← Book details Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 122 OF 152

Sashe 122

Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

……..
Najeeb Yashjub ya kira, ya ce masa “dan Allah ya zo yana da buk’atar ganinsa”.
Daga nan ya fara nema musu flight d’in Abuja kafin ya yi musu arranging barin k’asar gaba d’aya.
…
Komai na companies d’insa da ke a nan Nigeria Najeeb ɗin ya d’aura a kai, tukunna yace masa ”ya riƙe masa dan Allah, zai yi tafiya na tsawon wani lokacin, ya rik’e masa amana.”

Najeeb bai yi niyyar yi masa maganar ba, dan shi kansa kunyar abun da kuma tausayin Yash ɗin yake ji, amma kuma sai ya ga bai kamata ya b’oye masa cewar ya sani ba, dan haka cikin tsananin jin tausayin Abokin nasa ya dafa kafad’arsa tukunna yace
“ba a kanka aka fara ba! Komai ya yi zafi maganin sa Allah.”

D’an k’ura masa Ido Yash ya yi kafin ya d’auke kai ya fesar da iska yace”kai ma sun tura maka kenan!”

Jinjina Kai Najeeb ya yi ya ce ”a tare suka tura mana!
Na san ba za ka so ka zamo wanda zai fallasa abun har a kai ga kashe Yassir ba shiyasa na yi shiru ban yi maka maganar ba kawai!..
Haka suma masu bincike ban ce musu mun gano komai ba amma dai na ari Bakinka na ce musu mun zare hannunmu a binciken, sai dai kuma iyalan waenda aka karkashe a Estate d’in naka gaskiya sun kunno wuta sosai, dan bincike sosai suke yi! cewa ma ya yi ‘ko mu mun janye, yanzu haka sama da mutane ashirin ne tsaye tsayin daka a kan case d’in.’.”

A hankali Yashjub ya sunkuyar da kansa k’asa, ya yi shiruu kafin ya d’ago ya ja hanci yace
“kar ka gayawa kowa inda nake dan Allah…ba wai iyaka Yassir ne dalilin da ya sanya zan tafi ba”
Sai da ya yi shiru ya sake jan hanci tukunna yace”Yau su Daddy suka aura min Kausar….”
Dalla Dalla ya gayawa Najeeb bayanin komai da dalilinsa na k’in zama da Kausar…tashi d’aya Najeeb d’in ya goyi bayasa d’ari bisa d’ari.

Sai asubah tukunna suka gama shiryawa da had’a kan komai..

Kamar kar su rabu haka Yash da Najeeb su ke ji, Najeeb har da hawayensa dan mugun mugun tausayin Yash ɗin yakeji…
hakanan suka yi sallama daga haka driver ya d’auke su zuwa hotel bayan Yash ya damk’awa Najeeb makullan gidan ya ce masa ‘da safe ya kaiwa su Mommy’ dan ta ce za su kawo Kausar.
Dalilin ma da ya sanya ya k’i amincewa su zauna a cikin gidan kenan, gudun kar su ce za su kawo masa ita da safe.

Sai washegari da safe tukunna Ummi ta samu ƙarfin halin iya tunkarar Hajiya Mama…har ga Allah Hajiya Mama ta yi tunanin Ummi wasa take yi mata da farko, dan kwata-kwata ba ta tab’a tunanin su Daddy za su tafka wannan kwab’etar ba! daɗin daɗawa ba tare da sun shawarceta ba.
Sai da ta saka Ummi ta rantse mata tukunna ta yarda, Hankalinta a mugun tashe ranta a masifar b’ace ta kalli Ummi wadda ta fara dibi-dibin bata Baki tace”ke kanki kinsan babu ta inda za ki ce mini hakan ya dace ko?”

Shiruu Ummi ta yi, ta sunkuyar da kanta k’asa.

Ajiyar zuciya Hajiya Mama ta sauk’e kafin tace”to dan haka ki yi shiruu kawai, kar ma ki bawa kanki wahala.”
“Ina shi Yashjub d’in yake, ya sani??a gaban sa shima aka d’aura??”

A hankali Ummi tace”a’a..na dai kira na gaya masa nace ya zo a san abunyi, to dai tun jiyan bai zo ba yau kuma inata kiran wayarsa amma daga tashi har ta Manubiyan duk ba ya tafiya.”

Jinjina kai Hajiya Mama ta yi,fuskarta har ta yi jaaa!
Ta kalli Ummi tace”ki kirawomin su Imam d’in, ki ce na ce su zo yanzunnan!”

“Tam”Ummi tace, daga haka ta mik’e ta sa kai ta fice.

Ba’a yi mintuna goma ba, Daddy ya shigo da shirin tafiya office, Abhi wanda ke biye a bayansa kuma da jallabiya.
Ko gaisuwar su ba ta amsa ba, ta kalli Daddy ta ce ”ashe har kana iya tafiya office bayan masifar da ka k’ulla a gidanka jiya??”

A hankali ya sunkuyar da kansa k’asa yace”ki yi hkr Hajiya Mama, dama yanzu nake shirin shigowa mu tattauna kafin in wuce!”

Cikin fushi tace”Imam tattaunawa kuma ta nawa?
Sai da ka gama yanke decision da kai da munafuka!muguwa!!makirar matarka!!!!tukunna za ka zo ka ce mini za mu tattauna saboda ka raina ni??
Me za mu tattauna???.

Ina sauraronka gaya mini menene ya rage wanda ba ka riga ka yanke hukuncinsa ba da ya kamata ace mun tattauna?”

Shiruu ya yi, ya gagara cewa komai.
Cikin tsananin b’acin rai ta kallesu su duka biyun tace
“da ni da ku, duk mun shirya a kan za a sakawa Khadija ido, a bincike ta, a gano ta, sannan a nunawa Yaranta illarta da illar d’abiar da ta d’aurasu a kai tukunna a sallameta a cikin gidan nan!!
Amma saboda tsabar ku d’in ba jajurtattun maza bane ba, shine kuka bari a cikin awannin da basu wuce biyu ba Yarinya y’ar k’arama ‘Kausar’ da kuma Khadija suka juya muku tunani har kuka aurawa Yashjub Kausar!!!..
Daga ta yi y’ar drama da shirmenta shikenan har kun kamu??”

Da kyar Abhi ya iya cewa
“Hajiya mama cewa ta yi za ta tafi da Yaron. shi kuma Yashjub ko
Maganarmu ba ya ji, iyaka maganar Manubiya ya ke bi da farincikinta..a jiyan fa cewa ya yi wai sai abunda ta yanke tukunna shi za a yi”

Sakar Baki kawai Hajiya mama ta yi ta na kallonsa har ya dasa aya, tama kasa cewa komai.
Da kyar ta iya cewa”idan na fahimce ka, kishi kenan kuke yi da Manubiya kamar wasu mataa!!!shiyasa kuka aura masa Kausar saboda kar Manubiya ta yi dominating d’insa (ta mallakesa) ita kad’ai ko?”
“This is the dumbest thing
da na tab’a ji tunda uwata ta kawo
ni duniya wallahi tallahi!
Ina tunaninku ya tafi ina hankalinku ya tafi??
Kausar faaa!!”

Cikin son yi mata bayani Daddy yace”ai Kausar d’in ba fa wai mun aura masa ita forever bane, mun aura masa ita ne akan idan ta haihu sai su rabu”.

Mik’ewa kawai Hajiya mama ta yi, ta nufi wajen kayanta, ta fara fito dasu tana cewa”Bari
Ka ji in gaya maka,Indai Kausar ce to ba za ta tab’a rabuwa
da Yashjub ba, ba za ta yarda ba!.
Barr ganin wai da Yassir kuka santa,a yadda Khadija ta tsani Manubiya ba za ta bari Kausar ta bar Yashjub ba…
A tunanina auren ka da Khadija ya isheka ishara! ya Isa ka gane idan aka auresu ba sa fita,
tunda tun yaushe kake so ka saki Khadija ta saku???”
Ta yiwa Daddy wanda ya ƙaraso ya rik’e trollyn hannunta tambayar.

Ba ta jira jin amsar shi ba tace
“kuma saboda ku wawaye ne shine kuke tunanin Kausar za ta yarda a saketa?
Wai ma shin ina lissafinku ya tafi da Kausar d’in tace za ta tafi kuka biye mata har kuka yarda??
Khadija fa kad’ai sai Larai gareta a kaff fad’in duniyar nan, Wallahi ko ta tafi ƙarƙari ta yi wata biyu zuwa uku nasan ita da kanta za ta dawo, ko su su Larai d’in su nemota.
Kuma indai Khadija ita ta haifi Yashjub to ba zata bari Kausar ta b’ata masa suna ba, dan na san duk bakin su d’aya.

Abu simple!! very simple amma kuka gagara tsayawa ku yi lisssafi mai kyau sam, saboda an had’a da asiri da wayo!!!..
Saboda Allah kalli abunda kuka tafka!!
Ko
Shawara da ni bakuyi ba, kai da ake so a gyara gidanka a kub’utar da kai amma kalli yadda ka
sake damalmala komai!!!
dan ba ka isa ka ce ka rabu da Khadija ba muddin Kausar ce matar Yash…saboda ko ka kori Khadija a gidan nan indai Kausar tana a
matsayin Matar Yash wallahi ka yi ta banza ne…”

A hankali Abhi shima ya k’araso dan Daddy yana rik’e trollyn ta sakar masa ta cigaba da zaro kayayyakinta rai a tsananin b’aci tana magana tana had’a kaya…cikin lallami yace”Hajiya mama ki yi hak’uri dan Allah, mun yi laifi. wallahi ni
kaina sai yanzu na ke ganin rashin dacewar hakan.”

Juyawa ta yi ta kallesa tace”kad’an daga aikin Khadija!
Ai ba za ku san lokacin da kuka d’aura ba dama…”
Cikin chanja topic d’in tace”ka
fara yi mini shirye-shiryen tafiya, meanwhile ka kama mini d’aki a hotel kafin komai ya kammala dan wallahi na gama zaman cikin gidan nan!”

“Innalilla wa Ina ilaihirrajiun”
Daddy yace, kafin ya d’aura da cewa”Hajiya mama dan girman Allah ki yi hak’uri!!
ina cikin garin nan da gidana amma ace kina hotel!
dan Allah ki rufa mini asiri.
in dai har saboda Khadija ne to a yau za ta fita wallahi.”
Ya fad’i hakan kamar zai yi
kuka

Cikin b’acin rai tace”kar ka soma!!!ba zai you ka koreta saboda ni ba noMatter what!
sai dan halinta wanda na so in nuna maka ka runtse
Ido.
Ku zauna abunku kai da ita da surukarka, Allah ya kareka daga sharrinsu, zan dinga yi maka addu’a Ina daga chan…amma ba zan iya ci gaba da zaman a gidan nan ina tufka Khadija tana warware mini ba, kai kuma kana biye mata!!
Ba zai yiu ba ba ni da wannan lokacin considering my age(duba da shekaruna)
yanzu lokacine da ya kamata ace na duk’ufa ibada da neman gafarar Ubangijina.”

“Hajiya mama a yau Khadija za ta bar gid…”

Cikin fushi tace”wai
Ya ina magana ba ka ji nane??
Na ce maka ban yarda ba ko?
Ko shima taurin kai za ka yi mini ka nuna min iyaka ta?
A gaban Yaranta za ka koreta saboda ni ko me??
Ka manta yadda muka yi ni da kai a asibiti, ka manta abunda nace maka??

B’ata mini ran da ka yi ka k’i
jin maganata shiyasa zan tafi in bari ka yi komai da kanka dan ni kam na tsame hannuna!.
Ka bincika komai da kanka, ka nutsu ka gyara gidanka ta hanyar da ta dace ba wai ka koreta haka kurum a gaban ƴaƴanta saboda ni ba.”

Ya Bud’e baki zai yi magana tace”Wallahi zan baka mamaki fa?da musu da kai kakeso
In ji ko da b’acin ran da kuka d’ura mini?”
Chapter 122 · 0% Book details