← Book details Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 152

Sashe 25

Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kaff layin su Manubiya har ma da makwaftan layin sai da aka san yau an kawo lefe, dan convoy d’insu Hajiya Mama sai da ya cika layin taff.

Suna zuwa Yahanasu ta kira Manubiya ta ce mata “ga su sunzo”
ita kuma Manubiya ta sanar da Ya Musbah, dama sun ji zuwan nasu.

Aisha da Jidda, aka tura suka yi musu iso zuwa parlourn su Siyama inda yake nan a gyare tsaf sai tashin k’amshi yake yi.

Manubiya tana zaune a d’akinsu, ta ji anata wucewa da kaya ana hada-hada shiyasa tashi d’aya jikinta ya yi sanyii, hakanan ta koma gefe ta rakub’e ta yi shiruuu, tana jin yadda gabanta yake ta fad’uwa.

Sai da suka gama shigewa tsaff, tukunna anty Umma ta zo kiran su inna da mama domin su je su gaisa da surukan nasu, inna ce ta samu ta je yayinda mama ta ce “sa had’u next time(a gaba), bari ta zauna da amaryar”
Su anty umma sun so ta je amma tace “ba komai,”dan haka suka fita suka barta ita da Manubiya wadda ta fara hawaye kad’an-kad’an…cikin rarrashi mama ta shiga lallab’ata had’e da nasihar zamantakewar aure mai ratsa jiki.

Ba mom ba hatta Ummi ta sha mamakin gidansu Manu, dan a tunaninsu Yarinyar y’ar manya ce, ba wai reni ko wani abun ba, kawai dai sun yi tunanin Yash ba zai zo nan ba, amman tunda nan d’in ya zab’a to Allah ya basu zaman lafiya, inshaaAllah su kuma za su so ta su rik’eta amana.

Hajiya Mama ma ba ta ji komai ba, sai ma sake ganin hankalin Yash da ta yi dan ta san tabbas tunda ya zo nan tou tarbiyya da hankali ya bi ba wai kyalkyalin duniya ba!,
Ai kuwa Inna tana zuwa ta tabbatar da hakan, dan ba kad’an ba kawaici da nutsuwar Matar suka sake tabbatar mata da hankalin Amaryar tasu.

Cikin mutunta juna da barkwanci suka bada lefe akwatuna goma sha biyu da su taburmi, carpets…da dai kayan al’ada.
Su kuma su inna suka basu tukuicin naira dubu d’ari da hamsin suna ta jin kunya amman yadda Yahanasu ta sa Hannu ta karb’a cikin mutunci da karamci da kamala ne ya sanya suka d’an ji sanyi, dan su kansu sun san d’ari da hamsin ya yi kad’an a wannan uban kayan da suka cika musu gida da shi.

Hajiya Mama ta so a kira mata Manu su d’an gaisa, amman kuma yadda parlourn ya cika taff da jama’a ake jan numfashi da kyar ne ya sanya ta hak’ura, dan makwafta har sun fara shigowa….shiyasa suka yi musu sallama tare da fatan alkhairi bayan sun ce ”rana ita yau by this time ( i war hakan) inshaaAllah za su dawo su d’auki amaryarsu.

Hakanan aka rabu cikin mutunta juna, yayinda su Siyama Jidda da Aisha da Muhsin su ka yi musu rakiya da tray tray na pepper chicken, daughnuts, chin chin, meatpie, cakes da drinks…

Tunda suka zo ya yi parking ya kashe motar ya fara addu’a ‘Allah Ubangiji ya sa yau ma ya ganta….’
Indai ya samu suka had’u yau ɗin kuwa to sai ya karb’i numberta, shi kad’ai ya san wahalar da ya sha a cikin watannni ukun nan, da tunanin ta yake kwana yake tashi. Kunyar Yashjub ya ke ji shiyasa ya gagara ce masa ya karb’a masa numberta a wajen Manubiya……

BULAMA ✍️
0903 441 3252
*MANNUBIYA*
*Book 2*
*page 13*

Tunda suka zo ya yi parking ya kashe motar ya fara addu’a ‘Allah Ubangiji ya sa yau ma ya ganta….’
Indai ya samu suka had’u yau ɗin kuwa to sai ya karb’i numberta, shi kad’ai ya san wahalar da ya sha a cikin watannni ukun nan, da tunanin ta yake kwana yake tashi. Kunyar Yashjub ya ke ji shiyasa ya gagara ce masa ya karb’a masa numberta a wajen Manubiya……

Yana cikin wannan tunanin ya ga sun fito ita da Jidda rirriƙe da trays na gifts, da sauri ya yi wuff ya fice gudun kar ma su nufi wata motar da ba ta shi ba. Yana fita suka hangoshi kuma sun gane sa Abokin Yash ne shiyasa suka nefesa da niyyar gaidashi sannan su saka gifts d’in a cikin motarsa.

Kafin su k’arasa su Hajiya Mama suka fito kare da waya a kunnenta, wadda tun a kallo d’aya in aka yi mata za a fahimci tana cikin tsananin tashin hankali…
Da sauri duk d’insu suka nufi Najeeb ɗin dai-dai suma su Siyama sun iso kenan.

Da sauri mom ta ce ”Najeeb! Hurry up and call Yash, ku fara nema mana flight za mu wuce, Na’ima ta yi accident!”

Ta fad’i hakan a lokaci guda tana dialing number Abhi, kafin ta kara wayar a kunnenta.
Da sauri su kuma duk suka ce”subahanallah!” A gigice.

Tukunna ba tare da ɓata lokaci ba Najeeb ɗin ya zaro waya ya fara k’ok’arin kiran Yash, tukunna ya juya ya bud’ewa su Siyama gidan baya suka ajjiye gifts d’in….

Cikin rashin jin dad’i su Aisha suka shiga yi musu jaje, dukda ba su san wacecen Na’iman ba, tare da add’uar Allah ya kare gaba.

Sai da suka ga tashin motocin nasu tukunna suka juya suka nufi cikin gidan.

Already su Hajiya Mama suna da visa d’insu a Hannu shiyasa suka ci sa’ar samun flight dan a ranar suka samu na dare. K’arfe 3:00am daidai jirginsu ya d’aga gaba d’ayansu har da Abhi suka wuce uk.

Su Yasira ba k’aramin dad’i suka ji ba dan ko ba komai sun san sun rage zafi, Ummi kuwa kamar za ta yi kuka…ta so ta bi su amman kuma in aka ce itama sai an nema mata visa tukunna za su tafi to za ta b’ata musu lokaci, shiyasa ta hak’ura akan inshaaAllah za ta je ta ga jikin Na’iman in an shirya mata komai.
…
Mommy ce ta zauna a asibiti tare da Kausar, dan suna zuwa aka basu gado sakamokon jininta da suka ga ya yi mahaukacin hawa.

12:00am daidai Kausar d’in ta farka lokacin duk su Yassira sun tafi, tunda ta farka kuwa sam ta k’i yarda ko da had’a idanu ne ta yi da Mommyn,babu kalar rarrashin da Mommy ba ta yi mata ba amma ta k’i kulata, hakanan ta hak’ura ta mik’e ta fita ta je ta kira Dr aka zo aka shiga dubata.

Ko bayan fitar Dr d’in ma Mommy ci gaba da rarrashin Kausar ɗin ta yi amman ko arzik’in kallo ba ta samu daga gareta ba.

Suna zaune a haka kira ya shigo wayar Mommy, ganin sunan me kiran nata ne ya sanya ta saurin d’auka cike da
mamaki dan lokacin 2:00 ya wuce ma, a hankali ta ce ”Yasira, har yanzu ba ku yi bacci ba?”

Cike da farin ciki Yasirar tace mata”Hajiya Mama sun wuce, yanzun Yash ya tafi kai su airport gaba d’ayansu”.

Sai da Mommy ta tashi tsaye dan ba kad’an ba ta ji dad’in zancen Yassirar, tukunna tace”haka kurum suka tafi,Ina Larai?bata wayar….”

Sun jima sosai suna magana da Baba Larai….tukunna suka yi sallama, ta kashe wayar tana jin wani sanyi yana ratsata a ranta ta ce ”inshaaAllah daga yanzu mun fara samun nasara akan duk wani mak’iyinmu kenan, da izinin Allah.”

Ajiyar zuciya ta sauk’e tukunna ta koma kusa da Kausar ta zauna akan kujerar da ke kallonta, cikin kamo Hannunta ta fara magana “Kausar, a cikin kwana biyun nan da suka wuce kin b’ata min rai matuk’a, dan ban tab’a tunanin za ki gaya min abunda kika fad’a ba…duba da yadda na rufe idanuna na ke bin bayanki a ko Ina sannan akan komai.
Wallahi Allah Kausar yadda nake jin su Yassira haka nake jin ki a cikin zuciyata, kuma ko da ace su d’in ne a cikin situation d’in (halin) da kike ciki dole haka zan zuba idanu in hak’ura saboda babu yadda za mu yi.

Baba Larai ta yi iyakar bakin k’ok’arinta nima na yi amman abunda muke so d’in bai faru ba kuma tace ba ta da yadda zata yi, no way out(babu mafita), shin ya kike so mu yi?”
Ba ta jira jin amsarta ba ta d’aura da cewa”na fad’a miki zan kuma sake fad’a miki cewa ki yi hak’uri a yi auren nan!
Bayan auren inshaAllah da ni da ke da su Yassira da Baaba Larai za mu taru mu kwatar miki Yash, kuma na yi miki alk’awarin ba zan bari ki zauna da kishiya ba dan kafin ma ki shiga gidan na san ta dad’e da fita.
Amman fa idan kina so hakan ta faru dole sai kin kwantar da hankalinki kin nutsu kin yarda da mu an taru an yi abu d’aya tukunnan za mu taru mu taimaki juna.
Ban san me kike ji ba amman na san na fiki k’in auren nan, saboda ba ki san abunda auren ka iya janyomin ba shiyasa nake so ki yarda da ni saboda ko dan kai na ba zan tab’a barin Yarinyar nan ta yi lasting (ta daɗe) a gidan Yashjub ba dan zaman ta a tare da mu barazana ne ga duk wani farin ciki na da gata na.

Ahankali Kausar ta share hawayen ta tukunna tace”inshaaAllah Mommy zan yi yadda kike so.Sannan ki yi hak’uri da abunda na fad’a miki b’acin raine ya janyo hakan, ba zan sake ba.”

Wani sanyi ne ya lullub’e Mommy tashi d’aya ta mik’e ta koma kan gadon ta yi hugging Kausar tace”that’s my girl….”
Daga nan ta ci gaba da kwantar mata da hankali tana yi mata nuni da yadda suka fara samun galaba a kan Yash gashi Hajiya mama itama ta tafi, ta yi hak’uri ta bi komai a hankali za su yi nasara bi’izinillahi.
Chapter 25 · 0% Book details