Sashe 104
Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
K’urawa Yassir ido kawai Junior ya yi…a rayuwarsa wallahi ko tari idan Yassir ya yi ya san me yake nufi, shiyasa tun d’azu da ya sauk’o ya fahimci akwai abunda ya ke shiryawa yanzu kuwa da ya ga sun fara tsintar kayayyakin kausar kai tsaye tun kafin a tafi ga conclusion(ƙarshen al’lamarin) ya fahimci komai, ya gane ina suka dosa…Tabbas Yassir ya tabbata d’an iska…amma bari komai ya lafa zai titsiyeshi ya gaya masa dalilinsu shi da Kausar na aikata hakan kuma wallahi muddin ya ji dalilin bai gamsardashi ba to sai ya tona musu asiri,kasancewarsa best friend d’insa ba shi zai sa ya tsaya yana ji yana gani a k’ullawa Yashjub sharrin da bai ji ba bai gani ba.
Yusra za ta yi magana Daddy yace”Fita nace!”
Da k’arfi…
Ficewa suka yi ita da Yadira da Junior, tun kafin ace wani abun Munirat ma ta bi bayan su Yusra hakama Yasmeen.
Da sauri Yasira da Ya’isha
dan karma a koresu suma suka shiga suka wuce suka nufi d’akin da ya ke a nan k’asan, wanda suka ga k’ofar a d’an bud’e….
Kausar tana jin Yassir ya turo k’ofa ya shigo ta yi tsaki..
tabbas ta san Yassir da gangan ya bata k’ank’anin lokaci, wato ta samu ta shirya komai iyakar wanda suka tsara..gashi yanzu ko gama hakin jan Yashjub ba ta yi ba har ya zo wanda ba dan hakan ba wallahi ba ta ga dalilin da zai hanata cin moriyar wannan tsadadden lokacin mai muhimmanci ba.
Ahankali ta yi kissing Yashjub na kusan sakan biyar kafin
ta lalubo sachet water d’in da yake ajjiye a gefenta ta kawo dede setin fuskar su
ta matsa da k’arfin gaske
ya fashe da k’arfi toss!! A kan fuskarsa.
…..wata bagwariyar nannnauyar ajiyar zuciya
Yashjub ya sauk’e, tun lokacin da ya rungume Kausar
ya fara ganin dishi dishi
tace
“Zata kaisa d’aki ta kira Doctor”
tun daga wannan lokacin jin sa da ganinsa suka d’auke sai yanzu tukunna suka dawo
Abu d’aya ne ya basa tsananin mamaki, d’ayan kuma ya firgita sa ya saka shi a tashin hankali….na farko yadda gaba d’aya wannan mahaukaciyar desire d’in (sha’awar) da tsananin ciwon kai da jiri suka d’auke masa d’iff ya daina jinsu lokaci guda
Komai ya dauke, dan
Garau yake jinshi…
Sai kuma abu na biyu wanda ya firgita sa dan indai ba mafarki yakeyi ba tou tabbas yau mummunar bak’ar rana ce a garesa saboda kamar naked(tsirara) ya ke jinsa daga shi har Kausar d’in wadda tashi d’aya ya fahimci da ita yake
tare, tunda itan ce d’azu a tare dashi daga shi sai ita, kuma har yanzu ga k’amshin turarenta nan yana ji…
A hankali ya d’an fara k’ok’arin bud’e idanunsa domin ya tabbatar, ya ji Yasira
tace
“Subahanallah!!”
Sai kuma yaji
Mutane sun taho
rututu!! gaba d’aya sun antayo cikin d’akin…
Runtse idanun naasa kawai yayi, ya koma ya kwanta a kan
Kausar d’in, dan bai ma san me zai yi ba!
In Banda sunayen Allah babu abunda yake karantowa, yana ji kamar ya shak’e kansa!
Juyawa Ummi ta yi ta fita hankalinta a tsananin tashe ranta a masifar b’ace.
Tana fita Baba Larai ma ta fita…
Yahanasu kuwa kuka ta fashe da shi…..a ranta tace
“wannan wacce iriyar k’addara ce Yash da Manu suke ciki daga an toshe wannan sai wannan!waenna irin mugayen mutane ne haka Ubangiji ya taundumosu a tsakiyar su?!”
Ba za ta iya ci gaba da ganin wannan abun bak’in ciki, takaici da tashin hankalin ba, shiyasa kawai ta juya ta fita, dan tabbas idan ta ci gaba da zama to za ta iya kashe Kausar a take.
Kallonsu Yassira Daddy yayi kafin yace”kuma sai na ce muku ku fita!!!.
Ba na kori kowa ba tun d’azu???”
Ya daka musu tsawa
Dasauri duk suka fice,
d’akin ya rage daga Mommy, Daddy Kausar, Yash sai Yassir
wanda idanunshi suka kad’a sukayi jazir.
Suna had’a ido da
Kausar ɗin ta fashe da wani irin kuka, sannan ta fara k’ok’arin tashi
Cikin kukan tace
“Yassir pls….
Wallahi
dole ya yi min..forcing ɗina ya yi.”
D’aga mata hannu kawai yayi,hawaye suna zirara daga idanunsa, sai ya bud’e Baki zai yi magana sai ya kasa..
Yayi hakan ya fi sau uku,
kafin kawai ya juya ya fita.
Tausayin shi ne ya lullub’e Daddy…ya fara ji kamar ya rufe su da duka…cikin tsananin b’acin rai yace”Ki tattara kayanki ki bar gidan nan!
kafin nan da awa d’aya tak!”.
Daga haka ya juya ya fice
Dasauri Mommy ta bisa, har ya kai tsakaiyar parlour,
ta rik’o hannunsa tace
“Wallahi babu inda za ta je!
Wai mai yake damunka ne?
Mai ya sa a ko da yaushe idan Abu ya faru sai ka huce a kan Kausar ne?
Laifin ta ne?
Idan ma tanada laifi shi kuma Yashjub ɗin fa?
Kuma fa kana ji tace dole yayi mata a gabansa amman bai musa ba!”
Da mamaki Daddy yake kallonta kafin yace”Khadija ke wacce iriyar dabbar uwa ce???
Baki ganin abunda Yarinyar nan take mayar da ya’yanki ne?
Ta lalata Yassir yanzu ta koma kan Yashjub, mutum da aurensa!
Brothers fa
kuma
Ya’yanki Khadijah
amman bakya gani???”
Ya yi mata tambayar kamar zai
rufeta da duka tsabar takaici da tsana!
Bai jira Jin amsartaba yace
“My decision is final!
Kausar za ta bar mini gida kafin nan da awa d’aya!, tun kafin ta fara bin y’ay’ana mata tana lalata musu tarbiyyar da na sha wahala wajen yi,tunda ta riga ta gama lalata mazan…ba ku Isa ba wallahi,da ke da Kausar ba ku Isa ku tarwatsa mini zuri’ata ba.”
Daga haka ya juya zai fita ta sake ruk’o hannunsa,
Ido cikin ido tace
“Nima bari ka ji nawa decision ɗin!
‘babu inda Kausar za ta je!idan kuma ka nace akan hakan
Tou
Tabbas nima zan bita.”
Dasauri yace”Alhamdulillah!!!
abunda na dad’e Ina son gani kenan!
Bari kiji in gaya miki
Khadija ranar da za ki bar gidan nan ki bar cikin rayuwata
Itace
Ranar da nake kwad’ayin gani all my life!!”
Duk yadda Mommy ta so daurewa sai da hawaye suka zubo mata, cikin d’aci da barazana tace”shikenan zan tafi!da
Yassira
Yasmeen
Ya’isha
Yusra
da Yadira
sannan zan had’a har da Yahanasu tunda ni ce na zame mata uwa!
Yashjub da Yassir ma na san shekaruna suna yin gaba tare za mu zauna da su da matayensu,kaga wa gari ya waya?kai ne zaka k’are Kai d’aya kwal, daga kai sai Ummi da agolar y’ar ta wadda ba zata ji tausayinka ba idan ka tsufa!”
Cikin son fahimtar wani abu tace”kuma wallahi sai na ganka a prison tukunna hankalina zai kwanta, dan sai duniya ta ji abunda ka aikata ga amaryar ka Khadija,ka ce Mallan Lawal yana raye bai dad’e da rasuwa ba na ji shi babu hakkinsa a kanka amma Khadijah kam wallahi sai ka biya sakamokon abunda ka aikata wala da ranka ko kuma da lafiyarka!….
Babu abunda zan b’oyewa duniya , ko Yahanasu, kowa sai ya san abunda ka yi.Tunda ka nuna saboda hakan ne kawai kake jurar ganina a gidan nan ko?
To yau nima gashi na fito maka a mutum!
Idan ka ga dama ka cigaba da yi mini barazana ni ko Kausar akan barin gidan nan ka ga ikon Allah.Ka riga ka nuna mini babu so ko k’auna a tsakanina da kai, dan haka nima ba zan
ji tausayinka kamar shekarun baya ba,fito na fito za mu yi da kai a cikin gidan nan daga yau!
Ko dai ka hak’ura ka zauna da ni da Kausar
ko kuma ka sha mamaki!.”
Kallonta kawai Daddy yake yi, zuciyarsa ta na tunzura shi da ya shak’e ta ta mutu kowa ma ya huta.
Tabbas duk abunda Babba ya hango Yaro bai Isa ya gani ba, Hajiya mama ta yi gaskiya dan gashi tun yanzu ya fahimci tsaff Mommy zata rabashi da ya’yanshi, kuma kamar yadda ta fad’a tsaff za ta kaishi prison
wanda shima abunda yake so d’in kenan amman ba zai tafi prison ya bar y’ay’ansa a hannunta babu wanda yayi aure ba, iyaka muguwar illa da gurɓata masa tunanin yaƴa ma da ta yi kad’ai ya isa, kuma dole shi ya kamata ya dage ya gyara ba wai ya bada goyon baya wajen bata k’ofa ta ci gaba da aikata b’arna ga ahalinsa ba….
Ajiyar zuciya Mommy ta shiga sauk’ewa a b’oye dan a yadda Daddy ya yi shiru bai tanka mata game da lamarin Khadija ba ta fahimci abunda take tunani ba haka bane, dan yadda ransa yake a b’acen nan kuma ta sako maganar, to fa inda ace yana zargintane da tsaf zai yi mata zazzagar kwanyo…to amma me yasa ya yi hacking wayarta, sannan me yasa yake yi mata kallon da kowa ya gani ya san kallon tsana ne tsagwaronsa!!.
Daddy kuwa ya riga ya tsara ne akam zai yi yadda Hajiya Mama tace, shiyasa har zuciya ta ciyo shi zai yi ta ta k’are a take, sai kuma kawai ya yi shiru ya danne zuciyar tasa da kyar, ya zuba mata ido kawai tsanarta tana sake shigarsa.
Suna tsaye a haka…suka fara jiyo ihun Kausar.
a minute before now.
(Minti ɗaya kafin yanzu).
Su Daddy suna fita Yashjub ya mik’e ya zauna,
Jallabiyarsa da ya gani a yashe a k’asa ya d’auka ya saka tukunna ya janye bargon daga jikinsa.
Ya daina jin jiri, ya kuma daina ciwon kai sannan desire d’in ma ta tafi, amman fa dishi dishi yake gani tsabar tashin hankali.
Yana juyowa ya yi sauri ya d’auke kansa,saboda a yadda ya yaye bargon ya barta! a hakanta take still tana nan a kwance ko kyalle bata ja ta rufa ba.
Wata kalar arniyar tsanar ta ce ta lullub’esa tashi d’aya!bai san lokacin da ya yi kanta ba! ya hau kifa mata mari ba ji ba gani!.
Bayason dukan mata sam,
sannan shi kanshi ya san marin da yake kifawa Kausar a halin da ake ciki tsaff zai iya kashe ta!
Yasan idan ya kasheta
ya yi babban laifi amma gara ya kasheta ya tafi jail
a kan dai ya zauna bai yi mata komai ba ya barta tana rayuwa
a doron k’asa bayan shi ta tarwatsa shi ta tarwatsa rayuwarsa……