Sashe 150
Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ba kad’an ba Ammi ta shiga shock! Ba na wasa ba….
A kanta ta ke ta juya maganar tana mamaki, a ranta ta ce ‘yanzu Yash d’in Manu shine asalin d’an Mama?!Tabbas a duk yadda ka ga mutum kar ka taɓa rainasa…Bata ci zarafin mama ba sannan bata wulak’antata ba tun bayan da ta fahimci Maman ba ta da interest a kan Mijinta amma dukda haka a take sai ta ji wata kalar kunya da nauyinta sun yi mata k’awanya.
Da kyar Hajiya Mama ta b’anb’are Yash daga jikin Mama, ta kamo hannunta, ta ja ta ta kaita gaban Daddy wanda ya yi mutuwar tsaye, sannan ta kamo hannunsa ta saka hannun Mama a ciki tukunna ta juya ta shige cikin parlourn da su Daddyn suka fito a ciki yanzun…Yashjub ne kawai ya tsaya tare da Mama da Daddy yayinda kowa ya bi bayan Hajiya Mama suka shige parlourn Baba
Tabbas inda ace Mama tana gidan Daddy tuntuni to su kansu su Yasira sun san da tuni sun daɗe da fahimtar ita ce Mahaifiyar Yash, dan tabbas suna kama..
Daddy kuwa la shakka ya ga kamannin tun ba yau ba, amma kuma cikin hukuncin Ubangiji sai bai bawa hakan mahimmanci ba ballantana har ta kaisa ga yin magana ko ya zargi wani abun, daɗin daɗawa kuma shi har ga Allah bai taɓa tunanin cewa mommy zata iya musanya Ƴaƴan ba, ko da wasa da ikon Allah sam hakan bai taɓa zuwa kansa ba..
Shiyasa ko da ya ga kamannin sai ya bari akan wataƙila zaman da suka yi tare ta yawaita kallonta ne ya janyo hakan ko kuma dai wata mu’ujizar ta ubangiji ce ta sanya Yash ɗin yake kama da Khadija ko kuma ma idanunsa ne su ke nuna masa hakan, tunda ya ga Hajiya mama da Abhi sam basu taɓa yin maganar ba suma, dan haka sai ya yi zato ko shi kaɗai ya ke ganin fisgen kamannin Yash ɗin Da Khadijahnsa…
…
Su Hajiya Mama suna shiga cikin parlourn Baki’in dai dai nan kamar gwaggwo Suwaiba ta san suna nan itama ta shigo, Inna na biye a bayanta.
Suna shigewa Daddy ya fashe da wani irin kuka, sai kuma ya durk’usa a gaban Mamaa yana kuka yama kasa yin magana…
A hankali ta durk’usa itama, tana hawaye da kyar ta iya cewa”sharri aka yi mi….”
Cikin tarar numfashi yace
Baki da buƙatar ki yi mini bayanin komai saboda Wallahi na dad’e da gane gaskiya, na dad’e da fahimtar cewa sharri ne aka yi miki…ki yi hak’uri ki yafemini abunda na yi miki, wallahi kunyar kallon kwayar idanunki nake yi, ban kyauta miki ba, bai kamata ace na yarda da sharrin da aka k’ulla miki ba, ki yi hak’uri, ki yafe mini, ki manta da komai, ki yarda da ni a karo na biyu, inshaaAllah ba zakiyi dana sani ba….”
Kuka duk su biyun sukeyi, Mama tana mamaki da al’ajabin Mommy, dan tunda Yahanasu ta ce mata itace silar komai shikenan gaba ɗaya ta tsorata da lamarin
d’an Adam! matar da a ko da yaushe take yi mata kamar zata goyata ashe ba sonta take yi ba……
A hankali Yashjub ya k’arasa, ya had’e iyayen nasa su biyu waje guda ya rungumesu…tabbas inda ace a gida d’aya ya rayu da Mama to da ba za a ɗauki lokaci mai tsawo ba kafin ya fahimci itace asalin mahaifiyarsa ta gaskiya! saboda iyaka so da k’aunar matar da yake ji suna ratsashi a halinda ake ciki da kuma yadda yake jinta a cikin jinin jikinsa kad’ai ma ya san sun isa su fahimtar da shi itace Mahaifiyarsa.
Sun jima a haka kafin Yash ya cikasu ya kalli Daddy yace”mun yafe maka Daddy, zamu baka second chance…”
Duk murmushi suka yi, daga nan suka shiga tambayarta Ina ta shige, ita kuma ta gaya musu komai tun barinta gidan Daddy har kawo yanzu….
Sosai suka sake girmama da Al’amarin Ubangiji
Ga ta dai tare da Manu, amma kalli sai da Ubangiji ya k’addara saduwarsu a yau tukunna suka had’u..dama shi Yash a ko da yaushe idan za su gaisa da ita ta waya ya kanji yanayinsa ya chanja, itama kuma Maman haka Ashe duk jini da asalin soyayyar tsakanin uwa da d’a ne dalilin abunda sukeji.
Sun jima kafin su shiga parlourn da suke ta jiyo koke-koke da murna yana fitowa daga cikinsa, dama shi Yash da Daddy duk sun san menene, Mama kuwa sai da ta kusan suma da suka yi idanu biyu ita da Inna dan haka ta tafi taje suka rungume juna cikin tsananin farin ciki.
nan kuwa murna ta zame musu biyu , farinciki shima ba a magana, musamman ma Yash wanda yake ta mak’ale da Mama duk inda ta zauna a nan shima zai zauna kamar wani d’an yaye……
Kabarin Ya’isha suka nufa daga nan wanda ke anan k’auyen su Inna, suka yi mata addu’a, kowa yana kuka cike da alhini.
sai dare tukunna suka dawo dama already Yash ya yi magana da y’an sanda, dan haka suna zuwa suka tarar da su a k’ofar gidan Mommy suna jiransu….Mama Manubiya Yahanasu da su Yadira k’in shiga suka yi, Daddy Hajiya Mama da Yash ne suka shiga har cikin gidan.
sai da suka damk’a Mommy a hannun y’an sanda suka tabbata an tafi da ita tukunna suka wuce gida rayukansu fess!.
Ba k’aramin dad’i Daddy ya ji ba da ya fahimci ba ta gani…ya san lokaci yayi da zata fara ganin masifu da bala’i reflection d’in abubuwan da ta shuka….
A Daren ranar aka sake d’aurawa Daddy da Mama aure…Daddy ya lura da yadda jikin Ummi duk ya yi sanyi matuk’a dan shi kansa ya san zumud’i da rawar kan da yake yi ba kad’an baneba.
Shiyasa ya sameta ya taushe ta sosai, kuma yace mata ta kwantar da Hankalinta itama yana sonta kuma ta kasance tare da shi a worst times na rayuwarsu dan haka iinshaaAllah ba zai tab’a juya mata baya ba…”.
Ya san ba zai tab’a had’a son Ummi da Khadija ba amma in sha Allah zai kamanta adalci wannan karon.
Sai a lokacin itama Ummi ta samu kwarin guiwa ta d’an sake, Mama kuwa dama tunda ta ga Ummi ta san matsayinta kuma sam bata ji haushi ko kishinta ba tunda dama ita hakan ba d’abiarta baceba.. nan ta rungumi Ummi itama Ummin haka suka rungumi juna zaman lafiya abun sai wanda ya gani!……
Sai bayan kwanaki uku tukunna y’an sanda suka tsinci gawar Kausar da Yassir! da taimakon wallet d’insa suka gano identity d’insa da gidansu…
Dama a lokacin da basu ga Kausar tare da Mommy ba tunaninsu basu ya yi tana tare da Yassir ai kuwa ilai…
Hannu bibbiyu su Daddy suka karb’i gawarwakin suka yi musu wanka aka yi musu sutura aka sallace aka mik’asu gidanjensu na gaskiya.
Yasira ce taje ta sanar da Mommy rasuwar tasu…aikuwa nan ta haukace jininta ya hau..gashi ta so ta d’an karkato hankalin
Yasirar wai ko ta samu wani by her side amma tun daga ranar ko
mai irin muryaar Yasira ba ta sake gani ba…ga ba ido ga rashin lafiya gashi ba ta da kowa shiyasa ta sake shiga cikin masifa.
Ana i saura kwanaki huɗu
appointment d’in Manu wanda Dr ya basu su cika, suka wuce Berlin
Lokaci yana ciki suka wuce asibitin, nan kuwa aka fara bincikata ciki da waje.
‘….da gaske mahaifarta ta tab’u kamar yadda Dr ya fad’a musu a Nigeria! due to maganin da ta sha, amma kuma za a iya treating d’inta ta samu ta haihu, sai dai ba lalle ta iya haihuwar sama da Yara biyar ba….’
Manu ta ji dad’in good news d’in Alhamdulillah, amma dukda haka sai da ta koka!…
…Astaghfirullah, amma a k’aiyyadewa Mutum haihuwa a ganinta hakan ma damuwa ce…..
Yash kuwa kamar ya zuba ruwa a k’asa ya sha, haka ya ji!!
hakanan ya yi ta jero hamdala ga Ubangiji subahanahu wata ala..
…Manu d’insa zata haihu, kuma har morethan 4 kids ma ai kuwa shi kam Alhamdulillah…
Ya san dai babu dad’i ace mutum yanada matsala kuma ga iya Ƴaƴan da zai iya Haifa, amma shi kam Alhamdulillah!!!Alhamdulillah!!!
….
Sosai ta samu cikakkiyar kulawa, sannan aka d’aurata a kan magani… Watannnin uku suka yi a Berlin suka juyo da d’an cikinta, cikin da su kansu basu san da shi ba sai da suka dawo Nigeria da sati d’aya tukunna ta fara ganin alamu, aikuwa tana gwadawa ta ga positive.
Sai da ta yi kuka ta godewa Allah ta yi sujjada, hankalinta ya ɗan dawo jikinta..tukunna ta fad’a wanka ta yi ta fito, ta chab’a kwalliya dan Yash ya kusan dawowa.
Dama ta gama girki dan haka ta jere girke girken da ta yi akan dining…..Gwaggo tana tafiya ta d’auko disposable plate mai murfi ta saka masa pt d’in a ciki akan tissue ta rufe ta ajjiye, kamar had’in baki dai dai nan ya turo k’ofa ya shigo…
Murmushi suka sakarwa juna, kafin ya ware Hannuwansa alamun ta zo garesa, kamar jira take yi kuwa ta tafi ta fad’a jikinsa ya mayarda hannuwan nasa ya k’ank’ameta yana mai sauk’e wata nannuyar ajiyar zuciya a baiyyane, a dai-dai saitin kunnenta yace”I love you!irin sosai d’inna!!!”
Dariya duk suka yi, sun jima a hakan kafin ta jasa zuwa dining d’in ta zaunar da shi..
Sai da ya sakar mata murmushi tukunna yace”yau kenan tun kafin in yi wanka za a bani abinci?”
Itama murmushin ta yi kafin tace”Inada surprise ne”
Wani irin kallo ya shiga yi mata yana murmushi kamar zai cinye ta, kafin yace”to bismillah,zuba mini.”
Waje ta nema ta zauna a kan cinyarsa ta zagaye wuyansa da hannayenta tukunna tace”special na girka maka…shi yana ciki, sannan ga kuma waenanna a kan dining…
A cikin kalmomi biyun da zan fad’a yanzu ka d’auki guda d’aya ‘Ni’ ko ‘Kai’”
Dariya ya yi sosai, har sai da kyawawan hak’oransa suka baiyyana kafin yace”abun game ne kenan?
yau babyna tab’ara take ji naga alama.
Shikenan ki gama taki nima zan yi tawa!”
Ya fad’i hakan yana mai kashe mata ido d’aya kafin ya sakata a jikinsa sosai tukunnan yace “na zab’e ki!”