← Book details Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 152

Sashe 29

Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Anan cikin gida kuwa….
Su anty amarya suna nan a d’aki har yanzu ba wanda ya lek’o ko murna ko taya aiki, sun so su d’an lek’a su yi murna amma sai mazajensu suka sake hanasu,hatta su Salaha rufe su a d’aki maman su ta yi hakanan Yaran suka hak’ura ba dan sun so ba….sai dai kuma ko mintuna talatin ba ta yi da rufe k’ofar ba aka zo aka fara bubbuga mata tana bud’ewa ta ga mak’oftan da take shiri da su ne suka shigo wunin biki hakanan suka shige suka zazzauna mata, kafin minti d’aya parlourn nata ya cika har ma da na su Baba Habu suma duk sai da aka shiga, ba yadda suka iya dan duk wanda ya fi shiri da su a neighbors idan ya zo wajen su ya ke zuwa ya zauna bayan ya je ya ga amarya….

Su Siyama ma haka suka dinga kai abincin suna ajjiyewa da fara’a a fuskokinsu kamar ba su san me ma suka yi ba, shiyasa gaba d’aya kunya ta kama su dan gashi dai ko Allah sanya alkhairi ba su je sunyi ba amman wunin biki ya kankama a parlukansu.
…..
Anan waje kuwa, sun sha hotuna abunsu…haka aka yi komai aka kammala da ikon Allah cikin kwanciyar hankali da tsananin farin ciki.
Sai da su Daddy suka wuce, Abokan Yash suma duk suka wuwwuce dan bai cewa kowa zai shiga ya ga amarya ba saboda tsabar kishi, tukunna shi da Najeeb suka k’arasa wajen Ya Musbah wanda suke tsaye da shi da Ya Nafi’u suka mik’a musu Hannu aka yi musabaha suka yi wa juna Allah ya sanya alkhairi kafin Najeeb yace”Am, muna so za mu ga Amaryar,
za a d’an yi
hoto, sannan za mu gaida su Inna”

Ahankali Ya Musbah wanda gaba d’aya yake jinsa upsidedown (a wani irin juye) ya jinjina musu Kai, kafin ya ce ”Bara in sanar da su
Innar”
Daga haka ya wuce ciki….

Su Siyama suna gamawa, suka yi sauri suka shiga wanka, dan Aisha su take jira..za su je su kwashi kaya su kai gidan Amarya.
Suna fitowa suka ha shiri da hanzari…
Ba komai a fuskokinsu sai Vaseline, sannam ankon
su da suka yi na atamfa shi
suka saka dan har Aisha
Itama shi ta saka da Mama,
A shape aka yi wa Siyama, Jidda kuma riga da skirt…
Kalar Atamfar, kalar light blue ne da fari, shiyasa ta karb’i jikinsu ta sake fito da ainihin kyawun hasken fatar su…Tsayin su kusan d’aya ne, sai dai Jidda ta d’an fi Siyama jiki kad’an.
Farin mayafi Siyama ta rufa ta yi d’aurin ta mai kyau, Yayinda Jidda ta rufa blue vail itanma sosai d’aurin ta ya yi kyau.

Suna fitowa daga side d’in su Siyaman, suka had’u da Ya Musbah…sak’on Yashjub ya gaya musu saboda d’akin su Innar ya cika taff shiyasa bai samu ya iya shiga ba.
Yana gama gaya musu sak’on ya juya ya koma d’akinshi ko waje wajen Nafi’un ma bai koma ba, dan kansa wani kalar azababban ciwo yake yi masa..ba dan bai gama yarda da tsubb’ace-taubb’ace ba to da babu abunda zai sa ya k’i yarda da cewa ‘Baraka tsafi ta yi masa!’
Idan fa ya rufe ido har ganinta yakeyi, sannan ji yake kamar ya je ya d’auko ta kawai ya dawo da ita, bai tab’a missing (kewar) Mutum kalar yadda yake missing (kewar) Baraka ba!!!
Sannan a iyaka kwana biyu kawai, ya ji soyayyarta da k’aunarta sun dawo mishi sun zauna daram sun mamaye koina, sab’anin kwanankin baya da ya tsani ya ji ko da sunanta ne.
Dama tun sati biyu bayan da ya sake ta ya fara jin hakan, amman abun bai yi tsanani kamar yanzu ba.

A shagub’e ya ɗan gwada tuntuɓar Nafi’u ba wai kai tsaye ba, wanda amsar da Nafi’un ya basa ya sanya ya fahimci tabbas indai har ya dawo da Baraka gidansa to Abotarsu shi da Nafiu za ta iya tarwatsewa, shi kuwa a yadda yake jin Nafi’u yanzu ya ma fi k’arfin Aboki a wajen sa sai dai d’an uwa shiyasa sam ba ya son abunda zai shiga tsakanin su…..To! Nafi’u ma ya nuna baya so ina kuma ga Inna
wadda aka yi wa abun!

Shiyasa gaba d’aya yake a burkice, bai ma san ta ina zai fara kallon family d’inshi ya ce musu ‘zai dawo da Baraka’ ba!
Shi kuma tabbas a yanda yake jin Baraka a halin yanzu in dai har bai dawo da ita ba tou akwai matsala…….
….
Jidda ce ta wuce d’akin dan sanar da su Inna yayinda Siyama ta nufi parlournsu, ta shiga tattarewa bayan ta cewa bak’in ciki “dan Allah angwaye za su shigo”, su kuma sun fita.

Tana cikin tattarewa Jidda ta kirata ta ce “su inna da anty umma sun ce a bari su Yashjub d’in su gaida su a d’akin kawai……
saboda akwai Matar Mai Unguwa kuma gurguwa ce, so idan akace sai ta sake jan kujerarta zuwa parlourn su Siyaman wani sabon aiki ne….
Amma dukda haka gata nan zuwa ita da Adda Manu, su Innar sun ce ta je parlourn su zauna su yi hotunan a ciki”

Mata wajen biyar ne a d’akin, ga kuma matan uncle da su anty umma suka cewa su Jidda su je su kira, tafe!
shiyasa anty umma da mama suka nemi waje a bayan gidan suka zauna, wanda dama abunda maman take so kenan shiyasa ta san yadda ta yi ta ja anty Umma, dan har ga Allah bata so ta had’u da Angon!!!
saboda bata san wanne hali za ta shiga ba idan zarginta ya tabbata, ko kuma akasin hakan…tsabar yadda ta rud’e..ita ba ma ta san me zata ce tana so ba a halin yanzu…ya tabbata ko kuma kar ya tabbata.

Sai da aka d’an tartare d’akin aka saka turaren wuta tukunna
aka cewa su Jidda su je su shigo dasu….
matan su Uncle ɗin da aka tsammata, ko da aka gaya musu ma basu tashi zuwan ba, dan yaddda suke ganin ran mazajen nasu a mugun b’ace, kuma sun san akan auren ne aka b’ata musu rai yasanya bama su gwada tambayar su zuwa su gaisa da Angwayen ba gudun b’acin rai……

Yashjub yana tsaye suna waya da Yassira, ya hango Yassir yana sallama da Abokansa, suna wucewa ya ga shima ya bud’e mota yana shirin shiga ya wuce, dan haka ya yi saurin cewa Yasira “ina zuwa” daga haka ya kashe wayar ya d’an d’aga murya ya kira sunan Yassir.

Sai da ya yi tsaki, tukunna ya rufe motar ya juya ya na kallonshi…
yaffito shi Yashjub d’in ya yi da Hannu, daga haka ya d’auke Kai ya ci gaba da magana da Najeeb.

Kamar zai kama da wuta! Haka
Yassir yakeji tsabar takaici..sai da ya taushi zuciyarsa da kyar tukunna ya fara k’ok’arin takawa zuwa inda Yashjub d’in yake, dan dama a kumbure ya ke saboda sai da suka yi shi da Daddy da Abhi suma kafin su wuce! Akan yadda yake ta faman ciccin magani yake kuma k’in
shiga a yi abu dashi, sune har da zaginshi Abhi yana ce mishi mai bak’in hali, tukunna suka wuce. shiyasa tun d’azun yake a wuya, yanzu kuma ga Yash shima yana shirin k’arasa kaishi bango…sam sun kasa la’akari da yadda ya danne kanshi ya shigo cikin wannan mugun layin dukdan saboda su amma still babu godiya babu jinjinawa kalli abubuwan da akeyi ta masa…..da kyar dai ya dan danne kansa dan wani mugun takaici yake ji, tukunna cikin takunshi fuskar nan tamau ya fara takawa izuwa inda suke, a ranshi yana aiyyana
“tabbas ya san sai ya sha maganin allergy dan he’s allergic to (yana da rashin jituwa da) warin kwata, kuma kwatocin layin kusan duk a bud’e suke, gaba d’aya koina wari yake yi…dole ne ma ya je ya ga Likita”
Yana cikin tunanin asibitin da ya kamata ya je ɗin ne ya k’arasa inda suke tsaye, ya tsaya kawai ba tare da ya ce komai ba.

Kallonsa Yashjub d’in yayi
kafin da mamaki ya ce “ya na ga kana shirin tafiya? Ba za ka
shigo mu gaishe da su ba?.
Ka tsaya idan muka gaida su muma duk wucewa za mu yi, sai mu tafi tare.”

Yassir ji ya yi kamar ya d’aura Hannu aka ya kurma uban ihu tsabar takaici….yanzu dan rainin hankali wannan mugun gidan yake so ya shigar da shi cikinsa saboda tsabar son wulakanci?!
iyaka layin da ya shigo da su bai ishe sa ba shine sai ya danna shi a cikin gidan nan kenan! A ranshi yace “Tabbas na ga alama sai na yi wa Mutumin nan da gaske tukunna zai d’aga min ƙafa”
A fili kuma cikin tsananin tsageranci da wulak’anci ya kalli idon Yash d’in tukunna ya ce”ka san dai Allah d’aya ne ko?!
To wallahi Allah idan na shiga gidan nan sai an yi deworming d’ina!(sai an bani maganin tsutsotsi da ƙananun kwari)….
Yanzu haka I’ve fallen sick(har na fara rashin lafiya).

Na san ka san Ina reacting to ƙazanta da ababen ƙyama amma dukda hakan sai faman k’ok’arin forcing d’ina kake yi, haba mana!…”

Sakar Baki kawai sir Najeeb yayi yana kallonshi shi
Yashjub kuwa ya zo iya wuya jira kawai yake Yassir ɗin ya kai aya shi kuma ya fara cin ubanshi, tunda ya lura
bashi da hankali…
Manubiya da family d’in nata ne ƙazantar ko
me?
tabbas yau kam Yassir ya kuma kaishi bango zai kuma sha mamaki…..
Chapter 29 · 0% Book details