Sashe 146
Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Kamar yadda Abbakar ya yi masa bayani, hakanan ya maimaita sak a gabanta, sannan ya tashi ya kaimata proof ɗin itama ya nuna mata a wayrsa.
Abbakar yana kuka ya durk’usa a gaban Manubiya yace”dan Allah dan Annabi ta yafe masa!!!…….”
Manubiya ba ta iya ko kallonsa ba, da kyar itama tana kuka sosai ta mik’a masa wayarsa tace”ya tashi ya fita , ba ta son ganinsa!”
Dama ya yi tsammanin hakan daga gareta, amma ya ji dad’in nauyin da ya sauk’e a kansa, dan haka ya mik’e ya yi musu addu’ar ‘Allah ya barsu tare, ya kawar da idanun mak’iya daga kansu’
daga haka ya sa kai ya fice….
…..wasu lokutan a rayuwa dole mu aminta sannan mu rungumi cewa ‘ba fa komai ne abunda muke so zai zamo mallakinmu ba!….asalima wasu lokutan abun kwata-kwata ba alkhairi bane a rayuwarmu!
Sannan idan muka tilasta muka nace akan sai mun samu abunnan to fa in banda koma baya da dak’ile kai babu abunda muke yi wa rayuwartamu!!!…
Tabbas inda ace ya raba Manu da Yash to da ya tarwatsa rayuwar mutane uku! da shi! da ita! da Yash! Tarwatsawa ta har gaban abada, kuma ba zai tab’a samun farin cikin da yake nema ba.
Dan haka Ya godewa Ubangiji da ya wayar masa da Kai ya nuna masa gaskiya..ya san yana son Manubiya fiye da tsammani, amma zai yi k’ok’ari ya manta da ita ya yi moving on a rayuwarsa, ya nemi farin ciki ya daina mayar da kansa baya yana b’atawa kansa lokaci….
Da wannan lissafin ya fice daga cikin gidan yana sharar kwallah, zuciyarsa fal da na sani.
Abbakar yana fita Yash ya mik’e ya k’arasa inda Manubiya take nan a zaune tana kuka….a hankali ya sa hannu ya dafa ta wanda hakan ya sanya ta juyo da sauri ta fad’a jikinsa ta fashe da wani sabon kukan da ya fi nafarko...cikin kukan tace”yanzu ta tabbata ba zan haihu ba kenan??”
Da sauri ya sa
*MANNUBIYA*
*Book 2*
*page 44*

Da sauri ya sa Hannu ya toshe mata Baki tukunna ya ce ”fad’arsu ba fad’ar Allah baceba! Sannan abunda suka yi miki bai isa ya hanaki haihuwa ba sai dai izinin Ubangiji..ki kwantar da hankalinki Baby ki tuna na sha gaya miki ba zan taɓa bari ki yi kuka ba dan sam bai kamata in bari ki yi kuka ba Munnubiya, sannan na daɗe da yi wa kaina alƙawarin in dai har kinada ni to zan gwada ƙarshen abunda zan iya yi in share miki dukkan hawayenki sannan in baki dukkan farin ciki….shiyasa tun a wanchan lokacin na fara shirye-shirye…
Akwai Doctor d’in da za ki gani a Berlin daga yanzu zuwa ko wanne lokaci, dan zai bamu Appointment very soon, na sani…ki daina kuka Manu na san Ubangiji zai bamu haihuwa InshaaAllah Allah ba zai barmu haka ba..na dad’e da yin believing akan zaki haifa mini Yara inshaaAllah zamu zama parents muma...”
Ya ƙarashe maganar a hankali cikin sake janyota Jikinsa ya rungume tukunna ya ci gaba da kwantar mata da hankali, sosai.
Har sai da ya ga ta daina kuka hankalinta ya d’an kwanta tukunna ya kyaleta.
Cikin sharar hawaye ta d’ago ta kallesa tace”inaso insan abunda yake damunka tun kwanakin baya..kar ka b’oye mini dan na san kana da damuwa bayan wannan!!”
Shiruu ya yi, ya d’an k’ura mata ido kamar ba zai ce komai ba, sai kuma yace”Ya’isha ta rasu! Rana d’aya suka rasu ita da Inna..ban san wanne tudu wanne gangare ba amma Mommy ce sila.
A jeji ma ta je zata binne ta ko sutura ba ta yi mata ba….
kuma har yau bata gayawa kowa ba…
Tun a ranar nake k’ok’ari nake so in d’auko y’an sanda a tafi da Mommy amma na gagara kulle mahaifiyata da Hannuna..kuma shirun nan da na yi ni kaina na san ban kyautawa Ya’isha da kaina da kowa ba ma!!!….”
Kukan da ya ci k’arfinsa ne yasanya shi yin shiruuu…kafin chan yace”Mannubiya na tsorata da lamarin Mommy, na firgita sosai, Mommy ta firgita ni, al’amarin ya gigitani da yawa….”
Yadda yake kuka yana magana ne ya sanya ta rungumesa da sauri, wanda hakan ya sa ya yi shiru da maganakawai ya ci gaba da kuka, kamar yadda itama take kuka kamar ranta zai fita…..
Sun fi awa d’aya a parlourn, kafin ta je ta samu Baba, Allah ya so ta bai yi bacci ba, nan tace masa”za su tafi!”
Dare ya yi sosai sosai, amma bai Hana ba dan ya ji dad’in shiryawar da suka yi, dan tunda har tazo ta ce zata tafi to ya san komai normal kenan, dama shi bayaso ta yi yaji ta zo ta kwana masa a gida….hakanan ya je suka yi sallama da Yash ya sanya musu albarka..suka wuce gida tare…..:
Washegari da sassafe su Manu suka hau shiri, dan za su fita su fara shirye-shiryen tafiyar da ta taso musu bagatatan saboda jiya cikin dare suka yi receiving letter daga babban likitan da zata gani a Berlin..zai gansu in the next ten days.
Tun a masallaci Yash ya sanar da Daddy cewa ”Ya dawo da Manu tun jiya, yau kuma suna so za fita da sassafe dan za su fara shirye shiryen tafiya, Manu zataje ta ga Doctor”…
suna gama shiri, sun fito kenan, Yashjub yana reverse kawai suka ga Munirat ta kutso kai cikin gidan, sanye da baban Hijabi!
Ta yi k’iba sosai, fuskarta ta kukkumbura dan da kyar ma Yash ya iya ganeta Manu ce dai tana ganinta ta ganeta.
Fita duk su biyun suka yi daga cikin motar, suka tsaya suna kallonta har ta k’araso garesu…….
Jiya su Junior basu koma gidansu ba, direct daga wajen Manu gidan Daddy suka wuto kawai suka kwana a nan!.
Suna zaune da shi da Daddy, Yasmeen, Yahanasu da Ummi suna breakfast Yash da Manu suka shigo….
Murmushi Daddy ya yi, haka itama Ummi da suka gansu…
Suna shirin yin magana Yash ya k’araso cikin parlourn ya ware murya ya shiga kwala kiran “Kausar!!!”
Da mugun k’arfi.
BULAMA ✍️
0903 441 3252
*MANNUBIYA*
*Book 2*
*final episode*
Idanunta biyu a lokacin, Yaron ya dameta da kukan yunwa!
Dan rabonsa da abinci tun jiya kafin ta tafi wajen makeup.
Kamar ba zata je ba, sai kuma ta mik’e ta nufi k’asan..
Duk mik’ewa su Ummi suka yi, suna masu buk’atar k’arin bayani…tashi d’aya Ummi ta tafi Luu zata fad’i sakamokon ganin Munirat da ta yi ta shigo tana hawaye, da sauri Daddy ya yi saurin rik’eta shima ya mayar da hankalinsa ga Munirat ɗin cikin kid’ima ya ce ”Munirat!!”
Duk sai a lokacin su Yasmeen suka lura da ita, Kausar kuma ta yi turuss ta ja ta tsaya ta gagara k’arasowa nan k’asan, idanunta kyam!! a kan Munirat….
A zuciye Yash ya k’arasa ya fincikota ya wurgota tsakiyar parlourn, wanda sai da ta kai k’asa ta zube tsabar yadda ya yi cilli da ita….cikin tsana da kyama ya k’arasa ya tsaya a gabanta ya ce mata “ina d’anta????”
Gaba d’aya kowa kansu ya yi, dan babu wanda ya fahimci inda Yash d’in ya dosa….
Ganin an zagaye su asirinta yana shirin tonuwa ne ya sanyata ta mik’e cikin in ina tace”Ya Yash, D’an wa kuma??? ban gane ba..”
Mahaukacin Marin da ya zuba mata sai da ya yi sanadiyyar fashewar hancinta da bakinta!
cikin tsawa ya ce ”Kausar ina d’anta!????”
Dafashi Daddy ya yi, jikinsa yana karkarwa ya ce ”Yash, me kake magana akai haka ne, mai ya faru??”
Dai-dai nan Hajiya mama da Yadira waenda suka ji ife ifensa suma suka sauk’o k’asan……
Jikinsa yana wani irin karkarawa yace”Daddy ka barta ta bani amsa, sannan ta yi bayani da Bakinta!!”
Sai kuma ya kalli Kausar a karo na uku ya daka mata tsawa yace
“Kausar ina d’an Munirat???”
Luuu haka Ummi ta tafi ta zube a wajen!!!
Saboda dama ita tunda Munirat d’in ta shigo da ta kalleta ta fahimci kamar haihuwa ta yi, kuma sai da Yash d’in ya fara waennan maganganun tukunna kwakwalwarta ta shiga tariyo mata alamomi da dama data gani a tartare da Munirat d’in kafin ta gudu……
Salati duk y’an parlourn suka d’auka dan suma sun fara d’aukar haske, yayinda Kausar ta fashe da kuka ta durk’ushe a wajen tace “wallahi ni bansan mai kake magana a kai ba…..”