Sashe 36
Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tsaki Ya’isha tayi,dai dai
Jidda ta kama handle d’in k’ofar ta bud’e da niyyar fita ita kuma Yasmeen tace
“Nikam ace wai mutane ko darajar privacy basu saniba
saboda Allah, kamar wasu
dabbobi!”Daga haka suma suka nufo k’ofar da niyyar fita da kuma bi ta kan Jiddan idan ba ta ba su hanya da wuri ba.
Duk ba su lura da Najeeb a bakin k’ofar ba, sai da Ya’isha ta zo zata wuce tukunna suka yi ido biyu da shi.
Kallon ta yayi sosai kafin ya maida dubansa ga Jidda yace
“Anata nemanki! ki je sama wajensu Ummi, za ki taya su da wani abun”
Jinjina kai kawai ta iya yi dan ita kam ta gama shiga shock bayan b’acin rai da kuma mamaki…su da suke a matsayin surukan juna amma kalli yadda suke musu magana kamar masu shirin shiga filin dambe!. A tunaninta wayayyun mutane masu kud’i da illimi kamar su ba za su yi wannan tumasancin ba.
Shi kansa Sir Najeeb tunanin da yake yi kenan….ya san Ya’isha ba ta da kunya kuma tana da tsiwa amman sam bai yi zaton hakan daga garesu gaba d’ayansu ba.
Ya ma rasa me zai ce shine matsalarsu ko yana damunsu! shin kishi ne! ko haushi! ko bak’in ciki! ko rashin sanin ya kamata?.
Shiyasa Jidda tana wucewa
shima ya juya zai wuce ko second look bai yi tunanin sake yi musu ba.
Ahankali ya ji Ya’isha tace “Ya
Najeeb!”
Kamar ba zai juyo ba sai
kuma ya juya ya ce ”Naam
Ya’isha!”
Wuceshi Yasmeen ta zo ta yi, ta basu sarari shi da Ya’ishan.
Ganin ta yi shiru ta ƙi yin magana kuma sai wani irin kallo take yi masa ne ya sa yace “Inada abubuwan yi fa Ya’isha, akwai matsala ne??”
Ya yi mata tambayar yana d’an juyawa yana kallon masu aiki dake a cikin parlourn dan har sun kusan kammalawa.
Ba k’aramin b’aci kuwa ranta ya sake yi ba, shiyasa itama ta fito bakin k’ofar ta tsaya daff da shi sannan ta ce ”A ganinka bai kamata mu yi magana anan ba ko? shiyasa kake k’ok’arin zillewa, gudun kar ta ganmu tare??”
Dama ya san sai ta yi maganar Siyama, shi kuwa har ga Allah bai shiryawa maganar yanzu ba dan ya san tsaf zai iya kawo ƙarshen alaƙar da ke tsakanin shi da ita nan take!!! shi kuma ba ya so su rabun ta hanyar da bata dace ba, ya fi so a rabu cikin lumana…
Sai da ta sake cewa”Bakace komaiba”
tukunna ya juyo yace
“Tou me kike so in ce miki??
Ya’isha Meyene matsalarku da Mutanen nan? Daga ke har su Yasmeen!
Har ga Allah kun bani kunya wallahi!
Kuma na tabbatar kin san me zai faru idan Yash ya ji haukar da kukeyi ko?
Dama ashe kishi tsakanin Matar wa da siblings d’inshi gaskiya ne??
Dan ni dai ban tab’a gani ba sai a kanku, gaskiya!.
sannan kishin naku ma is way too local(ya yi zubin rashin wayewa da yawa) haba mana!.
Ki gayawa su Yasmeen,
kar su sake yin wani shirmen, kema kuma ki nutsu!
Amarya za a kawo, idan kuma ba haka ba to wallahi zan fad’a ma Yash.”
Yana gama fad’in haka ya fara k’ok’arin juyawa sakamokon hango Munirat da Siyama da yayi sun tunkarosu da kaskon turaren wuta…..ya san
abunda yakeyi is so selfish (ya yi son kai da yawa) amman Yaisha ita ta janyo komai tun farko! Dan in da ace tana bashi lokacinta to da wataƙila a lokacin da ya ga Siyama months ago (watannin baya da su ka shuɗe), da ba lalle ya saka ran samunta ba, zai iya rarrashin zuciyarshi ya hak’ura da ita
duk da ya san zai sha wahala.
Amman Ya’isha ita ta banzatar da shi, shi kuma ya kamu ya fad’a yayi dakon soyayyar Siyama har na tsawon kusan 4 months, sannan yanzu da ya sake ganinta a yadda yakeji wallahi ko goya sa Ya’isha takeyi ba za ta samu gurbi a zuciyarsa ba dan Siyama ta mamaye ko Ina shiyasa shi kansa ya ke d’an jin tausayin Ya’ishan dan har ga
Allah ba ta da matsayin da zata hana shi zama selfish(yin son kai), bata da matsayin da zata sa yak’i rabuwa da ita, kuma bata da matsayin da zata hanasa bin zab’in zuciyarsa……
Ba k’aramin mamaki ya shiga ba da ya ji Ya’ishan ta ruk’o hannunshi, dan haka ya juyo a mugun firgice
Ita kanta su Siyaman ta hango
shiyasa ta yin hakan, Hannun
ya kalla kafin ya d’ago! Ranshi a mugun b’ace yana shirin fara magana ya ga fuskarta shab’e-shab’e da hawaye.
Da mamaki ya ce ”Ke!lafiyarki kuwa?”
Cikin kuka tace”na san saboda sister d’inta kake ta wahalar da ni, haba Ya Najeeb!
Ta ya kake tunanin ba zan ji
haushinsu in kuma tsanesu gaba d’aya ba? kalli fa yadda ka ganni a halin da ka ganni amman sam baka damu ba maimakon hakan ma barazana ka ke yi min akan za ka gayawa Yash mun tab’a dangin matarsa.
Shekara nawa muna tare
tashi d’aya ka juya min baya ya kake so in yi?
Shin ba ka tsoron hakki?
Idan ka yaudareni fa Allah ba zai barka ba.
A tunanina a matsayin k’anwa nake a wajen ka bayan masoyiya, ta yaya za ka min haka tashi d’aya sannan kuma kace ni da y’an uwana ba za mu ji haushin su ba?”
Tausayinta ne ya d’an kama shi ganin yadda take kuka wiwi…tabbas ya kamata ya rabu da Ya’isha da wurwuri ya yi setting nata free tun kafin a samu lahani da ɓarnar da ta fi hakan….”
Yana cikin wannan tunanin ya ji kansa ya wani irin sarawa sakamokon rungumar da ta yi masa.
Cikin kuka tace
“Allah ban shirya barwa kowa kai ba”.
Bai tsaya wata wata ba ya zarota da dukkan k’arfinsa cikin fushi ya ce ”ba ki da hankali ne? wanne irin shirme ne wannan?..”
Ya fad’i hakan yana juyawa domin ya ga ko Siyama ta gansu, bai ga kowa ba amman tabbas ya san ta gansu….ji ya yi kamar ya rufe Ya’isha da duka! Ko hannunshi bata tab’a rik’ewa ba sai yau! kuma yau d’in ma har da runguma tsabar iskanci…..
Ganin idan ya ci gaba da tsayuwa a gaban ta zai iya mammaketa ne ya sa kawai ya juya da sauri, ko a parlourn bai yarda ya ci gaba da zama ba tashi d’aya ya fice, ya na fita ya nufi motarsa ya shige ya zauna ya kunna ac…..
Bashi da tantama Siyama ta gansu tabbas shiyasa ta yi sauri ta gudu, shikenan ya san tun kafin
aje ko Ina har ta fara yi masa kallon d’an iska kuma mayaudari.
Suna shiga kitchen Siyama ta cika Hannun Munirat tukunna ta dafe k’irjinta ta na mamakin
zafin kishin Najeeb da ta ji!
Yau ne fa kawai suka d’an samu momment amman kalli yadda zuciyarta take tafarfasa na ganin shi da wata da tayi.
Dariya Munirat ta yi kafin ta ce ”Tab! Amman ba ki riga kin shiga university ba ko?
Kina ina couple suke yin abunda ya fi wannan ma in public! Dan kinga d’an wannan shine duk kika koma haka sai kace wadda taga wani abu babba….”
Cikin katseta
Siyama tace”couple?Mijinta ne?”
“A’a, amman saurayinta ne
kuma shi za ta aura, na ji Mommyn su tana fada rannan
Kamar sun kai kusan 7 years tare,
tun tana secondary school…amma gaskiya ni kaina ta bani mamaki saboda ban tab’a ganin wani d’an gidan da bad behavior haka ba
bayaga Kausar sai
Kuma Yassir, ban yi tunanin suna irin hakan ba suma, shi kansa Ya Najeeb d’in he looks decent(kamar nutsatstse)..
Anyways sha…su ta shafa!.
Kina gayamin Manubiya a buk take? maybe ma mun taba haɗuwa fa”
Sai yanzu Munirat ta lura da yadda sam hankalin Siyaman baya a kanta.
Dan haka ta d’an kyasta ƴan yatsunta ta ce ”Hey!”
Firgigit Siyama ta yi,
dakyar ta d’an daidaita b’acin ranta tukunna ta kalleta ta ce ”Yassir! wanda suka kawo mu shi da Ya Najeeb ko?,dama daga ganinshi wanann d’an iska ne”
sai kuma ta yi sauri ta ce ”Au, yi haƙuri, brother dinki ne ko?”
Shiruuu Munirat ta yi daga jin zancen Yassir…wanda zuwa wannan lokacin ta gama tsara yadda za ta yi su shirya dan tana mugun son Yassir gaskiya…..
“Munirat kin yi shiru”
Muryar Siyama ta katse mata tunani.
Numfashi Munirat ta fesar kafin tace”A’a ba brother d’ina bane, mu bar maganarsa kawai”
“Ok”Siyama ta ce kafin ta d’aura da cewa “dama na ga kamar yana ɗan ciki da ƴar uwata ne shiyasa na ke so in d’an yi confirming halinsa kafin komai.”
Dasauri Munirat tace”da gaske?
wanann farar ko?”
“Eh” kawai Siyama tace
daga haka ta chanja hirar
ba tare da ta tsaya ta lura da fuska da kuma yanayin Munirat ɗin ba..
A parlour Su Baba Larai suka zauna Yassira kuma ta wuce sama wajen Yahanasu, ba abunda ya basu mamaki ya kuma basu takaici kamar yadda su Aisha suka rarrabu
Kamar irin sun fahimci wani abun kuma sun lura Yahanasu ce ta nace akan
ayi hakan…….
Tana zaune akan couch d’in
private balcony na d’akin, tana tunani ta ji an bud’e k’ofa, shiyasa ta mik’e da sauri
ta shigo cikin dakin.
Ido biyu sukayi da Yassira dan haka tace “Ashe kece”
“Ko akwai wani da ki ke tsammanin zai shigo bayan ni ɗin?
Kema ki ka shigo ballantana kuma ni?
A tunanina da lissafina na san na fi ki iko da d’akin nan da gidan nan ma gaba daya”
Yassira ta fad’i hakan tana mai k’arewa d’akin kallo.
Numfashi Yahanasu ta fesar kafin ta matsa kusa da ita ta tsaya tukunna ta ce ”daga ƙarshe dai! Gashi kin fito da fuskarki ta asali kenan ko?
Hakan yafi ai! Dan kin san ni I hate pretence(na tsani riya), sannan FYI (ina so ki san cewa) da ni da ke duk iko d’aya muke dashi da d’akin nan,
Kawai ke kina rayuwa ne cikin ruɗi!”