zai rufewa duk wani wanda zai d’aga mata hankali wajen bin diddigi da tambayar ‘Ina Ya’isha’ Baki.
Hakanan suka je wani k’ungurmi daji, ya hak’a rami! yana shirin d’auko Ya’isha ya sakata a ramin aka kirasa…..
Kiran mai matuk’ar mahimmanci ne, dan haka ya cewa mommy ‘ta yi masa hak’uri, dole
zai tafi, ita ta k’arasa sakata ta rufe ramin ta koma gida’.
hakanan ya wuce ya barta a wajen, jikinsa yana karkarwa dan babban mutum ne ya kirasa wanda ya san a k’allan a lalace yau sai ya samu sama da miliyan biyu…..
Tsoro da fargabar dajin gata tare da gawa ne suka sanya Mommy saka Ya’isha cikin ramin anyhow! ba tare da nutsuwa, tsari ko hankali ba…dan ta Ka ma ta fara zurata kuma ta tura gangar jikin akan kan nata wanda har sai da wuyan Ya’ishan ya yi ƙara, sannan ko gama rufewa ma ba ta yi ba, hakanan ta yi sauri ta bar wajen jikinta ya na karkarwa, tana kuka.
Bata wani jima da komawa gidan ba, su Yasira suka dawo…
Jikinsu daga ita har Yusra duk a sanyaye, haka dai suka gaisa Yasira tana mai bin Mommyn da wani irin kallo itama Yusran haka…
kafin chan Yasira ta d’an yi waige waige tace mata “Ina Ya’isha?”
hakanan
Mommy ta had’e fuska, tace musu”ta turata k’auye! tunda sun hana a tsayar da numfashi, to ta turata k’auye zata yo musu mai sauk’i…”
Shiruu Yasira ta yi kawai Tana kallonta…sam ba ta son ta zargi Mommy amma kuma duba da inda suka je sannan da abunda ta ji ta gani a jiya, ya sanya hankalinta ya kasa kwanciya ɗari bisa ɗari da Momyn tun lokacin da ta ji labarin rasuwar Inna…
Ta jima tana tunani kafin tace mata
“Ina fatan bakiyi komai ba Mommy”
cikin alhini ta d’aura da cewa”Mahaifiyar Manubiya ta rasu yau! ki shirye mu je, mu yi musu gaisuwa.”
Daga haka ta mik’e da niyyar kimtsawa ta fito inyaso sai su tafi.
Shiruu ta ga Mommyn ta yi, ta shiga mugun shock! kafin kawai ta ga ta mik’e tsaye…..
K’iri k’iri tashi ɗaya ta hau bori!!
Ta inda ta ke shiga ba ta nan ta ke fita ba! Ta nace akan
“ba zata je ba, sannan suma kuma ta hanasu zuwa ba za su je ba!!
Wai ai suma su Manubiyan jiya ba su zo mata gaisuwar Larai ba!”