← Book details Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 152

Sashe 7

Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

‘’Good! Saboda gaskiya yau ba za ki fita daga d’akin nan ba
sai na san matsayina a cikin zuciyarki.
Inaso mu wuce
wannan stage ɗin mai ƙunshe da su kauda kai! Kasa kallona! Jin kunyata da kike yi, mu shiga next stage (mataki na gaba)
saboda in samu in dinga faiyyace miki yadda na ke ji game da ke!! Saboda feelings ɗin sun cika mini zuciya da gangar jikina dayawa.

Dan haka, ina sauraronki”

Shiruu ta yi, shima haka.
duk suna anan tsaye ba wanda ya sake cewa komai…
Manubiya ji ta yi inama ace ba ta zo ba, gashi kwata-kwata ya k’i ya daina kallonta dede da na second d’aya, gashi ya titsiyeta, shiyasa ta ji kamar ta fashe masa da kuka…….

Sun fi mintuna goma a haka,
sam tama k’i ta yarda ta kalli direction d’in shi ballantana ta fad’i masa abunda yake son ji d’in.

A hankali ta ji ya sauk’e ajiyar zuciya, kawai! Sai kuma ya koma ya nemi waje ya zauna akan gadon jinyar nasa.
“Na gode, ki gaida su Inna.
InshaaAllah zan zo in gaida ita da zarar na fita a nan.”
Ya fad’i hakan cikin kumbura fuska.

Duk kuma sai ta ji ba dad’i. Har za ta wuce ta fita, sai kuma ta tsaya kamar wadda ba ta son yin magana ta ce ’’Tun d’azu nake ta tambayar ka ya jiki baka ce komai ba, ya aka yi
hakan ta faru? Ya kuma hak’urin driver d’in ka’’

Numfashi ya fesar kafin ya ce ’’Jikina Alhamdulillah da sauk’i kafin ki zo!
Amman yanzu kam na san idan kika tafi kika barni a haka
akwai matsala.
Hak’uri da godiya, sannan tsautsayi da k’addara ne ya janyo hakan, sai mu yi adduar Allah ya kare gaba’’
Ya k’arashe maganar tasa yana mai zaro wayarshi daga cikin aljihu, ya fara daddanawa…
shi ala dole ya yi fushi da ita,
watakil in ta ga hakan ya san za ta yi masa yadda yake so.
Yana addua Allah yasa maganarta ta zama positive, dukda bashi da tantama akan itama tana sonshi, amma yana so ya ji ya tabbatar.

‘’Allah ya ji k’an musulmi, Allah ya baka lafiya, Allah ya kare gaba’’ tace da shi kamar yadda shima ya jero mata, kafin ahankali ta fara tafiya zuwaga k’ofar, zata fita.

D’an d’agowa ya ke yi yana satar kallonta yana kallon wayar tashi, ganin tana shirin ficewa ne ya sanya ya yi sauri ya mik’e ya ce ’’au, ba za ki tambayeni
me zai dawo min da ciwon nawa bayan kin tafi ba ko??”

Duk yadda ta so daurewa sai da murmushi mai had’e da y’ar siririyar dariya ya sub’uce mata, a ranta tace “Mutumin da ya had’e rai shi ala dole ya yi fushi yayi zuciya
amma kalli shine ya mik’e yanzu yake wannan batu.”

Sarai ya ji sautin murmushin nata, dan haka ya k’araso ya tsaya a gabanta ya ce ‘’Dariya ma kike yi min ko??’’
Ya fad’i hakan cikin b’ata fuska
kamar wani k’aramin Yaro.

Wani d’an siririn murmushi
wanda ya sanya Yash ya ji kamar zai suma ta saki kafin a hankali ta ce ’’na san mecece amsar da za ka ba ni, shiyasa ban tambaya ba’’

Cikin tarar numfashinta yace
‘’Mecece amsar??’’

Sai da ta d’an kalleshi kad’an tukunna ta sunkuyar da kanta ta ce ‘’Cewa za ka yi saboda ban fad’i abunda kake son ji ba, kuma ai na ga ma fushi ka yi da ni yanzun.’’

A hankali cikin yin k’asa da murya ya ce ‘’ni, na yi fushi dake??’’ bai jira jin amsartaba yace ‘’Never!’’
kafin ya d’aura da cewa “Kin san rashin amsar taki ce za ta k’aramin rashin lafiya, amma shine kika zab’i ki tafi ki barni a haka??
Saboda kin tsane ni, ko?.
Wannan sarkin nacin.’’
Yayi maganar yana nuna kanshi

Da sauri ta d’ago ta kalle sa tashi d’aya ta ce ‘’A’a’’

Dukda yadda ya ji sanyi a ranshi amma sai ya dake ya sake had’e fuska ya ce “to yaya ne?’’

‘’Ba sai na fad’a ba na san ka sani’’
Ta bashi amsar tana mamakin yadda sam ba ya gajiya da kallonta, tunda ta shigo cikin d’akin
ba ta jin ya d’auke idanunsa a kanta in ba lokacin da ya yi fushi ya d’auko waya ba, ita
har tsarguwa da wannan kallon nashi takeyi….kullum in suka had’u kamar ranar ya fara ganinta…

Muryarshi ce ta katseta jin yana cewa ‘’i’ll love to hear it (zan so in ji),
ba ki san taimakon da za ki yi min ba idan kika fad’a Manu’’
Kamar zai yi kuka yace “so plssssss’’ ya ja plss d’in sosai har cikin ranta sai da ta ji,tukunna ya ce
“Idan amsarki ‘Yes’ ne ina da buƙatar in ji kin faɗa min yanzu, ji kawai nake so in yi. Na garu dayawa, a tausaya min
haka mana…….’’

A hankali cikin tarar numfashinsa ya ji ta ce “Yes!’’

‘’Yes what?(eh me?)”
Ya yi mata tambayar yana kallonta yana murmushi
sosai.

Turo Baki ta yi, ta saka tafukan hannayenta ta rufe fuskarta da su tukunna ta yi ƙasa da kanta, dan kunya take ji sosai, sannan ta yi tunanin da ta basa amsar zai kyaleta ne amma ta ga alama wannan so yake su kai dare anan ana abu d’aya.

Yashjub kuwa tsabar murna ji
yake kamar ya zare Hannun sanna ya janyota jikinsa ya rungume.…..ahankali ya ce ’’ pls mana, kin ce min yess kawai kin barni,elaborate mana(ki min ƙarin bayai mana), sannan na ce fa bana son wannan sunkuyar da kan, a d’an rage wannan kunyar ta yi yawa fa…’’

Knocking ya ji an d’an yi dan haka da sauri ya juya ya murza key sannan ya juyo gareta ya ce ’’um..”
alamun ita yake sauraro.

Zaro idanu ta yi waje, kafin a rikice ta ce
‘’Dan Allah ka bud’e, wataƙilan su
Jidda ne suka dawo, har da Ya Musbah muke tafe, dan Allah ka bud’e kar su yi tunanin wani abun’’ Ta fad’i hakan ahankali k’asa-k’asa kamar wani zai jiyo ta sanann duk a rikice.

Ba k’aramin dariya ta basa ba ganin yadda duk ta tsure tashi d’aya, a ransa yace ‘’perfect(dai-dai kenan)”

Amman sai ya dake, ya wani mak’e kafad’a sannan ya ce ’’um um, ni kam ba zan bud’e ba’’
sai kuma ya d’an sake matsawa kusa da ita kafin ya ci gaba da cewa ’’har sai kin fad’a min komai yau,
tukunna, babu ruwana ko waye ya zo to ya jira Queen ce take zuba mulki da jan aji dan haka shima ta shafe sa.’’

Dai-dai nan aka sake yin wani knocking d’in, sai da ta d’an zabura kafin ta kalli k’ofar sannan ta kalleshi a gigice ta ce ‘’to me kake so in ce??
ko waye fa a bakin k’ofar nan na san ya ji lokacin da ka saka key, kuma yanzu kana bud’ewa sai a ganmu tsulum mu biyu kawai ka ga ai hakan babu dad’i, na riga na ce maka ‘yes’
ai, dan Allah ka bud’e k’ofar nan’’

Cikin tarar numfashi ta yace ‘’waye zai bud’e k’ofar?? Ai in gaya miki muna nan ni da ke har abada muddin ba ki bani amsata ba, bari ma kiga in zare key d’in in cilla shi ta window’’
Ya fad’i hakan yana mai juyawa

Da sauri tace ‘’ɗan tsaya to!’’

Sai da ya d’an yi y’ar guntuwar dariya tukunna ya juyo.

Kamar za ta fashe da kuka ta ce ‘’to me zan ce?’’

‘’Abinda yake a cikin zuciyarki game da ni’’ Ya ba ta amsar kanshi tsaye.

Kallon shi ta yi ahankali ta d’aga Kai ta ce ’’Yes….’’
sai kuma ta yi saurin sunkuyar da kanta ta ce ’’na ce maka yes tun d’azu…’’
ta fad’i hakan kamar za ta fashe da kuka, dan ita har ga Allah wallahi kunyar gaya masa complete abun kuma kai tsaye ido da ido take ji.

Juyawa kawai ta ga ya yi, ya zare key d’in.

Still kuma har yanzu anata faman knocking k’ofar

Da sauri ta ce ’’me kuma na sake yi?’’

Kallo ta ya yi kafin ya ce ’’Yess’’

Da d’an mamaki ta ce’’yes kuma?me kenan?’’

‘’Yauwa exactly my point, kinga kema ai ba ki gane ba ko?
Dan haka ya kamata ki fahimci nima ban gane me ‘yes’ d’in ki take nufi ba.
if you want to express yourself, all you have to say is
(Idan kina so ki gaya min abunda ya ke a cikin Zuciyarki game dani a dunƙule, iyakar abunda za ki ce shine) ‘i love you Yashjub’, ni har ga Allah banga abun wahala a y’an waennan kalmomin ba…’’

Knocking aka yi da k’arfi sosai wannan karon, Manubiya ba ta san lokacin da ta fara bubbuga k’afafunta ba kamar wata y’ar Yarinya tana cewa ‘’ni kam Allah A’a, dan Allah kawai ka bud’e’’.

Shagala yayi kawai yana kallonta, sai da suka suka had’a ido sai kuma ta tsaya chak! Tsabar kunya kasa ma cigaba da fuskantar sa ta yi dan haka sai ta yi saurin juyawa.

Murmushi ya yi da sauri ya ce ‘’a’a pls, kar ki daina, you look cute’’

Bugun da akayi da mugun k’arfi wannan karon ne yasanya ta juyo ta ce ’’dan Allah’’
Ta fad’i hakan hawaye suna
taruwa a kyawawan idanunta ai kuwa a take idanun nata suka fara kyalli
wanda hakan ya sake d’imauta Yash.
Chapter 7 · 0% Book details