← Book details Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 101 OF 152

Sashe 101

Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sun jima sosai a wajen, da kyar Hajiya Mama ta sa Daddy ya hak’ura da korar mommy, suka tsayar akan za su saka ido a kan Mommyn kuma su san yadda suka yi suka nunawa su Yasira abunda suke yi ba dai dai ne ba, a samu su dawo da su hanya….
Ba dan Hajiya Mama ce ta rok’esa ba wallahi da ba zai k’ara kwana d’aya da Mommy a cikin gidansa ba ! kuma sai ya wulak’antata ya k’ask’antar da ita, dukda ya san ba shi da tsayayyiyar hujja da zai nuna ya ce ita ta yiwa Khadija sharri sannan ita ta yi sanadiyyar zubewar cikin Manu, amma ya san itace, kuma shi kawai ba zai iya sake ci gaba da jurarta a cikin gidansa ba ya tsaneta!….
sai dai kuma abunda Hajiya Mama ta fad’a gaskiya ne, shiyasa da kyar ya aminta ya kuma zab’i su biyo mata ta yadda ta bi da su, dan ta hakan ne za su yi nasara a kanta…idan ya koreta yanzu bai rabata da su Yasira ba ai aikin banza kenan, kuma ya barta da gatan ta.
Shi kuma so yake yi ta wulak’anta ta shiga masifar da sai ta zab’i mutuwa akan rayuwa, sai ya rabata da duk wani kwanciyar hankali da jin dad’i kamar yadda ta yi masa.

A take a lokacin ya warware ragowar igiyar aurensa d’aya da ta yi saura a kanta, dama kwanaki tun farko da ta hana auren Yassir da Kausar ta taso masa da maganar Khadija ya sake ta ba tare da ya fad’a mata ba gudun ma kar ta tada masa hankali, ya bari a kan sai ta  fita daga idda tukunna zai sallameta,tausayinta ya ji ta kuma ci darajar y’ay’anta shiyasa kawai ya mayar da ita a wannan lokacin yanzu kuwa ya riga ya rufe ya gama babu sauran aure a tsakanin su shi da ita kuma sai ya zo korarta tukunna zai sanar mata ya dad’e ma da sakin nata.!…

Awa biyu su Inna suka yi, daga nan suka tafi ita da Muhsin suka bar Siyama, suna tafiya Yahanasu ta zo,itama tsoro da tsananin tashin hankali sun rufar mata, dan ita kam tana tsaka mai wuya ne a wannan al’amarin saboda itama Ummi tana gama gaya mata lissafinta da zarginta akan Mommy ya dira.

Ita ta zauna a wajen Manu ita da Hajiya Mama da Siyama,dan ita Hajiya Mama ma tace”a asibitin ma za ta kwana da Manubiya”

A chan gida kuwa, zuwan Kausar biyu side d’in Yash amma a rufe, gashi duk wayoyinsa a kashe, dan haka ta gayawa Yassir shi kuma yace”kar ta damu…gasunan zuwa idan suka zo dole zai bud’e, daga nan sai su san abun yi.

Bayan awanni uku!!…
Su Mommy ne suka fara dawowa sai
Ummi daga baya Daddy…babu kalar bugun da ba a yi wa Yashjub ba amma ya k’i bud’ewa.Najeeb ma ya zo shi da Yahanasu dan zuwa yanzu Manubiya ta farka kamar kuma kamar yadda ta yi bacci da sunansa a bakinta tana farkawa ma da sunansa ta fara.
Daddy ne ya je ya nemo spare key da kyar, ya samo ya zo ya bud’e k’ofar suka shiga, amma wani abun takaicin iyaka waiting parlour da corridor kawai suka tarar dan ya rufe k’ofar shiga da ma duk wasu k’ofofi.

Zuwa  yanzu sun fara tsorata, shiyasa Daddy ya ware murya ya shiga kwala masa kira….
Tun a bugun farko Yash ya ji su, duk kuma abunda suke yi yana jinsu, kuma ya saka a ransa ba zai kula kowa ba dan yana matuƙar buƙatar sarari….
Sun fi minti ashirin a wajen Daddy da Najeeb har ma da Yassir da Junior waenda suka zagaya ta baya saitin d’akinsa suna ta faman kwala masa kira!
Jin muryar Daddy har ta dashe yana kiransa yana haki da nishi su Najeeb kuma suna cewa bari kawai a nemo masu b’alle k’ofa ne ya sa kawai ya mik’e ba don ya so ba ya nufi k’asan.

Ta cikin glass door d’in suka hangosa ya taho, dan haka hankalinsu ya d’an kwanta, yana zuwa ya d’auki key d’in a jikin k’atoton frame d’in da ya mak’ala ya saka ya murza ya bud’e musu, daga haka ya koma cikin parlourn ya nemi guri ya zauna, dan bibbiyu yake gani..wani Irin mahaukacin jiri yake yi.

Jiki a salub’e hakanan suka shigo suka nemi guri suka zazzauna.
Kasa magana duk suka yi, kowa ya yi shiru suna mamakin yadda ya rame tashi d’aya fuskarsa ta yi jazir ya yi wujuga-wujuga.
Yahanasu ce tace”Yash bawa fa baya wuce k’addararsa,duk abunda kaga bai zama naka ba it wasn’t yours to begin with! (Dama chan ba nakan bane ba).
Allahn da ya baka ya karba, shi zai mayar maka da mafi alkhairi, kar ka azabtar da kanka, ka rungumi k’addara mana! Ka daure kar ka karaya, ita ma Manubiya tana da buk’atarka, a gareka ne za ta samu support da kwarin guiwa….idan har kai ɗin ka karaya haka shin ta ina zaka fara bata support ka kwantar mata da nata hankalin??”

Ga mamakinsu kawai sai suka ga hawaye sun shiga sintiri a kan fuskarsa babu k’akk’autawa, abunda dayawansu ba su tab’a gani ba, dan haka suka shiga al’ajabi!!
Mommy kuwa kamar ta zuba ruwa a k’asa ta sha ita da Baba larai, cikin jan hanci da share fuskarsa da tafin hannunsa ya juya ya kalli Daddy yace”Daddy Ina buƙatar sarari…i want to be alone!dan Allah.”
Ajiyar zuciya Daddy ya sauk’e, shi kad’ai ya san me yake ji, ji yake yi kamar ya yi super ya damk’i wuyan Mommy har sai ya ga ta daina numfashi.
Cikin jinjina kai yace”okay Yash,amma kar ka sake kulle k’ofofin ka.”
Daga haka ya d’an yi tapping kafad’arsa tukunna ya mik’e yace”kowa ya fito”
ba tare da ya yarda ya kalli saitin inda Mommy take ba, daga haka ya sa kai ya fice.

Haka nan duk suka fita ɗaya bayan ɗaya, aka bar Yashjub Najeeb sai Yahanasu, Yusra da Yadira tun kafin a je koina har sun fara dana sanin abunda suka aikata, dan basu yi tunannin d’an uwan nasu zai shiga wannan halin ba,a tunaninsu kawai zai sake ta ne ta tafi shikenan a wuce gurin! Sam ba su yi tunanin zai tsaya yana azabtar da kansa har haka ba, su sai yanzun ne ma kwakwalwarsu ta yi lissafin tabbas fa zai shiga damuwa da tashin hankali, dan a yadda yake son Manubiya dole ya shiga masifa idan aka ce ta ci amanarsa…..sannan! Bai kamata ace su ji suna jin tausayinta ba amma yadda suka ganta a asibitin a kwance rai a hannun Allah ga ciki ya zube haka nan sai ta basu tausayi, shiyasa gaba d’aya suka shiga wani yanayi har sai da su Mommy suka lura.
Ya’isha kam ko a jikinta, daddana wayarta ma take yi tana bawa Yassira wadda take office update dan ita da Yasmeen ne kawai babu a wajen, sun tafi aiki.
Tana gama tura mata ta ja ta tsaya, jiran fitowar Najeeb, su kuma suka wuce.

Suna gama fita Najeeb ya k’arasa ya murza key ya dawo ya zauna a kusa da shi, cikin tattausan lafazi yace”Yash akwai wata matsalar ta daban ne?”
Ya yi masa tambayar, yana mai kafe sa da ido.
d’agowa shima Yashjub d’in ya yi, ya zuba masa shanyayyun kuma rinannun idanunsa kafin yace”Najeeb tunda nake a rayuwata ban tab’a kwallafa rai akan abu, kamar yadda na kwallafa akan Manubiya da Babyn da na rasa a yau ba,a ganinka hakan bai Isa ya jefa ni a damuwa ba?”

Numfashi Najeeb ya sauk’e kafin yace”sorry for your lost Yash, Allah ya sa mai ceto ne, ya baka masu albarka.”
Sai kuma ya sake fesar da numfashi kafin yace
“Yashjub baka tab’a b’oye mini komai ba sai yau, dan tabbas na san bayaga b’arin da Manu ta yi akwai wani abun da yake damunka, saboda Yashjub d’in da na sani ba zai bar Manubiya a asibiti ita kad’ai a wannan lokaci da tafi buk’atar sa ba.”

Runtse idanuwa Yashjub ya yi, ba tare da ya bud’e ba yace”Najeeb ka je kawai,kaina ya na ciwo, ina da buk’atar kasancewa ni d’aya!”

Cikin d’an b’acin rai Yahansu tace”Yash amma ka bani mamaki matuk’a!dan inda ace wani ne ya gaya mini cewa ka hau ka zauna akan abunda Doctor ya gaya maka wallahi ba zan yarda ba.”
Da sauri ya mik’e tsaye yace”Yaha plssss.Not now!”
Ya fad’i hakan cikin d’an b’acin rai.
Itama cikin b’acin rai tace”yanzu zamu yi Yash!yanzu za mu yi saboda yanzu nake so in tabbatar kaine kuwa ko ko dai wani ne mai kama da kai ya zo mana, dan Yash d’in da na sani ba zai yarda da k’azafin da Likita ya yi ba.”

Cikin rashin fahimta Najeeb yace”Yahanasu me kike cewa?me kike nufi?, kun bar ni a duhu.”
Sai da ta gama zabgawa Yash harara, dan ji take yi kamar ta rufesa da duka,tukunna ta juya ga Najeeb tace”Nima d’azu Ummi take gaya mini,Doctor d’in cewa ya yi maganin zubar da ciki ta yi ta sha har cikin ya zube.”

Da sauri Yash ya lumshe idanuwansa, ya koma ya zauna dab’asss! a kan kujerar, yana jin kansa yana wani irin juyawa, dan Yahansu tana fara maganar ya ji komai ya dawo masa sabo, ciwon da zafin da zuciya da kwakwalwarsa sukeyi sun sake hauhawa.

Cikin rashin jin dad’i sannan a hankali Najeeb yace”kai kuma sai ka yarda da shi?”
Ya yi maganar yana kallon Yashjub.

Cikin tarar numfashinsa Yash ya kallesa yace”Nima ban sani ba!iyaka abunda zan iya fad’a kenan ‘nima ban sani ba’!”

“Ka yarda kenan!ka yarda mana, dan idan ba haka ba da baza ka shiga wannan halin ba! Da ba za ka k’i zuwa inda take ba, Yash wallahi ka bani mamaki.”
Cewar Yaha.

Kallonta ya yi zuciyarsa tana wani Irin tafarfasa yace”kin san me na gani?kin san me na ji?”

“Sai ka fad’a!”
Ta bashi amsa cikin takaici…

Tiryan tiryan ya shiga zaiyyano musu yadda suka yi da Abbakar a yau kafin ya je asibiti…..
Chapter 101 · 0% Book details