← Book details Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 58 OF 152

Sashe 58

Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ashe haka take!wacce iriyar kyakkyawar halitta ce wannan mai tafiya da imanin d’an Adam…tabbas ya zama dole Yashjub ya mutu kwanan nan
ta yadda cikin sauk’i zai had’a Kausar da Manubiya a matsayin matansa ya yi rayuwa mai dad’i.Dan bayan Kausar ba ya jin akwai wata da ya ji yana so ya yi rayuwar aure da ita bayan wannan baiwar Allahn.

“Yasir’’
d’in da Yashjub yace maasa a d’an zafafe ne ya dawo dashi daga duniyar da ya lula.
Wani lumshe idanuwa yayi wanda hakan ya kuma k’ular da Yashjub, kafin ya bud’e ya ce
“Welcome”
Sai kuma ya juya ya kalli Manubiya wadda tashi d’aya ta ji kamar ta rufe sa da duka ganin irin kallon da ya shiga yi mata….
Murmushi ya d’an yi yace “antynmu, barka da zuwa, bismillah”
Ya fad’i hakan yana nuna mata k’ofa, kafin ya d’aura da cewa
‘’Yau dai Ya Yash ya bari anga fuskarki”

Da kyar da mugun kyar Manubiya ta k’ak’alo wani d’an guntun murmushi wanda ya tsaya a iyaka labb’anta ne tukunna ta bi bayan Yash wanda ta ga ya juya kawai ya ruk’o hannunta suka nufi cikin parlourn.

Bayan su kawai Yassir ya bi da kallo yanajin yadda k’irjinsa yake wani irin bugawa…yadda
ya kafe Manubiya da ido yana k’are mata kallo hatta yanayin kwalliyar stones d’in jikin rigar ta sai da ya gani ya haddace ta cikin mayafin ta.

Suna shigewa ya sauk’e wata nannauyar ajiyar zuciya ya jinjina kansa kafin yace “da sake!”

daga haka ya sa kai shima ya nufi cikin parlourn…

A main parlourn gidan suka samu Mommy, Baba larai, Ya’isha da Kausar a zaune suna magana da alama mai mahimmanci ce,
sallamarsu ce ta sanya sukayi sauri duk suka d’ago suka zuba musu idanu….
tashi d’aya yanayin fuskar Ya’isha ya sauya ganin Yashjub d’in ne ma ya ruk’o wa Manubiya jaka.
Da sauri ita kuma Kausar ta mik’e ta wuce sama
Yayinda Baaba larai ta mik’e ta fara cewa “Lale marhababiki Amarya surukar mu…
Yashjub bismillah mana, k’araso!
Ku shigo ciki, ya ka barta nan bakin k’ofa a tsaye..”
Ta fad’i hakan tana nufar su tana Isa ta kamo Hannun Manubiya ta zare a cikin na Yashjub ta ja ta suka nufi cikin parlourn.

Dakyar Manubiya ta iya janye idanuwanta a kan Baba larai,
sarai ta shaida ta..itace suka ce sai ta durk’usa sannan duk wani mai hankali yana kallon fuskarta tashi d’aya zai shaida ba farin ciki takeyi da auren ba, amma kalli yau itace kamar zata cinye ta! Tabbas waennan shaid’anu ne!!! wato idan a gaban Yashjub ne ba za su nuna mata k’iyayya ba kenan!
dan ta lura da Yasira ma d’azu saida ta bari babu Yashjub a wajen tukunna ta gaggaya mata maganganu…..

A gefen Mommy daff da ita Baaba Larai ta zaunar da Manubiya kafin ta ce ”bari in je in kawo muku ruwa, sannu Amarya, lalle marhaba”
Ta fad’i hakan tana mai wucewa da sauri har da d’an yin tuntub’e.

Yashjub ne ya d’an tsayar da ita ya sanar da ita batun kayan zak’’i, dan haka ta karb’i makullin motar tasa tace ‘bari ta nunawa su gwaggo su kwasa su saka a kitchen.’

A hankali Ya’isha ta mik’e kamar ba itace ta baro gidan d’azu tana fushi ba ta k’arasa wajen Yash tace “kawo jakar ni in rik’e mata”
Ta fad’i hakan tana mai amsar jakar.

Tashi d’aya kawai sai ya ji kunyar Mommy ta kama shi, dan haka ya cika mata jakar ya k’arasa inda Mommyn take ya zauna a gefen ta dai-dai nan su Yassira ma suka fara sauk’owa, da alamar Kausar ce ta gaya musu Yash d’in ya zo…..

tare suka sauk’o gaba d’ayansu har da Daddy, da alamun tare suke da shi a saman, shi Yashjub ma bai yi tunanin Daddyn yana nan ba, ya d’auka yana office duba da yadda shi baya nan Yasira ma ya ga yau ba ta je ba.

A hankali Manubiya wadda tun d’azu ta ke jin nauyin zama a kusa da Mommy ta d’an sullub’o daga kan kujerar tace “Mommy Ina wuni”

Saida Mommy ta yi namijin k’ok’ari dagasken gaske tukunna ta iya dafa kanta a hankali tace “lafiya y’ar albarka, ya bak’unta”

“Alhamdulillah”tace, a ranta tanajin wani sanyi dan yadda Mommyn ta yi mata ya sanya ta ji dad’i sosai, ta kuma fahimci itan tana sonta ba kamar su Yassira ba..ta san dama zuwa d’auko ta da kai lefe ba hurumin Mommy bane amma da aka d’aukota tace “a wuce da ita ba sai ta zo ta gaida ita ba!” da kuma yadda take kiranta a waya amma ba ta amsawa ya sa ta d’an ji tsoro ta shiga damuwa da tunani…..

Muryar Daddy ce ta katseta jin yana cewa”Manubiya mik’e ki zauna a kan kujera mana, tashi
kinji”

Murmushi ta yi sai da Yashjub wanda shima yaketa zuba murmushi dan ba kad’an ba ya ji dad’in yadda iyayen nasa suka nuna kulawar su ga matar tasa, ya d’an sunkuya ya kalleta a hankali yace “mik’e ki zauna mana..
Daddy yana magana”
Tukunna ta mik’e ta zauna a kusa da Mommy inda take tun farko tanajin wani nauyi da girmanta yana ratsa ta, dai dai nan su Daddy suka k’araso suka zazzauna, shima saida ta durk’usa har k’asa tukunna ta gaidashi ya amsa da kulawa.

Da sauri yace”Ummi bata sauk’o ba Yassira je ki ki kirata”
sai kuma ya zaro waya yace “Bari in kirata”
ya fad’i hakan yana dialing number Ummi, ba ta dad’e tana ringing ba ta d’auka.
Tana d’auka yace “ki zo munyi bak’i”
daga haka ya katse kiran yana mai tambayar Manubiya “ya bak’un ta”
Cike da girmamawa da kunya suke amsa shi.

Suna a haka Munirat suka sauk’o ita da Ummi.
Da sauri Munirat ta k’arasa ta je ta zauna a kusa da Manubiya tana “oyoyo antynmu, ashe kune Ina wuni”
sai kuma ta kalli Yash ta gaidashi.
Kamar yadda Manubiya ta yi wa Mommy da Daddy haka ta zamo ta gaida Ummi itama..ta kuwa ji dad’i, dan haka ta shiga tambayar ta ya sabon waje ya su Innarta…. mik’ewa Yash ya yi yace”Bara mu lek’a Yahanasu,ya jikin nata?.”
Da sauri Mommy tace”da sauk’i!.Munirat ta kai Manubiya wajen Yahanasu, kai kuma ka zauna munada magana da kai!”
Shiruu ya d’an yi, da sam bai ji dad’i ba , ya san Manubiya zataga kamar an ware ta ne…
Yana cikin wannan tunanin suka mik’e ita da Munirat suka nufi d’akin Yahansun jiki ba kwari.

Lumshe ido Yashjub ya yi har su ka shige bai bud’e ba..

Muryar Daddy ce ta dawo da shi daga duniyar tunanin da ya lula jin yana cewa
“Yash, mai ya faru yau ka koro k’annenka daga zuwan su na farko gidanka?”

Da sauri ya bud’e idanuwansa ya kallesa, sai kuma yayi kan Yassira a zuciye….

Da sauri Mommy ta mik’e ta tsaya a gaban Yasirar tace”ai ni za ka daka ba ita ba! tunda nice nan na gayawa Daddyn naku, ba ita ba!”

Ummi ba ta san kan labarin ba,
ba kuma ta san abunda ya faru ba amman tashi d’aya ta fahimci laifin su Yassirar ne…baya ga haka saboda Allah ta ya Daddy zai biyewa Mommy a zuwan Yashjub da Manubiya na farko gida a fara da case!
Su da ya kamata ace sun saka su a gaba sun yi musu fad’a da nasiha , sannan sun yi k’ok’ari wajen basu chance su fahimci juna, amman kalli yadda tun farko aka sallami Manubiya akace a rakata d’akin Yahanasu, saboda Allah wanne irin rashin lissafi ne wannan?,ya suke tunanin Yarinyar za ta ji saboda Allah…..
Ta san inhar ta zauna to tabbas za a yi fad’a da ita ne,
shiyasa kawai sai ta mik’e tace
‘’Am Daddy bara in d’an baku guri dan Allah”tana gama fad’in haka ta wuce sama, bata yarda ta kuma had’a ido da Daddyn ba….sai da ta had’a da sauk’ar AlK’urani da addu’o’i tukunna ta daina jin matsananciyar tsanar sa, haka kurum ta samu sun shirya shima ya daina fushi da ita da kyar !
ba ta ga dalilin da zai sa ta zauna a wajen da zata fad’i abunda zai ji haushi su yi fad’a su sake komawa ruwa ba.

“Ta fi Nono fari”
Mommy tace a cikin zuciyarta, kafin ta maida hankalin ta ga Yashjub wanda ya ke cewa Yassira da ta b’oye a bayanta “k’ara ta kika kawo?
ke ba ki fad’i abunda kuka yi ba?”
Cikin tarar numfashin sa Daddy yace
‘’Mai sukayi?’’

Tun kafin Yash yayi magana
Ya’isha tace
‘’Wallahi Daddy bamuyi komai ba, dama tunda mukaje ta tare hanya ta hanamu wucewa, sai da ya zo tukunna ta matsa.
Ina ga yanayin fuskar ta ya kalla dan tanata faman kumbure kumbure shine ya kira Yasira ya ce ta kwashemu mu tafi’’

Wani irin takaici ne ya lullub’e Yashjub wanda ya sa ya ji kamar ya finciko Ya’isha daga kusa da Daddy ya feffella mata mari…ya godewa Allah da ba a kusa da shi take ba dan ya san yau da sai ya illatata!
Ganin Yaran suna neman haukatasa ne yasa ya koma ya zauna, ya dafe kansa wanda ya fara sara masa.

Gyaran murya Daddy ya yi kafin yace”Yashjub!! tun wanchan ranar a asibiti na fad’a maka kar ka bada k’ofar da matarka za ta raina y’an uwanka! And again a washegarin ranar da ka yi aure ma sai da na rok’ek’a da kaina akan kar ka bada k’ofar da kawunan ku zai rabu a ta dalilinta, amman naga abunda ka dage, ka durfafa sannan kuma ka ke ta ƙoƙarin yi kenan….
Sam!ban ga dalilin da zai sanya dan ka yi aure ka tsame y’an uwanka a jikinka ba, ba zai yiu ba!!
ba zan zauna in zuba ido zumuncin ku ya tarwatse ba saboda rashin tunanin ka da kuma gigin giyar soyayyar da ka kurb’a.”

Yashjub ji yayi kamar ya d’aura hannu aka yayi ta faman zunduma ihu…ta ya Daddy zai biyewa waennan Yaran, ya hau kan maganganunsu ya zauna daram, sannan ji fa tone d’insa sai kace na mace, yana magana kamar ta mata…
yanzu wannan d’an k’ank’anin abun har ya kai a titsiyesa a gaban su haka…….

Muryar Daddy ce ta katsesa jin yana cewa”ina sauraron ka,
ka fad’amin exactly abunda ya faru.
Chapter 58 · 0% Book details