← Book details Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 129 OF 152

Sashe 129

Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hankalina ba k’aramin tashi ya yi ba da na ji ƙishin ƙishin d’in Na’ima ta cewa Yassir Yashjub take so, dan dukda cewa na san mun cire masa son mata da sha’awar su a rai!
amman kuma na san in dai har Na’ima ta gayawa su Daddy tana son shi tofa dole ya aureta, kuma yau da gobe sai Allah, na san duk girman abunda muka yi dole wata rana Na’ima ta iya samun ciki…Shiyasa muka k’arawa abun namu k’aimi, gaba d’aya ya kuma tsanar mata sannan muka fara aiki a kan ya dawo a yi ayi ko shi ya ɗaura ko kuma mu san dabarar da muka yi aka d’aura Yassir da Yassira a kan komai na dukiyarsa before or after (kafin ko kuma bayan) mun kashe sa!
Dan na daɗe da yiwa kaina alk’awarin ‘jinin Khadija (amarya) bai Isa ya rayu ya ji dad’i har ya yi aure ba, saboda yadda Yashjub da mahaifiyarsa suka d’aga mini hankali ba su chanchanci rayuwa ba!’
That is my revenge….
(Hakan itace sakayya ta a garesu).

Kwatsam!! Sai kuma tauraron Mace ta fara b’ullowa wadda Baba larai tace ita za ta kawo
k’arshena muddin muka bari aka yi auren….

Yo dama ai ko ina hauka Yash bai Isa ya yi aure ya haihu ya ji dadi sannan Yaro ya shigo cikin gadon sa ba….ga kuma maganar Matar ma ta zo har da su batun kawo k’arshena! shiyasa na tsani kuma bana son Manubiya kamar mutuwa ta!”.

Ajiyar zuciya Mommy ta sauk’e, kafin ta kalli Yahanasu tace
“yanzu na san kin fahimci dalilina na aikata duk wani abunda na aikata, kuma inda ace ba na sonki ko ban d’auke ki a matsayin jinina ba Yahanasu da ba zan tab’a zama in faiyyace miki komai in bud’e miki cikina kamar haka ba!!.
Na san na yi laifi, na san na yi kuskure amma Yahanasu Daddynku shine ummulaba’isin komai da na fara aikatawa, sannan da tafiya ta yi tafiya na san kema kin fahimci saboda Yassir da kuma ku na aikata ragowar abubuwan da na aikata….
Sannan Manubiya had’ari ce ga rayuwata, shiyasa ya zame mini dole in….”

Cikin tarar numfashinta Yahansun tana wani irin kuka kamar ranta zai fita tace
“Mommy babu ruwan Mannubiya da duk wani abu da ya sameki da kuma yake shirin samunki!
Ubangiji ne ya fara nuna miki k’arshenki!!…”
Wani irin abu ne ya rik’e mata zuciya da mak’ogaro dan haka ta yi shiru dan numfashinta ya tsaya…da kyar ta samu ya dawo, ai kuwa tashi d’aya ta matsa ta kamo hannun Mommy ta fara janta, sai da suka isa bak’in k’ofa tukunna ta bud’e tukunna ta had’e hannuwanta waje guda tace”dan girman Allah ki fita, ki fita kafin ki sa zuciyata ta buga!!!!”

Tabbas Mommy ta fahimci tarkon ta ya kama kurciya, dan yadda tayi ɗinnan ya sanya ta fahimci ba za ta iya yin komai ba kamar yadda take ik’irari…kuma yadda ta bud’e mata cikinta ta fad’a mata sirrinta ta san hakan ma sake k’ulle Yahansun ta yi da jijiyoyin jikinta, dan haka ba za ta iya yin komai ba.
Shiyasa kawai ta shafa fuskarta a hankali ta d’an goge mata hawayenta, daga haka ta sa Kai ta fice hankalinta a d’an kwance dan tun d’azu da Yahansu tace
‘guilty conscious zai addabeta idan ta fad’i abubuwan da ta aikata aka hukuntata’
Ya sanya ta fahimci iyakar abunda ya kamata ta ƙara yi shine ‘ta sake nunawa Yahanasun itan fa itace mahaifiyarta, kuma tana sonta’
daga nan ta san za ta ƙarasa rufe mata baki ta sanyata ta yi shiru cikin hikimarta, shiyasa ta bud’e mata cikinta saboda tana so Yahanasun ta ga ita mommyn ta yarda da ita, kuma ta d’auke ta y’a.

Kafin Yahanasun ta gama fita daga al’ajabi da mamaki ta dawo dai dai, ita kuma InshaaAllah kafin nan za ta san yadda zata yi da su Daddy, za ta san yadda za yi destroying ɗinsu, kar ma su sake bata ciwon kai

Mommy tana fita da sauri Yahanasu ta mayar da k’ofar ta rufe, k’irjinta yana dukan tara tara, dan bayaga haushi da takaici har ga Allah zuwa yanzu kam tsoron Mommy take ji!!
Anya kuwa Mommy tana da zuciya a cikin k’irjinta??
ita da Baba Larai anya kuwa za su ga Annabi?
ashe dama akwai mutane irinsu har yanzu a duniya?….
A da ita tana jin haushin Mommy saboda abubuwan da ta yiyyi ashe ba ta ji duka ba, ba ta san duka ba!!!!
“Innalillahi wa inna ilaihirrajiun”
Ta shiga ambato a cikin zuciyarta kanta yana wani irin sarawa…

tabbas kamar yadda Mommy ta yi zato a yadda ta zauna ta bud’ewa Yahansu cikinta hakan ya sanya Yahanasun ta d’an ji d’arr sannan kuma ta yarda Mommy ta d’auke ta a matsayin y’a!!
Ba wai ta yafe mata abubuwan da ta yiyyi ba kawai dai hakan ya sanya ta sake fad’awa cikin duniyar tsoron tona mata asiri saboda ta san idan ta tona mata asirin to fa azabar lamarin ba zai bartaba ya dinga addabarta kenan yana bibiyarta yana damunta har ƙarshen rayuwata, tunda duk dai lalacewa uwa uwace, ta san dole za ta ji guilt, dan haka gara kawai ta barta Ubangiji ya nuna mata iyakarta…
Ba za ta sake da ita ba ba kuma za ta kula ta ba, babu ruwan kowa da kowa kamar dai da, dan tabbas Mommy ba uwar da zaka sake ka yi mu’amala da ita baceba,she is everything Bad!…..

Sai da Baba larai ta yi sati d’aya tukunna Mommy ta basu izini suka fara nemanta, sai dai kuma babu kalar kiran da ba su yi mata ba amma wayarta ba ta shiga kuma sun kira k’auyensu ance bata je ba, dan haka hankalinsu ya tashi matuk’a.

A b’angaren Kausar da Yassir kuwa ko da yayi mata maganar aurenta da Yashjub nuna masa ta yi itama ba ta so, kuma wai abunda ta yi a ranar da aka ɗaura musu auren ta yi ne saboda ta yi tunanin Yash d’in zai fara bata wani abun daga cikin dukiyar sa, ko ya ba ta gida ya ce ta zauna a inda za ta je d’in…amma ita sam ba ta yi tunanin su Daddy za su yi musu aure ba.
Dan haka ya taimaka ya taya ta nemo Yash ta samu ya sauwwak’e mata, ita kam aurensa ba ya cikin plan d’insu.’

Dukda wannan bayanin nata still Sai da Yassir ya nuna mata b’acin ransa na k’in tuntunb’arsa da ta yi kafin ta yi abun, ita kuma ta basa hak’uri sosai tare da alk’awarin ba za ta k’ara ba, tukunna ya yi mata alk’awarin nemo Yash a duk inda yake ko ta message ne a samu ya sake ta…Hakanan suka rabu daga shi har ita babu wanda ya san ba aure ma tsakanin Kausar da Yashjub d’in.

Bayan kwana biyu Kausar ta san yadda ta yi ta bincika wayarsa ta d’auki number mutanen nan masu evidence (Yaran grenade)

Sai da ta b’oye numberta, tukunna ta tura musu message ta inda take cewa ”su turawa Yashjub da duk wasu mutanen da suke neman wanda ya yi aika aika a Estate d’in Yashjub ɗin shaidun da suka turawa Yash Yassir ya saka suka goge, ita kuma za ta basu ko nawa ne su ke so.”

Saboda ita har ga Allah Yassir ya ishe ta kuma ta san idan ba kama shi aka yi aka kashesa ba to tabbas ba zai barta ta sakata ta wala ba.

Abuja su Manubiya suka fara zuwa, kafin su gama shirye shiryen tafiya….sai bayan sati biyu tukunna suka isa Copenhagen Denmark suka yi settling!

Cikin rarrashin da tsoron shiga Hakki ta shiga k’ok’arin fahimtar da shi cewa “ko ba komai fa Kausar matarsace!!”

Har ga Allah sai da ya yi mata bayanin da shi kansa sai a cikin jirgi da kwakwalwarsa ta d’an huta tukunna ya tuna sannan itama ta tuna tabbas fa da gaske babu aure tsakanin Kausar da Yashjub saboda ba a d’aura aure da ciki!
A ranar tsakanin Manubiya da Yashjub ba za a ce ga wanda ya fi wani murna ba……daga nan suka kawar da duk wani b’acin rai suka shiga shimfid’a rayuwarsu mai dad’i a Copenhagen dan basu ga ranar dawowaba….

Mommy kuwa zuwa yanzu ta riga ta gama sanin me za ta yi game da auren Kausar da Yashjub…………

BULAMA ✍️
0903 441 3252
*MANNUBIYA*
*Book 2*
*page 41*

A b’angaren Mommy kuwa zuwa yanzu ta riga ta gama sanin me za ta yi game da auren Kausar da Yashjub.

Ta riga ta san zuwa yanzu Yashjub ya san babu aure a tsakaninsa da Kausar..kuma ita kanta zuwa yanzu ta san ba ta da lokacin da zata ce sai sun cire Manubiya tukunna za su kashe Yashjub! Shiyasa kawai ta ma hak’ura da sake k’ulla auren Yash da Kausar d’in a karo na biyu.
Ta dai ji Daddy yana cewa Ummi”Kausar d’in tana a matsayin matar Yash a idanun duniya har zuwa lokacin da za ta haihu. Gudun b’acin suna.”
So ita kuma kafin nan da zuwa lokacin da Kausar d’in zata haihu inshaaAllah burinta zai cika! kud’irinta zai cika! Kuma ta san barin Kausar d’in ma da aka yi a mazaunin matar Yash d’in Allah zai nuna hanyar da za su ci moriyar hakan inshaaAllah..
Kawai ita yanzu wuyarta ta san inda Baba Larai take, dan tana buƙatarta matuƙa yanzu kam, saboda ta riga ta gama tsarawa akan duk bala’i wuyarta Yashjub da Manubiya su sako k’afa a cikin k’asar Nigeria wallahi sai ta ga bayan su!…
Dole a yita ta k’are abun ya yi yawa, kuma anzo gab’ar da dole ta yi musu hakan cikin gaggawa idan ba haka ba kuwa to tana cikin masifa!!!!…
Zuwa wannan lokacin idanunta sun rufe..a iyaka saninta Ita da Yassir suna cikin gadon Yashjub dan haka ba sai ta wani jira sun yi abunda suka yi an mallaka masa dukiya gaba ɗayanta ba, iyaka kason da za su samu ma idan an raba gado ya isa!
Daganan su kuma su Daddy da Ummi da su Hajiya Mama duk za ta saka su a saiti InshaaAllah ta san me za ta yi musu, gara kawai a yita ta k’are……
Chapter 129 · 0% Book details