← Book details Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 130 OF 152

Sashe 130

Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

rashin sanin inda Baba larai take shine kawai yake kawo mata babban fullstop a mission d’in nata saboda Baba larai d’in ce za ta yi komai tun daga kan dawowar da take so suyi cikin gaggawa har zuwa kan mutuwarsu.

Tsakanin Mommy da Yahanasu sam babu jituwa kwata-kwata! Yahanasun ta k’i yarda ta ba ta chance har y’an gidan sun fara lura da yadda Mommyn take binta ita kuma tana kaucewa…
Mommyn har da ce mata “InshaaAllah za a karya abunda aka yi mata a samu ta yi aure!”
Ita kuwa Yahanasu tace”dan girman Allah kar su karya komai!
su barta a yadda ta ke ta yi Imanin Ubangiji ne kad’ai zai iya yin ikonsa a kanta.”

Kamar yadda Mommy ta yi zato, Yahansun ba ta tona mata asiri ba, ammafa tun daga wnanan ranar ko had’a hanya Yahanasu ta daina yarda ta yi da Mommy, k’ofar d’akinta kuwa kullum a rufe.
…..
……Wata d’aya wata biyu tun su Mommy suna d’aukar b’atan Baba Larai abun kamar wasa har suka zo suka fara tsorata, dan yau kwana sittin kenan babu ita babu alamarta, wayarta ba ta shiga, gashi suna tsananin buk’atarta dan Ya’isha ta d’aga musu hankali akan auren Najeeb da Siyama gashi Yash da Manubiya babu su babu dalilinsu! ba ma ta jin za su dawo bikin,
Yassir kam ya sake tab’arb’arewa company d’in da Yash ya bud’e masa ma ya tashi a aiki!! Hatta building d’in nasa ya sayar, motocinsa masu tsada ma ya siyar, kuma har yau ba a san Ina yake kai kuɗaɗen ba..
Kausar kam ba k’aramin Namijin k’okari take yi wajen danne zuciyar ta game da shi ba, gashi mutanen da ta addaba da kira a kan su tona masa asiri a samu a kashe sa ta hutu! sun daina ma sauraronta kamar waenda ya yi musu tsafi!
A fannin lamarin Yash kuwa ita kad’ai ta san me take ji ita kaɗai kuma ta san halinda take ciki!!
Ta kira sa! ta yi message!! amma duk baya shiga, ba ya tafiya!
tsabar bala’i har depression ta kamu da!
Da kyar ta samu ta nutsar da kanta ta ke shan magani ganin tana shirin haukacewa!!
Inda ace babu aurenta a kan Yash ya yi wannan dogon zangon da baza ta tab’u sosai ba
amma wannan zumar da aka lasa mata a baki aka janye shi yafi komai haukatata!!
……saboda Allah ace ranar da ake shirye shiryen kai ka gidan Miji mijin ya gudu!! kuma har yau bai dawo ba!(dan ita har yau ba ta san ba matar Yashjub bace ba ita.)
Dukda wannan bala’in da take ciki amma tana namijin
k’ok’ari wajen rik’e kanta da saisaita kanta, zuwa yanzu ba ta da komai against su Mommy amma haka kurum take jin ba za ta iya tattauna matsalarta da su ba! Ba za ta iya sake yarda da su ba….. abunda Mommy ta yi wa Baba larai ma ya sanya Kausar d’in ta d’an tsorata da Mommyn, ta ja jikinta sosai…
Doctor d’inta dai yace mata hakan alamace ta ciwon damuwan da ta kamu da shi saboda ta yi going through a lot a rayuwarta da yawa shiyasa ba za ta iya sake yarda da kowa ba(ta zama komai nata a sirrance), sai dai sam ita ba ta wani yarda ba,ta fi raja’a akan kawai dai shekarunta da suka ja ne suka sanya ta yi wayo ta zamo shiru shiru ta kuma koyi rik’e sirrinta.
A kaff y’an matan gidan har ma da Mommyn babu wanda ya lura da cewa ba ta ma da lafiya saboda kamar yadda take cikin masifa hakanan suma kowa a cikin masifar take!
Su Yasira zuwa yanzu rashin aure ne matsalarsu, dan auren Yadira da suka ga ya taho gadan gadan ya sake uzzura musu son aure a cikin zuk’atan su musamman ma Yasira wadda ta fissu shekaru, sai dai kuma ko talakan saurayi babu mai shi a kaff cikinsu, Ya’isha kuwa tata damuwar daban ce dan ji take muddin Najeeb ya auri Siyama a gaban idanunta to kuwa sai ta mutu!!!
Mommy kuwa nata tashin hankalin ya fi na kowa dan itama rashin auren nasu yana damunta amma ba kamar yadda komai ya rinchab’e mata ba!!
Ta ko’ina babu haske babu sauk’i babu nasara……Kausar d’in ma da ta shirya akan za ta yi mata Abu da Yashjub a kan Daddy gashi yanzu babu auren, kuma a yadda take ganin Daddy kwana biyun nan in dai ba irin wannan aikin aka yi ba tabbas akwai gagarumar matsala.

Da kyar ta samu ta dake ta sanarwa Kausar d’in da su Yasira ‘babu fa maganar aure’ dan tausayinta take ji gara kawai ta sani ta cire hope, aikuwa ranar duk dauriyar Kausar kasawa ta yi,sai da suka yi sati d’aya a asibiti tukunna ta dawo dai-dai da kyar ta fara gane waye ma a kanta.
Dole ta sanya Mommy ta fito mata a mutum ta ce mata ‘kawai ta hak’ura da Yashjub!!!
Ta yarda ta aminta da ita kawai idan ta ce mata ta taimaki kanta ta cire Yash a ranta, dan zuwa yanzu ya kamata ace ta fahimci zuciyar Yash ta Manu ce,dan haka dan Allah ta hak’ura kawai!…
Tana cikin masifa, gashi babu Baba Larai dan haka dan Allah ta ajjiye komai a gefe ta tashi ta tsaya mata
dan tana buƙatar ta tsaya mata ɗin a matsayinta na ƴaruwata kwara ɗaya wadda ta yi mata saura.
Dan haka ta taimaka mata, akwai labarin da zata bata amma ba yanzu ba sai nan gaba.
Ta ajjiye batun soyayya haka nan ta taimaka mata ta rai da tsira ake yanzu dan duk abunda ya sameta to itama ya shafeta farinciki da nasara ko kuma akasin hakan…

sannan su Daddy sun ce har ta haihu a idanun duniya tana a matsayin matar Yashjub ne…InshaaAllah a tsakankanin nan Ubangiji ta san zai nuna musu hanyar da za su bi komai ya tafi musu dai dai.”

Ita dai Kausar tace mata “to” ne kawai, amma bata gama fahimtar inda zancen nata ya nufa ba sakamokon bala’in da take a ciki, ita kanta yanzu kam ba ta san ta Ina za ta b’ullo ta sake zama mata ga Yashjub ba!!

Ta kasa yarda kanta da zuciyarta sun aminta da cewa ‘gaba d’aya hard work d’inta da baƙar wahalar da ta sha duk dan ta mallaki Yash sun tafi a banza lokaci guda kenan???inaa da sake!. Ba zai yiu ba gaskiyq!

Har yanzu babu Munirat babu labarinta, Ummi ta kuma zama abun tausayin Hankalinta gaba d’aya a tashe!
Daddy ne yake dan tausar ta shi da su Hajiya mama wanda shima Hajiya Maman ce take tausar sa take tsayar da shi ba dan itan ba da tuni ya san na yi da Mommy…dukda ya san ba shi da wata hujja a kanta amma kawai shi jurarta ne a cikin gidan ya ke masa azabar wahala! Ba zai iya ci gaba da jurarta ba,ya tsaneta.

A bangaren Mama itama zuwa yanzu ba ta da wani burin da ya wuce ta saka Yahanasu da Yashjub a idanunta dukda tana tambayar Manubiya ya suke tana jin komai dan har gaisawa
sukeyi ma da Yashjub amma tana buk’atar ta saka su a idanunta musamman ma da ta ji har yanzu Yahanasu ba ta yi aure ba!
Tashi ɗaya duk ta damu hankalinta ya kasa kwanciya dan ta san dole tana da buk’atar ta…..

Bayan watanni uku!!!

An yi auren Siyama da Najeeb gidansu yaana unguwar Badawa,haka shima Junior ya auri Yadira suna zaune a d’aya daga cikin gidajen Daddy dake a Unguwar Darmawa kafin ya kammala abunda ya zo yi ta karb’i transcript d’inta su wuce Uk.

Duk cikin aure biyun nan da aka yi, su Manubiya ba su zo ko d’aya ba, sun dai turo gudunmawa sun kuma yi addu’a.
Su Hajiya Mama ma da suka zo na su Junior ba su wani dad’e ba suka juya, dan ita dama da kyar ma ta yarda ta zo.

Ya’isha tana nan yau lafiya gobe ba lafiya, dan yadda ta kad’u ta damu da al’amarin sai da ya girgiza su Mommy, gashi har yanzu batama da shirin hak’ura da Najeeb ɗin.

Kausar ma tana nan tana fama, kullum ba lafiya ga ciki ya tsufa..jira kawai take yi su Yashjub su dawo wllahi duk bala’i sai ta san yadda ta yi ta koma masa sai dai ta rasa ranta a hanyar raba sa da Manubiya da kasancewa tare da shi.

Ya Musbah ma ya kammala karatun da ya yi, takardar tana fitowa ya fara shirye shirye cikin nasara kuwa ya zana waec ya yi jamb, yanzu haka neco ya ke yi, kuma ya ci jamb d’in, dan haka Najeeb ya sake zage damtse wajen nema masa gurbin karatu a fannin Business Administration a jami’ar Bayero uni,Kano.

Gwaggo Suwaiba ma ta zo,yanzu Mijinta shima Allah ya fara nuna masa k’arshensa kuma Itanma ta dage da addu’a sosai, dan cikin ikon Allah tana cikin wnnan hali na ha’ula’i Allah ya kawo mata wasu makwabta jajirtattu wajen fannin addu’a har Al’k’urani suke rubuwata da littafai…
sama-sama suka fara gaisawa, su kad’ai suke iya shiga gidan, sai da zama ya yi dad’i labari ya yi labari tukunna suka fahimci ashe ma Matar (maƙwabciyar tasu) tana da dangantaka da Mahaifiyarsu Inna da Gwaggwo suwaiban, amma irin dangantaka ta nesa ɗinnan.
Chapter 130 · 0% Book details