Sashe 75
Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ahankali ya d’ago lumsassun idanuwansa waenda suka cika taf da kwallah ya kafe ta da su kafin ya juyar da fuskar tsinken gareta wanda a yanzu jajayen layuka biyu suka fito rad’au!
Hannun ya na rawa ya saita mata shi a dai dai saitin fuskarta a lokaci guda kuma hawayen da suka tarar masa a idanu suka samu damar b’alle masa,a take yayi mata wata mahaukaciyar runguma ya fashe da wani irin kuka…..
Ita kanta Manubiya hawaye ne suka b’alle mata.
A take wani sanyin farin ciki da annashuwa mara misaltuwa ya mamaye masoyan…lamoo ta yi a jikinsa tana hawaye tana jin yadda yake kuka bilhakki da gaskiya jikinsa har karkarwa yake yi sannan zuciyarsa tana wani irin bugu..
Sun jima a haka kafin Manubiya ta d’an fara k’ok’arin zamewa a hankali tace
‘’Godiya za mu yi wa Ubangiji….’’
Ahankali ya sake matseta a jikinsa yace
“Tun d’azu nake godiya,Alhamdulillah Alhamdulillah Alhamdulillah ya rabbi…bayan fatar baki da zuciya ina so in yi godiya ga Ubangijina…..’’
Murmushi ta yi a hankali tace ‘ka yi ta sadaka’’
Sai da ya sauk’e wata k’ak’k’arfar ajiyar zuciya ya tsaida kuka da hawayen nasa da kyar tukunna ya cika ta ya d’ago fuskarta ya yi cupping a cikin tafukan hannuwansa sannan yace
‘’Thankyou Manu, na samu farin ciki sannan na zama cikakken Mutum domin ke, sannan gashi yanzu za ki bani kyautar da na dad’e Ina kwad’ayi, na gode Baby, I love you more than life itself(ina sonki fiye da rayuwa)….”
Ahankali ya sake sakata a jikinsa ya rungume.
Sun jima a haka yana ji kamar kar ya cikata su tsaya a haka har abada, kafin da kyar suka cika juna ya wanke fuskarsa suka fita.
Fuskar Yash kawai Yahanasu ta kalla ta fahimci kuka ya yi kuma tana da tabbacin kukan farin ciki ne, dan haka ta k’arasa garesu da sauri ta had’asu ta rungume cikin tsananin murna tace ‘’congratulations’’
A hankali
yayi murmushi ya ce ‘’Thankyou Yaha,‘’
wanda hakan ya sake tabbatar mata ai kuwa Baki har kunne haka ta hau murmushi mai had’e da dariya tana jin tsananin farin ciki.
Ita ta k’arba abun gwajin ta kaiwa Dr.
Cike da murna ya matsa kusa da su ya yi congratulating d’insu sannan ya d’aura da cewa “a halin yanzu ba zai ce ga exact satuka na cikin ba amma daga yanzu zuwa ko wanne lokaci suna iya zuwa clinic d’insa a yi gwaje gwaje a tabbatar da lafiyar Baby.”
A take Yashjub ya ce “su tafi yanzu tare da shi kawai”
Murmushi Dr d’in ya yi yana yaba tsananin kulawar Yashjub ga Babyn da matarsa..sai a lokacin tukunna Yasmeen ta matso tana murmushi ta yi congratulating d’insu
Dariya Yashjub ya yi yace “young Dr! sai na bawa Baby labarin yadda kika kusa d’ura masa allura ai, saboda rashin kwarewa…”
Ahankali ta sunkuyar da kanta k’asa tana murmushi a ranta tana jin kamar ta fashe da kuka tsabar da na sani da kunya da takaicin Mommy…a d’ayan b’angare na zuciyarta kuma tana jin wata nutsuwa dan tabbas ta ji dad’in zuwan Doctor wanda ba dan shi ɗin ba to da tuni ta aikata abunda ita kanta ba za ta tab’a yafewa kanta ba….
Waje suka nufa gaba d’ayansu banda Mannubiya…
Ba iyaka Manubiya wadda ke daga d’aki tana jiyo su ba hatta Yahanasu wadda dama ba ta so ma maganar ta fito ba, sai da ta ji kunyar yadda Yashjub ya zage yana mai sanarwa y’an parlourn ai Manubiya ciki gareta!.
Har gaban Daddy ya je ya tsaya ya gaya masa cike da tsananin murna da farin ciki..
Sai da ya gama fad’a ya ga kowa ya yi shiruu yana kallonsa a take kuma sai wata kalar kunya ta lullub’esa.
Murmushi Daddy ya yi yana jin wani farin cikin da ya dad’e bai ji ba kafin ya dafa kafad’ar Yashjub d’in yace
‘’Allah ya inganta Allah ya raya ya kawo mana sanyin idaniyar mu duniya lafiya.
Tun da nake da kai zan iya cewa ban tab’a ganin farin ciki irin wannan akan fuskarka ba.”
Sai da ya d’an k’uraa masa ido kafin yace “har kukan murna ka yi ne??”
Ya yi masa tambayar da alamun sigar zolaya wanda
hakan ya sa Yash d’in sake sunkuyar da kansa k’asa sai kuma ya juya da sauri yace
‘’Bari mu je asibiti’’
Ya fad’i hakan yana mai ficewa waje.
Sai da Yahanasu ta koma d’aki tukunna suka kimtsa suka fito.
Manubiya ta ji dad’in rashin ganin kowa a parlourn dan dama ba ta san ta Ina za ta fara had’a ido da su ba…..
Had’ad’d’en checkup ya sa aka yi mata.
Hankalinsa bai kwanta ba sai da ya sa akayi masa scanning da taimakon bayanin likitan ya ga location d’in jininsa d’an sati biyu tukunna..
Dr kansa ya sha kyauta…sai bayan sallar magrib bayan an gama yi mata allurai da k’arin ruwa leda d’aya suka karb’i magunguna tukunna suka nufi gida cike da murna da farin ciki…
Shi yake driving sai Manubiya a gefensa da Yahanasu a baya.
Sun zage da shi da Yahanasu suna ta lissafin kayayyakin Baby da abubuwan da ya kamata a fara siya…
Murmushi kawai Manubiya ta yi tana sauraron su tana jin wani sanyi a ranta tana kuma sake godewa Allah wanda ya bata Yashjub a matsayin Miji.
Sam murna da zumud’in da ya ke yi a kan cikin ya gagara b’oyuwa, dan ko baka tab’a ganin sa ba tashi d’aya za ka fahimci yana cikin tsananin farin ciki a yau.
Wayarta ce ta d’auki k’ara, wanda hakan ne ya katse musu hirar tasu
shi da Yahanasu.
Kamar ba za ta d’auka ba
sai kuma ta sa hannu ta d’auka.
Tana nan kishingid’e a yadda take haka ta saka wayar a kunnenta ba tare da ta bud’e idanunta ba tace ‘’Assalam alaikom’’
Ahankali Abbakar ya lumshe ido daga d’ayan b’angaren yace ‘’Wslm Manu,ykk kwana dayawa’’
Shiruuu ta yi ta k’i yin magana ta k’i cewa komai
Cikin yanayin sanyin muryarsa yace ‘’Abbakar ne’’
Yanzun ma shiruu ta yi dan dama tun farko ita ta fahimci shi d’in ne..
Wato sai yanzu zai waiwayeta sai yanzu zai nemeta bayan haka kurum ya d’auke kafa ya kulle duk wata ƙofa da za ta haɗa su,
sai yanzu zai wani kira ta!.
Muryarsa take ji yana magana amma ba ta fahimtar sa sakamokon aman da ya taho mata tashi d’aya…dan haka kawai ta kashe wayar ta ajjiye a gefe ta d’ago ta kalli Yashjub. Wanda yake mamakin waye ne ya kira ta haka ta gagara cewa komai
Kuma kamar muryar Namiji ya ji yana magana.
Da sauri ta toshe Bakinta ta na yi masa nuni da ‘za ta yi amai’
dan haka ya ja ya faka a gefen titin da sauri ya bud’e motar ai kuwa ta shiga shek’awa…
Aman da ta yi sai da ya ba su tsoro tsabar yawan sa.
Ba yadda ba ta yi da shi kar ya koma ba amma haka ya juya akalar motar aka maida ita asibitin.
Suna zuwa kuwa Doctor ya yi admitting d’inta,sai a sannan Yahanasu ta kira su inna ta sanar da su haka ta kira Ummi itama dan ta ji ta shiru bata neme su ko ta ce za ta zo ba kuma d’azu bata ganta a k’asa a parlourn ba dama.
Ba ta yi mamakin jin Ummin bama ta san ciki ne da Manubiyan ba
Tace mata “d’azu ta je side d’in Daddy ta tarar ya fita da ta sauk’o ta tambayi Yadira kuma tace mata wai sun je gidan su Manubiya ne za ta gaida iyayenta”
“Hmm”kawai Yahanasu tace
Daganan ta mik’awa Manubiya wayar suka gaisa da Ummi har ma da Yashjub ta yi musu murna daga nan tace musu gata nan zuwa inshaaAllah.A daren kuwa ta zo.
Su inna ne dai Yashjub ya kira ya lallab’a su yace “jikin nata da sauki su bari gobe su zo yanzu dare ya yi”.
Aikuwa washegari da sassafe d’akin ya cika taff su Inna da Ummi duk suka baiyyana,
Manubiya har da kukan shagwab’a da ta ga su Innaa.
Gata kam ranar ta ganshi har da d’an hawayen farin cikin ta.
Abinci kala kala daga wajen Ummi Inna har da Mama wadda shigar ta gidan kenan ta tarar ana shiri dan haka ta ce “su jira”
Haka taje ta had’o mata d’an Malale mai d’an karen dad’i tace a kawo mata bayan ta kira ta ji ya jikin nata….
Yassir gaba d’aya ya fice daga haiyyacinsa!!
A tsarin sa sai bayan kamar kwana d’aya zai aiwatar da shirin sa amma kuma farin cikin da ya ga Daddy yanata yi ne ya sake hassala shi dan d’azu ma da Daddyn zai fita ji yayi yana waya a kan Yashjub d’in, wanda ya san kuma gift ko wani abun zai k’ara masa in ba da kyar ba.
Ga Kausar kuma da ya lura da yadda ta burkice itama tashi d’aya…abun ba k’aramin sake hassala shi ya yi ba.
Shiyasa kawai ya shiga d’aki ya rufe ya shiga aiwatar da shirin nasa.
Suna zaune ana ta hira da Ummi da Innaa kawai sukaga an turo k’ofa an shigo.
Ita kanta Manubiya ba ta yi tsammanin ganin Mommy ba
duba da yadda kaff cikin su babu wanda ya d’au waya ya kirata har ta kwana ta ke shirin wuni….
Cike da sallama faram faram Mommy ta shigo suka hau gaisawa Yasira da Ya’isha suna a bayanta.
Yahanasu ce ta bawa Mommy kujera ta zauna bayan sun gaisa.
Cike da girmamawa su Jidda da Muhsin ma suka gaida ita sab’anin su Ya’isha da suka koma gefe suka k’ame kamar ba su ga su Innaa ba.
Suna zaune d’akin ya yi jugum tun shigowar su Mommy
Yashjub suka shigo shi da Najeeb wanda ya d’an rame kana ganin sa ka san yana cikin damuwa…