Sashe 112
Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Shiruu duk aka yi itama Kausar d’in ba ta ce komai ba, kuma ba ta bar kallon Junior wanda shima itan yake kallo ba!
Da kyar Mommy ta rarrashi kanta ta danne zuciyarta tace”Hajiya mama ki yi h…”
Cikin tsananin b’acin rai da takaici tace “kin san Allah Khadija zan baki kyakkyawan mari wallahi tallahi!!wannan kissar taki ba ta samu guri a cikin kaina ba tun wuri ki daina, idan za ki fito mini a Khadijar ki to ki fito, idan kuma ba za ki fito ba wallahi kin ji na rantse kika sake tsomo mini Baki a cikin issues d’ina sai na make ki!,bak’ar ashana kawai.”
Mik’ewa Ya’isha ta yi kamar za ta tashi sama ta wuce sama ranta a mugun b’ace…cikin takaici Hajiya mama tace”an ce da Uwarta bak’ar ashana ta ji haushi bayan gaskiya aka fad’a tunda kalli attitude d’in da bak’ar ashanar ta koyar da ita,nni fa uwar ubanta ce amma kalli abunda ta yi mini…..”
Shiruu duk akayi kowa ya yi tsit dan haka Hajiya Mama ta juya ga Kausar tace”zaki gaida mutane ko na saka Junior ya koya miki ladabi yanzunnan?? Ke har kin isa ki bawa mutane wannan attitude d’in?
kin hana jamaa sukuni kin yi kane kane a gidan mutum amma dukda haka saboda ke d’in ba y’ar halak bace ba shine za ki fara wannan sabon halin?
A baki ci a baki sha Allah na tuba in ba dan mu d’in ba ai da sai dai ki shiga duniya inda kika fito…”
Cikin katseta sannan kamar irin kin isheni d’in nan ta juyo ta kalleta ido cikin ido tace”Hajiya Mama Ina wuni”
Da k’arfi…..
Mik’ewa tsaye Ummi ta yi Hajiya mama ma ta yunk’ura amma kafin su yi wani abun tuni Junior ya d’auke ta da mari!”
“Allah ya yi maka albarka imam!”
Hajiya mama ta fad’a kafin ta sake kallon Kausar tace”Shegiyar Yarinyar da ba ta san wa yayi mata gata ba!”.
Difff!!! Haka kowa yayi tsit.
Ajiyar zuciya Ummi ta sauk’e kafin ta ce”Hajiya Mama ki yi hak’uri, ki bar ta da halinta, ba ta chanchanci lokacinki ba”
Wani kallo Kausar ta watsawa Ummi wanda hakan yasa Ummin itama ta kafeta da ido kafin tace”
Ko za ki dakeni ne Kausar??
Shin kin chanchanci lokacin nata ne?”
Yassira ce ta matso tace”dakata Ummi ba ma son shishshigi,Allah mun gode maka kaff cikin mu babu wadda ta tab’a guduwa yawon karuwanci…wannan al’amarin famiy kaɗai ya shafa, dan haka ki ja bakinkki ki yi shiru ki bar Hajiya mama ita za mu iya d’aga mata k’afa….
Kausar is our sister, ba za mu zuba miki ido ki taka ta haka ba.”
Yasira ta kora mata warning ta na huci,kasancewar sun d’an samu saɓani da Kausar ba shi zai sa ta tsaya ta zuba ido a wulak’antata ba.
Wani wawan Mari Hajiya mama ta yarfawa Yassira cikin
fushi tace”na san uwarki bata baki tarbiyya ba amma ban yi tunanin kin zubar da wadda imam ya baki ba…”
Sai kuma ta juya ta kalli Ummi tace “Ai dama na sani wallahi muddin shegiyar y’ar nan tana cikin gidan nan tou babu batun tarbiyya….”
A hankali a hankali Kausar take shak’ar turaren hannunta ba tare da kowa ya lura ba amma kuma amai ya k’i zuwa..gashi tana gani kamar har taron ya kusan watsewa.
Dai dai nan Yassir wanda sauk’owarsa kenan ya k’araso wajen da hanzari ganinsu carko carko, ya kalli Yassira wadda har yanzu take dafe da k’unci tana kallon Hajiya mama yace
“Me ya faru?”
Cikin fushi tace”ka tambayeta!
Na tabbata ko mai zan ce maka cewa za ta yi ba dai dai bane ba,ka san a ko da yaushe itace mai gaskiya.”
Tana gama fad’in haka ta juya fuuu ta haye sama.
Kasa ma magana Hajiya mama ta yi tsabar mamaki da al’ajabi kawai
ta tsaya sake da Baki.
Sai kuma ta juya kan Kausar a fusace tace”Wallahi b’oyayyen Ubanki ma bai Isa shiga tsakani na nida jikokina ba!
Imam ja mini ita ka fitar a cikin gidan nan
It’s an order…”
Dasauri Yassir ya shiga tsakanin Imam da Kausar yace”Hold on!” Cikin fushi, kafin ya kalli Hajiya mama yace”Nobody is throwing nobody out!
(Babu wanda zai kori wani a cikin gidan nan).
Hajiya mama abunda kike yi fa ya yi yawa…tare kika ga mun taso da Kausar tun Yarinta har kawo yanzu, dan haka zai fiye miki idan ki ka bar ik’irarin korar ta a cikin gidan nan, dan za ki janyowa kanki matsala ne!”
Ya fad’i hakan yana me kafeta da manyan idanuwansa da suke nuna tabbacin gaskiyar maganar da ya gama fad’a.
Cikin tsananin fushi
Hajiya mama tace
“Ok!!!..bari in kira ubanka!
wanda na Haifa shi kuma ya haifeka, daga nan sai inga shi wa zai zab’a
Ni ko Kausar.
Dan yau ko ni ko ita a cikin gidan nan.”
Tana gama fad’in haka ta
Cewa Yahansu ‘ta bata wayarta.’
Cikin nustuwa Yahanasu ta d’auki wayar ta mik’a
mata, a ranta tana adduar ‘Allah Ubangiji ya sa a kori Kausar yau!’
Tun ranar da ta shiryawa Yash wannan tarkon ta gama cire duk wani hope na shiryuwa a kan Kausar.
Da wannan tunanin ta mik’awa Hajiya mana wayar tata, ita kuma
ta karb’a ta gyara zaman gilashin idanunta ta lalumo number Daddy ta danna call, sannan ta d’ago ta kallesu tace”Yassir da Yassira sun janyo mata yau, sai ta tafi.”
Dai dai nan Daddy ya amsa kiran cikin bada order tace”ka zo kai da d’an uwanka har da Yashjub duk Ina buk’atar ganinku a k’asa yanzu.”
Daga haka ta kashe wayar.
Tana kashewa su Yasmeen Yadira da Yusra suka matso suka yanyameta suna rarrashinta amman fur ta k’i sauraron kowa ta nace ta kafe Itafa Kausar yau sai ta bar gidan d’anta.
Gashi sai tujara take zubawa Kausar d’in harma da Mommy da Baba larai, shiyasa cikin fushi Kausar ta matso tace”na ji ya Isa haka zan fita zan tafi,tujarar ta Isa haka.”
Ta k’arashe maganar cikin tsawa!
Zaro ido Hajiya mama ta yi
batasan lokacin da ta yi kan Kausar ta kifa mata marin da ya sa ta tafi za ta fad’i ba
Da sauri cikin fushi Yassir ya yi kanta amma bai yi nasarar rik’eta ba dan sai da ta fad’i kuma fad’uwar ma ruf da ciki shiyasa tsabar takaici b’acin rai da firgicin ganin yadda Kausar d’in ta fad’i a kan cikinta bai san lokacin da ya d’aga
hannu zai kifawa Hajiya mama mari ba!.
Da mugun sauri Junior ya rik’e sa cikin tsananin b’acin rai yace”baka da hankali!!!
Seriously?
Marinta za ka yi?”
Dunk’ule hannu Yassir ya yi jajayen idanunsa
cikin na Hajiya mama
wadda ta shiga tsananin tashin hankali ba na wasa ba.
Da style Kausar ta sake saka hannunta a karo na biyar a kan Hancinta, ta shak’i turaren da tun d’azu yake ta taso mata da amai yak’i fitowa, aikuwa tashi d’aya wannan karon ya taho
gadan gadan ta shiga shek’awa ba na wasa ba, dan sai da ta zauna a wajen tsabar yadda ya taho da k’arfi.
Gaba d’ayan su kanta suka yi kowa hankali a tashe!
Har ta gama babu wanda ya iya cewa uffan!
A hankali Yassir ya durk’usa ya ce”taso mu je sama sannu”
K’asa k’asa yadda babu wanda ya Isa ya ji tace”Yassir ka daina haka mana,kar ka lalata komai.”
Shiruuu yayi,ya d’anyi nazari, kafin ya mik’e tsaye ya kalleta
ya kalli aman ya yi shiruuu kawai.
Ahankali Yassira ta matso tace
“Dama ba ki da lafiya??”
Ta yi mata tambayar tana yi
mata wani irin kallon k’urilla wanda duk sai yanzu suka lura da yadda Kausar d’in ta sake kod’ewa ta yi ɗauuuu!!.
Da kyar ta iya cewa”lafiya ta k’alau..haka kurum nima na ji aman ya taho mini!”
Wataƙila na ci wani abun
ne mara dad’i, shine ya b’ata mini ciki.”
“Eh kam tabbas…ya b’ata miki ciki indeed!”
Hajiya mama tace, kafin ta kalli Junior tace
“Hurry!maza d’auko kit d’inka ka zo yanzunnan.”
Sai kuma ta kalli Kausar tace”wallahi ba ki isa kwashe albarkar gidan d’ana a karo na biyu ba!”
Da hanzari Mommy ta matso a d’an rikice tace”Hajiya mama
kar ki damu!
Kince ta fita shikenan za ta fita ba sai su Daddy sun shiga an yi ta case ba.
InshaaAllah zan siya mata gida, zan san yadda zan yi da yardar Allah.
Muje Kausar.”
Ta fad’i hakan tana mai kama hannun Kausar.
“Ka ji makira ko!!!
Wato kin riga kin san da batun cikin shiyasa za ki janyeta ku tafi ko?
Tou na chanja shawara! Za ta tafi amma sai an aunata an tabbatar yadda zan fi samun hujja akanta… na tabbatar
shi kansa wannan Yaron bai san da cikin da dalilinshiba
duba da yanayin yadda ya shiga shock tashi d’aya.”
Yasmeen ce ta matso tace
“Bara muje in aunata sai a kawo miki result d’in.”
Cikin fushi Hajiya mama tace
“Daga kan Khadijah zuwa kan ya’yan da ta Haifa da Larai duk wanda ya sake mini magana kafin Junior ya d’auko Abu ya gwada Kausar sai ranshi ya yi
mugun mugun b’aci wallahi!
Kun d’auke ni wawiya ko?
A tunanin ku zan yarda da ku ne a kan batun wannan ƴar?.
Yau sai asirinta ya sake tonuwa,
kowa sai ya fahimta kuma ya gasgata shegen cikin da ta sake kwasowa a karo na ba adadi!!
Karya kawai!!!
kuma kar inga kowa ya bar nan har sai an gama komai
Junior wuce nace ka je ka d’auko kit ka dawo yanzun nan!!.”
Ta fadi hakan cikin dakawa Junior tsawa.
Juyawa ya yi ya fice a take.
Junior bai dawo ba, suna tsaye su duka su Daddy suka sauk’o, dan sai da suka tsaya suka d’an yi magana game da kiran da Hajiya Mama ta yi tukunna suka sauk’o.
Basuyi mamakin ganin gaba daya y’an gidan a k’asan a
tsaye cirko cirko ba!saboda dama tunda Hajiya mama ta kirasu sunsan case ne.