Sashe 110
Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Side d’in Daddy ya je, ya tarar dasu su biyar shi Yahansu, Ummi, Hajiya Mama da Abhi sunata hira ana raha gwanin ban shaawa. yana shiga shima suka ja sa da hira duk yadda yake jin kunya da nauyin Daddy Yahanasu da Ummi sai da ya d’an ware aka yi hirar da shi..kafin a shiga bawa Ummi kwarin guiwa aka d’an kwantar mata da hankali tare da jaddada mata suna nan suna bincike za a nemo Munirat inshaaAllah…..
Ya jima sosai kafin ya mik’e yayi musu sallama ya tafi.
Yana sauk’owa daga stairs d’in Daddy ya hango Kausar da Yassir suna hawowa saman (tsakiya) daga chan k’asa.
Gefen fuskarta ta wajen idonta na dama har yanzu da y’ar guntuwar plasta ragowar ciwukan kuma sun fito rad’au!kasancewarta fara ya sa suka yi tambari ana hangota ake hangosu.
Bai tab’a ganinta da Hijab ba sai yau!
A take ya ji gaba d’aya ransa ya yi wani irin mugun b’aci, hankalansa ya tashi,
Duniyarsa ta tsaya chak!
Wani irin kallon tsana ya shiga binta da shi…magana take yiwa Yassir amma sai maganar tata ta tsaya sakamokon jikinta da ya bata kamar yana wajen ne…..
Da sauri ta d’ago ta kalli direction d’in da ta ga kamar inuwar mutum.
Sanye yake da kaftan
Nude colour, da baƙar hula, d’inkin ya yi masifar yi masa kyau…ya d’an rame amman ya k’ara haske, hancinsa ya k’ara tsayi sannan sumar sa ta d’an k’aru both fuskarsa da kansa wanda hakan ya sake fito da ainihin kyawunsa da kuma ramar da yayi..so da k’aunar Yasjub a jininta da ruhinta yake! ba ta ji akwai wata y’a mace da take yiwa wani namiji kwatankwacin k’aunar da take yi wa Yashjub,babu ita a kaff fad’in duniyar nan!.
kallonsa kawai take yi kamar wadda za ta had’iye shi ne, Yayinda shima yake jifanta da nasa kallon na tsantsar tsana da kyama..idanunta har ciccikowa suka yi tsabar tsantsar k’auna, a take ta shiga sauk’e ajiyar zuciya a jere a jere…
Sai a sannan ne Yassir ya gansa tsaye.
D’auke kai kawai yayi ya wuce gaba kafin yace mata
“Muje”
Ya fad’i hakan yana mai nufar side d’inta.
Har ta d’an d’aga k’afa zatayi gaba ta ji Yashjub yace
“Kausar!”.
Gaban tane ya bada wani dumm!!da mugun k’arfi,shauk’i da tsoro suka yi mata k’awanya kafin jikinta ya d’auki karkarwa a take.!
Kad’an ta d’an juya ta kalli saitin inda yake kawai ta ga ya nufota gadan-gadan!.
Tabbas sun shirya komai itada Yassir kuma ya tafi yadda suka tsara..yadda ya kamata, amma sai yanzu ta san ta yi kuskure
da ba su tanadi abunda za ta
fad’awa Yash a irin wannan lokacin ba.
Sannan ta san Yashjub yanada kwakwalwa, kuma ta san duk yadda ta yi k’ok’ari ta kawar da duk wani shakku dole akwai wani abu da zai d’an fahimta.Sam ba ta shiryawa wannan lokacin ba kawai ita idonta ya rufe, hankalinta ya fi karkata a kan ranar da abun ya faru..kawai ita
kowa ya yarda akwai abunda ya faru tsankaninsu…
Tana wannan tunanin ya k’araso daff da ita ya tsaya.
Yassir ma ya d’an tsorata,
dan ya lura da yanayin Yashjub d’in, da kuma kallon rashin yardar da ya ga yana yi wa Kausar tun d’azun…a hankali
ya matso yace masa
“Yash batada lafiya!daga asibiti muke,
Doctor ya bata pain reliever,
yace kuma ta huta sosai.”
“Wuce ka tafi side d’inka!”
Kawai ya ce, ba tare da ya kallesa ba.
Cije labb’ansa na k’asa ya yi, yana jin wani tsananin takaici da tsanar Yash d’in tana ratsashi….Cikin d’aci yace”Doctor yace ta huta saboda
dukan da ka yi mata ba na wasa bane, har yau bata gama warkewa ba….”
Ya fad’i hakan yana ji kamar ya rufesa da duka, a duk lokacin da ya tuna dukan da Yash ya yi mata kuma daɗin daɗawa a lokacin da aka yi dukan har dacikinsa a jikin Kausar ɗin, sai ya ji kamar ya yi hauka!.
D’agowa kawai Yash ya yi, ya zuba masa lumsasssun idanunsa waenda suka fara kad’awa sukayi ja kad’an.
Yanayin kallon da ya ga yana yi masa ne yasa ya fahimci akwai matsala idan ya biye sa, saboda shima a zuciye yake kamar yadda shima yake a zuciye, dan haka ya san idan ya ci gaba da tsayuwa za a yi b’arna, dan haka kawai ya juya fuuu ya nufi k’asa yana ji kamar zuciyarsa za ta tarwatse.
Kasa d’agowa tayi ta kalli Yash
bayan wucewar Yassir…duk
wani ƙarfin hali da tsaurin idonta yau sai ta nema ta rasa.Gaba d’aya ta rud’e ta rikice, har yanzu jikinta karkarwa yakeyi kad’an-kad’an.
Ji yake kamar ya rufeta da wani sabon dukan, amman sai ya danne zuciyarsa..babu alamun wasa ko tantama, a hankali yace”Inaso inji gaskiyar komai daga Bakinki.
Na farko ki gaya mini me kika bani na sha,na biyu inaso da Bakinki ki gaya mini cewar babu abunda ya faru tsakaninmu…Kausar kin san ni ba Yaro bane kuma da aurena dan haka na riga na fahimci komai…
Amma ina so in ji daga gareki, Ina so da bakinki ki fad’a mini komai!
kuma ki sani hakan shine zaman lafiyarki.”
A kaff cikin maganganunsa, inda yake cewa”kuma inada aure”ya fi komai d’aga mata hankali da b’ata mata rai dan tashi ɗaya wani sabon kishinsa ya dirar mata.
Wasu hawaye ya ga sun hau sintiri a kan farar fuskarta….
Ranta ya riga ya b’aci kishinsa ya fusatata shiyasa ta kai iya wuya ta k’ulu ta k’ule kuma ta riga ta fahimci tabbas fa idan ta bari ta yi laushi to kwab’arta za ta yi ruwa!
Dan haka ta dake ta murzawa idanunta toka ta sake matsowa daff da shi tukunna ta fara magana”Yash!!Ina sonka!
Ni kaina bansan yawa da adadin son da nake yi maka ba,
amman ko da ace sonka zai kashe ni ba zan tab’a aikata abunda kake tunanin na aikata ba!
Saboda na san ranka ba zai so ba, kuma ni a ko da yaushe farin cikin ka shine a saman komai na rayuwata.
Tayaya kake tunanin zan so ka ji kunya?Tayaya kake tunanin zan so Mommy ta ganmu bayan na san idan hakan ta faru zan rasa yardarta ne…
Tayaya kake tunanin zan fito a matsayin karuwa a idanunka bayan ni a ko da yaushe burina shine ‘in gyarru in shiryu’
ko Allah zai sa ka yarda da ni ka amince ka bani matsayin matarka!
I’m honored and happy for that night, amman wallahi Yash ka yarda da ni ba haka na so ba!
Babu yadda zan yi ne a wannan daren na yi ta ce maka a’a a’a! amma ba ka saurara mini ba, ni kaina na yi mamakin ka shiyasa nake tunanin watak’ilan a office asibiti ko wani gurin ne aka yi mixing drink d’inka ko aka shaka maka wani abun baka sani ba….
Dan wallahi tallahi nikam ban san komai ba, kuma ban yi maka komai ba.”
Cikin katseta yace
“Ni duk ba wannan na tambayeki ba!
Akwai abunda ya faru tsakanin mu ko babu??
Iyakar abunda na ke so in sani kenan ko kuma
ince in tabbatar daga bakin ki saboda tuni na riga na san komai.”
Ya k’arashe maganar tashi cikin tsananin b’acin rai.
Tabbas zuwa yanzu Kausar ta fahimci ta d’an fara yin galaba a kansa, kuma ta lura kamar bai fahimci komai ba kamar yadda yake ta ik’irari dan a maganganun da ya yi yanzu ya riga ya kwafsa, sannan kuma ta fahimci da ta yi maganar wannan rana ne ya fara burkicewa!
dan haka tashi d’aya ta san abunyi.A hankali ta matso kamar za ta shige jikinsa wanda hakan ya sa ya d’an ja baya yana watsa mata wani irin kallo..
Itanma shi take kallo ido cikin ido tace”Yash you really don’t remember anything??…da gaske baka iya tuna komai??”
Ba ta jira jin amsar shi ba tace”bari in tuna maka!”
Wasu maganganu da bayanai ta fara yi masa na rashin d’a’a da tarbiyya!…a cewarta wai duk shi ne ya aikata hakan a gareta a wannan ranar…
cikin tsananin tashin hankali ya sa Hannu da mugun sauri ya toshe mata Baki yana kallon cikin idanunta yace”ba ki da hankali,ba ki san nan hanyar wucewar Daddy ba ne??”
Sai kuma ya cikata da sauri, ya ture ta, tashi d’aya ya nufi hanyar stairs d’in da zai sada shi da k’asa…har ya juyo zai sake yi mata magana sai kuma kawai ya sauk’a jikinsa yana wani irin karkarwa kansa yana mugun sarawa…”Innalillahi wa inna ilaihirrajiun”
Ya shiga ambata…da ya sani da bai tunkari Kausar da wannan maganar ba, yana so ya sake sakawa zuciyarsa salama ta hanyar tabbatarwa kansa ba abunda ya faru tsakaninshi da ita amma maimakon hakan gashi ya tasowa kansa da tashin hankali..dan a kaff cikin maganganu da yanayin ta sam bai ga alamun rashin gaskiya ba.
Gaba d’aya hankalinsa ya tashi, ya sake duburcewa
dan d’an guntun hope d’in dayake dashi yanzu kam ya rasa shi, saboda ya gama tabbatarwa gaskiya Kausar take fad’i…shiysa ya zab’i zai rungumi wannan mummunar k’addarar ya yi k’ok’ari ya cinye jarabawarsa kawai, ba zai sake saka hope ko bincike ba……
Yana sauk’a da niyyar tafiya gida aka fara kiran sallah, dan haka ya nufi masallaci…tare suka yi sallar da su Daddy waenda ana idarwa suka tilasta masa ya bisu domin su yi lunch tare.
Daddy ya daina cin abinci a k’asa saboda Mommy, dan haka suna shiga suka wuce sama su uku, yayinda dinning area na k’asan ya cika da kowa da kowa saboda Ummi ma zuwa yanzu ta d’an ware da taimakon hope da kwantar da hankalin da Hajiya mama suke ta bata, shiyasa take d’an shiga mutane har da ita ake cin abinci.