Sashe 14
Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
In da rabo…idan Allah ya k’addara za ta ga y’ar tata sannan ta ga jikokin ta Alhamdulillah!
Idan kuma Allah ya riga ya k’addara sun rabu kenan har abada to
Allah yasa hakan shine mafi alkhairi…
Ita dai fatan ta shine ‘Allah ya sa itama y’artata ta samu
wadda za ta tsaya mata kamar yadda itama za ta tsayawa Manu da zuciya d’aya!’
Tunda ita kam ba ta da ikon zuwa
ko da kusa da ita ne, ballantana ta kula da ita.
Ba za ta yi tsammani ko ta dogara akan cewa ‘kishiyarta wadda ta bari a wanchan gidan! Za ta yi wa ƴartata uwa ta ko wanne fanni na rayuwarta ba!’
Dukda kuwa ba ta tab’a kama kishiyar tata da wani mugun hali ba amma kishiya a duk inda take kishiya ce.
Ta san dai ba za ta cutar da y’ar tata tunda ta san tanada hali mai kyau daɗin daɗawa kuma mijinsu ba zai taɓa bari ba dan yana tsananin son ƴaƴansa, amma kuma ta san ba za ta tsaya mata ta kula da ita ba kamar yadda ko waccce uwa take yi wa y’arta tsakaninta da Allah! Sannan ba gajiyawa..Dan duk girman ƴa Mace to tana buk’atar uwa ko wadda za ta zame mata tamkar uwa a rayuwarta a kullum da ko da yaushe .
Da yamma lik’is Likitar
Inna ta dawo…kamar ko yaushe yanzun ma ba kyama ba komai haka take kula da duba Inna da wasu ingina,
sannan ta d’an yi mata exercise.
Sai da duhu yayi tukunna ta tafi…
Wani abun mamakin kafin dare kusan kaff mak’oftansu Manubiya sai da suka shigo, har k’awayenta waenda sukayi islamiyya tare ita tama manta da wasu dan ba harka suke yi tare ba tun rabuwar makarantar amma haka suka dinga shigowa suna yi mata Allah sanya alkairi sannan suna
tambayar ta anko da event nawa ne.
Ita kam sai dai ta ce musu “ba komai, babu event’’ kawai.
Haka dai suke tafiya suna masu nanata mata akan ‘idan an fitar ko an chanza ra’ayi za’ayi event d’in, kar ta manta da su ta sanar musu da wuri dan Allah’’
Gaba d’aya ita kam ta shiga damuwa, duk ta yi jigum ta zama so silent.
Sai da hayaniyar ta ragu, tukunna ta samu ta aika Muhsin ya je ya karb’o mata wayarta daga charji dan kwana biyu Nepa suna gwada musu hali.
Dama ta san sai ta ga misscalls d’insa, dan haka ko tsayawa k’irgawa ma ba ta yi ba ta shiga kiransa dan itama ta yi missing d’insa, iya wunin yau da ba ta ji muryarsa ba duk wani iri ta ke jinta!!
Tana tsananin son Yashjub amma kuma ba ta so ta yi aure a d’auke ta a rabata da ahalinta….
‘’Assalam alaiki Matar Yashjub!!’’
Muryarsa ta katse mata tunani, ba ta san lokacin da murmushi ya sub’uce mata ba, dan wani sanyi ta ji yana ratsata daga jin sunan da ya kira ta da shi…
Cikin sanyin muryar a hankali ta ce “ameen wa alaikaAssalam’’
Murmushi ya yi kafin ya ce ’’ba ki ce mijin Manubiya ba’’
Shiruu ta yi tana murmushi k’asa-k’asa dan haka ya ce ’’ashe wata za ta ganni na zo yanzunnan, tunda na san hanya, kuma wallahi idan na zo sai k…. “
“ameen wa alaikaAssalam Mijin Manubiya’’
Ta fad’i hakan cikin tarar numfashinsa, dan tana tuna abunda taurin kanta ya janyo mata ranar chan a asibiti.
Aikuwa murmushi da dariyar da ya shiga yi sai da ta yi mamaki da dariya itama, kafin chan ta ji ya sauk’e ajiyar zuciya tukunna yace “bana jin akwai sunan da aka tab’a kirana da shi na ji dad’i kamar wannan, da farko da na kira ki fushi nakeyi dake akan cillar da wayarki da kika yi tun d’azu na kasa samunki, amman yanzu kam na daina dan kin yi bribing d’ina (kin bani cin hanci na) da wannan daddad’an sunan…
Ɗan sake fad’a in ji….’’
Sai da ya sake cewa ’’plsssss mana’’ kamar zai yi kuka tukunna ta ce ’’Mijin Manubiya’’
Cikin tsananin nishad’i ya sauk’e wata nannauyar ajiyar zuciya kafin yace “Allah ya barmu tare, Allah ya tabbatar mana da alkhairi’’
Ahankali tace “Ameen’’
Daganan suka shiga hira….
Manubiya in banda mamaki ba abunda take yi dan murna da zumud’in da Yash yake yi har tsoro ya fara bata, kamar a kanshi za’a fara aure a duniyar nan..
wani abun ya bata dariya wani abun ya sata jin kunya, har sunan y’arsu ta farko sai da ya tsayar dan shi yace ‘’ya fi son ta haifa masa baby girl a farko mai kama da ita sak! sak!!InshaaAllah, amman in Namiji Allah ya fara basu shima zai yi tsananin murna muddin daga gareta ne, babu abunda zai gani yanzu a gaba bayan auren su wanda zai sanya shi matuk’ar farincikin da sai ya kusan suma kamar ya ga jninsa shi da ita, ranar bai san wani kalar farin ciki zai yi ba, yana masifar son Yara dama yana kuma masifar sonta dan haka ta ƙiyasta ta ga kalar dad’in da zai ji idan ya samu babies daga wajenta…..’’
Ita kam Manubiya gaba d’aya hirar tasa sai ta fara zame mata uncomfortable, dan yadda yake batun soyayyar da zai nuna mata!ciki!da haihuwa!…..
kanshi tsaye ba kara abun ya girmewa tunaninta, gaba d’aya ji take yi kamar ta nutse, shiyasa ta samu ta yi masa wayo ta ce ’’bacci take ji sosai’’
dan ta samu ya barta, da kyar kuwa ya barta bayan ya ce mata’’ta shirya gobe inshaaAllah zai zo su d’an fita, su sayi abubuwan buk’ata da za ta yi amfani da su a biki’’.
Kafin ya d’aura mata da zazzafan ‘i love you’ ɗin da sai da ta ji sa har tafin k’afafunta da tsakiyar kanta, tukunna suka kashe wayar.
Tana ajjiye wayar ta shak’i numfashi sannan ta sauk’e wata nannauyar ajiyar zuciya kamar wadda ta yi gasar rik’e numfashi.
••••••
Sai dare bayan sun kammala dinner tukunna Abokin Daddy ya yi musu sallama ya tafi, ko cikin gida Abhi bai bari sun shiga ba, anan garden d’in inda suka zauna da Abokin Daddyn, ya cewa Daddy
“ya tsaya, yana so za su yi magana’’.
Murmushi kawai Daddy ya yi, saboda dama ya lura da yanayin Abhi ɗin tun d’azu, shiyasa a hankali tun kafin Abhi ya ce wani abun shi ya dafa kafad’arsa ya ce ‘’Abhi,
da mai kud’i da talaka duk Ubangiji ne ya haliccesu..
Yashjub Yarinyar ya nuna yana so itace zab’insa, namu kawai mu goya mishi baya, mu aura masa ita, ko da kuwa a bukka take’’
Cikin katse shi Abhi yace
“seriously???
Talaucin
nasu is too much, Yashjub is way too rich Ya je wajen ta’’
Numfashi Daddy ya fesar kafin ya ce ‘’and yet he did(gashi kuma ya je ɗin), so dan Allah Abhi kawai mu yi supporting d’insa…mu goyi bayansa pls.”
ya fad’i hakan a gajiye.
Shiruu Abhi ya yi yana tunani a cikin ransa….
‘wallahi in da ace ya san irin wannan Yash zai kwaso to da ya gwammaci ya yi masa auren dole da y’arsa Naeema, Yarinyar tana son shi(yash) shiyasa ma ta ce ita zata zauna a gida har a yi bikin a k’are dan ba zata iya ganin auren sa ba. baya so ya yi masa dole shiyasa bai tada maganar ba, amma yanzu kam yana dana sani dan gwara auren dole akan wannan auren da yake shirin yi…..’’
Cikin son fahimtar da shi Daddy ya ce ’’na san kaine a matsayin uba, tunda a wajen ka yake…
Kar ka ga kamar na yi maka shishshigi, dan Allah ka fahimceni brother.
Sannan kar ka nuna kamar ba ka so dan za ka bawa Hajiya Mama k’ofa ne itama ta fara. Dukda na san ita ba zata k’i auren saboda talaucin Yarinyar ba amma indai ta ga kana kakkaucewa to tashi d’aya za ta saka ayar tambaya akan lamarin sannan ta fara cewa itama bata so….ka san kuma na riga na yi musu (su Yashjub) alk’awari tun ba yau ba kuma nima hankalina sai ya fi kwanciya idan ya auri wadda yakeso….
Sannan Yash is very obidient(yana da hankali da biyayya), baya biye-biyen mata, dan haka a ganina tunda har ya nuna wannan ɗin ya ce yana so to the best thing(abu mafi kyautuwa) da za mu yi shine mu aura masa ita.
A yadda yake son Manubiya hana shi aurenta shine abu na ƙarshe da za mu iya aikata masa a wannan halin da da yake ciki..idan ka lura ba ya shiri da kowa! Kullum yana cikin yanayi na rashin walwala, ga kuma Khadijah wadda har gobe ta k’i ta gyara halinta ballantana a samu ya sake da ita…..Abhi farin cikin ƴaƴana nakeso
Ingani, idan ni bana cikin farin ciki bai kamata ace suma ba za su yi ba”.
Shiruu kawai Abhi ya yi, dan a take ya ji tausayin d’an uwan nashi ya lullub’e shi…
Ya lura tabbas idan suka zubawa Khadijah da Kausar harma da Baaba Larai ido to tsaf za su kashe mishi d’an uwa da bak’in ciki!
Tunda ya san ba zai iya yin magana ba, kuma ba zai iya aikata komai ba…
Haka kurum Mata ta tattaro gaba d’aya danginta ta tare a gidan ta ƙi gaba ta ƙi baya?!
Suna sane da yadda ta hanashi k’ara aure bayan kowa ya san yanaso ya yi,
sai yanzu da Allah yayi.
D’an bubbuga kafaɗanshi Daddy ya yi a hankali, kafin ya ce ’’yanzu mu je ciki, tunda ka zo ba ka shiga ba, ba ka ga amarya ba ma’’.
Girgiza Kai kawai Abhi ya yi kafin ya ce ‘’idan Hajiya Mama ta zo ma gaisa da ita a tare’’
Yana shirin shigewa Yashjub ya k’araso wajen, tun d’azu da safe da suka fita shi da Najeeb sai yanzu ya dawo…
Har k’asa ya durk’usa ya yi
musu godiya bayan sun gaisa, daga nan suka wuce tare shi da Abhi dan a side d’insa dama Abhin ya sauk’a…
Hakanan da Abhi da Daddy suka yi ta mamakin tsananin murna da walwalar Yashjub d’in ta yau, abunda ba su saba gani ba.