Sashe 68
Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Ahankali yace”kar fa ki saka damuwa a ranki..
Ki yi hak’uri idan na d’aga miki hankali”
Girgiza kai kawai ta yi tace “ba komai”ta d’an yi murmushi daganan ta mik’e, shi kuma ya fad’a toilet domin yin wanka.
Har ya fito a yadda ya shiga ya barta hakan ya dawo ya tarar da mood d’in ta, shiyasa ya yi ta janta da wasa yana k’arfin halin ganin ta sake dan shima a damuwar yake,
Ya san it’s too soon amman yawanci ana samu da wuri ai.
A haka suka yi breakfast d’in kowa da abunda yake tunani kafin yace “ta zo su je su d’an kammala shirin tafiyar tasu, dan jibi suke so su wuce uk su duba jikin Na’ima su yi musu two weeks inshaaAllah daga nan sai su wuce Nigeria.
Ko da suka fita gajiya ga ciwon marar period d’in da take yi ne ya sa Yash ya dawo da ita, bayan ta gama duk abunda ya kamata, shi kuma ya koma.
Sai dare ya samu ya dawo
Washegari komai nasu ya kammala ta inda zasu bar Cyprus nan da kwana biyu.
A cikin kwana biyun nan saida Yashjub ya san yadda ya yi ya cire mata damuwa dan ya lura tunda ya yi maganar ciki hankalinta a tashe yake.
Ba wai dan hankalin nata ya kwanta ba ta sake ta ke walwala dan ta lura ba zai barta ba idan har ba ta sake d’in ba
Amman a chan k’asan zuciyarta tana da damuwa da ta duk’ufa gayawa Allah.
Tun daga nan zaman su ya dawo kamar farko suka koma wasai abunsu dan shima Yash d’in daurewa yayi sosai ya ke k’ok’ari wajen b’oye tasa damuwar.
A ranar tafiyarsu Manubiya ji ta yi kamar kar su tafi.Ta ji dad’in Cyprus kwarai ta ji dad’in gidan ta ji dad’in rayuwar da sukayi fiye da komai a rayuwarta, rayuwar da ta tabbata ko wacce mace idan ta samu za ta ji dad’i za ta yi alfahari da sannan zata ajjiye a kwakwalawarta har k’arshen rayuwarta.
dan tabbas rayuwa ce mai tsada mai dad’i da mutun bai Isa ya mance ba…
Da rana wajajen 2:34 british airways ya sauk’e su a Heathrow Airport London.
Suna fitowa Yashjub ya hango Junior ya nufosu yana murmushi, dan haka shima ya sake rik’e hannun Manubiya suka nufe sa.
Yana zuwa ya yi hugging Yashjub kafin ya juya ga Manubiya suka gaisa cikin girmama juna, daga nan suka nufi inda ya yi parking motarsa da su da waenda suka d’aukar musu luggage d’insu.
“Ga inda ake k’anin miji mai hankali”
Manubiya ta fad’i hakan a k’asan ranta.
A bakin wani babban gida mai d’ankaren kyau Junior ya tsayar da motar, ya danna horn
kafin mai gadi ya ja musu suka nufi ciki.
A bakin entrance na shiga babban parlourn gidan suka tarar da Hajiya mama tana jiran su….tunda Manubiya ta fito ta kafeta da ido ta shiga yaba Yarinyar a ranta, gata da nutsuwa dan tunda ta tunkaro ta kanta yake a k’asa kuma tana lure da yadda ta zame hannunta a cikin na Yashjub a hankali a time d’in da ta lura da ita.
Murmushi ta yi lokacin da suka k’araso, Manubiya tana shirin durk’usawa Hajiya mama ta yi sauri ta tarota ta sakata a jikinta ta rungume..
dai dai nan mom ma ta fito…haka itama ta yi hugging Manubiya cike da so sunata murna kamar za su maida ita ciki kafin su nufi cikin parlourn da ita!
Saida suka zazzauna tukunna Manubiya ta samu ta zamo daga kan kujerar ta gaida su da girmamawa
murmushi kawai sukayi suka amsa
kafin Hajiya mama ta d’aga Kai ta kalli Yashjub tace
“To fad’o mini a ka…yau kenan miskilancin ta kaina ya biyo”.
Da sauri Junior yace
“Inaaaaa!Hajiya mama ai this is a new B Yashjub fa”ya fad‘i hakan yana mai nuna Yash kafin ya d’aura da cewa”ai ya daina miskilanci yanzu,tunda fa muka taho yake zubawa sweetheart d’insa surutu, yana nuna mata wajaje da favorite places d’insa.
Love ya chanja shi ya koma mai surutu”
Dariya duk sukayi yayinda Yashjub ya d’an yi murmushi ya na mai sunkuyar da kai a ranshi kuwa shi kansa yana mamakin yadda soyayya ta chanja shi….
Sai da ya kuma yin wani murmushin mai cike da ma’anoni tukunna ya kalli Hajiya mama yace”Ba fa ki kulani ba.
A bakin k’ofa kika barni, kika ja hannun kishiyar ki ko ‘hi’ baku ce min ba daga ke har mom..”
Murmushi mom ta yi ta mik’e ta k’arasa ta je ta yi huggin nashi tace”welcome welcome”
Daga nan ya yarda ya bita ta zaunar da shi kusa da ita.
Lek’awa Hajiya mama ta yi ta rankwashe sa tace
“Da wani katoton kansa!wa za ka yi wa shagwab’a??”
Kwashewa da dariya Junior ya yi, dan haka Yashjub ya d’ago yana masa irin kallon ‘ka fa fita a idona’d’innan! wanda ya sa Junior d’in saurin gimtse dariyar tasa ya shiga yin ta k’asa k’asa sai kuma duk aka sa dariya
banda Yashjub wanda ya ke kallon Manubiya da kalar tausayin irin ‘har da ke ake mini dariya’ ɗinnan.
Masu abinci ne suka fara gabatar musu da kalolin dishes…
saida aka kaisu d’aki suka yi wanka suka yi sallah tukunna aka kaisu wajen Na’ima,jikin nata da sauk’i dan k’afar tata ta d’auko warkewa ma
Ba yabo ba fallasa ta amshi Manubiya har da y’ar tsokana,
daga nan aka fita parlourn har ita.
Suna zama Abhi ya shigo dan haka suka shiga gaida shi, ya ji dad’in ganin su kuwa dan haka aka zauna har da shi aka shiga hira…
Dakyar kuwa Manubiya ta samu ta iya cin abinci a cikinsu dan da har Yashjub ya d’auka zai kai mata d’aki da ya lura ba za ta iya ci a tsakiyar su ba amman sai Hajiya mama tace ya barri a bar ta ta saba ta sake da su ita batason wannan takurawa da ake kira da kunyar surukai…ta d’auketa kamar best friend d’inta.
Da wasa da dariya da raha haka suka dinga janta har ta samu ta d’an sake ta d’an ci abincin tana ta yaba kara da kirkin su
A ranta tace”inama ace sune family d’in Yashjub na Nigeria, da ta more…”
Gashi dai sunada komai amma da ta basu tsarabar Cyprus ba kad’an ba ta ga murna a fuskokinsu, nan ta sake tabbatarwa tabbas waennan sun san darajar d’an Adam.
Sosai take jin dad’in yadda Junior yake respecting ɗinta!
ba wai respect in the form of seniority ba no, respect ta yadda ko a kusa da ita baya zama kamar yadda Yassir yake yi, tsakanin ta da shi mutunta juna.
Hajiya mama kuwa da gaske take da tacewa Manubiya ta d’auke ta kamar babbar k’awarta dan janta ta ke yi a jiki suna hira sosai tun Manubiya tana nok’ewa har ta d’an sake dan Hajiya mama har labarin shagalin bikin ta ta bata tace “lokacin maman Mommy itace babbar k’awarta……..”
Kamar yau sukazo Uk sai gashi har sun yi two weeks gobe za su tafi tare da tarin alkhairin su Mom..
Tabbas Manubiya ta ji dad’in zama da su, ta ji d’adin yadda suka jata a jiki basu nuna kyama ko wani abu makamancin hakan ba
Dan har gaisawa da Inna da Baba sukayi a waya kuma yanzu haka ma sunada number Innar..
A bangaren mutumin nata kuwa, abun ba a cewa komai,
tana yin wanka ya ci gaba da honeymoon d’in sa babu kama Hannun Yaro dan shi ba ruwan sa da a inda suke sam bai damu da su Hajiya mama ba…
Haka nan ranar da za su tafi Hajiya mama da Mom suka had’awa Manubiyan goma ta arzik’i kayan alkhairi kala kala suna ji kamar kar su rabu da Yarinyar….Sai da Hajiya mama ta yi musu addu’o’i sosai tukunna suka yi musu rakiya compound d’in gidan Junior ya ja su ya kai su airport kamar yadda ya d’ukosu, suka tafi da kewar su da kuma tsammanin su dan Hajiya mama wadda tace “nan da sati biyu zatazo inshaaAllah”
saboda akwai aikin da Junior zai yi anan kano ɗin har na tsawon shekara d’aya, so za su taho tare da shi….”
K’arfe 2:00pm daidai jirginsu ya yi landing a Aminu kano international airport, Nigeria….
3 months ago…(watanni uku baya)
Da farko su Mommy b’oyewa Kausar batun tafiyar su Yashjub sukayi, dan sun san zata d’aga hankalinta…