← Book details Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 152

Sashe 4

Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da suka had’u da Manubiya kuma na ga tashin hankali a Idanunta ba kad’an ba…a ganina a nawa tunanin da nake yi shine
‘Ta ga ba za ta iya karawa ko ta kada Manubiya ba shiyasa ta yanke shawarar ta kasheni kenan kowa ya rasa’ ko ya abun yake??
I’m confused…’’

Ajiyar zuciya Yahanasu ta sauk’e kafin ta ce ’’ka tabbatar
tayoyin kunce su akayi ko?’’

Jin jina Kai yayi kafin ya ce ’’na tabbatar Yaha”

‘’To ka bari a yi bincike mana Yash’’

Ya jima yana nazari kafin ya sauk’e ajiyar zuciya ya d’an furzar da iska tukunna a hankali ya ce ’’i don’t want to dig up more dirt….ba na so garin bincike in je in bincikowa kaina abunda zai tarwatsa min farin ciki saboda kin ji da Kunnenki yanzun nan Daddy ya gama cewa yana buk’atar zaman lafiya a tsakanina da Mommy..A ganina indai har Mommy za ta iya rufe ido ta goyawa Kausar baya su ci amanar Yassir sannan kuma ta so ta k’ulla aurenta da ni
to ba na jin akwai abunda ba za ta iya goya mata baya ido rufe akai ba.’’

Da sauri Yahansu ta ce ’’no no no no Yash! Mommy ba za ta tab’a supporting Kausar ta kashe ka ba’’

Cikin tarar numfashi ta yace’’Yeah, na san da wannan, ba wai hakan na ke nufi ba amma na san idan
aka fara bincike, to shakka babu mommy za ta rufe ido ne ta bi bayan Kausar, kuma na san ba zata tab’a bari ayi interrogating d’inta ba!!
Ni kuma in dai har hakan ta faru to daga ranar ni da Mommy mun raba gari kenan har abada
saboda Zuciya da Kaina ba za su iya jurar ganin ta na goyon bayan wanda ya so ya kasheni ba!
Kinga kuwa babu zaman lafiya kenan kuma ni
kaina na san daga hakan na janyowa kaina bala’i ne saboda fushin uwa ma kad’ai fitina ne ballantana kuma ince zan raba gari da ita.”
Wata zazzaafar ajiyar zuciya ya sauk’e kafin ya ci gaba da cewa
“Kamar yadda na gaya miki da farko, gara kawai a barshi dan ba na so in bincikowa kaina abunda zai zamto silar damuna ko ma ya tarwatsani….
Kawai daga yanzu zan dinga kiyayewa ina kula in kuma yi takatsantsan, sannan in sha Allah zan zauna da ita lafiya…

Inaga kawai gara in haƙura in yarda sannan in rungumi cewa ‘mahaifiyar da ta haifeni bata wani damu da ni ba!’…sam ban yi sa’a ta wannan fannin ba.’’

A hankali Yahanasu ta sunkuyar da kanta k’asa muryarta na d’an rawa cikin
son kwantar mishi da hankali da kawar mishi da tunanin ta ce
‘’Komai zai yi dai dai, komai zai gyaru…..it will be okay, we all will be okay.’’

‘‘InshaaAllah’’ya ce
Daganan duk suka yi shiru
….
Sunanan zaune, familyn drivern nasa suka iso, dan haka ya mik’e ya fita…

Shi bai samu zuwa har k’auyen ba, Daddy da wasu daga cikin drebobinsu waenda su ka zo asibitinne suka bi Mutanen har chan kauyen da baifi tafiyar mintuna talatin ba, inda za’a yi masa sutura a binne sa.

Bai dad’e da dawowa d’akin ba Likita ya shigo ya sake duba shi, daga nan ya yi masa allurar bacci.

Ba shi ya tashi ba sai da su Ummi suka dawo ita da Munirat
da abinci nik’i-nik’i.

Ya ji zafin rashin ganin su Ya’isha
amman kamar yadda su Daddy suka ce dukda ya san ba su fi sa gaskiya ba amma shima kawai sai ya bar abun akan ‘sun ji haushin fifita Yahanasu da yayi akan su ne’ shiyasa suka yi fushi da shi, idan ba dan hakan ba da wallahi wannan attitude d’in da suka bashi shikuma sai ya nuna musu origin d’in attitude tunda basu da kunya.

Sallah ya fara yi tukunna ya ci abinci kad’an da taimakon d’uren Yahanasu…..
Ranar Yashjub ya bawa su Ummi mamaki dan ba su yi
tunanin yana magana har haka ba, abu d’aya da suka fahimta tashi d’aya shine
‘In dai
kana buk’atar ya yi maka hira sosai da fara’a to ka sako maganar Manubiya’,
dan haka suka samu abunyi kuwa,
haka nan suka dinga hirarta, dama kuma suma ɗin abunda suke so kenan.

Ya kuwa ji dad’in yadda su ke k’aunar Manubiyan tun kafin su ganta
Babban burinshi a yanzu shine
su Mommy ma su k’aunaci Manubiya kamar yadda su Ummi suke k’aunar ta.
Tabbas ya na son y’an uwanshi ko ba komai jininshi ne su ɗin,
Bai san wanne kalar shed’an da sabon iskanci ne ya shiga kwakwalwarsu suka fito da wannan shirmen ba amma it definitely has to end(dole ma su daina), bai
damu da wacce hanya zai bi ba ta rarrashi ko ta k’arfi
iyakar abunda ya sani shine ‘it has to end’!.
….
Dakyar Munirat ta rabu da shi ta hak’ura, dan da itama cewa ta yi sai an kira Manu ta gaishe ta.
Shi kuma Yash baya so ya kira ta, sai zuwa gobe, gudun kar ta ji muryarsa wani iri ta fahimci ba shi da lafiya, dan baya so ma ta sani balle hankalinta ya tashi.

Yahanasu ta so ta kwana da shi amman ya tubure akan ‘shi ba Yaro bane, kuma ai ciwon nashi ba mai tsanani bane’

Ba yadda suka iya haka suka hak’ura suka shirya suka tafi.

Suna zuwa gida,
Yahanasu ta tura masa wani a cikin masu gadin su, shi ya zo ya kwana da shi.
••••••
A b’angaren su Manubiya kuwa, ganin abun ya fi k’arfinsu kuma ba yadda za su yi ne ya sanya su Ya Nafi’u suka samu dattawan layin akan maganar su Uncle.

Dakyar kuwa aka samu aka shawo kan su Baba Habu da Uncle da
kaka mallan wanda ya fi kowa zak’ewa akan sai su Baba sun tashi a gidan…..da kyar suka
hak’ura bayan an yanke an kuma ja layi
akan
‘Babu ruwan kowa da kowa!
Kuma ko kallon banza in su Manubiya suka sake yi wa wani a cikin Ƴaƴan gidan
to sai sun fuskanci shariah.’

Dayawa daga cikin dattawan tun a kallo ɗaya Baba ya ke basu tausayi, dan duk wani mai imani in ya ganshi a wannan lokacin to dole ya tausaya masa saboda duk ya yi wani iri gashi ya zama so silent, ko a wajen meeting d’in ma ‘’To’’ kawai ya dinga cewa.

Kuma ko bai fito ya faɗa ba, ana ganinshi kai tsaye za a fahimci
Abunda su Uncle sukayi masa
ya girgizashi matuk’a……..

BULAMA ✍️
0903 441 3252
*MANNUBIYA*
*Book 2*
*page 03*

Yassir yana fita daga asibitin, direct gida ya nufa dan yana buk’atar ya ganewa idanunsa wanne hali
Kausar take ciki….
Wanda dole ya san zai kasance ɗaya daga cikin biyu
‘Ko dai tana chan ta b’oye kanta tanata kuka' ko kuma dai ‘bata damu da Yashjub d’in ba shiyasa bai ganta a asibitin ba….’

A b’angaren Kausar kuwa, sai a wannan lokacin ne ta samu maganin baccin da ta sha ya sake ta.
Dan haka ta mik’e ta nufi toilet, tana cikin wanke fuskarta ta fara jiyo muryar Baaba Larai a cikin d’akin nata tana cewa “Kausar wai baccin uban me kike yi ne haka tun d’azu…’’
Dan haka ta yi maza ta k’arasa wanke fuskar tata ta fito.
‘’Lafiyarki kuwa??’’
Muryar Baba Larai ta katse mata tunanin da ta fito tana yi.
A hankali ta d’an sauk’e ajiyar zuciya kafin ta ce ’’na d’an sha maganin bacci over dose ne,
shiyasa har yanzu kaina yake juyawa’’

Girgiza Kai Baba Larai ta yi kafin tace “Ni dai fa ince, na ga ban ga kin fito an tafi da ke ba’’

‘’ina?’’
Kausar ta yi mata tambayar cikin katseta.

‘’Yashjub ne yayi hatsari, shine aka tafi asibiti tun d…..’’

Da k’arfi Kausar d’in tace “what!!!’’ Cikin katseta, sai kuma ta tafi luuu za ta fad’i.
Da sauri Baba Larai ta tarota a rikice ta ce “relax, ba abunda ya same shi sai gocewar k’ashi kawai a Hannu, amma Baba Iliya kam an amsa kira’’

Ajiyar zuciya Kausar ta sauk’e,
da kyar ta k’arasa bakin gadonta ta zauna kafin tana haki da kyar ta samu ta iya cewa ‘’ba shi yake driving d’in ba kenan?’’
sai kuma ta sake mik’ewa, ganin tana shirin zubewa yasa ta ce ’’Baaaba, d’an rik’e ni, jiri nakeyi,bari in je asibitin, ki zo ki taya ni sauk’a’’.

Matsowa Baba Larai ta yi ta rik’eta sannan ta ce ‘’ki nutsu, su Mommy sun kirani yanzu suma suna hanya, ki nutsu sosai mu jira ta dawo tukunna..’’

Cikin fushi ta hankad’e ta tukunna ta ce ’’Baaba kin san me kike fad’a kuwa?
In nutsu kamar yaya? Yashjub ne fa ba lafiya yana kwance ya yi hatsari shine kike ce min wani in nutsu??’’.

‘’Shikenan.Bismillah’’
Baaba Larai tace da ita daga haka ta juya ta fita.

Yassira Kausar d’in ta kira, domin ta tambayeta sunan asibitin amma kamar yadda Baaba Larai ta ce mata itama Yasirar haka ta ce “ta yi hak’uri ba sai ta je ba, suna hanya suma, akwai d’an case ne dan haka in aka ga ita ta je abun zai rinchab’e.

Kuma don ta sani, yanzunnan suma Yasmeen take ce musu ta ji a bakin likitan yana cewa wa’enda suka kawo
su Yash d’in sun ce wai kamar kunce tayoyin motar tasa akayi.’’

Tashi d’aya hankalinta ya sake tashi, ko sallamar da Yassira ta yi mata ma ba ta ji ba!
Ji ta yi kawai ta kashe wayar….

Zato zunubi amma tunani da zarginta tashi d’aya akan Yassir ya dira!!
Dan a lissafinta in ba shi ɗin ba ta san kaf gidan babu wanda zai yi wannan aika-aikar tunda dai su babu wanda ya ke shigo musu gida, bayaga haka kuma in ba black snake wanda suka tab’a yin fad’a da Yash d’in ba ta san Yash bashi da wani Abokin fad’a, yo yaushe ma ya dawo k’asar dududu.
To amman mai yasa Yassir zai yi haka
saboda kishi ko me?
Tabbas dama ta san yana zargin ta, ta san bai gama yarda da ita ba, amma sam ba ta yi tunanin abun nasa ya kai har haka ba.
Chapter 4 · 0% Book details