Sashe 98
Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Hirarsu suke sosai,dukda Manu murmushi da eh ko a’a take ta cewa amma hirar tana yi mata dad’i.
A bakin Hajiya Maman take jin maganar Yadira da Junior ta inda take cewa”ta cewa Daddy kawai ya tsayar da date dan al’amarin Yaran gidan ya fara bata tsoro, dan haka tunda har Junior ya nuna Yadira yake so gara kawai a saka rana a yi aure, ragowar suma za ta bincika musu Miji a cikin jikokin k’awayenta na nan Nigeria da suke in contact with!
ya zama dole a tashi a tsaya a kansu, dan sun rik’a dayawa.”
Ita dai Manubiya murmushi ta yi tace”Allah ya tabbatar da alkhairi”
Dan zuwa yanzu ciwon cikin da ya addabeta sama sama tun d’azu ya k’ara k’arfi!
Tana ji Ummi tana cewa”ta ji suna cewa Yadiran fa ba ta son Junior d’in…!”
Ita kuma Hajiya Maman tace”Wallahi ko za ta mutu sai ta auresa!,Junior ba shi da wani mugun Hali, dan haka dole ta aure sa.”
“Washh!”
Manu tace sakamokon wani mahaukacin murd’awa da cikinta ya yi.
Da sauri duk suka kalleta, sai kuma suka rufar mata sakamokon yadda suka ga ta rik’e ciki ta runtse idanuwa da mugun k’arfi.
‘Sannu’, suka shiga jera mata, bayan Ummi ta rik’eta, Hajiya Mama kuma ta fara k’ok’arin kiran Yashjub.
Yadda Manubiya ta fashe da wani irin kuka ta shiga kiran sunayen Allah ne ya sa Hajiya Mama ta ajjiye wayar, ita da Ummi suka fara k’ok’arin kinkimarta dai dai nan Junior ya shigo.
Da sauri Hajiya Mama tace”ya fito da mota ga su nan sauk’owa zai kaisu asibiti.
Munirat da Ummi ne suka sauk’ar da ita, suka sakata a mota, suna ta faman jera mata sannu!!
Junior da Hajiya Mama da Manubiya sai Munirat wadda ta d’aura kan Manu akan cinyarta ne suka fara yin gaba suka nufi asibitin, Ummi kuma sai da ta koma ta sanarwa su Mommy tukunna ta bi bayansu a motarta, da taimakon kwatancen Munirat da suke waya ta Isa asibitin……
Yashjub yana zaune a office, gaba d’aya tunani ya yi masa yawa, dan sai yanzu ya ke ganin rashin kyautawar sa ga Manu…waya ya d’auko da niyyar kiranta amma sai shigowar Racheal ya katse masa hanzari…..
Cikin takunta ta k’araso tace”Sir,a guy named Abbakar is here to see you!he said he’s a friend of your wife.
(Wani mai suna Abbakar ya na son ganinka, ya ce shi ɗin Abokin Matarka ne Manu).”
A take k’irjin Yashjub ya buga,
sai da ya d’an d’au lokaci kafin ya samu ya d’ago a hankali ya kalleta yace”send him away(ki sa shi ya tafi kawai)”
Duk wani Abu da zai kawo matsala tsakaninsa da Manu ba ya so,gudan sa yake yi.
Ya san ya tsani Abbakar,yana kishinsa saboda Manubiya shiyasa ya zab’i k’in ganinsa.
Har ta juya za ta fita sai kuma ta juya tace”Sir he said it’s very important and urgent,he need to see you!..(ya ce abun yana da mahimmanci kuma na gaggawa ne, yanada buƙatar ganinka.)”
Wannan karon cikin d’an fushi yace”Racheal!send him awayyy!!!(racheal! Ki sallameshi ya tafi kawai!)”
“Ok sir”
Ta ce,daga haka ta juya ta fita.
Dafe kansa wanda zuwa yanzu ya fara sara masa ya yi…ya d’an jima a zaune kafin ya gama yanke shawarar miƙewa da niyyar zuwa gidan nasu ya samu Manubiya, shiruu da kyaliya bai kamata ace ya fara shiga tsakaninsu tun yanzu ba…abunda ya yi kwata-kwata bai kyauta ba….
Yana wannan tunanin ya sauk’a ya shiga motarsa yana shirin kunnawa Abbakar ya k’araso wajen…tunda ya fito ya gansa dama, dan haka ya sake tamke fuska tamau.
Cike da kwarin guiwa Abbakar ya k’araso, ya na zuwa ya d’an yi knocking glass d’in motar wajen mai zaman banza kafin ya bud’e ya shiga ya zauna.
Shiruu Yashjub ya yi, sai kuma kawai ya kunna motar ya ja ya fice.
Sai da suka d’an yi nisa tukunna ya faka ya juya ya kallesa yace”I made myself pretty clear, kuma na san Racheal ta gaya maka..”
Cikin tarar numfashinsa Abbakar yace”inada buƙatar ganinka ne dole,shiysa ka ga na yi hakan..”
Yashjub ji yake kamar ya bud’e motar ya hanakad’a Yaron waje, dan ya yi tunanin idan ya yi masa hakan zai fita amma sam baiga alamun shakka ko shirin fita daga garesa ba ,shi kuma har ga Allah ba zai iya jurarsa ba…. ko sunan shi ba ya so ya ji an kira wallahi…ga kuma gudun zuciya..
“Am…Yashjub ban yi
Mamakin yadda kake yi min ɗinnan ba, dan na san haushina kake ji kamar yadda nima nake jin haushinka!”
Muryar Abbakar ta katse masa tunani..
Juyawa kawai ya yi ya zuba masa jajayen idanunsa..wanda hakan ba k’aramin dad’i ya yi wa Abbakar ba dan ya hango trigger…
Cikin sauk’e numfashi ya ci gaba da cewa”A da na so in b’oye maka kamar yadda Manu ta buk’ata, amma kuma sai na ga rashin dacewar hakan, dan bai kamata mu yi ta b’atawa kanmu lokaci ba, shiysa na zab’i in tunkare ka…”
Cikin katsesa da tsananin fushi Yashjub yace”Kaii!dan ubanka na yi maka kama da Yaro???ni za ka zowa da wannan shirmen?fice mini a mota kafin na illataka!!!”
Murmushi ya ga Abbakar d’in ya yi kafin yace”idan ni ban maida kai Yaro ba ai Manubiya ta maida kai Yaro, jariri ma kuwa..gashi kuma ina k’ok’arin wayar maka da kai amma kak’i ka saurare ni!.”
Kama sitiyarin motar Yash ya yi da mahaukacin k’arfi ya d’aura kansa a kai ya shiga karanto addu’o’i dan ya san tabbas tsaf zai iya kai Abbakar lahira muddin ya ce zai biye sa…
Tsabar b’acin rai zuwa yanzu sama sama yake iya jin Abbakar d’in yana cewa”Tun Yarinta muka taso ni da Manubiya..ba ta yi tunanin Ina sonta ba shiyasa ta karb’i soyayyarka…yanzu kuma ta fahimci Ina k’aunarta dan haka a shirye take ta barka domin ni Yash!
saboda tace ko dan family d’inka ma ba za ta iya rayuwa da kai ba, gashi ba ta son ka…kawai matsalar itace tace mini ba ta san ta yaya za ta gaya maka ba!
tana jin kunyarka, har gida ka siyawa iyayenta…ganin duk mu uku muna ta b’atawa kanmu lokacine ya sa na yanke shawarar tunkarar ka a yi ta ta k’are.”
A hankali Yashjub ya zare makullin motar ya d’ago kansa ko kallon Abbakar bai yi ba, haka ya bud’e ya sa kai ya fita, dan tabbas shaid’an ya fara kad’a masa ganga maganganun Abbakar sun fara tasiri a kansa gashi zuciya
In banda tunzuroshi ya rufarwa Abbakar ɗin babu abunda take yi!
shi kuma ya san muddin ya biye Yaron a halin nan da yake ciki to sai dai wani ba shi ba.
Bai san shima Abbakar d’in ya fito ba sai hannunsa da ya ji ya kamo ya saka masa wayarsa yace”idan baka yarda da ni ba ka duba wannan.”
Duk yadda Yashjub ya so ya yi k’ok’ari kar ya kalli wayar sai da ya kalla…chat d’inta ne da Abbakar har yana ce mata shifa yana kishi gaskiya ta daina yarda da yash, ita kuma ta yi masa alk’awarin ta daina sannan tace”ba za ta iya haihuwa da shi ba, ba za ta iya haifar niece ko nephew d’in su Yasira ba, shi kuma ya yi mata recommending magani ya ce ta dinga sha kullum guda d’aya a hankali cikin zai zube………
Kafin yashjub ya gama karantawa ya had’a wata uwar zufa fuskarsa ta yi jaa…how dare he! ta yaya ma zai fara mishi wannan shegen zancen sannan daɗin daɗawa har yana da ƙarfin halin nuna mishi kamar Irin shi ne ya saka Matarsa ta ke k’aurace masa ɗinnan, sannan har yana da bakin yin magana akan cikin jikinta HOW DARE He!!!…..
Cikin son k’aryata zancensa kafin ya ci ubansa ya shiga bincikawa yana dubawa da kyau, sai dai kuma duk ta inda ya so ya k’aryata d’in abun ya gagara…..ya duba number ya fi sau a k’irga amma number Manubiya ne da komai nata…
Gashi kuma tabbas wannan itace number da take ta kiran Manubiya amma ba ta tab’a d’auka a gaban sa ba!dan ya ga number ya haddace tsananta bincike ne ba ya so shiyasa bai tab’a kira ba.
“Innalillahi wa inna ilaihirrajiun”
Yashjub ya shiga maimaitawa a cikin zuciyarsa, yana jin wani kalar gagarumin tashin hankalin yana yi masa k’awanya.
“Actually wannan sirrin mu ne bai kamata in gaya maka ba amma kuma bani da wani zaɓin da ya wuce in gaya maka ɗin..…dalilin da ya sa na nuna maka na san idan ba gani ka yi ba to ba za ka tab’a yarda ba,ni kuma har ga Allah na gaji dan tun kuna Cyprus ake Abu d’aya, shiyasa ita kanta Manu d’in ma na shalllake ta na yi gaban kaina, gara ka san gaskiya mu daina b’atawa kanmu lokaci.…
Mahaukacin Marin da Yash ya d’aukesa da shi ne ya saka shi a silent…ba ji ba gani ya rufe sa da duka sai da ya ga ya daina motsi tukunna ya tsallakesa ya shige cikin motarsa yana jin abunda bai ma san me ya ke ji ba!!…..
Tafiyar mintuna uku ya yi, ya ja ya faka dan wani irin duhu duhu yake gani…ji yake kamar ya koma ya cinnawa abbakar wuta ko ya samu ya ji sauk’in abunda yake ji a cikin zuciyarsa…kansa har yanzu ya kasa yarda da ɗaukar kalar ƙarfin hali da tsaurin idon Yaron!
Ɗayar zuciyarsa kuma tana ta faman tunzurashi da son tabbatar masa da maganganun Abbakar d’in , saboda gashi har gudunsa da take yi Abbakar d’in ne kenan ya hanata ashe, adduarsa d’aya kar maganar zubar da ciki ya zamo gaskiya infact Allah ya sa ma mafarki ne yake yi, ya samu ya farka ! a yanzu, ko kuma ya ga wani abunda zai nuna masa wannan al’amarin k’arya ne…..
Wayarsa ce ta d’auki k’ara a karo na bakwai…. da mugun kyar ya zaro wayar daga aljihu da niyyar kasheta gaba d’aya amma sai ya ga sunan Hajiya Mama yana yawo a kan screen d’in, dan haka ya d’auka ya kara a kunnensa ba tare da ya ce komai ba.
“Ka zo! Yanzunnan..muna asibiti, Manu ba ta da lafiya….”
Daga haka ta gaya masa sunan asibitin da kwatance, ta kashe, dan suma hankalinsu gaba d’aya a tashe yake ganin yadda jini ya kuncewa Manubiya….