← Book details Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 152

Sashe 18

Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cike da kasala ya ce “ lafiya “ idanunsa a kanta yana mamakin mai ya same ta haka da ta k’ara wannan azabb’en kyan cikin k’ank’ani lokaci, a gefe guda kuma na zuciyarsa yana jin takaicin kasancewar drivern da ke gaba na cikin motar, dan ya san shima tabbas ya shak’i wannan sumamman k’amshin da take ta zubawa, addu’ar sa d’aya kar drivern ya zo gaisheta yace zai juyo, haka kurum ya k’are mata kallo, dan shi a rayuwarsa baya son abunda zai sa ake kalle masa ita balle yanzu da shi kansa yake jin numfashinsa yana shirin d’aukewa…..yana cikin wannan tunanin ya ji ta cewa drivern’’ina wuni’’

Cikin girmamawa da yin k’asa da kai drivern ya gaisheta ba tare da ya juyo ba, daganan ya kunna motar bayan Yash ya fad’amasa Ina suka nufa, suka d’au hanya…..

Dukda drivern ne ya kamata ya gaidasu amman sai Yash ya ji dad’in yadda Manu da Muhsin suka girmama dattijon Mutumin dan ko Muhsin shima bayan sun gaisa sai da ya gaida drivern…wanda hakan ya nuna sun san girman d’an Adam da farin gemu saɓanin su Yasmeen.

A k’ofar shagon wata shahararriyar mai d’inki suka yi parking, tukunna drivern ya kashe motar ya fita haka ma Muhsin…
bai yi gigin bud’e musu ba dan bai san ko za su tattauna ba kafin su fito, dan haka ya koma gefe ya ja ya tsaya haka shima Muhsin.

A hankali cikin wata murya kamar ta wanda ba ya son yin magana ya ce ’’mu je ko?’’

Jin jina Kai ta yi tukunna ta sa Hannu da niyyar bud’ewa amma sai ta gagara, ta juyo da niyyar yin magana ta ga ya bud’e side d’insa ya fita ya zagaya.

Da kansa ya bud’e mata, dan ko da drivern ya matso ma d’aga masa hannu kawai ya yi ya tsaidashi.

Ahankali duk tana jin kunya da nauyi sun lullub’eta haka ta sa k’afa ta fito, sai da ta gama fitowa tukunna ya rufe marfin motar ya ja ya gyara mata mayafinta wanda ya d’an zame yana shirin sauk’a daga kanta tukunna suka nufi k’atoton shagon, suka bar driver cikin tsananin mamakin yau Oga ya zama driver!
Amma kuma har ga Allah ya ji dad’i kuma sun matuk’ar burgesa, hatta Muhsin ma da yake Yaro sai da suka burgesa, bai bisu har ciki ba ya tsaya a wajen driver suka shiga hirar su.

Suna shiga wajen ta ga ashe har ya bayar da kaya wajen kala ashirin majorments d’inta kawai ake buk’ata…dan haka suka shiga wani d’aki Matar ta aunata aunin kwakwaf dan ba abunda ba ta gwada ba saboda wai za’ayi d’inkin nikkah wanda zai yi fitting ragowar ma duk ana so su yi fittng tunda a lefe ya ce mata za’a saka dan haka dole kayan su fito rasss!!!

Hakanan ta yi ta janta da hira dan matar professional tailor ce,
mai kirki kanta a waye shiyasa kamar za ta goya ta.

Manu ta ji dad’in yadda Yash ya yi respecting decision d’inta (ya mutunta shawararta), dan tunda ta ji matar tace ‘’iyaka d’inkin nikkah, ragowar kuma na lefe” to ta san ya yarda shi da y’an gidansu akan ‘babu wani event d’in da za su yi kenan.’

Babu maganar deposite dan Yash complete ya juyewa Matar kud’in d’inkunan kaff a account, har suka fito suka shiga mota suka fara tafiya kan Manubiya bai daina juyawa ba…sai da aka tura kud’in tukunna ta ji dan wallahi ba dan hakan ba to da ba za ta yarda a yi wannan uban b’arnar kud’in a iyaka d’inkuna ba….

Ba gida suka koma ba wajen jewelries da shoe and bag d’in da za ta yi amfani da su sukaje
suka sissiya, daganan
suka biya mudassir…

Ya riga ya sayi komai amma akwai d’akin dama da ya ware akan itace za ta zab’a da kanta sai kuma deco (kayan ado na gida) da kayan kitchen da yake da bukatar ta k’ara da zaɓinta akan waenda ya sissiya, shiyasa ya kaita ya ce ta tayashi zab’e dan ya kasa..
Siyayya sosai kuwa suka yi dan har sai da ta fara tunanin wataƙila ko harda iyayenshi zai chanjawa kayan kyale-kyale da na kitchen saboda bikin, dan uban kayan da suka d’iba wasu aka yi order abun ba ‘a cewa komai.

Tabbas ta yi mamaki matuk’a
amman da ta tuna yawan estates d’in shi da business d’in da yake yi, sai
taga kud’in da suka bata tsoro waenda suka kashe a iyaka yau ɗin kad’ai ba komai bane a wajensa.

Ta san Yash yana sonta kuma ta san so gaskiya ne, amma yadda taga yake rawar k’afa da waensu abubuwan duk akanta wasu lokutan har tsoro da mamaki takeyi…duk wani kud’i! dukiya!class! ajjiyewa yakeyi a gefe
ya sauk’ar da kanshi k’asa sannan ya kawar ya goge gaskiyar cewa ‘shi ɗin sam ba ajinta bane ba, ba class ɗinsu ɗaya ba’.
Yadda yake ɗaukarta yake yi mata a gaban kowa da koina kamar wata sarauniya tabbas hakan yana bata alajabi, gashi dai ya san itan ma tana sonshi
ballantana tace ko campaign yake yi….

Ita kam tabbas ta yarda ta amince she’s fortunate, infact she’s morethan fortunate…
(ta yi sa’a! A zahirin gaskiya ma kalmar ‘mai sa’a’ ta yi kaɗan wajen baiyyana kalar sa’ar da ta yi ba).
….
Sai chaan dare tukunna suka d’auki hanyar gida, bayan ya loda na lodawa ya kira wani driver d’insa ya naɗa shi a matsayin mai jagora, sun tafi kai kayan da za a kai gidan amarya…

Ta gaji lik’is, dan haka ta na gishingid’ewa bacci ya kwasheta.

Ahankali ya d’an tab’o Muhsin wanda suke ta hira da drivern dan har sun saba sosai kamar wasu sa’anni, sai da ya juyo tukunna Yash ya d’aura yatsarshi akan bakinsa alamun su yi shiru kar su tasheta…

jinjina kai Muhsin yayi ya juya yana murmushi, bai gama sanin meye so ba amman yana jin dad’in yadda ya Yash ya damu da Addar su,
shima drivern ya gani kuma ya fahimci mai Yash yake nufi shiyasa ya yi shiruu ya bada himma a tuk’in da yake yi.

A hankali kamar mai shirin d’aukar cracked egg haka Yash ya d’auki wata suite d’insa dake a cikin jakar kujerar driver ta baya, ya d’an matsa kusa da ita kad’an ya lullub’a mata dan ya lura ba ta son sanyin.

Manu bata da nauyin bacci
shiyasa yana rufa mata ta farka, amma ba ta bud’e idanunta ba…ta ji dad’i a ranta, duba da yadda yanzun suka gama fad’a kuma yayi fushi da ita amma kalli yadda yake kula da ita, ba ta son yin fad’a da shi amma ta lura idan ba hakan ta yi masa ba to ba zai hak’ura ba, ba kuma zai bar maganar ba!. Saboda Allah ta ya dan su Baba sun aura masa ita sai kuma kawai aga sun kwashe kaya su koma gidan da ya ce ya basu, a ganinta hakan ba dacewa bane ba, ta san sun zama family amman kuma idan suka yi haka ai sun sake da yawa, idan ma zai basu gida gaskiya ba yanzu ba besides ta san ma Baba ba zai tab’a yarda ba…

Tana wannan tunanin ta ji an yi
parking an kashe motar, ta na ji Muhsin ya yi musu sai da safe da godiya ya jidi laidojin gabansh ya fita, dan haka ta yi saurin bud’e idanunta dan ta lura ba shi da niyyar tashinta,dai-dai nan drivern ma ya fita kenan..da sauri tace’’mun gode, sai da safe” daga haka ta fara kokawa da shegiyar handle d’in da ta rasa dalilinta na k’in bud’uwa a koda yaushe idan ta ja.

Murmushi ya yi kafin ya ce ’’kar mu rabu muna fad’a mana, ai tunda kin nuna bakyaso ba zan sake yin maganar ba, amma ki yi tunani akai pls’’

Jinjina kai kawai ta yi, ta ci gaba da k’ok’arin bud’ewa…

Murmushi ya yi ya ce ’’ba fa za a bud’e k’ofar nan ba sai kin yi min murmushi.’’

Jin tayi shiru ya sanya cikin wata kalar kasalalliyar murya ya ce ’’kin san Allah zan yi miki cakulkuli’’

Sai da ta zabura sosai kamar ya riga ya yi mata cakulkulin ne, tukunna ta juyo kamar za ta fashe da kuka ta ce ’’dan Allah ka yi hak’uri, dare fa ya yi, ka bud’e min’’

Ganin yadda ta fara fita a haiyyacintane ya sanya ya fahimci kad’aicewar tasu ce ba ta so, dan haka tashi d’aya ya sa Hannu ta gaba ya bud’e mata sannan ya bud’e tashi k’ofar ya fice da niyyar zagayawa domin ya bud’e mata amman tuni ta yi wuff ta fice dai-dai shikuma ya zagayo, tashi d’aya ya ji ta sauk’e wata nannuyar ajiyar zuciya kamar wadda ta yi
y’ar tsere….
murmushi kawai ya yi, yana mamakin yadda daga sun zauna a mota iya su biyu duk ta bi ta gigice, a ranshi ya ce ’’Yarinya za ki yi bayani ne’’.

Duk taurin kanta kuwa sai da ta yi masa murmushin nan tukunna ya kyaleta.

Da shi da ita da driver suka yi jidon ragowar siyayyar da ya yi mata har soro, ya ajjiye mata,
yana sake mamakin gidan tukunna ya bata wata jaka mai d’an karen kyau ya ce ”invitation ne a ciki ta bawa su Baba, zai turo mata na waya ma sai ta tuttura, shi kam ba wanda bai riga ya turama a cikin friends d’insa ba”

Karb’a ta yi, ita dai har i yau ta kasa daima mamakin zumud’i irin na Yash, kafin yayi mata sallama
suka rabu yana jin kamar ya d’auke ta su koma.

Tabbas inda ace irin wata d’aya d’in nan aka saka aurensa da Manubiya tou da bai san ya zai yi ba kafin ta zo….wata kalar zazzafar k’aunace ta ke d’awainiya da shi…the more yana sake saninta yana sake shaƙuwa da ita the more k’aunar tata take sake dagargaza mishi lisaafi! tunani! da zuciya…..
Chapter 18 · 0% Book details