Sashe 108
Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sun jima suna kuka, babu mai rarrashin wani, kafin da kyar Yaha tashiga rarrashinsa tana basa baki…cikin sheshek’ar kuka tace”Yash har gara kai!
InshaaAllah na san akwai ranar da za ta zo maka wadda za ka fahimci Mahaifiyarka ta na son ka ba son kashe ka take yi ba sannan tana son dukkanin abunda kake so infact tana son ka fiye da komai ma da kowa a duniyar nan!
Saɓanin ni! da zan rayu da sannan in rungumi gaskiyar cewa ‘mahaifiyata ba ta sona, ba ta k’aunata, ba ta damu da ni ba, iyakar amfanin da take ganin inada shi a wajenta shine ‘ta dinga amfani da ni wajen ganin ta cimma wata manufa tata’…”
Cikin katseta Yashjub yace”Yahanasu ki daina cewa haka!babu kyau, kin san fa ta rasu. kar ki k’ara mata nauyi…kwakwalwata ba za ta iya tuno mini ita ba amma a ko da yaushe hajiya mama tana sanar da ni ‘ita d’in mutumiyar kirki ce,’
kar ki ce za ki shiga abunda ya faru tsakaninta da Daddy har ta kaisa ga cewa ‘kar mu sake ko da ambatar sunanta ne!’ wannan tsakaninsu ne, kuma kinga har yau ba mu san menene ba balle mu shiga!
kawai ke dai har ma da ni kamata ya yi mu bi ta da addu’a da fatan samun aljannah…dan Allah Yaha kar in sake ji kin yi wannan furucin game da mahaifiyarki!.Mommy kuma tunda Allah ki ka ce to na san gagara misali ne….dan haka nima zan yi addu’ar abunda kika fad’a d’in ya tabbata, zan yi addu’ar ‘Allah ya sa duk zargi ne kawai muke yi ba gaskiya ba.”
Kallonsa take yi tashi d’aya wani Irin yanayi na tausayi k’unci da rashin jin dad’i suka lullub’eta.Ba ta san lokacin da ta kuma tafiya jikinsa ta sake fashewa da wani sabon kukan ba.!
Sun jima a haka kafin da kyar suka samu suka rarraashi junansu ta sake jaddada masa”ya bi komai a hankali, kamar yadda suka gaya masa, kar ya d’au mataki a kan kowa ba tare da kwakkwaran shaida ba.”
Awannnin Manubiya biyu tana barci kafin suka ga ta fara motsi…duk su biyun tashi d’aya k’irjinsu ya buga, kafin Yash ya dake ya mik’e ya k’arasa ya zauna a setin kanta bakin gadon, yacewa Yahansu ta je ta kira Likitan.
Tana gama bud’e idanunta Doctor ya shigo…yana nan inda yake aka gama dubata Dr d’in ya fita.
Yana fita tun kafin su yi magana ta kalli Yahanasu tace”d’azu kin ce za mu yi magana.Dan Allah kar ki ce mini akan maganar message d’in da aka turo mini ne, dan Allah Adda Yaha ku ce abunda aka rubuta a jiki k’arya ne.”
Yahanasu tana shirin yin magana Yash ya ce “gaskiya ne.”
A hankali ta saki wani irin kuka mai cin rai….mik’ewa Yahanasu ta yi ta fice zuciyarta sam babu dad’i.
Sai da Yash ya sauk’e wata nannauyar ajiyar zuciya ya had’iye wani abu mai d’aci da ya mak’ale masa a mak’oshi, tukunna tiryan tiryan ya fara zaiyyano mata duk wani abu da zai iya tunawa wanda ya faru a jiyan, bai b’oye mata komai ba…
D’ari bisa d’ari ta yarda da shi, sai dai kishi takaici da bak’in cikin da suka tarar mata ne suka sanya take jin zuciyarta kamar za ta hantsilo ta fito waje, har wani Jan numfashi take yi yana kufce mata.
Dai dai nan Mommy ta ja ta tsaya a bakin k’ofar ita da Ya’isha waenda zuwansu kenan.
Kamar zai fashe da kuka yace”mun so mu d’an jinkirta, saboda yanayin jikinki daga baya sai mu gaya miki amma kuma sai aka turo miki message……
Ga gaskiya nan na faiyyace miki ita Baby, ga kuma message d’in nan da aka turo miki da kuma abunda ya faru da ni dan haka ya kamata ace in kin haɗa su waje ɗaya su sanya ki fahimci so ake yi a raba mu, dan Allah dan Allah dan Annabi kar ki bada k’ofa, ki yarda da ni plss, dan Allah….”
Ya faɗi hakan cikin rungumeta.
Tabbas wannan abu ne mai nauyi na tashin hankali da ya sameta, dan za ta iya cewa bata tab’a shiga rikici da k’unci kamar na yau ba amma kuma ya zama dole ta bawa mijinta support sannan kamar yadda ya fad’a tabbas so ake yi a raba su,dan haka ita kuma duk rintsi duk wuya ba za ta bud’e k’ofa a shiga a raba su ɗin ba…..da izinin Allah.
Wani irin zafi da rikitaccen tashin hankali ta ke jinta a ciki amma ya zame mata dole ta danne kanta ta taushi zuciyarta ta tsaya musu…dan haka cikin sharar hawaye ta sa hannu ta rungumo sa itama kamar yadda ya yi mata tace”I trust you! (Na yarda dakai)
kuma babu wanda ya Isa ya rabamu, ba zan bada k’ofa ba…duk runsti duk wuya ba za mu karaya ba.Abunda ya faru jiya babban al’amari ne , amma na dad’e Ina neman tukuicin da zan k’ara maka na k’aunar da kake yi mini tsakaninka da Allah ban samu ba..
Ya Yash a matsayina na matarka Ina so ka saka a ranka kamar babu abunda ya faru tsakaninka da Kausar, ka goge hakan a kwakwalwarka nima na goge!ina so mu manta da duk wani takaici da bak’in ciki na daren jiya….indai saboda ni ne kake damuwa da fargabar mai zan yi tunani ko mai zan ce a kan case d’in, to inaso ka san cewa Manubiya ta goge komai ba ta rik’e a rai ba, bata saka a gaba ba dan babu komai a gabanta sai burin farantawa mijinta, dan haka ka cire damuwa, ka cire bak’in ciki mu ci gaba da rayuwar mu cikin farin ciki…inshaaAllah da ni da kai har abada ba za a ji kanmu ba.”
Kuka sosai Yash ya ke yi ya k’ank’ameta a jikinsa yana godewa Ubangiji da ya basa mar’atussaliha….ya ma rasa bakin magana, in banda sake ruk’umk’umeta babu abunda ya ke yi yana ji kamar ya maida ita cikin cikinsa.
Shiruu Mommy ta yi, har sai da Ya’isha tace”hmmm..mu shiga Mommy, za ta ci ubanta ne!.”
Tukunna suka d’an gyara daga tsayuwar lab’en da suka yi suka fara knocking.
Gaba d’aya Mommy kanta ya d’au zafi, tabbas Manubiya fa sai sun sake tsayuwa a kanta sun k’ara k’arfi fiye da tunani, dan shakka babu Yarinyar nan ta wuce tunanin su gashi shegen naci gareta…ita da ta zo ta d’anyi b’arin zance akan case d’in a samu ta ji ta yadda za ta d’aga hankali har sai ta ji komai daga nan su yi baram baram da Yashjub ɗin ta tafi, sai gashi an samu wani d’an albarka ya tura mata message ma gaba d’aya, amma dukda hakan ji abunda take cewa!..tana da tabbacin Kausar ce ta turo message d’in! tabbas dama tundaga jiya ta fahimci akwai abunda Kausar take shiryawa….ta d’an ji zafin yadda ta tsame su daga duk wani shirinta! ta fara yin gaban kanta ita kad’ai, amma kuma da wata wainar gara wata!da Manubiya gara ta bi bayan Kausar sau million ma, dan haka a nan (bayan kausar) za ta tsaya!…..
A yadda ta ji furucin Manu na yanzu ta riga ta gama yanke shawarar abunda za ta yi….ba dare ba rana ita da Baba larai za su duk’ufa daga yau! Wallahi indai ta haifu cikin uwarta da ubanta sai ta juyawa Daddy lissafi ya aurawa Kausar Yashjub, daga nan sai ta ga k’arshen soyayya!!! sai ta ga k’arshen naci!!!
za ta ga yadda Manu za ta yi idan Yash ya k’ara aure, za ta ga k’arshen maratussalaha da Manubiya ta ke playing….
Yadda yashjub ya karb’esu ita da Ya’isha sai da suka sha jinin jikinsu…ga Daddy ya juya musu baya yanzu kuma Yashjub! tabbas Manubiya ta tabbata mugun tsuro a cikin family d’insu, amma ba komai inshaaAllah komai ya kusan zuwa k’arshe.
An riga an yi abunda suka zo yi,
shiyasa kawai suka yi musu sallama suka fito jiki duk ba kwari…..ba kad’an ba yadda Yash ya yi musu abun ya tab’asu, Mommy ta d’an tsorata akan kar fa kwab’arta ta yi ruwa, dan muddin Yash da Daddy suka zargesu suka juya musu baya suka fara gano su to fa akwai Babbar matsala, dan haka dole ta tashi ta tsaya tun wuri ta gyara abunda ya fara lalacewa a tsakaninta da su Yashjub…..
A samu Yashjub ya auri Kausar Manubiya kuma ta kama gabanta…..
Gashi ta nemi fad’a kacha kacha da Daddy amma ba komai za ta gyara inshaaAllah….
Bayan sati biyu….
Babban abunda ya fi d’agawa Ummi har ma da su Yahanasu hankali shine ‘guduwar da Munirat ta yyi’…haka kurum kwanaki tara da suka wuce ta rubuta wasik’a akan ‘kar a nemeta ta tafi ba za ta dawo ba’ har yau babu inda ba a duba ba babu Munirat babu mai kama da ita,Ummi sai da ta yi sati d’aya a asibiti tukunna aka sallamota tsabar masifa…su Yasira kuwa an samu abunda ake so k’iri k’iri a gabanta suke yi mata dariyar mugunta suke cewa karuwanci Munirat ɗin ta tafi…
Mommy ta so su shirya da Daddy, amma abunda ya yi mata sai da ya sakata a al’ajabi! Dan korar kare ya yi mata a lokacin da ta je d’akinsa neman shirin, kuma har yau ko kallo ba ya shiga tsakaninsu, in kuwa ya kalleta to harara ce! Ko abinci ya daina ci a dining d’in k’asa duk dan saboda ita.
Wannan al’amari ba k’aramin d’aga mata hankali ya yi ba, har y’ar rama sai da ta yi. Gashi Yash da Manu suma shiruu ba a jin kansu, su da suka zubar da cikin suka k’ulla sharri saboda ya koreta amma sai take gani kamar hakan ma sake had’a kansu waje guda ya yi!..su Yasira kuwa ana sallamar ta a asibiti Hajiya Mama ta ce su dawo gidan Ubansu, shiyasa gaba d’aya mommy ta sake burkicewa, gashi ta ga hajiya mama ba ta da ranar tafiya, dan da farko sunyi tunanin rako Junior ta yi za ta d’anyi sati d’aya daga nan ta koma…