Sashe 16
Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Daddy ya ji dad’in yadda Ummin ta yi farin ciki da zuwan Mahaifiyar tasa, ya san Hajiya Mama ba sa shiri kwata-kwata da Mommy kamar ba y’ar aminiyarta a farko ba haka take rufe ido ta tsigale ta tass!sannan ya ji abunda ta yi mata yanzu amma dukda haka yadda Mommy ta nuna tashin hankalinta wanda gashi har ya kai ta gagara sauk’owa a yi breakfast da ita hakan ba kad’an ba ya sosa masa rai, dan ya san daga ita har su Yasmeen da suka k’i zama duk saboda
Hajiya maman ne, amma zai ci ubansu in ya samu lokacinsu dan uwa ba ta fi uwa ba.
Faram faram kamar su Ummi da Hajiya Mama za su cinye juna haka aka shiga gaisawa ana murnar had’uwa, har ma
da Sameeha dan Itanma suna waya suna chatting da Ummin.
kamar yadda suka yi wa Ummi haka suka yi wa Munirat Itama, ta ji dad’i kuwa
matuk’a, dan ko ba komai ta fahimci ba duka aka taru aka zama d’aya ba, kuma yanzu ta tabbatar Ummin ta za ta d’an rage zafi tunda ga oga kwata kwata ta gani da idanunta ba wai a waya ba,
ta na sonta kuma tana ji da ita.
Su kad’ai sai Daddy da Abhi ne aka yi break fast d’in yau, dan ko Ya’isha ma k’in zama ta yi tace musu in ta tsaya za ta makara wani aiki da ya shafi masters ɗinta da take yi.
Tana fita Hajiya Mama ta kalli Daddy tace ‘’Saboda shegiya!
da kai da matarka kun janyowa y’ay’anku karatu a Nigeria’’
Kallon Ummi ta yi, sai kuma ta kalli Daddy kafin ta ci gaba da cewa “ai ni ban san irin power da wannan shegiyar Yarinyar take da ita a cikin gidan nan ba, Saddik’a saboda fa ni da Daddy mun ce ‘idan kausar ta fita k’asar waje karatu za ta sake lalacewa, dan haka a barta ta yi
karatu anan gida Nigeria’ shine
ita uwar Yaran tace ’tunda Kausar ba ta fita waje ba to babu wanda zai sake yin karatu a waje’.
Duk dan kar ran y’ar gwal d’in ya b’aci! Akan
ranta ya b’aci gara na ya’yanta ya b’aci, kuma shima Imam din ya zuba mata ido ya k’i tab’uka komai akai, shiyasa ka kaf cikinsu Yassira ce kawai ta zo ta yi karatunta
Itanma dan ta riga Kausar d’in farawa ne da wata d’aya shiyasa aka barta ta kammala Oxford, sai Yash da Yassir da Yahanasu tunda su sun riga ta yi’’
Hajiya Mama ta faiyyace hakan cikin d’an b’acin rai.
Shiruu Ummi ta yi ta rasa abin cewa, dan haka kawai sai ta sunkuyar da kanta.
Cikin b’acin rai still Hajiya Mama tace ‘’Kuma ai gaskiya aka fad’a, tun kafin fa ta tafi makarantar k’asar wajen ta yi ciki ta haihu d’an ba rai,lokacin tana gama secondary school.
Me kike tunanin zai faru inda an barta ta je wata k’asar..?’’
Ahankali Abhi ya ce ’’Maaamaaa’’
Ya d’an jaaa maganar.
Sai a lokacin Hajiya Mama ta lura da yadda gaba d’aya ita kanta Ummin she’s not comfortable( ta kasa sakewa) da zancen, dan haka ta yi shiruu kawai tana mai sake tabbatar da innocence ɗin Ummin, a ranta ta ce ’’tabbas ban ga ta zama ba, dan matar nan ba ta san komai ba,
sannan ba ta san wacece Khadija(mommy) ba, ya kamata a yi wani abun tun kafin ta cutar da ita
that is if(matuƙar kuwa)
ta kasa cireta a gidan kenan…’’
Shiruu dining d’in ya yi, ba a jin k’arar komai sai cokula sai
kuma albarkar da Hajiya Mama taketa sakawa Ummi, dan ta ji dad’in girkin da ta tarar Ummin ta yi da kanta kuma ya yi mata dad’i sosai.
Ummi kuwa Baki har kunne, dan ba kad’an ba take jin dad’in addu’o’in da Hajiya Mama take ta zuba mata.
Sosai Daddy ya ji dad’in yadda Ummi da Hajiya Mama suka fahimci juna suke shiri da kuma yadda Ummin take girmama Hajiya Mama
shiyasa ya yanke shawarar zai sake tuntub’ar ta wataƙilan zuwa yanzu ya san ta huce..shi dai ba zai bata hak’uri ba duk rintsi! dukda zuwa yanzu shi kansa ya san ya garu!Ummi ba yaji ta yi ba tana cikin gidan shi amman fushin ta gareshi ya fara illata shi matuk’a…..
Ganinta a tsakiyar manya yasanya gaba d’aya ta ke ta jinta unconfortable (a takure), shiyasa ta yi sauri ta kammala, daga haka ta mik’e tace musu’’ta k’oshi’’ ta yi musu sai anjima kafin ta
nufi sama.
Kusan karo da juna suka yi da Yassir wanda yake sauk’owa k’asan, sanye da suite har da brieficase, ya yi masifar yin kyau! Ana ganinsa an san office zai tafi.
Sarai ya lura da ita amman sai ya d’auke kai kawai ya wuce, wanda hakan kuwa ba k’aramin gigita Munirat yayi ba! Dan ba ta yi tunanin zai iya yi mata haka ba..tun jiya take jiran kiranshi bai kira ta ba sannan yanzu kalli abunda ya yi mata duk dan shekaran jiya ya ce ‘’su had’u a gidan Abokinsa’’ ita kuma ta k’i yarda, ta ma yi fushi tace ‘’ita ya ma daina yi mata irin maganar nan bata so’’
dga haka ta kashe wayar, to ashe shima ya d’au zafi da gaske tunda gashi ya d’auke mata d’iff…anya kuwa ba za ta sauk’ar da kai tun wuri ba su shirya ta nuna masa komai ba komai ba, dan tana jin tsoro kar ta je ta taro match d’in da ba za ta iya ba, saboda ita dai wllahi a yadda ta ke ji ta san ba za ta iya rayuwa babu Yassir ba….
Ya yi mamakin ganin Hajiya Mama dan haka ya yi saurin k’arasawa suka gaisa ba yabo ba fallasa kafin ya tambayesu Junior.
Ya kuwa ji dad’i kwarai da ya ji Junior ya zo, bai wani damu ba da aka ce mishi Na’ima ba za ta zo ba dan bai damu da Yarinyar ba saboda
muguwar gidahumace,
kamar ba a uk aka haifeta ta girma ba, ga ta da shegiyar rowa bata taɓa bari a amfana da Jikinta, sannan tun ranar da ta fito mishi a mutum ta gaya mishi Yash take so ya fita sabgarta, ko chatting d’in kirki ba sa yi!
shi mantawa ma yakeyi da ita in ba a family group ya ga ta yi magana ba.
Kad’an ya d’an chakali abinchin, kafin ya mik’e ya yi musu sallama ya ce ‘’bara ya je office’’
Duk jama’ar wajen sai da su ka fahimvi asalin farin cikin da Daddy ya shiga a take! Dan sai murmushi yake ta zubawa sakamokon ganin Yassir da ya yi a shirye caff! Zai tafi office kuma da wurwuri haka, a ranshi ya godewa Allah ya shiga addu’a ‘Allah ya sa fad’an da aka yiwa Yassir ya shige sa kenan, Allah ya sa ya shiryu kenan har abada’.
Kasa hak’ura Daddy ya yi sai da ya mik’e har bakin k’ofa ya je ya shafa kansa ya yi masa addu’o’i tare da fatan nasara tukunna ya koma ya zauna yana ta zuba murmushi.
Tunda Yassir yake a rayuwar sa bai tab’a jin guilty conscious(jin laifin abunda ya aikata) irin na yau ba, ya san saboda Daddy ya ga zai je aiki ne ya sa yaketa wannan murnar alhalin a asalin gaskiya shi ba aiki ne zai kaisa ba..wani Abokinsa ne ya had’a shi da wata Yarinya! yarinyar ta had’u matuk’a mahaifinsu ya rasu kuma itace babba shine take neman aiki, shiyasa aka had’ata da shi, shi kuma yace su had’u yau ya ga ko za su daidaita……
‘’Tunanin mai kake yi??’’muryar Daddy ta katse masa tunani, wandaya juyo daga inda ya ke zaune yana kallonshi…
murmushi kawai ya yi bayan ya kallesa daga haka ya yi waving d’insu ya sa kai ya fice.
Dukda uwar suite d’in da ya ci kuwa, yana fara magana Yarinyar ta fahimci inda ya dosa ta kuma
fahimci ba aiki ake son ba ta ba, dan haka ta mik’e tsulum ta fice ta bar sa cikin tsananin mamakin ta. Dan ko irin sallamar nan ba ta yi masa ba hakanan kawai ta mik’e ba um ba um um ta fice ta bar masa office d’insa…..
Ko mintuna uku bai k’ara ba shima ya fice daga company d’in ransa a mugun b’ace, yana mmakin yadda sam ya daina cin galaba a kan y’an mata anyhow, kamar wani wanda aka yiwa asiri….
duk wani abu mai kyau na gidan Daddy Yashjub ya d’auke harma da farin jinin y’an mata……
Ko da ya dawo gida, direct side d’in Yash ya nufa wajen Junior, aikuwa kafin awa d’aya ya ware war suka yi ta hira abunsu
dan kusan Junior shine best friend d’in Yassir, saboda halin su kusan d’aya ne dan indai aka zo batun Mata to kowannen su sai a hankali kawai sai dai unlike Yassir (saɓanin Yassir) shi Junior ya san class d’insa sannan shi Mutum ne mai himma da kwazo sosai, dan yanzu haka Doctor ne shi wanda ya yi fice saboda tarin nasarorin da ya samu a aikinsa dukda kuwa bai jima da farawa ba, sannan yana gab da zama consultant..dan bai fi wata biyu zuwa uku ya zama ba.
Junior ya yi mamaki da ya cewa Yassir ‘’ya zo su je su gaida antynsu (matar Yashjub)” dan kai tsaye ya ji Yassir ya ce ‘’shi bai ma tab’a ganinta ba’’
amma kumada
Junior d’in da ya tuna waye Yashjub sai ya ga hakan a wajenshi ba komai bane, dan haka ya kawar da zancen su ka fad’a wata hirar.
….
Mommy tana shiga cikin d’akinta ta fashe da wani irin kuka mai hawaye wiwi kamar wata Yarinya.
Ta kasa tsaye ta kasa zaune, sai faman safa da marwa take yi tana hawaye tunda ta shigo cikin d’akin.
A haka Baaba Larai ta turo k’ofar d’akin ta shigo dan d’azu tana parlourn Kausar wadda itama damuwa ta sauk’arwa da zazzab’i ta fara jiyo
Hajiya Mama da Mommyn shiyasa ta bari sai da suka wuce tukunna ta biyo ta ga halin da y’ar uwartata take a ciki.
Da mugun sauri ta rufe k’ofar ta k’arasa kusa da ita ta rik’eta tace’’subhanallah Mommy….’’