Sashe 109
Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kwanciyar Hankalinta d’aya zuwa biyu a yanzu, na farko ta riga ta san Manu babu ita babu haihuwa, sannan al’amarin Kausar da Yashjub akwai haske dan aiki tuk’uru suke yi babu dare babu rana, dukda kuwa ita da Kausar d’in ba su fahimci juna ba har yanzu..saboda Mommyn ta yi tambayar duniya amma kullum amsa d’aya Kausar d’in take Bata itace”Yashjub raping ɗinta ya yi(fyaɗe ya yi mata)”tsabar ta rainawa Mommyn hankali, shiyasa ita kuma mommyn ta rabu da ita ta d’au fushi da ita, ko taimakon ma da suke yi mata har gobe ba ta sani ba.
Su Yasira ma sun d’an ji haushin abunda Kausar ta yiwa Yashjub, gashi suma da suka tambayeta amsa d’aya ta basu irin wadda ta bawa Mommy shiyasa suka daina kulata suka yi fushi da ita…ita kam ko a jikinta, dan idanunta sun rufe, ba ta damu da kowa da komai ba! babban burin ta a halin da ake ciki shine ta ga ta auri Yash, daganan kowa ya yi ta kansa.
Abhi ma ya zo, dan Daddy da kansa ya kirasa da ya ji labarin yana Niger sun je wani aiki, shine ya kirasa yace ‘dan Allah idan sun gama ya biyo Nigeria’
saboda kwana biyu gaba d’aya Daddyn a hargitse yake, ya rasa me yake yi masa dad’i, kansa ya d’au zafi..shiyasa ya hana Hajiya Mama ma tafiya, yake kuma buk’atar Abhi d’in shima a kusa da shi.
Junior da Yadira ma an saka musu rana, nan da wata uku.
su Siyama ma jiya aka je aka yi tambaya aka bayar, kuma an saka har ranar auren wata uku suma……
Ko da Junior ya tunkari Yassir game da zancen Yash…tashi d’aya Yassir ya faiyyace masa komai, bai b’oye ba!
saboda ya san ya riga ya fahimta.
Cikin tsananin b’acin rai Junior ya hau zaginsa, sannan yace ‘bai taɓa zaton zai iya yiwa Yashjub haka ba, kuma yana gargaɗinsa da ya yi sauri ya gyara kuskurensa ko kuma ya tona masa asiri wallahi.!
…..A lokacin da suke makaranta akwai wani video da Yassir d’in ya tab’a yiwa Junior shi da wata Yarinyar da yake ta so itakuma Yarinyar ta k’i sauraronsa…sai da suka bata abu ta sha ta bugu tukunna aka yi video d’in na rashin ɗa’a! abun ba mutunci dai babu kyan gani…..y’ar Nigeria ce, y’ar manyan mutane, gidansu babban gida shiyasa a wannan lokacin suka dinga amfani da video ɗin suna tsoratata da tirsasa mata wajen yin duk abunda suka buƙata daga gareta..ko me suka ce suna so ta yi musu sai ta yi, idan suka kirata dole ta je..ba kalar tujarar da Yarinyar nan ba ta gani daga garesu ba har aka samu ta gama makarantar ta kama gabanta ba tare da sun saki video d’inba..a wannan lokacin an yi ne akan za a yanke fuskar junior da jikinsa a saki video d’in ita kad’ai.To yanzu kuma Yassir ya tabbatarwa Junior muddin ya faɗawa Yash ko wani a gidan abunda ya ke iƙirarin zai faɗa ɗin to wallahi fuska da jikin duka su biyun zai bari ya saki video d’in, kuma ya nunawa kowa har su Daddy da Yadira, daganan sai ya ga ta yadda zai auri Yadira..
Junior Bai ga alamun wasa a fuskar Yassir ba, kuma ya san tsaf zai
Iya tunda har ya iya yin dakon video d’in har kawo yanxu saboda shi Junior ɗin ya san sun goge videon sam bai yi tunanin Yassir yana da shi har yanzu ba….
Sai da suka yi kacha -kacha a ranar, tukunna suka rabu baram baram.
ba ma a b’angare d’aya suka kwana ba, dan Junior k’aura ya yi ya koma side d’in Yashjub inda Abhi yake.
Tambayar duniya ya cewa Abhi ɗin ‘ba komai, yana son zama kusa da shi ne kawai’
dan haka ya rabu da shi ba dan ya yarda ba.
..
Yassir ya fi kowa tashin hankali a cikin sati biyun da suka gabata, daɗin daɗawar da ya sa shi zage dantse ya yi wa junior wuta wuta ma kenan dan ya lura in ya barshi ya ƙara masa nashi shirmen akan abubuwan da su ke damunsa to tsaf zai iya yin hauka!!
abubuwa sun taru ta ko’ina sun yi nasa yawa!
….Sam bai ga alamun fushi ko jin haushin Yashjub daga Daddy ba kamar yadda suka yi zato shi da Kausar, Sannan Yashjub da Manubiya shiru, kuma ya san ta ga message d’in da ya tura mata, amma ko jiya da ya tambayi spy d’insa na gidan ce masa ya yi ‘tana nan, Yash d’in ma ya daina fita aiki….’
wani irin kishinta yake yi idan ya tuno
tana tare da shi gashi shi fa har ga Allah hak’urinsa ya k’are a kanta…
ita kuma Hajiya mama da Daddy sun ce daga kansa har zuwa kan Yadira kowa ya zauna a gida, kar wanda ya je musu for now a barsu su huta.
Gashi waenda aka kama akan batun lamarin case d’in estate, ya yi
musu alk’awarin zai saka a sake su su gudu amma har yau abun ya gagara, dan waenda yake tunanin zai bada cin hanci su taimaka mutanen su gudu sun ce babu ruwansu case d’in a hannu manya yake…
Su kuma Yaran waenda aka kama d’in sun ce “hak’urinsu ya k’are, dan haka sun bashi kwana d’aya tak! Ko ya yi wani Abun ko kuma wallahi za su kai sunansa da recording d’in wayoyin da aka dinga yi da shi har ma da wasu videos da bai tab’a sanin akwai su ba..
su tona masa asiri”
saboda horo mai tsanani ake yiwa oganin nasu gashi an hana a gansu, yanzu haka ma suna tunanin an kashe d’aya ne……..
Kausar ma jikinta da sauk’i, ko da suka je asibiti cewa aka yi ba sai anyi wani plastic surgery ba, kawai magani aka dinga shafa mata, a jiya kuma da ciwon ya warke har ta fara shafa maganin scar saboda kar ta yi tabo a fuska.
Yashjub ma ya tara gaba d’aya footage na cctv camera amma tsoro da fargabar cikar zarginsa sun hana shi dubawa..
BULAMA ✍️
0903 441 3252
*MANNUBIYA*
*Book 2*
*page 36*
Yau dai ya shirya akan zai daure ya duba..
Sannan zai daure ya je gida ya gaida su Daddy, yana kiransu kullum suna gaisawa, amma ba ya zuwa yau sati biyu kenan, dan tsantsar kunyarsu yake ji! A duk lokacin da ya tuna yadda suka gansa shi da Kausar sai ya ji kamar ya binne kansa,shiyasa sam ya gagara sake fuskantar su.
Daɗin daɗawa ya na son ganin Kausar, ya fahimci ba ta mutu ba, dan bai ji ana zaman makoki ba dan haka yanada tambayoyin
da yake buk’atar ta amsa masa…kafin ya san abunda zai yi mata na gaba,dan wallahi sai ta zab’i mutuwa a kan rayuwa…
Tun bayan kwana biyu da faruwar al’amarin ya fahimci wani Abu da yake adduar Allah ya sa hakan ne ‘in banda coconut oil d’in da ya ji a jikinsa ya kuma gani a ranar da tace wani Abu ya shiga tsakaninsu bai ga komai a tare da shi ba, sannan da ya zauna ya yi lissafi time duration d’in ya yi ƙaranci, shiyasa kwakwalwarsa ta basa babu abunda ya shiga tsakaninsu! To amma a yadda take son shi me ya sa hakan ta kasance? me ye ribar ta idan ta bari aka kamasu kawai ba tare da wani abun ya shiga tsakaninsu ba??’
Ita kad’ai ce za ta iya amsa masa wannan tambayoyin nasa, kuma a yadda ta daku a hannunsa ya san ta d’an shiga saiti ta tsorata, shiyasa ya yanke shawarar ya tunkare ta akan batun.Idan ma wani abun take shiryawa tun wuri ya datse !,shi ya san yadda zai bi da ita ta fad’i masa komai cikin sauk’i.
Hajiya Mama kuwa babu tambayar da ba ta yi ba amma aka k’i gaya mata asalin menene ya sami Kausar…Daddy ya lallab’a Ummi ta yi mata k’arya ba don ta so ba tace”daga bene ta fad’o”
Abhi kawai Daddy ya gayawa wanda shima sai da Daddyn ya yi da na sanin gaya masa, dan cewa ya yi wallahi sai ta bar gidan a ranar, da kyar Daddy ya rik’esa ya gaya masa komai yadda suka yi da Hajiya Mama da kuma abunda itama Mommyn tace masa a ranar da case d’in ya faru.Ya san idan suka kori Kausar kamar yadda ta fad’a zata tona masa asiri, kuma ta kwashe gaba d’aya y’ay’an sai dai a yi gida biyu…sam abun ba zai yi kyau ba.
Tunda Abhi ya ke bai tab’a jin tsanar Mommy da Kausar irin na ranar ba, don sai da ya yi kwana biyu tukunna ya d’an sauk’o…Shiyasa shima ya bayar da goyon baya aka b’oyewa Hajiya Mama saboda sun san idan ta sani babban tashin hankali zata kunnowa kowa! Ta d’agawa kowa hankali har ita kanta ba tare da anbi komai a hankali ba an gano Mommy an tona mata asiri ba.
….
Sai da Yashjub ya tabbatar Manubiya ba ta buk’atar komai, ya kira mata Siyama ta zo tukunna ya ce bari ya je ya gaida su Daddy ta basa awa ɗaya yanzun zai dawo, inshaaAllah…..
Dama tun a waya ya lura da yanayin Mommy kamar tana fushi ne da shi, Aikuwa yana zuwa ya tabbatar dan ganin sa a zahiri da tayi ya sanya ta kasa b’oye takaicin da haushinsan da take iya dannewa ta waya…da kyar suka gaisa daga haka ta mik’e ta fad’a d’akinta ta barsa shi da Baba larai.
Shima d’in a wuya yake da ita, dan Wallahi da kyar ya danne zuciyarsa ma ya shigo side d’innata, ko ganinta ba ya son yi daga ita har Baba larai d’in tata, dama a gis gis suka gaisa tana shigewa shima ya mik’e ya fita ko sallama bai yiwa Baba larai d’in ba.