Sashe 64
Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
K’ura mata ido ya yi, sai kuma ahankali ya d’an matsa ya kamo hannunta yana kallon fuskarta da serious face yace “are u okay??”
dan har wani jaa yaga idanuwanta da kan hancinta sun yi, irin mutum yana cikin tsananin tashin hankali da b’acin ran nan.
Ba ta kulasa ba kuma ya ga alamun bazata kula shin ba,
dan haka ya sake matso ta a hankali da kyar kamar wanda yake jin tsoro yace”mai ta ce miki?
Mayene ya faru dear, tell me, menene matsalar??”
Tashi d’aya ta fashe da wani irin gigitaccen kuka wanda ya gigita Yashjub, yana shirin sake matsowa tace
“Kar ka tab’ani, ka fita kawai, bana son ganin ka!”
Kamar zai fashe da kuka yace
‘’baby ni d’in ne bakya son gani?
Ki yi hak’uri komai zai yi daidai, yanzu sai kin d’anyi hak’uri da su am…”
Cikin katseshi sannan da k’arfi tace
“Ka fita nace!!”
Da k’arfi kamar ba mijinta take yi wa magana ba.
Ahankali ya lumshe idanuwansa ya bud’e kafin yace “to mu je d’akina sai mu yi magana ko??..
Idan bakya son zama da ita a kusa ne, mu je sama d’akina, ki kwashi kayanki ma gabad’aya daga nan sai ki koma chan da zama ko?”
Wani kuka ta sake rushewa da shi ta durk’ushe a wajen tace
“Dan Allah ka fita, bana son ganin ka!”
Wani irin bugawa zuciyar Yashjub ta yi, dan kalamanta sun dake sa sosai…shiruu ya yi, kafin kawai ya juya kamar mara lakka a jiki haka nan ya fice ya rufo mata k’ofar.
d’akin Yadira yace mata”Ko da wasa kar ta kuskura ta je inda Manubiya take, ko sun had’u daga nan har gobe bai yadda ta yi mata ko da kallon banza ba,
Infact ta zauna a d’akinta ma kar ta kuskura ta fita koina sai gobe, ai taci abinci..”
Da “to” kawai ta amsa shi daga haka ya juya ya fita.
Yana fita Yadira ta yi wani murmushi dan da da farko ta d’an ji tausayinsa ta ji babu dad’i, amman da ta tuno hud’ubar su Mommy da Yasira sai ta ware….
A take ta d’auki hoton fuskarta Inda shatin Hannun Manubiya ya fito, tun daga kan Daddy har zuwa kan Yusra babu wanda bata turawa ba tace “Manubiya ta mare ta daga zuwan ta yau!”
Daga nan kuma ta kira su Baba larai tace “ta zuba abunda aka bata successfullly.”
Yashjub yana fita Mannubiya ta sake sakin wani irin kuka kamar ranta zai fita….
Ta jima tana kuka kafin ta mik’e da kyar ta fad’a toilet, sai a lokacin ta lura da gari gari a zuzzube a cikin bathtub d’in ta da kuma k’asan tiles d’in..
Tashi d’aya ta fahimci mai ya faru a wajen ta kuma fara tunanin ko dai shiyasa ta ji ta tsani Yash lokaci guda!…
kawar da tunanin ta yi da sauri ta yi ta’auzi da isthigfari a ranta tace “Mutum bai Isa ya yi wa bawa komai ba sai abunda Ubangiji ya riga ya tsara”
Sai da ta fara yin fitsari ta zuzzuba a duk wajajen da ta ga garin daganan ta wanke band’akin ta yi wanka ta d’auro alwallah ta fito still tana jin b’acin rai da takaicin da kuma tsanar Yash amma ba kamar
d’azu ba….
D’aukar wayarta ta yi da niyyar kiran Jidda, amma sai ta ci karo da text na rashin mutunci daga Ya’isha!!…
ita Manubiya bata ma san wa ya bawa Ya’ishar numberta ba, dan itama ba ta da tata number, sai da taga ta rubuta sunanta a farko kafin ta d’aura da zage zage tukunna ra fahimci ita ce…
Hatta kakanninta saida Ya’isha ta zage su tass!!!
Gori kala-kala babu kalar wanda ba ta yi mata ba!
zage-zage kuwa har da ashar, haka nan ta dinga rubuto sunan musa tana danna masa zagi…kuma ta tabbatar mata cewar ‘wallahi ko budad’e ko bujuma sai ta ramawa Yadira marin da ta yi mata…
A zuciye Manubiya ta fara typing d’in reply…
kamar kuma wadda ta tuna wani abun sai ta ta tsaya ta danne yatsar ta akan delete ta goge tass!.
Hawaye ne suka fara sintiri akan kyakkyawar fuskarta, kafin ta yi jifa da wayar a kan gadon ta zube a wajen ta fashe da wani irin kuka wanda ta dad’e rabon ta da tayi irinsa…
Ta jima tana kuka kamar ranta zai fita kafin ta d’auki waya ta kira Jidda…
Jidda, tana zaune kiran Manubiya ya shigo wayarta, dama ita take jira dan d’azu bata kaiga tambayar ta daliin kukan da suka sameta tana yi ba Manubiyan tace mata tana zuwa za ta kirata…
Tana d’auka ta kara a kunneta tace”assalam alaikom”
Muryar jidda da Manubiya ta ji ne ya sa ta sake fashewa da wani sabon kukan.
A rikice Jidda ta mik’e tsaye sai kuma ta d’an kalli Inna ganin tana baccinta ya sa ta fita da sauri.
Tana fita tace “subahannallah, Adda Manu mai ya faru???..dan Allah ki yi shiru.”Ta fad’i hakan wasu hawaye suna zubo mata itama……
Da kyar Jidda ta samu Manubiya ta yi shiru, ta shiga gaya mata abunda su Yasira su ka yi mata tun safiya har izuwa yanzu.
Sai da Jidda ta yi da gaske tukunna ta iya hana kanta kuka, dan ta san tana fara kuka za ta karyawa Manubiya kwarin guiwa ne.
Ahankali cikin rarrashi tace
“Adda Manu sai da su Innaa suka gaya miki zaman aure dama duk hak’uri ne…ki yi hak’uri, kar ki d’aga hankalinki, ki yi k’ok’ari ki cinye jarabawarki…kuma ni har ga Allah na d’an ji sanyi a raina tunda matsalar ba daga Ya Yash take ba.
Su waennan sisters d’in nasa na san dolen ki ne su ɗin amman tunda basuda kirki sai ki ja jikinki ki rabu dasu gaba d’aya, ita kuma Yadira idan nice ke Allah sai na ga dama zan had’u da ita….
Karki d’aga hankalinki ki lalata rayuwar aurenki tun kafin ki somata saboda su.
Idan suka zo inda kike ki yi musu iyaka mutuncin da ya kamata, da zarar sun fara miki rashin mutunci ki tartara su ki watsar ki shige d’aki na san Ya Yash zai fahimta.
Sannan kamar yadda kika fara yau to ki ci gaba da hakan, ko da wasa karki basu fuskar shige miki d’aki, dan nan ne turakarki, nan ne kaff gidan zaki shige ki zauna idan sun fara haukar su ba tare da sun biyo ki ba, wannan ni kaina na baki goyon baya, ki tsaya ki sanarwa Ya Yash kar su dinga shigar miki anyhow.
Sannan maganar fad’uwar gaba da garin da kike tunanin ta zuba miki kar ma ki saka hakan a ranki balle ya yi tasiri..babu bawan da ya isa ya yi wa mutum abunda Ubangiji bai k’addara ba. Ke dai kawai ki yi ta addua ki dage da Azkar kuma zan turo miki da wasu addu’o’i ma dana gani an turo a group na y’an class d’inmu sannan zan san yadda zan yi in sanarwa Inna ba tare da ta fahimci komai ba itama ta dinga yi miki addua.
Sannan dan Allah Adda Manu, abunda kika ce kin yi masa muna gama wayar nan ki tashi ki je ki basa hak’uri, tunda ma ya nuna cewa ki tafi d’akin nasa ni a gani na kawai ki kwashe kayanki ki koma chan saman sannan ki ce masa ba kyaso kowa ya dinga shigar muku, idan ya yarda hakan ya fi tunda dama ai turakarku ba kowa ne ya dace ya dinga shiga ba, kuma d’akin yana da girma zai isheku.
Dan Allah ki kwantar da hankalinki, ki cire komai a ranki sanann batun Kausar d’innan itama kar ki ma bari ta d’aga miki hankali, ke dai ki dage da addua a ko da yaushe da sallar dare, InshaaAllah ba su Isa su yi miki komai ba Wallahi….”
Ahankali Manubiya ta share hawayenta tana jin
sanyi da nutsuwa suna ratsata sakamakon shawarwari da kwarin guiwar da ta samu daga wajen Jidda.
Sai da ta sauk’e ajiyar zuciya tukunna tace “na gode jidda”
kamar itace k’aramar.
Ko da ta yiwa Jidda zancen makaranta tace”ta ga kamar yanaso ya hanata ci gaba da karatu”
Tashi d’aya cike da bata kwarin guiwa Jidda tace
“Yashjub ba zai tab’a hanata ta k’arasa karatunta ba.
Kawai yanzu tunda tafiya za su yi ta hak’ura ta bi sa ɗin, su je su dawo, ta san daganan zai
san abun yi kamar yadda ya fad’a, maybe yace ta k’arasa Online tunda ya fad’a mata baya son cud’anyar ta da maza ne.
Amman ita kam tana ba ta tabbacin ‘Yashjub ba zai hanata makarantaba’ tunda shima ya fad’a da kansa yace yanaso ta yi karatun, kuma ai gidan su y’an boko ne so karma ta saka hakan a ranta…..”
Sai da Jidda ta kuma jaddada mata ta dage da addua tukunna suka yi sallama da juna suka katse kiran.
A hankali ta kife kanta akan gadon ta saki wani siririn kuka…
Sam ita ba ma ta san lokacin da Yashjub ya shigo ba sai da ta ji ya zauna nan bakin gadon kusa da ita.
A hankali ta d’ago da fuskarta…gaba d’aya sai hankalinsa ya kuma tashi sakamokon yadda ya ga fuskartata ta yi har ta kumbura idanuwanta sun yi luhu-luhu.
Kamar zai fashe da kuka sannan kamar mai tsoron tab’ata haka ya matso ya ruk’o hannuwanta ahankali yace”I’m not supposed to make u cry (bai kamata in saka ki kuka ba)
dan Allah ki daina”
Ya fad’i hakan hawaye suna masu ciccikowa a idanuwansa.
A hankali ta share hawayen nata, ta matsa jikinsa..aikuwa bai yi wata-wata ba ya rungumeta yana mai sauk’e wata nannauyar ajiyar zuciya.
Haka kur’um sai ta tsinci kanta da jin tausayinsa, da kuma jin kunyar sa da ta tuna yadda ta dinga turesa d’azu tana korar sa amma kalli sai da ya dawo…ahankali cikin sanyin murya tace ‘’ka yi hak’uri’’
Wata nannauyar ajiyar zuciya ya sauk’e mai tafe da
murmushi yana mai jin nishad’i da tsantsar k’aunarta suna ratsashi, d’ago ta ya yi ya yi cupping face nata a cikin hannunsa kafin yace ‘’Manubiya ba ta laifi a wajen Yashjub! ko ta manta ne?’’
Wani irin kuka ta saka ta sake cusa fuskarta a k’irjinsa..