← Book details Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 70 OF 152

Sashe 70

Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ko kallon Kausar bai yi ba,
ko da ta matso ma tana kwarkwasa ta gaida shi bai amsa ba sai da Mommy tace’’Kausar fa tana gaida kai,”tukunna yace ‘’Alhamdulillah’’ ba tare da ya kalle ta ba, dukda haka bata damu ba haka ta matsa kusa da shi sosai ta tsaya ana magana wanda hakan ba kad’an ba ya sake tunzura lissafin Yassir.
Sosai ran Ummi itama ya b’aci duba da yadda Kausar d’in ta matso kusa da Yashjub sosai
kuma Mommy ta rik’e masa hannu ta hanasa matsawa ana hira ana dariya kamar irin so take ma Manubiya ta gani.
Shiyasa tun kafin Manubiyan ta juya ita kuma ta kamo Hannunta suka yi ciki su da Munirat da Yahanasu….
Bata barta ma ta zauna a parlourn ba chan sama side d’inta ta kaita har bedroom d’inta tace “ta huta”daga nan ta cewa Munirat ta kawo
mata abincin da suka yi..
Sai dai a ga shishshiginta amman ba za a yi wannan cin kashin a gaban idanunta ta kyale ba,
Dama tunda ta ji su Mommy sun dage a kan Yassir ya kawo su nan ta fahimci akwai abunda suke son yi….kuma ita har ga Allah girkin da Mommyn ta yi musu ba ta yarda da shi ba, dan haka ba za ta bari ta ci ba, shiyasa ta cewa Munirat ta kawo wa Manubiyan wanda su suka dafa.

Yashjub ya so su zauna a side d’insa amman sai Mommy tace”tunda na kwana d’aya ne, kawai su zauna a guest room inyaso gobe sai su wuce”
“To”kawai yace ba dan ya so ba dan 3 months ago Yahanasu ce masa ta yi ‘ya zauna da matarsa kawai a uk har abada
In kuma hakan bai yiu ba to kar ya kuskura ya dinga favoring d’inta sannan ya d’an rage nuna mata soyayya a gaban su Mommy’…..shima kuma ya fahimci hakan sannan dama ya sa a ransa ba kwana kusa za su dawo d’in ba amma duk yadda yaso ya dad’e ya yi kamar 2 years haka sai ya ji ya kasa, kuma bazai ma yiu ba saboda aiyyukansa duk suna nan, shiysa ya fara shirin dawowa to a wannan time d’in ne ma Daddy ya kira sa wanda kiran da ya yi masa da yanayin yadda ya yi masa magana da sanyin murya gaba d’aya ya kashe masa jiki, duk abunda ya shirya ma zai fahimtar masa kuma zai yi a kan su Yassira gaba d’aya sai ya ji ba zai iya ba dan Daddy d’in sounds so disturbed (ya ji Daddy ɗin a dame sosai) kamar irin ya gaji da damuwa da cases d’innan, tunda har ya sauk’o da kansa…
kuma kamar akwai abunda ya taso masa yake damunsa wataƙilan case d’in marigayiya…shine babba a ganinsa bai kamata ace shine zai saka Daddy a damuwa ko
ya k’ara masa damuwa ba..kwanaki ya yi masa wuta wuta yanzu kuma tunda ya sauk’o to Alhamdulillah shi kuma inshaaAllah ba zai taimaka wajen sake d’aga masa hankali ba,shiyasa ya yanke a kan zai yi ta addu’a kawai komai ya daidaita kuma inshaaAllah ba zai yi abunda Manu za ta kwana a ciki ba…

Baba larai ce tace “mu shiga ciki mana, ku gaisa da Daddy, a ci abinci ko?
Naga su Manubiyan ma har sun wuce.
Tun safe Mommyn naka take yi muku girki..babu wanda ya ci abinci ku ake ta jira”.

Murmushi ya yi ya kalli Mommy yace ‘’Thankyou Mommy’’
Daganan duk suka shige cikin parlourn, Yashjub ya nufi chan sama wajen Daddy, yayinda su Mommy suka fara rarraba idon neman su Manubiya…
Da sauri Baba larai ta matsa kusa da ita k’asa k’asa tace
“To!Ummi ta yi sama da ita, kuma in ba da kyar ba ta cika mata ciki da nata abincin, kinga shikenan mun yi shiri da wahalar banza kenan….”
A zabure Mommy ta nufi sama d’akin Ummi.

Tun d’azu dama Ummi ta lura kamar Manubiyan bata jin dad’i, dan haka suna zama, da Munirat ta fita d’ebo abinci Ummin ta kalli Manu tace
“Baki da lafiya ne?”

Sai da ta d’an sunkuyar da kanta k’asa dan gaba d’aya kunyar Ummin take ji, gashi ta hanata zama a k’asa kan kafet ta d’aura ta akan gadonta d’are-d’are,
tukunna tace
“Zazzab’i nake ji da amai”

Wani kalar murmushi Ummi ta yi kafin tace “Sannu..
Inaga flight d’in ne ya ja miki hakan, akwai pottage na san za ki ji dad’in sa sosai, yanzu Munirat za ta kawo, sannu ko”

Ahankali ta jinjina Kai tace “Nagode Ummi”
Daganan ta d’auko wayarta ta shiga kiran su Innaa, tun a mota Jidda ta kirata ita kuma tace mata sun iso,
amma ita Jidda tana skul, ta kira Innar kuma bata d’auka ba shine yanzu take sake gwadawa….

Ummi na cikin gaisawa da inna Mommy ta shigo…sai da ta basu mamaki sakamokon ganin ta a hargitse da suka yi,
dan haka sukayi sallama da Inna tukunna Ummi ta bata dukkannin attention d’inta tace “ya na ganki a gigice, ince dai lafiya ko?”

Tabbas zuwa yanzu Ummi ta fara kai Mommy bango da yanayin maganganunta masu harshen damo marasa respect!!!.
Ba ta ita take ba yanzun
amman tabbas za ta samu lokacin ta soon,
Shiyasa kawai ta k’ak’alo murmushi da kyar tukunna tace “lafiya k’alau Ummi,
naga ban ganku a k’asa bane, shine na biyo d’aukar y’ar tawa”.

Ita kanta Manubiya sai da ta ji wani bambarakwai, dan yanayin kulawar da su Mommyn suke ba ta yau ɗin ta musamman ce, saboda ko a waya idan za su gaisa da ita ba ta cika yi mata irin hakan ba.

Murmushi Ummi ta yi, tana shirin yin magana Munirat ta shigo d’auke da tray..cikin
tattausan lafazi tace
“Ai ni kam wai da har na yi shishshigi, na sa Munirat ta d’ebo mata abinci, ki bari kawai ta ci anan ɗin dan naga duk kunya take ji, ga kuma gajiya”.

Jinjina Kai kawai Mommy ta yi daganan ta juya ta fita..tana fita ta hango Yashjub yana sauk’owa tare da Daddy.
Cikin sanyin jiki ta k’arasa, suka gaisa da Daddy, dama Yashjub d’in take nema ga kuma har da Daddy a kusa da shi dan haka a ranta tace “perfect’’.
Cikin sanyin murya tace
‘’Am ko za ka yi wa Manubiya magana ta fito mu je ku ci abinci, na gama had’a dining a k’asa Inata jiranku tun dazu’’

Murmushi ya yi yace ‘’ok Mommy.
Bara in kira ta, tana d’akin Ummi ko?”

Jinjina kai ta yi kawai.

Daga haka ya wuce itama ta nufi k’asa Daddy ma ya wuce k’asan.

Yashjub yana shiga ya tarar da su Yahanasu suna ta faman k’ok’arin zuba mata abinci…
Sai da suka gaisa da Ummi dan d’azu su Mommy ba su bashi dama ba tukunna ya kalli Yahanasu wadda ta gama zubawa Manu abinci ta mik’a mata ta fara k’ok’arin bud’e d’aya kular.
Bai so zai ce wani abun ba dan ya san Ummi zata ji babu dad’i amman kuma Mommy ta yi masa magana kuma a gaban Daddy sannan ita da kanta aka ce ta yi girkin shiyasa kawai ya dake ya ce “Am Yaha!ko za ku sauk’o da ita da abincin k’asa ko?,basu gaisa ma da Daddy ba”

“Ok”kawai Yahanasun tace,
Daga nan shi kuma ya juya ya fita dan baiji dad’i ba!
Ummi zata ga kamar ya gwale ta ne.

Yana fita Ummi ta girgiza Kai kawai, ta riga ta san ba yin kansa bane ba.
Daga haka tace musu su sauk’a da abincin.

Ba a dad’e da zama ba, su Manubiya ma suka sauk’o wadda zuwa yanzu zazzab’i ya yi mata ruff! daurewa kawai take yi, ga wani Irin amai da ya taso mata tun d’azu da su Yahanasu suka fara bud’e kuloli har yanzu bai kwanta ba.

Suna k’arasawa ta sunkuya har k’asa ta gaida Daddy, da kulawa ya amsa yana tambayar ta ya Cyprus sannan ya suka baro su Hajiya mama, ta amsa masa da “Alhamdulillah,suna lafiya Alhamdulillah.”
Da kyar saboda wani jirijiri da ta ji yana d’ibar ta ga amai da ta ji yana shirin taho mata gadan-gadan.

Cikin murmushi Daddy yace “MashaaAllah.
Bismillah, have lunch with us’’
Ya fad’i hakan yana mai nuni da table d’in dake nan a cike a gaban sa mak’il da abinci.
‘’tam,na gode Daddy” tace, daganan ta mik’e tsaye aikuwa tashi d’aya wani irin gigitaccen jiri ya kwasheta, ta tafi luuu za ta zube, da sauri Yassir wanda shigowar sa kenan ya sa hannu ya tareta had’i da rungumeta tsamtsan a jikinsa!!
Tashi d’aya wani yanayi na gigita da fitinar da bai tab’a ji ba ya sauk’ar masa sakamokon tsananin laushi da d’umin jikinta da ya ji…

Duk mik’ewa suka yi.
A mugun rikice Mommy ta shiga cewa “Subahanallah Manubiya lafiyarki? sannu kin ji, Yashjub dama bata da lafiya?”

Cikin tsananin b’acin rai Yash ya ƙarasa ya finciko ta daga jikin Yassir ɗin, tsabar tsananin kishi bai san lokacin da ya rufeta da wani irin fad’a ba
‘’Baki da hankali? Ba za ki iya rik’e kanki ba? Za ki kama ki tafi ki fad’a masa a jiki?yanzu……”

Cikin tarar numfashinsa Ummi wadda ta lura da yadda Manubiyan take jin jiki ta k’arasa, ta ce ” yi hak’uri Yash
gajiya ce da kuma jiri,
a yi mata uzuri ko?
duba ka ga halin da take ciki mana.”

Sai a lokacin ya fahimci yadda ta fara hawaye ta ido d’aya, gashi ta dafe kanta ta runtse idanuwanta da k’arfi.
A hankali ya cika mata hannu
kawai ya juya ya nufi cikin parlourn….

Wani kalar farin ciki ne ya lullub’e su Yassira ganin yadda Yash d’in ya yi mata, yayinda Mommy ta fara shiga masifaffan tashin hankali dan yanayin manubiya ya bata tsoro.

Ummi ce ta d’an ruk’ota ta share mata hawayen tace
“Kar ki yi kuka a gaban mutane mana”
Ba tare da kowa ya gani ba
ta d’an sake share mata fuska tace”Mu je ki ci abinci sai mu je sama ki sha magani, in ma asibiti za mu je sai aje ko?
ki yi hak’uri”
A hankali Manubiya ta d’aga mata Kai alamun to dan ita mamaki ma ya hanata jin haushin Yash..anya kuwa shine ya yi mata wannan tujarar a gaban jama a har da wani cewa ‘bata da hankali!’…
Chapter 70 · 0% Book details