Sashe 134
Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Cikin tsananin jin tausayinsa Hajiya mama ta shiga Bashi baki tana cewa”kar ka damu ba komai…dukda ba haka na so ace ka yanke hukuncin da wuri cikin fushi ba, amma ba komai, inshaaAllah komai zai yi dai-dai,mai gaskiya shi ke da riba a ko da yaushe, inshaaAllah za su dawo gareka, za su gane gaskiya . mu dai namu addu’a!!”.
…..
Har sama su Yadira suka bisa, suka d’urkusa suka rik’e k’afafuwansa! suna kuka akan ‘ya yi hak’uri, ko babu aure a tsakanin shi da Mommy ya barta ta ci gaba da zama a gidan, ko a k’asa ne ya bata d’aki’
amma furr!! Daddy ya k’i yarda ya k’i amincewa, k’arshema a gaban su ya kira y’an sanda ya cewa ƴan sandan “su zo gidansa!”
Yana gaama wayar ya kallesu yace”Wallahi idan Mommy da Yassir ba su fice masa daga gida ba, har suka bari y’an sandan nan suka zo, to sai ya sa an tafi da su cell!”.
Kuka sosai Yaran suke yi suna magiya, amma Daddy sam ya k’i sauraronsu.
Hatta Ummi wadda suka zo suka tarar da ita tare da shi a d’akin sai da Yadira ta rik’e Hannunta tana kuka tana cewa “dan Allah ta saka baki, ta tayasu bashi hak’uri.”
Hakanan Ummin ta fara bawa Daddyn hak’uri itama dan sosai zuciyarta ta tab’u da al’amarin gwanin ban tausayi, ta san Mommy ba ta kirki amma ko dan Yasmeen da Yadira da ta tabbatar sun shiryu sosai tun kwanakin baya yanzu kuma suke irin wannan kukan ya kamata a ce an tausaya musu……
Sai dai fa duk wannan abun da suke yi ko a kwalar rigar Daddy, fad’a musu kawai yake yi yana sake maimaitawa “wallahi idan har suka bari y’an sanda suka zo to
sai sun tafi da su Mommy.!”
Suna cikin wannan halin Ya’isha ta kira su tace
“idan har za su bisu to su sauk’o, ita da Yasira suna k’asa suna jiransu!”
Dan ita dama tun lokacin da Yasira ta kira ta ta sanar mata ko yunk’urin lallab’a Daddyn ma ba ta yi ba, kuma wallahi ta gama sakawa a ranta sai ya nemesu ruwa a jallo!!!.
A b’angaren Yassir kuwa, yana chan side d’insa yana jiran azo a ce masa ai Mommy ta wankesa komai ya wuce, amma kawai sai ganin Yasira ya yi a hargitse, da kyar ta ɗan nutsu ta samu ta ita ce masa”Mommy ta suma, Ashe Daddy yanata sakinta ita ba ma ta sani ba, yanzu babu aure a tsakaninsu, sannan su Yasmeen suna chan suna ta lallab’ata Daddy amma ya k’i yarda su ci gaba da zama a gidan, ya ma kira y’an sanda ya ce ‘a zo a tafi da su(shi da Mommy)’.
Dan haka kawai ya taho su tafi gidan Mommy wanda ke a tudun Yola, Ya’isha ta kwaso keys, a samu a kira Likita Mommy ta farfad’o dan Yasmeen ta kasa yin komai kuka kawai take yi, idan ta farfad’o suka nutsu sai su san abun yi!.”
Da farko dafe kai Yassir ya yi da mugun k’arfi da hannuwansa duka biyun, kafin ya cika ya fara fatali yana fashe fashen da hattaHannuwan nasa duk sai da suka tsatstsage suna fidda jini!
Haushinsa Yasira take ji d’azu, amma har ga Allah zuwa yanzu duk sai ya bata tausayi, dan haka ta matsa ta rungume sa, wanda hakan ya sa ya fashe da wani Irin kuka ya sakar mata dukkannin nauyinsa suka zube suka durk’ushe a wajen duk su biyun suna kuka!!
Cikin wani irin kuka yace”Yasira ba laifina bane ba, Daddy ya fi fifita Yashjub ya bashi duk dukiyar family d’innan bayan kamata ya yi ace ni da shi munada equal right….”
Muryarsa ce ta sark’afe sakamokon kukan da ya ci k’arfinsa, dan haka ya sake sakinsa da mugun k’arfi…
Tabbas zuwa yanzu kam Yasira itama ta yarda ‘idan Yassir yanada mugun mugun laifi tou Daddy ne silar komai tun asalin farko! wallahi duk Daddy ne ya damalmala komai ya hargitsa komai! Saboda tsantsar kafiya da son kansa, sannan yanzu ma gashi yana shirin sake maimaita kuskuren da ya yi a farko a karo na biyu, tunda gashi saboda ba ya son mommyn ayanzu baya buƙatar zama da ita shiyasa ya zaɓi shi ya samawa zuciyarsa salama ta hanyar daina ganinta kwata kwata su kuma ya baƙanta musu rai..’
shiyasa tausayinsu ita da y’an uwan nata da Mommynsu ya sake lullub’eta, kawai sai ta kuma rushewa da wani kukan….
Sun jima a haka suna kuka kafin dakyar Yasira ta d’ago fuskarta tace”Yassir a situation d’innan da kake a ciki, kar ka bari ka shiga case da hukuma, kamar yadda ya fad’a gara ka tashi mu bar masa gida!
Tabbas abunda ka yi ba ka kyauta ba Yassir amma kar ka damu kana da mu!
Kana da y’an uwa tunda na fahimci pushing d’inka aka yi…ka taso mu tafi mu je mu fara ji da Mommy, a samu ta farfad’o sai a san abunyi…..”
Kamar wani k’armin Yaro hakanan ya shiga d’aga mata kai, dan a mugun tsorace yake bai saba shiga masifa da tashin hankali irin wannan ba…
abubuwansa masu mahimmanci kawai ya kwasa, daga nan ya rufo side d’in nasa suka nufi motocinsu.
Dai-dai nan Yusra ta sauk’o itama da akwatinta dan Yasmeen tace a nan ita za ta zauna.
tuni, Ya’isha da Junior sun saka Mommy a motar Ya’ishan, shiyasa tana ganin su ta kunna motar tata amma sai fitowar Kausar wadda ta hango a gigice ya sanya ta kashe motar ta fito.
…..
Da kyar suka sanya Kausar ta hak’ura da binsu, a cewarsu ‘ta zauna a nan ta zame musu ido a nan d’in kafin su dawo, sannan ta samu ta haihu a nan dan sai ya fiye mata tunda ga Yash ɗin ma nan ya dawo’.
inshaaAllah za su san abun yi! Akan duk wata matsala tasu, ta kwantar da hankalinta komai zai gyaru!
za su dinga waya suna communicating, kar ma ta soma binsu yanzu gudun kar Daddy ya samu damar korarta itama…..
Sun ci kuka sosai Yassir ma ce mata ya yi kawai za su yi waya, daga haka suka shige motocinsu suka fice daga gidan Yasmeen kuma wadda ba ta bisu ba ta kamo hannun Kausar d’in suka koma ciki dan ta yi nauyi sosai…duk su biyun suna kuka wiwi haka nan suka nufi cikin gidan…
Su Yadira kuma direct gidansu suka wuce dan kukan da take ta yi sosai ya d’agawa Junior hankali, Shiyasa ya hanata binsu ma saboda condition d’inta.
A tunanin Kausar Daddy zai koreta itama, amma sai ta ga ko kallonta bai yi ba..
hakanan ya wuce ta ya fita wajen y’an sandan da suka k’araso yanzun domin ya sallamesu, a ransa ya gama tsara’itama zai koreta ne amma sai ta haihu tukunna bayan sun karb’i d’an sun bawa Manubiya….’
Yashjub tun d’azu yake ta jin k’arar bud’e gate ana rufewa shiyasa hankalinsa ya sake tashi dan tashi d’aya kwakwalwarsa ta bashi Allah dai ya sa ba harda Mommy aka bar gidan ba.
……
Duk yadda suka yi tunanin abun zai yiu a gida gagara ya yi, dan bayan sun kai kayyakinsu, abun na mommy sai ya ci tura, har sai da suka danganata da asibiti tukunna ta farfad’o da kyar.!
Ai kuwa tana tari tana hawaye hankali a tashe kamar tab’abb’iya ta shiga tambayarsu “ya ake ciki? A ina take?”
Ya’isha ce ta iya yi mata bayani…
Aikuwa cikin masifa da tashin hankali ta rufe su ta fad’a tace “dan meyaasa suka yarda suka fitar da ita daga cikin gidan??..”
Sai kuma ta fashe da kuka ta fara jero Allah ya isa a Hajiya Mama da Manubiya dan sam batajin haushin Daddy kamar yadda takejin masifaffiyar tsanarsu a cikin ranta ba!
Hatta su Yasira ma sai da ta dasa musu matsananciyar tsanar su Abhi da Hajiya mama a cikin ransu bayan ta Manubiya da take zaune daram a ransu dama.
Duk yadda suka so su rarrashi mommy su bata baki sam abun ya gagara, gashi dama suma a wuya suke, shiyasa kawai suka fashe mata da kuka…ba ta damu da kukansu ba ballanta ta sarara musu, magana kawai take yi kamar tab’abb’iya kuma ta nace akan Itafa sai sun d’auketa sun mayar gidan Daddy dan Kwata Kwata jikinta babu kwari itan dan haka tama kasa tashi da kanta, shiyasa kawai Yassir ya juya ya fita ya je ya kira likita, yana zuwa ya yi mata allurar bacci da kyar dan sai da su Yassir suka danneta tukunna aka samu aka yi amma da sam ta k’i tsayawa.
Sosai Yassir yake jin tsanar Yashjub tana dad’a shigarsa, ga tsoro ga tashin hankali…
Suma su Yasira sun ji haushin rashin zuwan Yashjub d’in asibiti domin ya ga Mommy, matuk’a.
Sai chan dare tukunna Mommy ta farka…tashi d’aya komai ya dawo mata sabo wanda hakan ya sanya ta ji inama ba ta farka ba.
Ɗaya bayan ɗaya ta fara kallonsu tashin hankalin ta yana sake hauhawa sakamokon yadda ta ga fuskokinsu sharkaff da hawaye dagaje dagaje, kowa ta yi tagumi..
Yassir da Yassira kuma basa nan.
A d’an rikice ta tashi ta zauna ta kallesu tace “Ya’isha mai kuma ya faru??”
Sai a lokacin ma suka lura ashe ta farka, dan haka daga Ya’ishan har Yusra haka nan suka nufeta da sauri suka fad’a jikinta suka fashe da wani irin kuka.
Zuwa yanzu jikin Mommy har wani irin karkarwa yake yi!
A hankali ta zaro su daga jikinta k’irjinta yana dukan tara tara tace”ku fad’a mini menene kafin zuciyata ta buga”
Sai da ta sake tambayar su!ta maimaita!!ta daka musu tsawa a karo na uku! tukunna da kyar Yusra ta bud’e wayarta ta kai mata wajen hoton sannan ta mik’a mata tana wani irin kuka.
A hankali jiki na karkarwa Mommy ta saka hannu ta karb’a hoton…………..Babu idanuwa sannan an yanke nonuwa da private part da y’an yatsun k’afa da hannu amma hakan bai hanata gane Larai tashi d’aya ba.
Jifa ta yi da wayar a mugun tsorace sai kuma ta turesu ta mik’e ta d’aura Hannu a ka ta fasa wata razananniyar k’ara.