← Book details Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 66 OF 152

Sashe 66

Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Runtse ido Yashjub ya yi, yayinda Manubiya ta yi saurin zare hannunta a cikin na Yashjub ta d’an matsar gefe kad’an.
“Babu alamar hankali ko sanin ya kamata a tsarin Yassir kwata kwata”
Ta fad’i hakan a k’asan ranta tana mai sake had’e rai sannan ta d’an chuno baki
Hakan da ta yi kuwa ba ta sani ba ba k’aramin burge Yassir ɗin ta yi ba…k’arasa shigowa cikin d’akin ya yi sarai ya lura da kallon mamakin da Yashjub yakeyi masa amman ya watsar da shi ya k’araso gaban su ya tsaya yana mai cewa
“Waenchan ne luggage d’in ko?bara in fara ragewa.
Antynmu Ina kwana”
Dakyar tace”lafiya” daga nan ta ja k’aramin trolley d’in da yake a gefenta ta fice daga d’akin.

A parlourn chan k’asa ta had’u da Yadira, bata ko sake kallon inda take ba, itama Yadirar haka bata kalleta ba bata kuma kulata ba.
Haka Manubiya ta fice ta Isa parking lot d’in gidan ta tsaya dan ba ta san a cikin motoci ukun a wacce za su fita ba.

Ta yi mamakin ganin har da Yadira a y’an kwaso kaya dan tana tsaye taga sun sauk’o gaba d’ayansu. Ba ta yi mamakin ganin Yadira ta fito da iyaka akwati d’ayan da ta zo da shi ba maimakon duka biyun, saboda dama ita ta san ba tafiya zatayi ba gaba d’aya, kuma dama bata d’auka a ka ba, k’ark’ari dai abunda ta sani shine bazata d’auki raini ba kowa ya tsaya a iya matsayinsa idan kuma ta ga rawar kan mutun ya yi yawa tou zata dawo da shi saiti, ta yi musu na bak’unta kafin ta gama sanin alk’iblar su yanzu kuwa tunda ta riga ta fahimta shikenan…
Bazata wulak’anta su ba ba za ta k’i su ba tunda dangin mijin ta ne su ɗin amman fa bazata tsaya a taka ta ba.

Dole sai dai a yi mota biyu dan haka Yashjub ya bawa drivern d’ayar motar aka saka akwatin Yadira a ciki,su kuma akwatunan su a boot d’in motar da za su shiga..har zai
hana Yassir ya tuk’asu zuwa airport d’in yace kawai ya zauna shima a motar driver tare da Yadira sai kuma ya kyalesa
suka zauna a gaba su biyu Manubiya tana a baya…
Hakanan suka musu rakiya zuwa mallan Aminu Kano international airport,sai da sukaga jirgin su yana shirin boardin tukunna Yadira da Yassir suka nufi gidan Daddy
shi kuma drivern ya maidawa Yashjub motarsa guda d’aya ya fakata ya rufe harabar gidan da aka bar masa makullin ya kama gaban sa dan Yassir yace masa”kar ya damu zai ajjiye d’aya motar Yashjub d’in a gidan Daddy kawai.”

Yashjub so yake yi su dad’e sosai a tafiyar nan su fahimci juna da shi da matarsa, dan ya san su Yasira har ma da Mommy ba za su ba su wannan chance d’in ba…Shiyasa ya riga ya gama tsarawa akan ba za su dawo kwana kusa ba sai sun huta sun sha soyayyarsu kafin nan kuma ya san inshaaAllah Daddy ya huce dan ya san yanzu haka ya sake hawa game da case d’in Yadira dan haka ba fahimtarsa zai yi a kan komai ba,shiyasa zai bar shi ya huce ya d’an yi nesa da su kafin su dawo ya samu ya takawa y’an gidansu burki ba tare da Daddy ya ja masa layi ba, dan ba zai iya rayuwar da suke so ya yi ba, ba zai zuba ido yana kallon hawayen matarsa a kullum saboda su ba, dole a chanza tsari…

Kasancewar Airline na Cyprus ba ya zuwa Nigeria a ya sanya tafiyar ta su ta kasance da transit a Egypt dan egypt air d’in suka bi..
A babban hotel na Egypt suka sauk’a dama Yashjub ya san sai sun d’au lokaci ai kuwa ilai sai da sukayi awanni dan sai cikin dare wajajen 2 tukunna komai ya yi settling suka d’auki hanyar Cyprus.

Flight d’in su yana landing suna fitowa suka samu mota…
Tare suka saka kayayyakin a boot da shi da drivern daga nan suka d’au hanya bayan Yashjub ya basa adress d’in inda zai kai su.

Ita kam Manubiya ta yi laushi
shiyasa suna shiga motar da ya janyota ta gishingid’a a jikinsa sai bacci.
Sai da suka k’arasa tukunna ta ji ana tashin ta a hankali…cikin
kulawa kamar ya samu kwai haka yake lallab’ata yana tashin ta kamar baya so dan ba dan drivern na jiran su zai
koma ba to da ba dalilin da zai
sanya ya tashe ta, yadda yaga tana baccin ta peacefully ya san ba k’aramin dad’i baccin ya yi mata ba.

Tana bud’e ido suka yi ido biyu dan haka ta sakar masa wani lallausan murmushi kafin ta d’an gyara ta mik’e ta zauna.

Cikin kulawa yace mata “mun iso, bara in bud’e, a rufe ne gate d’in.
“Tou” kawai ta ce.

Ta na jinsa da shi da drivern suka fita suna ta faman zuge gate, sai da aka gama parking motar tukunna ya lek’o ya mik’o mata hannu yace “muje ko”
Jinjina kai ta yi a hankali, kafin ta miƙa masa nata hannun ta ya riƙe sannan ta fito daga bayan motar.
dama tunda yace mata zai bud’e gate ta yi mamaki dan ita a tunanin ta za ta ga hotel ne amman sai ta ga gida flat mai d’ankaren kyau mai d’auke da d’an madaidaicin compound..
Murmushi ta yi suna fitowa dan gidan ba kad’an ba ya d’auki hankalin ta ya burgeta gashi dai d’an mitsitsi amman ya k’ayatu iya k’ayatuwa.

Sai da driver d’in ya taya Yash suka gama kai kayan bakin k’ofar shiga, drivern ya tafi ya rufe gate d’in tukunna ya dawo.
Yana zuwa ya sunkuya ya d’auke ta in a bridal style..
Murmushin ta yi ta zagaye hannunta a wuyansa,a haka suka k’arasa bakin k’ofar..
Tumb d’insa ya saka wata murya ta yi welcomin d’in shi had’e da fad’ar sunansa daga nan ya tura suka shige cikin k’ayataccen parlourn…
Saida ya kai ta kan one seater tukunna ya zaunar da ita ya zauna a gefen ta kafin yace
“Do u like it ? Gidan! Ya yi miki kyau?”
Sai da ta kuma k’arewa parlourn kallo tukunna tace “Sosai ma kuwa, ya yi kyau, over”
Ta fad’i hakan tana kallon parlourn..
murmushi yayi ya sauk’e ajiyar zuciya kafin yace
“MashaaAllah, na ji matuk’ar dad’i da kikace ya yi miki saboda dama Inata adduar Allah yasa yayi miki kyau…wannan shine Gida na farko da na fara siya a rayuwata,yana da matuƙar mahimmanci a gareni, its soo dear to me shiyasa na mallakawa wadda ta fi kusanci da ni zuciyata da kuma ruhina…
Gidanki ne…da na baki, as a
gift, halak malak”

Da sauri ta juyo ta kalle shi,
sai kuma ta kalli parlourn kafin ta sake juyowa tace
“Bai yi yawa ba kuwa?…ba ma a Nigeria ba fa..”
Cikin janyota jikinsa yace
‘’gifts ɗin da kika bani Baby sun fi k’arfin wannan, idan na ce zan biya ko zan kamanta to fa sai na baki komai nawa tass ba tare da na kamo k’afar biyan ki ba ma..to amma kinsan an ce yaba kyauta tukuici, shiyasa na baki nawa tukuicin, ki karb’a kawai ke dai ki yi mini alk’awarin kasancewa a tare da ni a ko da yaushe..idan ki ka yi mini haka kin gama min komai Baby…”
“Already, takardun a ƙarƙashin sunanki su ke, tomb print d’in kawai za mu mayar ya koma naki shima.”

Ahankali tana kallonsa tace”da ni da kai ɗaya ne we are one, remember?
Dan haka ba sai an chanja tombprint d’inba..a ko da yaushe za mu kasance tare har abada inshaaAllah”
Sai kuma ta sunkuyar da kanta kafin ta d’ago ta kallesa kawai ta kasa magana, dan Wallahi ita ba ma ta san ta Ina za ta fara yi masa godiya ba, gaba d’aya ya saka ta a shock!
Da kyar ta bud’e Bakinta tace
“Nagode Sosai, Allah ya saka da allhairi na s……”
Da sauri ya rufe mata baki yace “ni ne da godiya”
Bai sake ba ta damar yin magana ba sakamokon kissing dinta da ya fara yi da sauri da sauri…
yadda ta ji jikinsa har karkawa yake yi ne ya sanya ta hak’ura kawai dan ta san ba sarara mata zai yi ba……

Sai da gari ya fara haske tukunna ya samu kanshi..
bayan kamar mintuna biyu haka, ya d’ago yana kallonta yana mayar da numfashi still, yace”mu je mu yi sallah, sai in nuna miki gidan naki, ke kika tsayar da mu ba mu yi tour ba”
ya fad’i hakan yana murmushi.

Turo baki ta yi ta d’an kauda kai dan haka ya yi dariya ya fara yi mata cakulkuli….
duk yadda ta so dakewa sai ta gagara ta fara dariya itama, a haka ya d’auke ta suka nufi d’aki tana cewa”dole ma ta yi kib’a ko dan yadda yake d’aukarta anyhow ɗinnan in ya so daganan sai ta ga yadda zai yi…..”

Wanka suka fara yi suka yi sallar Asubah suka ci abincin da ya yo musu order, tukunna ya ce su je ya nuna mata gidan…

D’akuna uku ne sai kitchen da store da tafkeken parlour.
Ta baya kuma pool ne da pool house sai garden ata gaban gidan mai d’ankaren kyau….

Suna gama zagayen ya kira masu gyaran gida aka zo aka gyara aka share aka goge koina tass tass.
Sun ci sa’a kusa da restaurant suke shiyasa order d’insu ba ya d’aukar lokaci…..sai la’asar tukunna komai ya kammala suka yi wanka sukai sallah.
Kwata kwata hutun awa uku ya bari suka yi daganan ya d’aura daga inda ya tsaya…ita kamar wanda ake yiwa ruwan energy ma haka take ganinsa dan sam ba ya gajiya…..
Chapter 66 · 0% Book details