Sashe 40
Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Su Yasmeen kuma super ce a jikinsu ita da Yusra(super babba!), su kam har d’auri suka yi suka rufa mayafansu a kafaɗa..
amman suma dank’ara dank’aran gold d’in jikinsu Hannu wuya kunne da y’an yatsu kad’ai abun kallo ne.
Yadira ce kawai mai material
d’inkin fitted gown amma
itama kana gani kasan yadin yaji kud’i, A kunneta kawai ta saka gold sai agogon ta na gold, ko zobe ba ta saka ba ita.
Maganar gaskiya
kaff gurin kayansu ne ya haskaka ko Ina!, dan tun a waje kafin su shigo babu mai kyallin su! Duk wanda ya shigo cikin layin kuwa idan ya kalli kowa a lokaci guda kai tsaye zai fahimci su ɗin ne dai suka zama pronounce, ga wayoyin Hannayensu kalar wadda ake yayi ta shekarar. Shiyasa suka zama abun kallo sannan
behaviour d’insu (ɗabi’arsu) itama ta zamana
kowa ya gani saboda idanun
kowa a kansu ya ke dama….
Suna shiga parlourn wata mata tace “Allahu Akbar! Ga dangin ango!”
Dakyar Yassira ta d’an yi murmushi sannan ta ce ”na jini ma kuwa”
Ta yi maganar tana kallon Munirat wadda ta fito daga d’akin da Manubiya take ciki d’auke da kaskon turaren wuta a Hannunta”.
Murmushi Munirat d’in ta yi kafin tace mata ”ina wuni, har kun iso?”
K’ura mata ido kawai ta d’an yi kafin ta d’auke Kai ta maida dubanta ga Matan da su ke karkad’e kan kujeru duk sun rikice sun ga gwalagwalai da sutura, dan tashin Mutane ma akayi akan kujerun aka shiga karkad’e musu inda za su zauna.
Ba wani datti a wajen
amman dukda haka sai da Matar da ta karkad’e wajen tukunna ta ce musu “bismillah” ya fi sau biyar sannan dakyar Yassira ta d’an zauna ita da Yasmeen da Baaba Larai, su Yusra kuwa a tsaye suka tsaya akan kafet da takalman su!Sam ba su damu da yadda su ke tattaka abincin
da aka ci aka zuzzubar akan
kafet d’in yana mammannewa ba, wayoyinsu kawai su ke daddannawa.
Ita Yassira abunda ya fi damunta ma shine kar ta je ta kwashi infection a jikin kujerun
dan har wani danshi danshi ta ji bayan ta d’an d’osana mazaunanta akai ta zauna…jin yadda danshin yake sake ratsata ne ya sanya ta ga inaa! Ba za ta iya ba! Dan haka tashi d’aya ta mik’e ta zare d’an kwalinta dama a ka ta rufa mayafin shiyasa ta zaro shi ta shimfid’e
akan kujerar tukunna ta koma ta zauna, wanda hakan da ta yi sam bai yi wa rabin Matan parlourn da suka san ciwon kansu dad’i ba.
Dariya k’asa-k’asa Yasmeen ta yi wanda hakan ya sake k’ular da su Siyama waenda suka dawo daga d’aukowa su Ummi fararen kujerun zama suka shigo yanzun.
Ba tare da sun kalli su Yasmeen d’in ba suka wuce suka ajjiyewa su Ummi kujerun fuskokinsu tamau. Suna ajjiyewa Ummi ta ce ”Siyama ki barshi ba sai kun yi wahala ba ai,”
Murmushi kawai Siyama ta yi tace”ba komai Ummi, bismillah”
Dai-dai nan Inna, Iya ramma da Maman Siyama suka fito daga cikin d’aki.
Su Inna basu damu ba suka zauna a chan gefen carpet yayinda su Yasira suka hahharɗe k’afafu akan kujera, Su Ummi ma inda su Innar su ke suka k’arasa su ka zazzauna aka shiga gaisawa cikin mutunta juna
ana gabatarwa.
Yahanasu ce ta gabatar musu da tun daga kan Baba Larai har izuwa kan Yadira, su kuma suka nuna Inna farar bafulatana mai k’aramin jiki kkyakkaywar gaske a matsayin mahaifiyar Manubiya
Maman Siyama kuma a matsayin gwaggon ta.
Ummi ce ta ce musu “Ita Ummin sa ce step mom, Mahifiyarsa tana gida bata samu zuwa ba”.
Kamar jira Yasmeen take ta
tari numfashinta tace “Eh! Tanada allergy.. (rashin jituwar jiki..) shiyasa duba da yanayin arean nan yasa ba ta zo ba”.
Rabin Matan ba su gane me take nufi bama sai y’an kad’an
ne suka fahimceta.
Shiruu Ummi ta yi haka ma kowa kafin Yahanasu ta ɗan yi murmushi ta kawo k’arshen shirun ta hanyar cewa “ko za’a
fito mana da Amaryar tamu wuce!Na ga magariba har ta gabato”
Sai a sannan maman Siyama tace”da ikon Allah, bari in je in kawo muku ita”
Daga haka suka mik’e su biyu ita da Iya ramma
sannan sukace Ummi ta biyo su.
Ba wai Yaro kaɗai ko Babba idan ya kalli fuskar Baaba Larai a wannan lokacin to sai ta bashi tsoro!!!
Ta had’e rai ta yi tamau da fuska ta kumbura, gashi Idanunta sun yi jaa!!!
Ita a nata lissafin..
..wai tsabar an rainasu shiyasa ko saka su ma ba a yi itada su Yassira a cikin karɓan Amarya da bayarwan ba! Sai Ummi da Yahanasu kawai suke komai, sam su ba a d’aukesu da mahimmanci ba.
Ga kuma takaici da tsanar Manubiya da ahalinta baki d’aya, Gashi ba su samu sun yi abunda suka yi niyya d’azu za su yi a gidan Amaryar ba..Shiyasa gaba d’aya ranta ya b’aci ta kumbura ta yi suntum! Tana mai jin kamar ta d’aura Hannu a ka ta yi ya zabga uban ihu….
Ba a yi mintuna shida ba suka fito da Manubiya, sanye cikin fara k’al d’in alkayabba sai
kyalli da tashin k’amshi takeyi.
A gefen Ummi suka ajjiyeta, tana zama Ummi ta rungomo ta izuwa jikinta sannan ta ce ”Allah ya yi miki albarka, Allah ya sa ki zame mana sanyin idaniya”
“Ameen” gaba d’aya kowa ya ce ana raha daga nan aka bawa Ummi amanarta, suka karb’a Hannu bibbiyu ita da
Yahanasu, aka yi addu’a aka shafa kafin a fara shirin mik’ewa…..Yassira ta ce
“Yauwa Inada magana,
saboda akwai al’adar da muka saba da ita mu y’an gidanmu!”
Runtse idanu Yahanasu ta yi,
kafin ta buɗe ta kalli Yassirar ta ce
“Yassira inaga gara mu wuce kawai, yamma ta yi”
Murmushin rainin hankali Yasirar ta yi mata kafin tace
“Nop!ba zai ɗauki lokaci mai tsayi ba ai.”
Sannan ta kalli Inna ta ce ”and da farko kafin komai, inaga ya kamata in d’an buɗe sannan in faiyyace muku wani abu”
Ta yi maganar idanunta cikin idon Inna, kafin ta ci gaba da cewa “Ita wannan wadda kika bata amanar y’arki!
Matar Babanmu ce, itama
kamar uwa take a wajen mu
amman ba ta san cikakkiyar Al’adar gidanmu ba! Dan ko
shekara d’aya ba ta yi a gidan ba.
Wannan itace yayar Mahaifiyarmu wadda aka turo ta wakilceta”
ta yi maganar tana nuna Baba Larai kafin ta ci gaba da cewa
“A haƙiƙanin gaskiya, yadda al’adar mu take..
..Mu da muka zo d’aukar amarya, to tun daga kan Baaba Larai har izuwa kan Yadira dole ne sai Manubiya ta bi mu ɗaya bayan ɗaya ta durk’usa a gabanmu, sannan ta gaishe mu! A matsayinmu na dangin Mijinta, daga nan ne idan mun ga muna so za mu karb’e ta mu yarda da ita tukunna mu d’auke ta mu tafi da ita’.”
Cikin tarar numfashinta Ummi tace “Yassira wanne irin shirme ne wannan???”
Da d’an murmushi kwance a kan fuskar Yasmeen ta ce
‘’Ai gaskiya ce Ummi, kuma
ai ba abun zafi bane ba,
kamar dai wasa haka game ɗin ya ke!
Ke dai kawai ki
Kalla…it will be fun.”
Ta k’arashe maganar tana murmushi.
Yusra ce ta d’aura da cewa
“ai ya kamata ta san mu sannan ta san matsayin mu na siblings d’in Mijinta(kannen mijinta) tun yanzu! Ta san cewa idan ta shigo za ta girmama mu ne ta bamu girman mu!
A garinmu hakan shine ma main purpose (babban maƙasudi) na b’ullo da wannan al’adar….
Wanda a yadda ake ɗinnan banga alamun hakan daga gareta ko wani a cikin parlourn nan ba, dan na lura
kamar ba ma a san da mu ba!
Ko irin y’ar amanar ta ma ɗinnan ba a bamu ba Ummi kad’ai aka bawa.
So ya kamata ta yi gaisuwa ta yi durk’uso kafin mu d’auke ta
mu kaita gidan Ya Yashjub d’inmu mai tsada…
Ku duba fa ku ga yadda za
mu d’auke ta daga nan!” Yusran ta fad’i hakan tana kallon parlourn tana nunawa da Hannunta kafin ta ci gaba da cewa
“mu kaita chan aljannar duniya, gidan Ya Yash!…
A ganina ko cewa muka yi ta kwanta ta gaida mu bai kamata ace kun yi jayayya ba.
Bayaga hakan ma ba wai mu muka tsara ba Al’Ada ce ta Mahaifiyarmu sannan Mahaifiyar Ya Yash, mune wakilanta, dan haka a gaskiya babu inda Amarya za ta je ba tare da an gwada kuma anyi abu guda ɗayan da zai yi nuni da an darajata an daraja mu sannan an karrama Al adarmu ba……”
Ganin kowa yayi tsit an kasa magana ne yasa
Siyama cewa “Tou inaga za ku iya kwasar motocinku ku koma, saboda an samu gagarumar rashin fahimta! Ta inda mu muke ganin mun yi muku alfarma na baku one in town ɗin ƴar uwarmu da mukayi, kuma kuma naga kuna ganin kamar kun yi mana alfarma ne…”
Da sauri iya ramma ta ce ”Siyama ya Isa haka!”
Ba dan Siyama ta so ba ta yi shiru tana mai rama hararar da taga Baba larai tana yi mata.
Bayan Ya’isha
Baba larai ce second halittar da Siyama ta fi tsana a cikin su, Ita wallahi tunda take bata tab’a ganin babbar kwabo babbar banza irin wannan matar ba…
Matsawa Iya ramma ta d’an yi tukunna ta kalli Ummi
tace “y’an uwansa ne kika ce ko?”
Jinjina kai Ummi tayi tana shirin yin magana
Yassira ta ce ”Daga Yashjub! sai ni da d’an uwana twin brother d’ina Yassir!
sai wannan Yasmeen! sai wachchar Ya’isha!
sai Yusra sai y’ar autarmu
Yadira!”
Tana dasa aya ta d’aura da cewa”ku ne fa kuke ganin kamar cin fuska ne yin hakan ko wani abun na daban, alhalin mu al’ada kawai muke so mu raya,
kuma munaso dangantakarmu da Amaryar ta samu kyakkyawan tushe!! Shine fa kawai!.
Ku ne kuke ta dagula abubuwa, you guys should just
let her bow down!(kawai ku barta ta durƙusa mana), a yi a wuce
wajen.”
Jinjina kai tsohuwar ta yi
kafin tace “na ji, na fahimceki!”
Sai kuma ta kamo Hannun Manubiya ta mik’ar da ita tsaye dakyar tukunna ta ce ”y’ar albarka!mu je ki gaidasu”.
D’iff!
Haka parlourn ya yi tsit, ba wanda ya iya cewa uffan!