← Book details Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 152

Sashe 38

Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ba dan Yahanasu ta so ba ta barsu suka tafi su kad’ai amman da har ta d’auki waya za ta kira musu Najeeb.

Sallama suka yi musu daga haka suka fita suka yi tafiyarsu a adaidaita sahu.

Ba kad’an ba Munirat ta girgiza da ganin gidansu Manubiya,
hatta su Jiddan sai da suka d’an fahimta.

BULAMA ✍️
0903 441 3252
*MANNUBIYA*
*Book 2*
*page 18*

Manubiya tana chan d’akin su Siyama, dan Inna kara ta yi ta ce “a tafi da ita chan ɗin, idan an zo d’aukarta a d’auke ta a chan.”
Haka nan aka wuce da ita d’akin Anty Umma bayan Innar, Baba, Ya Nafi’u da Ya Musbah sun gama yi mata fad’a, sun yi mata sallama had’e da saka albarka..da kyar aka b’anb’are Manubiya daga jikin su Baba tana wani Irin kuka kamar za ta shid’e!

Ba k’aramin mamaki Inna ta ji ba da ta ga maman Abbakar
da maman Baraka sun zo mata, dan ana fita da Manubiya sai ga su sun zo suna ta washe Baki kamar ba su ba, sai da suka zauna a d’akin suka shiga yi mata Allah ya sanya alkhairi tukunna ta tabbatar da gaske wajen nata suka zo dan sam ita bata yi tsammanin ko iskar su ba…kasancewarta Mace mai kawaici ya sanya kawai ta karb’esu ba yabo ba fallasa, daga haka ta gaya musu inda Amaryar take.

Kan Manubiya har juyawa ya soma yi saboda tsabar turaren wuta, a
nan makwaftan dama akwai wata mai siyar da kayayyakin gyara, haka aka had’a da wanda Inna ta basu kafin su fito da na matar da na wajen su mama ake ta banka mata, saboda dama ita Inna kunyar fulani ba lalle ta barta ta cewa Manubiyan ta yi ba.
Haka suka d’aura ta akan kujerar tsugunno itakam kanta in banda ciwo ma ba abunda yake yi mata.
Har zuwa wannan lokacin ba matar Baba Habu ba matan Uncle babu y’ay’ansu, kamar
ba biki akeyi ba.

Adaidaita sahun su Siyama tana yin parking, motocin Abokan Ango suka k’araso suma wajen guda goma.

Ba k’aramin dad’i Siyama ta ji ba da taga babu motar Najeeb a ciki, wanda abunda ba ta sani ba ashe mota ya chanza…d’azu da Yahanasu ta yi shirin kiransa ashe ya shiga ita bata sani ba, daga jin yadda Siyaman take bada uzurin ƙin jiran nasa da aka ce su yi!
tashi d’aya ya fahimci dodging d’insa (guje masa) take yi, shiyasa ya chanjo mota mai tint yana tunani da addu’ar shigarta motar, dan yana buk’atar su fahimci juna a yau, ya samu ya wanke bak’in fentin da ta yi masa.

Ana ajjiyesu ya hange ta kuwa, murmushi ya yi dan a take wani irin sanyi ya shiga
ratsashi…..
ya san ya yi mata laifi,
kuma Ya’isha ta b’ata mishi sunanshi a idon Siyaman
amman kuma abunda ta yi ɗin
wanda yake nuni da kamar kishinsa ne takeyi, hakan ba k’aramin dad’i ya yi masa ba….

Ba kad’an ba Munirat ta girgiza da ganin gidansu Manubiya
hatta su Jidda sai da suka d’an fahimta, gudun kar su ji ba dad’i ne ya sanya ta yi sauri ta ware dan ita kawai mamaki ta d’an yi ba wai kyama ko wani abun ba saboda ta san da talaka da mai kud’i duk Allah ɗaya ne ya yi su.

Kudin yana cikin jakar Jidda shiyasa ta tsaya sallamar mai napep d’in su Siyama kuma suka ce bari suyi sauri suje su sanar da su Anty Umma, a fara shirye-shirye.

Tana gama bada kud’in, ta juyo kenan, kawai ta ga Mutum a tsaye a daff da ita…..
Ba ta d’ago ta kalli fuskarsa ba
amman tabbas ta fahimci shine, sannan ga k’amshin turarensa wanda ta sanshi da shi
shekara da shekaru!....
She’s not suppose to be feeling this way(bai kamata ace ta na jin hakan a kansa ba!)
Dan kamata ya yi ace babu wani sauran son shi da k’aunar sa da ya rage dede da kwayar zarrah a cikin zuciyarta, sai dai kuma tashi d’aya ta ji komai ya dawo mata sabo! kamar ma bai tab’a yi mata laifi a rayuwa ba ballantana har son nashi ya ragu!!! haka takeji a halin yanzu ba ta da wani burin da ya wuce ta d’ago ta kalli kyakkyawar fuskarsa ma’abociyar murmushi wadda ta bada gudunmawa kwarai da gaske
wajen sace zuciyarta!
Ta yi misssing d’insa sosai, sannan ta tabbatarwa da kanta har yanzu tana son abunta, amman kuma ba zata iya fatali da abunda ya yi da kuma wahalar da y’an uwanta suka sha duk a ta dalilinsa ba.!
Dan haka da sauri ta yunk’ura za ta matsa shi ma ya yi sauri
ya sake shiga gabanta ya tsaya har sai da goshinta ya ɗan bugi k’irjinsa!.

Sosai ta ke iyaka bakin ƙoƙarinta amman tabbas ta ga alamun
Al’ameen ya rantse sai ya karya lagonta ya kawo ƙarshen juriyarta….ba ta san
lokacin da hawaye suka fara sintiri a kan kyakkyawar fuskarta ba, tana mai jin wani irin yanayin shauk’i k’auna tausayi mai tafe da rashin jin dad’in hakan da ta ke ji game da shi.

Wata nannauyar ajiyar zuciya ta ji ya sauk’e kafin ya ce
“Ba ki ma yi missing d’ina ba ko?Takura miki ma na yi ko?
Jidda kin tsaneni har haka
ko kalllona ma bakya son yi?”
Ya k’arashe maganar tasa a hankali, sannan kamar mai shirin fashewa da kuka!.

Sai da ta yi kokawa da Zuciyarta tukunna ta samu ta d’aga mishi kanta alamar ‘EH’.

Shiruuu yayi kamar baya wajen
shiyasa ta d’an d’ago ta kalle sa….
ba ta yi zaton ganin hawaye a idonshi guda d’aya ba amman sai ta yi sauri ta saka a ranta crocodile tears (hawayen ƙarya) ne, sannan ta yi saurin mayar da kanta k’asa….

So take ta ce ya matsa ta wuce amman ta kasa saboda a asalin gaskiya sam bata k’aunar matsawar tashi
daga inda take.

Ajiyar zuciya ya sauk’e
tare da fesar da numfashin da har sai da ta ji calm scent d’in numfashinsa kafin ya ce ”Na san dole za ki ji haushina, dole
za ki yi fushi da ni amman ba ki san yadda na ji da kika ce ko ganina bakya son yi ba, a tunani na mun wuce haka!.
Amman ba komai, laifina ne,
na d’auki alhakin saboda Jidda bakya laifi a wajena kin riga kin sani.
Alfarma d’aya nake nema a wajen ki,
dan Allah dan Annabi ki yi min adalci ki taimaka ki bani lokaci
In yi miki bayani sannan in faiyyace miki komai,
dan Allah pls”
Ya k’arashe maganar tasa yana mai had’e hannayensa biyu waje d’aya alamun rok’o, ba tare da ya damu da a waje su ke ba.

D’agowa ta yi ta kallesa da idanuwanta waenda suka cicciko da hawaye kafin tace
”Ya Al Ameen!
ni da kai
ba zai yiu ba!.

Baka san halin da ahalina suka shiga ba duk a ta dalilin biyewa son zuciya da nacin mu, idan
akwai alfarmar da zan rok’a a duniya a halin yanzu daga gareka itace ka fita a harka ta! ka hak’ura dani! ka rabu dani har abada dan girman Allah”

Da sauri ya ce ”Jidda kin san ba zan iya ba”
D’an matsawa gareta ya yi wanda hakan yasanya ta ja baya da sauri, kamar zai fashe da kuka ya share fuskarsa da duk hannunwansa biyu sannan
ya d’an ja hanci kafin ya ce ”Pls just one more chance! Zan gyara komai in saita komai, na yi miki alƙawari…
sannan zan yi miki clearifying komai dan na san
kina jin haushi na ne akan rashin nemanki da na yi tun bayan tafiya ta, Inada dalili Jidda kuma na san idan kika ji za ki yi mini uzuri”

Sunkuyar da Kanta ta yi sosai ta share hawayenta, daga haka ta zagayesa dan ba ta ga amfanin tsayuwar tasu ba, ita kunya ma takeji wani a cikin y’an gidan su ya ganta da Ya Al’ameen.

Tana wuce sa ta ji ya rik’o vail d’inta, da sauri ta juyo da niyyar ce masa ya cikata amman sai ta gagara sakamakon ido biyu da suka yi da Ya Musbah.
Tashi d’aya ta rikice wanda hakan yasa Al’ameen d’in waigawa shima,

shi kansa sai da ya d’an ji kunyar Musbahu dan haka ya d’an lumshe ido ya bud’e kafin ya k’arasa juyawa gaba d’ayanshi.

Ganin yadda Ya Musbahn ya k’i kallon either of them instead kawai ya tsurawa hannun Al’ameen wanda ke rik’e da mayafin Jiddan ne ya sanya Al Ameen d’in cikata a hankali, daga haka ya d’an fesar da numfashi ya kallesa sosai tukunna ya mik’a masa Hannu alamun su yi musabaha.

Ba tare da ya kallesa ko hannun nasa ba ya cewa Jidda
“Wuce ki shiga gida!”

Kamar jira takeyi
kuwa hakanan ta wuce wuff
har tana d’an tuntub’e.

Bata san ya sukayi ba amman ko da ta je gaff da shiga gidan ta juyo sai ta tsinci Ya Musbah yana magana da Al’ameen d’in
kuma daga gani ba maganar dad’i bace, dan ran Ya Musbah a mugun b’ace yake yi masa
maganar, har yatsa taga yana nunawa Al’ameen d’in.

Tana shiga d’akin su ta fara nufa, ba kowa daga Inna sai Mama sai wata y’ar tsohuwa(iya ramma).
Inna tana had’a y’an ragowar kayayyakin Manubiya waenda suka yi saura tana hawaye, Mama tana zauna a gefenta suna rarrashinta ita da iya ramma.
Anan ta zauna ta shiga taya Innar, suna yi suna hawaye duk su biyun, sun k’i ma su ji rarrrashin da ake ta yi musu.

Jidda ba ta yi mintina uku da zama ba…suna gama zuge akwatin wayar Mama ta hau k’ara, cikin mutuwar jiki ta k’arasa ta d’auki wayar a hankali ta kara a kunnenta, dan duk su Inna sun gama kashe mata jiki…
“Subahanallah”
Suka ji Mama ta ambata kafin tace”ki yi hak’uri ki daina kuka, gani nan zuwa.”
Tana ajjiye wayar Inna ta mik’e ta na share hawayenta kafin ta shiga tambayar ta “mai ya faru?”
Chapter 38 · 0% Book details