Sashe 60
Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Cikin katse mata magana
Mommy tace
“Kar ki damu za ta dawo,
komai a hankali a keyi,
ki kwantar da hankalinki, kinji”
Ahankali Kausar ta jinjina Kai daganan ta matsa ta kwanta a jikin Mommy tana mai sauk’e wata nannnauyar ajiyar zuciya.
Mommy tana so ta fad’a mata zancen tafiyar su Yash honeymoon amma kuma bata san ta Ina za ta fara rarrashinta ba! Dan da kyar aka samu aka iya ruƙo sannan aka saita Kausar ɗin ta yarda ta ɗan nutsu sannan ta yi haƙuri da al’amarin a yadda ya zo da kuma batun ‘sai su Manu sun dawo mansion ɗin tukunna za a raba aurenta da Yash ɗin’, shiyasa ta ke tsoron gaya mata gudun kar ta sake burkice musu..
Gashi ita kanta Mommyn, tun jiya da ya gaya mata ta rasa Ina za ta sa kanta…fatanta shine Yadira ta yi abunda ta tura ta yi a gidan…inshaaAllah in dai har ta yi to ita Manubiyan ce da kanta za ta tarwatsa batun tafiyar tasu.
….
Suna fita Daddy ya sauk’e ajiyar zuciya, dan shima yana tsaye ta window yana kallonsu har suka fice….ya san he’s a little bit hard akan Yashjub (ya san ya ɗan tsaurarawa Yashjub)
amman kuma idan bai yi wa tufkar hanci da wuri ba tou tabbas akwai matsala.. duba da yadda Yash ya kori k’annensa ranar da aka je d’auko amarya dukda ya san laifin su Yasira ne amma a yadda shi da kansa ya rok’esa sannan ya ce su had’a kawunansu sam bai yi tunanin Yash zai sake korar su daga gidansa ba kuma du, baya ga haka kalli yadda yake nan nan da Manubiya!
Ya san zafin soyayya! Ya san yaya mutum yake ji! shiysa ya fahimci indai har bai tashi ya tsaya a kan Yash ya yi masa wuta-wuta ba to a yadda ya rikice a kan Yarinyar tsaf zai yi fatali da zumunci ya zab’i soyayya……
BULAMA ✍️
0903 441 3252
*MANNUBIYA*
*Book 2*
*page 24*
Tunda su Manubiya suka kamo hanya babu wanda yace ‘k’ala’ a cikin motar…Abu d’aya ta lura da shi shine yanayin Yash gaba d’aya ya chanja, kamar yana fushi.
Sam ba ta yi mamaki ko ta ji haushi akan tahowa da Yadira da suka yi ba, kawai dai ta saka a ranta wataƙila hutu za ta yi musu, ko kuma zaman d’aki ko kuma ma wataƙila za ta zauna a wajen su ne har abada, tunda a saninta dai Yash shine Babba a gidansu, kuma dole dama yadda yake da rufin asiri ya kamata ace yana ragewa Daddy waensu abubuwan.
Addu’arta d’aya itace
‘Allah Ubangiji ya sa Yadira kar ta zame mata matsala’…
dukda ta lura ko d’azu da suka zo ita da Yusra ne suka gaida ita, sannan yanzu ma bataga alamun rashin kunya ko rashin mutunci a tartare da Yarinyar ba, sai dai kuma ta fahimci ba sa yi mata rashin mutuncinsu idan a gaban Yash ne but yanayin Yarinyar na yanzu ta ga kamar ba irinsu bace ita, dan haka kawai sai ta saka kyakkyawan zato a ranta, ta yi ta addu’ar ‘Allah Ubangiji
ya sa su zauna lafiya ita da Yadira…’
dan tabbas ta san tafiyar Yadira ba kwana kusa bane, idan ma za ta tafin d’in kenan! Duba da yadda ta ganta da akwatunanta d’urma d’urma har guda biyu da jaka.
Ta san ko tafiyar ma da za su yi honeymoon definitely sai dai su barta a gidan a turo wata babba ko mai aiki ta zauna da ita kafin su dawo….
tanata wannan tunane tunanen ta ga Yash ya d’auki hanyar gidansu, ba ta san lokacin da ta fara zuba murmushi ba wanda har sai da Yashjub d’in ya ji ya d’an juyo ya kalleta, suna had’a ido ya d’aga mata gira d’aya kafin yayi wani d’an guntun murmushi ya maida hankalinsa ga tuk’in da ya ke yi.
Tun lokacin da su Ya Musbah suka bar gidan Manubiya yake k’unci!.
Gaba d’ayansu sun ji haushi, kuma sun ji babu dad’i game da halin da suka je suka tarar da y’ar uwar tasu a ciki amman kuma
dama Ya Nafi’u ya san akwai abunda yake damun Ya Musbahn kwana biyun nan, gashi yau ɗin tun kafin su je gidan Manubiyan ya ke la’akari da shi, ya kuma lura da damuwar tasa ta yau ma ta fi ta kullum….shiru kawai ya yi masa ya na mamakin yadda k’iri k’iri wai shine Ya Musbah yake b’oyewa damuwarsa, dan ya lura sam baya so ma ya fahimci yana da damuwar….
Shiyasa yau kam ya na yin parking a k’ofar gidan, ya cewa su Aisha “su shiga wajen inna, za su taho nan ba da jimawa ba da shi da ya Musbah.
Sai da Ya Musbah ya bud’ewa Muhsin wanda suke zaune a gaban Motar tare da shi ya fita,
tukunna ya juya ya kalli ya Nafi’u ba tare da ya rufo murfin motar ba yace
‘’Jiya ma ka tambayeni, kuma amsa d’aya zan baka,
‘babu abunda yake damuna’
Saboda dagaske babu abunda yake damun nawa‘’.
Cikin tarar numfashinsa Ya Nafi’u yace
‘’Ko kuma dai ba za ka gaya min ba, saboda ka san ba zan tab’a goya maka baya ba ko?,
Haba Musbahu, na fa san a kan Baraka ne ka shiga wannan damuwar.”
kafin ya gyara zama ya fuskance sa da kyau tukunna ya d’aura da cewa
“har wanne dad’i ku ka yi da Baraka da har zai sanya kake missing d’inta har haka?.
Baraka fa Musbahu!”
Ya k’arashe maganar tasa cikin rashin jin dad’i.
Shiruuu Ya Musbah ya yi kafin yace
“ba fa a kan Baraka na shiga damuwa ba! Shin ba ka ga halin da muka tadda Manubiya sannan muka baro ta a ciki ba ne?”
Cikin tarar numfashinsa Ya Nafi’u yace“Jiya waye ya je wajen Baraka bayan sallar Magrib???”
Da sauri Ya Musbah ya d’ago ya kalle sa, sai kuma cikin fushi yace “Bibiyata kake yi?”.
“Babu zancen bibiya a nan!
amsa kawai nakeso ka bani”.
Kamar Ya Musbah ba zai ce komai ba, sai kuma ya kallesa yace
‘’Wajen mai sunan baba na je, ko ban Isa na je naga d’ana ba??”
Cikin katsesshi sannan cikin tsananin fushi Ya Nafi’u yace
‘’ba za ka tsaya ka gaya min gaskiya ba? Yau nine na zama wanda za ka yi wa wannan k’umbiya k’umbiyar???
Shikenan ka je ka yi ta yi, dama shawara ce zan baka amma tunda na ga bakaso fine!
In dai Baraka ce bismillah, ga ka ga ita, amma inaso ka san cewa ba za ta tab’a chanza zani ba.”
Ya fad’i hakan yana mai k’ok’arin zare makullin motar ya fita.
A hankali Ya Musbah ya ce
‘’d’an tsaya Nafi’u.”
Shiruu Ya Naif’un ya yi kamar ba zai kula sa ba, sai kuma ya juya yana kallon sa tare da basa dukkannin hankalinsa.
Ahankali Ya Musbah ya sauk’e ajiyar zuciya kafin yace
“Ina son ta, har yanzu’’
Wani irin kululun takaicin Baraka da tsantsar tausayin Ya Musbah ne suka lullub’e Ya Nafi’u a lokaci guda.
Da kyar ya had’iye abunda ya ji ya tokare masa mak’oshi, yana shirin yin magana ya ji Ya Musbah ya ci gaba da cewa
“Har gobe inason Baraka, har abada!.
Kai Abokina ne, kana fahimta ta akan komai, dan Allah ka fahimceni ka bani goyon baya akan wannan ma.
Itama ta shiryu, ta ce min za ta gyara halayyarta sannan tana so ta zo ta bawa su Inna ma hak’uri, kuma tace za ta rik’e Muhsin, idan ta dawo…
Har yanzu ba ta riga ta fita a idda ba, shiyasa da ni da ita muke so a had’u a gyara abun nan kafin ta fita idda kaga ba sai an yi sabon d’aurin aure ba.
Wannan shine abunda yaketa damu na, na rasa wa zan gayawa, kuma ni a ganina Baraka za ta zauna lafiya da ni da kowa ma tunda yanzu Ina aiki kuma Inada rufin asiri.”
Cikin tarar numfashinsa Ya Nafi’u yace
‘’Musbahu duk Matar da ba ta zauna ta ci talaucinka ba to bata yi deserving arzik’inka da kai kanka ba.
Musbahu Baraka bata da kirki, ta raina ka, ta raina iyayenka…..”
Shiruuu Ya Nafi’un ya d’an yi, ya tsagaita da magana sannan ya dafe kansa saboda ciwon da ya ji ya fara yi masa a sakamokon b’acin rai da takaicin Ya Musbah shi da Baraka.
Ya d’an jima bai ce komai ba kafin ya cika Kan nasa tukunna ya kalli Ya Musbah ya ci gaba da cewa “shikenan, tunda ka nace…sai ka je ka samu Inna ka ce mata kanaso za ka dawo da Baraka.”
Da d’an zafi Ya Musbah yace
‘’Ya za ka ce in je in samu Innaa?Bayan abunda Baraka ta yi mata taya kake zaton zan je in ce mata zan dawo da ita?
Ai wannan aikin ka ne!
Kai ka san ta inda za ka b’ullowa al’amarin, Kai ne za ka taimaka mini, shiyasa na ke gaya maka, saboda ka taimakeni‘’
Shiruu kawai Ya Nafi’u ya yi yana nazartar sa…bayaso ya zargi Baraka amma kuma kana ganin Ya Musbah da zantukansa tashi d’aya zaka fahimci tabbas aikin asiri ne, ko shakka babu ba haka ta bar sa ba.
Ya taso masa da maganar Innar ne saboda yanaso ya tuno masa da abunda Baraka ta yi wa Mahaifiyarsa ya ji zafin abun ya daina tunanin dawo da ita
amman it’s like kamar ma an goge wannan takaicin da wannan ranar ta k’unsa dan kwata-kwata bai hango haushi ko takaicin Baraka a idanunsa ba
bayaga zazzafar soyayyarta da tausayinta da ya ke hangowa a tattare da shi.
“Ba laifinta bane itama, sharrin shaid’an ne, amma ta yi mini alk’awarin ba za ta sake ba, har hak’uri tace za ta zo ta bayar.
ka yarda da ni Nafi’u Baraka ta shiryu tun ba yau ba”
Ya sake jin muryar Ya Musbah.