← Book details Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 147 OF 152

Sashe 147

Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Zuwa yanzu Yahanasu da Manu da Munirat sun samu Ummi ta farfad’o, dan haka Munirat ta mik’e ta k’arasa inda take ta tsaya tace
“Kausar baki fahimci abunda yake nufi ba? har kin manta yadda kikayi ta kuka kina rok’ata in rufa miki asiri kenan???”
Kallon kallon aka fara yi kafin Daddy ya shiga gaban kausar ya tsaya a gaban Munirat yace”ki yi mana bayani dalla dalla!”
….
Hawayenta ta share kafin ta fara magana
“Daddy ku yafe mini, na biyewa sharrin zuciya da son da nake yi wa Yassir na jefe kaina halakar da nakasa fuskantarku da tabon, wanda hakan ya sanya sai da na gudu na bar gidan nan dan ba zan iya facing kowa ba!!
Yassir ya yaudareni da kalmar so, ni kuma na biye masa saboda rashim wayo da biyewa son zuciya…haka muka taru da ni da shi muka dinga tafka b’arna har ta kaini ga samun ciki, kuma Likita ya tabbatar mini muddin na yi yink’urin zubarwa to kodai in mutu ko kuma in rasa mahaifata…shiyasa na dawo na samu Yassir dan a lokacin ma har mun rabu…sai da na dinga kuka a gabansa Ina magiya jinina ya hau
na shiga masifa mai tayin yawa tukunna ya yarda zai taimakeni, hakanan ya kaini wani gida flat mai two bedroom ya zuba mini kayan abinci ya yi gaba, bayan yace ‘idan na haihu in kirasa sai mu kai Yaron gidan marayu…….’.
Ban sake ganin Yassir ba, sai da cikina ya cika wata na biyar kwatsam suka zo mini da shi da Kausar, suka ce min ‘Kausar ta yi b’ari, suna buk’atar idan na haihu in bata Yaron a samu a rufawa juna asiri…’
Da farko ban yarda ba, dan ko da Yassir yace za a kai Yaron gidan marayu jinsa kawai nake yi amma na gama tsarawa Ina haihuwa zan bar garin da d’a na mace ko namiji, saboda Ina matuk’ar son abuna.

Magiya kuka da kuma nuna mini alfanun yin hakan da yadda za mu taimaki juna da Kausar da Yassir suka yi ne ya sanya na chanja ra’ayina na amince akan ‘idan na haihu Kausar sai ta karb’a, ni kuma sai in dawo gida gareku ba tare da kowa ya san abunda ya faru da ni ba, in yi rayuwa ta kamar farko.’

Tunda na haihu na ji ba zan iya bata d’ana ba….da mugun kyar na amince bayan Yassir ya lallab’ani, amma a jiya da na ji yana waya ana sanar masa abunda Kausar d’in ta yi wa Yarona ya sanya na fahimci bayarda shi a Kausar is the worst thing (shine abu mafi muni) da zan taɓa yi a rayuwana…

Shiyasa yanzu na dawo, kawai ku karb’i ɗana daga Hannunta ku bani abuna, inason ɗana wallahi, ba zan iya rabuwa da shi ba, ba zan iya bar mata shi ba.
daganan ku yafe ni, ku yafe min, na san na yi muku laifin da ni kaina ba zan iya yafewa kaina ba.”

Cikin kuka Kausar tace”Wallahi k’arya take yi”

itama Munirat cikin kuka tace”
Wallahi gaskiya nake fad’a….”
sai kuma ta kalli Yash tace
“and again…cikinta ba 12 days bane ba tun asalin farko k’arya ta yi muku suka had’a Baki da Junior akace naka ne, amma a lokacin da tace tanada ciki, cikin jikinta watanninsa biyu na ji komai kuma na ga komai a wayar Yassir!!!”.
Damk’ar wuyanta Kausar ta yi, cikin ihu da kururuwa ta hau cewa “wallahi k’arya take yi mini, sharri ne, Munirat waye ya turo ki??”

K’arasowa Junior ya yi da kyar ya kwace wuyan Munirat daga Hannun Kausar,
kowa su yake kallo…kunya kamar k’asa ta tsage ya shiga hakanan ya kallesu ya ce ”da gaske Munirat take! cikin Kausar da na duba a wanchan lokacin ya ma haura 2 months, amma na ce muku bai wuce 12 days ba saboda……………”
Tiryan tiryan ya zaiyyano musu komai da yadda Yassir ya yi tricking d’insa komai bai b’oyeba, kafin ya juya ga Yash ya Had’e hannuwansa biyu yana kuka Yash d’in ma yana hawaye yace”ka yafe mini dan Allah, kar ka rik’eni a rai, ka taimaka ka yafe mini…..”
……
Tuburan!! Haka Kausar ta kafe ta dinga rantse rantse akan ‘k’arya Munirat da Junior suke yi…’
….
Scannning d’in da yayi aka nemo, Yasmeen ta duba, ta tabbatar sannan ya nuna musu messages d’in da Yassir ya dinga yi masa a wannan rana amma dukda hakan Kausar tana tsaye tana kuka tanata faman rantse rantse akann ‘Itafa k’arya aka yi mata…’

Yashjub bai san lokacin da ya k’arasa ya damk’i wuyanta ba! Kamar ya samu k’ato haka ya kaita bango ya dinga gwara kanta wanda hakan ya yi sanadiyyar da har jini ya fara fitowa ta kunnenta…

Da mugun kyar su Daddy suka kwaceta daga Hannunsa, tana ganin haka ta fita da gudu….ta riga ta san asirinta ya tonu, kuma a halinda Yash yake tsaff zai iya kasheta, shiyasa kawai ta nufi gidan Mommy a hargitse, ta san idan ta je chan ɗin za su nemi mafita!!! Dan she ain’t giving up wallahi, bata shiryama haƙura ko saduda ba!.

Hakanan ta nufi titi, kowa yana kallonta, dan daga ita sai riga da wando manya na barci, da hula.
Ita kam sam bata damu ba..da kyar ta samu napep ta hau, ta yi masa kwatancen gidan Mommy suka wuce a haka, sanyi yana kad’ata kamar zai d’auke ranta.

Tana fita Yash ya rushe da wani irin kuka ya juya ya rungume Daddy faɗi yake
“AlhamdulillahC Alhamdulillah Alhamdulillah”
babu k’ak’k’autawa….Allah kad’ai ya san adadi da kalar dad’i da farincikin da ya tsinci kansa da nutsuwar da ya samu a lokacin da akace d’an Kausar ba nasa bane ba, kuma yanzu ya sake tabbatarwa babu abunda ya shiga tsakaninsa da ita.

Shima Daddy hawaye yake yi, a ransa cewa yake”Astaghfirullah Astaghfirullah how did I end up
With a son like Yassir!!!…total shame….”

Daddy da Hajiya Mama where very disappointed in Junior, amma kuma yanada nashi dalilin na yin hakan, kuma yanzu ya fito ya fad’i gaskiya shiyasa suka yi masa fad’a, sannan suka nuna masa illar k’arya a ko wanne hali!!!
Yadira ma da yake tunanin zata yi wani abun, bata yi komai ba, ta dai ji zafin al’amarin kasancewarsa da wata sosai, dukda kuwa abun ba yanzu baneba amma ba komai..inshaaAllah,zata rungumi mijinta su zauna lafiya ta kula da shi yadda ya kamata.

Sosai Junior ya sake luntsumawa kogin dana sani, dan da ace ya san haka zasu karb’i al’amarin to da bai zalinci Yashjub har hakan ba.

Hakanan aka d’auko Yaro a sama yanata tsala
Ihu aka bawa Munirat ɗin shi, sai a sannan Yash ya yarda ya kalli fuskarsa….

Har ta juya zata tafi, Ummi ta ruk’o ta, ta rungumeta, cikin kuka ta shigacewa “Munirat kar ki sake tafiya ki barni..kin yi laifi, amma nima inada nawa laifin…Dan kwata-kwata bai kamata ni da Ƴaruwarki mu yi dogon fushi da ke ba, wanda har ta kaiki ga rasa abokin shawara.
sannan ni kaina munirat na san bana paying attention a kanki sosai yadda ya kamata, dan inda wata uwarce to da ya ci ace ta gane y’arta tana d’auke da ciki ne tun a karon farko!…Saɓanin ni, da na fi maida hankali akan al’amuran rayuwata sama da ke ƴata wadda kika kasance Mace! Kuma budurwa! Da kowa ya san tana buƙatar Mahaifiyarta a ko da yaushe, domin kuwa duk wata uwa kamata ya yi ace ta shiga jikin ƴaarta sun saba sosai ta hanyar zamtowa Ƴarttata a ƙawa! Abokiyar shawara! Malama! ƴaruwa! Sannan abokiyar sirri…
amma ni kalli saboda tsabar sakacina ya ja mini har kika iya yarda da Yassir a kaina, dan inda ace na baki dama mun saba to da na san tabbas za ki nemi shawarata kuma idan na gaya miki to za ki ɗauki maganata sama da huɗubarsa…

Ki yi hak’uri ki yafe mini Munirat, mu yafewa juna, mu taru mu gyara kuskurenmu…”
Ummi ta ƙarashe faɗin hakan cikin sake fahshewa da kuka.

Sai da su Daddy suka saka Baki, tukunna Munirat ta yarda akan ‘zata zauna ɗin’
sannan ta sake neman yafiyarsu…

A nan parlourn gefe kad’an Ummi ta zaunar da ita ta ce ”ta bawa Yaron nono, dan ba a tab’a basa ba”

Ai kuwa tana saka masa a Baki ya kama yana sha a haukace yana sauƙe ajiyar zuciya, duk sai da ya basu tausayi.

Ummi da Daddy basu so samun shege a cikin zuriarsu ba, amma za su rungumi k’addara su karb’i Yaron hannu bibbiyu, inshaaAllah za su cinye wannan jarabawar….
…
Suna nan tsattsaye ana koke-koke da neman yafiya, su Yasira suka shigo ita da Yusra.

Da gudu Yusra ta tafi jikin Daddy ta fad’a, sannan ta fashe da kuka, hakama Yasira ta je ta rungumesa….

cikin kuka Yusra ta fara neman Yafiyarsa ta hanyar cewa ”ya yafe musu, sun yi kuskure amma yanzu sun gane gaskiya…basu san inda Ya’isha take ba…Mommy tace ta aiketa k’auye, saidai har yau ba ta dawo ba…ya taimakesu a nemota, tabbas sun san akwai abunda Mommy take b’oyewa…..”
Chapter 147 · 0% Book details