← Book details Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 74 OF 152

Sashe 74

Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

…Already dama sun riga sun gama had’a plan d’insu, shiyasa suna gama wayar su Baba Larai suka yi sauri suka bawa Yusran ledar allurorin da su Yasira suka je suka siyo, ta karb’a ta sauk’o ta nufi d’akin Yahanasu da shi….

Ita dai Mannubiya ta yi shiruuu tana ta istighfari a cikin ranta dan lokacin da Yasmeen tace ‘bata da ciki!’ kad’an ya rage ba ta yi sab’o ba….haka shima Yashjub ya yi shiruuu ransa a mugun dagule….yayinda Yasmeen take jin inama akwai wani waje da za ta gudu ta b’uya dan wallahi har ga Allah ba ta son yin allurar! Ba ta son ta kashewa Yashjub Baby!..

Ta kasa yarda da cewa ‘wai yau itace take shirin yin kisan kai, kisan kan ma kuma Babyn yayanta.!’.

Suna a haka Yusra ta yi sallama ta shigo, ta mik’awa Yasmeen laidar allurorin.

BULAMA ✍️
0903 441 3252
*MANNUBIYA*
*Book 2*
*page 28*

Yahanasu tana fita, ta nufi sama side d’in Daddy…dan wallahi sai dai fa a yi ta! A cikin gidan nan, amma ba za ta bari Yasmeen ta d’irkawa Mannubiya allura ba tare da an tsaya Likitan kwarai ya zo ya dubata ba!…
Ya za’ayi mace tana irin wannan aman ga jiri ga fever sannan kuma Amarya amma tace wani ‘ba ta da ciki!’
Ta san ba ta yi aure ba, kuma bata da sani akan wannan fannin amma tanada shekaru da hankalin da zata iya banbance Mace mai ciki da mara ciki.
In banda tsabar rainin wayo a ta ina aka tab’a tabbatar da ciki da rashin sa ba tare da an yi test na jini ko na fitsari ba!…

Babu b’oye-b’oye tana zuwa ta cewa Daddy “ga Yasmeen chan za ta yi wa Mannubiya allurar tsaida amai ba tare da ta duba ta ko ta bari Likitan da aka kira ya zo ya dubata ba.!!
Kuma allurar tana da k’arfi sosai!ba a cika son yin ta kai tsaye ba”.

Shiruu Daddy ya yi, kafin ya mik’e ya ce “mu je wajen nasu.”

Kusan a tare Daddy suka k’arasa bakin k’ofar shi da Mommy wadda duk yadda ta so yin fushi ta bar Yasira ta yi dealing da Yasmeen sam ta kasa hak’ura sai da ta sak’k’o a yi komai a gaban idanunta.
Tun ba ma da Yasmeen d’in ta kira Yusra tana cewa ta kawo mata ledar ba dan a lokacin sai da Mommyn tasa Yusra ta tambayeta tace “akwai?”
Ita kuma tace mata ‘yeah’kawai ba tare da ta bari su Yashjub d’in sun gane ba.
Shiyasa sam ta gagara sukuni ta sake burkicewa ta sauk’o ta nufi d’akin Yahansun a gigice, a hakan ma wai Baaba Larai ta ce mata ta nutsu ta ɗan saisaita kanta…

Su Daddy suna shiga itama ta shige
dai-dai Yasmeen tana shirin zurmuk’awa Manubiya allura a cinyar Hannu.

D’an dakatawa ta yi, ta tsaya kawai tana kallon su
Suna had’a ido da Daddy yace
‘’Yasmeen an yi duk wasu gwaje-gwaje da suka kamata ne???
Ku je asibiti a yi test har na jini mana’’
Wani kalar kallo Yassira ta shiga jifan Yahanasu da shi dan ta san ita ta je ta kirawo Daddy.
Mommy kuwa ta fi jin haushin Yasmeen! Ji takeyi kamar ta je ta rufe ta da mahaukacin duka! dan in da ba ta tsaya delay ba da tuni tun ɗazu komai ya kammala.
Sannan yanzun da ta ga sun shigo tunda har ta riga ta kai allurar kan cinyar Hannun Manubiyan meye nata na wani tsayawa ta d’ago maimakon kawai ta soka ta juye mata ruwan allurar..dama chan ba ta son yi ai shiyasa ta lalata musu komai!…
Har wani duhu-duhu take gani tsabar tashin hankali, ganin bakin Yasira take yi yana motsi alamar tana yi wa Daddy magana amman ba ta san ma mai take fad’a ba dan ba ta jin komai tsabar masifar da ta shiga.
Tana k’ok’arin ta bud’e Baki ta san dabarar da za ta yi su samu Daddy ya bari su yi allurar cikin sauk’i ta ji muryar Yash yana cewa
‘’Ok,d’an bani 2 minutes,’’ sai da ta kalle sa tukunna ta fahimci waya yake yi….
sai da ya ajjiye wayar tukunna ya kalli Daddy yace‘’Am Daddy family Dr ya zo,
Ince ya bari shikenan tunda kace asibiti za’aje ko?’’

‘’No, bar shi ya shigo d’in kawai, tunda ya riga ya zo. Ya’isha je ki shigo da shi.
Idan ya tafi sai a wuce asibitin, ba dad’i ka kirawo babban mutum ya baro aiki ya zo kuma a ce ya koma.’’

Wata kalar zufar da ta ketowa Mommy sai da Yahanasu ta ganta b’aro-b’aro a kan goshinta tsabar yawan ta.

Cikin in ina da rashin sanin tudun dafawa Mommyn tace
‘’Daddy nake ganin gara a ce ya tafi,
Namiji ne, bai kamata ya tab’a Matar aureba….”

“Ya’isha je ki shigo da shi mana!’’
Daddy ya fad’a da d’an k’arfi kamar ma bai san Mommyn tana magana ba, dan ya fara k’ulewa da ita!
Ya ga alama tana neman zarce gona da iri tun lokacin da ya goya mata baya a kan case d’in Yashjub da su Yasira ya bata goyon baya ita da su Yasira, ya ga alamar kamar so take ta dinga juyashi ya dinga biyeta akan komai….bayan shi ba wai bayanta ya bi ba ko a wanchan lokacin ma, kawai yana da nasa dalilin shiyasa….

Ganin har ya na shirin fita amma su basu da niyyar fita ne ya sa cikin kakkausar murya ya kalle su yace
“A bar Yahanasu, Manubiya, Yashjub da Yasmeen a d’akin kowa ya fito….jikin Mommy har karkarwa yake yi zuwa yanzu..
Ta riga ta san one more move daga gare ta to tsaf Daddy zai b’aro jirginta shiyasa kawai ta hak’ura ta yi kalmar shahada ta fice ta wuce sama d’akinta direct.

Ita dai Mannubiya ba da ban Daddy ne da kansa yace ‘a duba ta’ ba, to da babu abunda zai sa ta kuma tsayawa a duba ta, dan ba ta son ta sake ganin wani disappointment d’in a idananun Yashjub…

Su Daddy suna tsaye a parlourn Ya’isha ta shigo da Doctor, suna gama gaisawa da Daddy ta wuce da Doctor d’in ta kai sa har d’akin ta fito, itama ta nemi guri ta zauna hankalinta chaaa a tashe.

A Chan d’akin kuwa Dr yana shiga suka hau gaisawa da Yashjub, sai da ya kuma yi masa Allah ya sanya alkhairi tukunna cikin zolaya yace
‘’Ai ba wani abun tada hankali bane, amai is a normal thing a pregnancy, but bara dai in duba .”

Shiruu duk suka yi kafin ya fara shirin dubata…sai da ya kuma tambayar abubuwan da suke damunta da date na last period d’inta ya ji tukunna ya matsa kusa da ita ya hau aikinsa…
Kamar yadda Yasmeen ta ga alamun cikin a tattare da ita hakanan shima amma bai fad’a musu ba
Instead sai ya zaro pts a cikin box d’insa ya basu yace “gashi ta je ta gwada”

Cikin son fahimtar da shi Yashjub yace “Yasmeen fa ta duba ta yanzu, ba ciki ba ne”

Da d’an mamaki Dr d’in ya juya ya kalli Yasmeen kafin yace “da me kika duba ta??”

Dibi-dibi ta hau yi kafin tace ‘’ban ji a pulse d’inta ba, sannan na ga bp d’inta bai yi kamar na masu ciki ba”
Ta fad’i hakan tana addu’ar Allah ya sa kar ya haddasa mata case.
Sai da ya k’ura mata ido sosai
kafin cikin d’an b’acin rai yace ‘’Doctor Yasmeen kin san abunda kike yi kuwa?? A bp da pulse dama ake ganin ciki???
What else ki ka yi bayan BP d’in da kika gwada??”.
Cikin nemawa kanta mafita tace
‘’Duk na gigice ne saboda na ga tanata amai, I wasn’t myself shiyasa..gaba d’aya duk ta bani tausayi…”

Cikin fushi yace
‘’Really??!
Yanzu idan aka kawo miki family member d’inki in a critical condition (mummunan hali) Ashe ba za ki iya yin abunda ya kamata ba? Are u really this weak(har haka ki ke da rauni?)!!!”

Ahankali Manubiya ta d’an dafe kanta sakamokon sarawar da yake yi mata tace “wash!!!”
Sai da ya gama watsawa Yasmeen kallo tukunna ya juya ga su Yashjub ya shiga yi musu bayanin yadda za su yi amfani da pts d’in….

Suna wucewa cikin toilet d’in ya juya ga Yasmeen ya shiga yi mata fad’a had’e da yi mata nuni da abubuwan da ya kamata ta fara yi nan gaba idan an kawo mata patient a irin wannan halin..
Sannan yace “ta cire fargaba ta daina saurin giigicewe dan za ta jawa kanta problem ne kawai, saboda a gaskiya ko shi yau kam ta bashi kunya da mamaki maƙura!!!!”

Su Yashjub suna shiga toilet d’in Manubiya ta kalle sa tace
‘’Ko dai za mu ce masa mun yi kawai?
Ba na son gwadawa ni kam har ga Allah.’’
Ta fad’i hakan tana hard’e hannuwanta a k’irji.

A hankali Yashjub wanda ya samu hope da kwarin guiwa daga jin yadda Doctor d’in yace “Yasmeen ba ta gwada yadda ya kamata ba”ya matso kusa da ita yace
“Ki taimaka ki gwada! pls…for me?’’

Shiruu ta yi ta d’an sunkuyar da kanta k’asa tace “to ka fita”

Wata dariya yayi yace “Yarinya ba ki da wayo ashe….”

…Daki daki yadda aka nuna musu haka suka yi.
Dayake doctor d’in ya ce “idan sun gwada su ajjiye for five minutes saboda result d’in ya fito sosai”
Ya sa Yashjub ya karb’a ya ce bari ya kai kan window su jira time…..
Daga ita har shi gabansu fad’uwa kawai yake yi..
Haka nan ya nufi window da tsinken da niyyar ajjiyewa idanunsa a kai!
Kawai ya ga layi na biyu ya fara kamawa
Wani irin mahaukacin bugawa k’irjinsa yayi!!!
Da wani irin sauri ya juyo ya koma gareta ya tsaya a gabanta ya ma kasa magana kawai ya kafe abun da idanu yana ganin yadda layi na biyun yake kuma fitowa yana turuwa yana dad’a baiyyana.

Ganin yadda ya kad’u sannan ya mayar da ilahirin hankalinsa ga tsinken ne ya sa Manubiya matsowa tace ‘’mai kake kallo?’’k’irjinta yana d’an bugawa.
Chapter 74 · 0% Book details