← Book details Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 152

Sashe 28

Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A take ta ji gabanta ya yanke ya fad’i, tana son Yash amman ta rasa dalilin wannan fargaba da tsoron da suka lullub’eta tun shekran jiya suka k’i barinta, tun shekaran jiya hankalinta yake a tashe….
A hankali ta ji ya ce “Baby! Kin yi shiruu, ko ba a yau zan cire kunyar b…”
Cikin katseshi ta ce”na’aam!” Kamar irim ta amsa kiran da ake mata a gefe ɗinnan,
Sai kuma tace”inna tana kirana, bari in je?”
Dariya sosai ya yi dan ya fahimci zillewa take son yi, tukunna ya kylaleta kawai ba dan wayonta ba….cikin sanyin murya ya ce ”ki gaida ita….”
Ahankali tace “sai anjima”
Yana wani irin blushing yace”Allah ya kaimu”
Daga haka Manubiya ta yi saurin kashe wayar ta d’aura a kan k’irjinta tana haki akai akai, dariyar da Aisha ta kwashe da ita ne ya dawo da hankalinta cikin d’akin, sam ita ta ma manta da Aisha a d’akin wallahi….
Sosai Aisha take dariya kafin ta mik’e tsaye ta je ta ta tofawa y’arta wadda take ta bacci add’ua tukunna ta juyo ta kalli Manubiya cike da zolaya ta ce ”Yarinya ba ki ga komai, kuma ba ki ji komai ba.”
Tana gama fad’in haka ta sa Kai ta fice abinta…

Da sauri Manubiya ta cusa kanta a cikin cinyoyinta tana mai jin kunya!fargaba! da wani irin yanayin da ba ta tab’a tsintar kanta a ciki ba.

Har Yash ya kashe wayar ya ajjiye a gefe bai daina blushing ba, ya jima a zaune yanata tunane-tunane da zumud’i kafin ya mik’e ya fad’a bathroom.

A side d’in Yashjub daga shi sai Abokansa biyu da suka zo jiya..…Gidan kamar ba biki ake yi ba!bakowa, dan side d’in su Mommy ma ba kowa hatta y’ay’an uncle d’inta ma ba su zo ba sakamokon fad’an da suka yi da ita kacha kacha recently(ba da jimawa ba).
Yayar Munirat ma ta so zuwa amman sai ta had’u da laulayi mai tsanani shiyasa ta hak’ura akan bayan bikin in ta samu sai ta zo ta ga amarya ta yi Allah ya sanya alkhairi.

K’arfe 7:25am Yashjub ya fito daga wanka, k’arfe 8:00dai-dai ya shirya tsaf ya kafa hula ya d’auki makullin mota da wayoyinsa ya zuba a aljihu rik’e da babbar rigarsa ya nufi k’asa sai tashin k’amshi yake yi.

A zaune ya tarar da Abokansa suna breakfast akan dining table ko wanka ma ba su yi ba, tsadadden agogon da ke d’aure a tsintsiyar hannunsa ya kalla kafin ya ce ”ku yi sauri fa kar ku sa mu makara.”

Dariya d’ayan yayi kafin yace
“ango ka sha k’amshi”

“Bai sha ba tukun!.
Wai Yash da gaske yanzu kake so mu tafi? 8:00fa yanzun, ba sai 11:00 ne d’aurin auren naka ba?”cewar d’ayan

Cikin takunsa ya k’araso ya zo ya chake musu ya ce ”na san 11:00 ne mana, amman ai ya kamata mu tafi da wuri, pls ku taso in ba haka ba Wallahi zan yi gaba in barku”

Dariya suka yi daga nan suka fara tsokanarshi da’mai zumud’i’suna yi suna ƙoƙarin fahimtar da shi akan ya d’an jira amma inaa! Sam Yash ya k’i hak’ura, hakanan suna ji suna gani ya azalzalesu suka yi wanka suka shirya 8:30am suka fice daga sid’e d’insa, suka je suka gaida Daddy ya yi masa addu’a ya sa masa albarka haka itama Mommy da Ummi…daga haka suka fice daga gidan shi kam ko breakfast d’in ma bai yi ba.

Tun k’arfe 8:00am unguwar su Manubiya ta san yau akwai gagarumin d’aurin aure sakamokon motocin polisawa da sojoji da suka fara yi musu sallama, kafin 10:00am kuwa taff layin ya cika da jama’a, duk saurin Yash sai 10:00 am d’in tukunna shima ya samu ya k’arasa unguwar dan suna fita suka had’u da Najeeb da electrician d’in da zai yi wani wiring a gidan dan haka suka d’unguma gaba d’ayansu, da farko Yash so ya yi yace musu ‘su su je su tsaya a kan electrician d’in!shi kuma ya wuce’, sai kuma ya ga idan ya yi haka kamar yayi rashin kara ne ga kuma su Najeeb d’in da suke ta cewa “wallahi idan ya je tun yanzu dariya za’a yi masa,”
shiyasa kawai ya hak’ura ya bi su ba dan ya so ba.

10:30am dai-dai Daddy da Abhi suka k’araso tare da tawagar manyan mutane (Abokanansu,) ba iyaka layin ba hatta titin sai da ya cika da manya manyan motoci na alfarma…….

11:00am dai-dai dubban mutane suka shaida d’aurin auren Yashjub Iman kura
Da Amaryarsa
Manubiya Musa, akan sadaki naira dubu d’ari uku, lakadan ba ajalan ba.

BULAMA ✍️
0903 441 3252
*MANNUBIYA*
*Book 2*
*page 15*

Mai kwalliyar da Aisha ta d’auko tana kammala pinning mayafin Manubiya a jikin d’ankwalinta, suka ji loudspeaker tana ƙarar sanar da d’aurin auren Yashjub Imam Kura da Manubiya Musa wanda aka gama d’aurawa yanzun akan sadaki dubu d’ari uku, lakadan ba ajalan ba…sai kuma hayaniyar Maza ta fara tashi…..

Kukan da ya zame mata sana’a, shi ta saki kafin ta zube anan kan katifar, yayinda su Aisha kuma suka shiga jero hamdala, Matan da suke shigowa cikin gidan yanzun kuma suka shiga rangad’a gud’a…..nan da nan a cikin mintunan da ba su kai ashirin ba d’akin nasu har ma da gidan gaba d’ayansa ya cika taff da jama’a, ba masaka tsinke!…

Masu hoto da amarya na yi, masu Allah sanya alkhairi da hayaniya suna yi,…..itakam Manubiya gaba d’aya fuskarta ta kumbura, kwalliyar ma har ta fara d’an gogewa.

Suna cikin haka gwaggo Suwaiba ta kira waya, da Inna suka fara gaisawa ta yi mata Allah ya sanya alkhairi sannan ta sake bata hak’urin rashin zuwanta (dan k’iri k’iri jatau ya hanata zuwa) tukunna ta nemi magana ta Manu…..fad’a da nasiha ta yi mata, sannan ta sanya mata albarka daga haka suka yi sallama.

Duk yadda Manu ta so daurewa sam sai ta kasa, dan haka ta sake sakin hawayen da take ta rik’ewa tun ɗazun, tana yi tana sheshshek’a da jan hanci…..su kansu su Aisha zuwa wannan lokacin jikinsu ya fara yin sanyi,
dan sai yanzu suka sake tabbatarwa da cewa “Manubiya tafiya za ta yi ta barsu”
ga kuma fargaba da sanyin jikin da kan lullub’e kowa kama daga kan Amarya zuwa kam y’an uwanta
tashi d’aya a lokaci irin wannan ɗin duk suma sai ya bi ya lullub’esu gaba d’ayansu.

Jidda ce ta fara sakin kuka, ganin haka yasa itama Siyama ta saki nata kukan da take ta k’ok’arin dannewa….

murmushi kawai inna da mama suka yi, suka ci gaba da harhad’a abubuwan da sukeyi, ba tare da sun yi yunk’urin rarrashinsu ba, dan sun san muddin suka doshi inda suke tau tabbas suma kukan za su yi.
Musamman ma Mama wadda hankalinta yake a matuk’ar tashe! sannan kanta ya d’aure katamau tun lokacin da ta ji an ambaci ‘imam kura’ da kuma sunan angon, ta san wataƙila tsananin coincidence ne, amman dukda haka sai da ta shiga cikin tsananin fargaba.

Dakyar Aisha ta daure ta k’arasa inda Manubiyan take da niyyar rarrashinta amman tana zuwa itama kawai sai ta fara hawaye.

Dai-dai nan anty umma ta shigo tana cewa ”Siyama ku zo ku tayani fara zuba abinci kuna mimmik’awa jama’a, ga mutane chan suna ta shigowa har a b’angaren su Uncle, sannan ku kira su Musbahu a samu a fitar da takeaway d’innan kafin jama’a su watse…...”
Salati ta saka ganin yadda suke shirin mayar da d’akin kamar na zaman makoki, k’arasa shigowa cikin d’akin ta yi ta ajjiye k’atuwar kular hannunta tukunna ta k’arasa inda suke suka shiga rarrashin Manu ita da ragowar Matan da ke a cikin d’akin.

Da kyar aka samu suka yi shiru kuwa, tukunna ahankali cikin mutuwar jiki Aishar ta ce “Bari in je mu fara mik’a abincin”

Mik’ewa su Jidda suka yi suma, suka bi bayan Aisha……
Duk wannan girkin da hayaniyar d’aurin auren da ake ta yi babu wanda ya lek’a ya taya su inna girki sai anty umma sannan kaff gidan ya Yusuf ne kawai ya lek’a wajen d’aurin auren sai kaka mallan wanda ya daddannawa Baba Habu zagi da ya so ya hanashi zuwa….sune ba sa kula Baba kuma fa ya bisu ya basu hak’uri ya fi sau nawa, shekaran jiya ya bi su ya basu invitation amman sunce”wai sau d’aya ya gaiyyace su kuma bai sako su a cikin al’amarin sosai ba, sannan lokacin da aka kawo kud’i a gaban sa Nafi’u ya so yiwa Baba Habu rashin kunya amman bai ce komai ba sai daga baya ya biyosa zai basa hak’uri tsabar ya raina musu wayo.”
Shiyasa yanzun ma ba su je ba kuma ba su turo matayensu hidimar mata ba,kaka mallan ma sun so su hanasa zuwa amman ya k’i hanuwa dan shi tun sassafe ma ya shirya ya sanya farar shaddarsa ta sallah ya nufi masallacin bayan ya yiwa baba habu kaca-kaca…da shi kuwa aka dinga tarar bak’i…..babu wanda ya lura da su ba wanda ya san da su ma a wajen amman haka suka dinga faman shishshigi a gurin, da shi da Yusuf!
Shi Yusuf connection yake nema, Kaka mallan kuwa maula tuk’uru ya dinga yi a wajen..dan ko marok’in wajen bai kai ya shi a iya maula da tara abun duniya a wannan rana ba.

Ba wanda ya fi tsanar sa a kaff wajen kamar Yassir, dan ji yake yi kamar ya d’auke shi ya je ya jefa a rami kowa ya huta, ya tsani tsohon nan haka kurum bai mishi ba tun farkon had’uwar su. Ya tsani layin…gaba d’aya kunyar Abokansa guda biyu
da suka zo d’aurin auren tare yake yi, shiyasa fa dama shi bai gaiyyaci kowa ba! waennan d’inma dan Yashjub d’in ya sansu ne shiyasa ya gaiyyacesu da kansa su kuma suka zo,tunda suka shigo layin suke ta jero masa tambayoyi “me ya kawo Yashjub nan?
a nan kuma matar tashi take? waye waye…..”
Tou kuma yanzu ga kakanta
wanda idanunsa suka rufe har Yashjub d’in ya je ya cewa “ya bashi kud’in da za a rabawa almajirai anjima, ayi musu sauk’a”……
Chapter 28 · 0% Book details