← Book details Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 88 OF 152

Sashe 88

Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

bayaga haka ma, a sabon plan ɗinsa na shi da Kaudar wanda su ka gama haɗawa yau, shi dai bai ga wani amfanin da Munirat za ta yi musu ba!
Dan haka ya kalleta yace”ki je ki yi bacci please, kaina ciwo yake yi..kar ki sa raina ya b’aci”
Wani irin kuka ta fashe da shi tace
“you snake!!(mayaudari!!!).
Ashe dama duk yaudara ce Yassir?? Yau ni ce zan b’ata maka rai? Ka manta yadda kake cewa ba ka iya bacci idan ba na kusa da kai, ka manta duk kalolin k’aryayyakin da ka dinga zuba mini Yassir yau ni kake wulak’antawa kake pushing away….
Ina kiranka ba ka d’auka, ba ka replying messages d’ina, saboda ka riga ka samu abunda kake so, ko???”

Runtse idanuwa ya yi da k’arfi, kafin ya bud’e ya matso daff da ita, tukunna ya ce”ki fad’a ko nawa kike da buk’ata zan biyaki fansar budurcinki”
Wani mahaukacin mari ta zabga masa wanda sai da jinsa ya d’an d’auke na y’an sakanni!!!.
Cikin tsananin b’acin rai ya d’ago ya zuba mata manyan idanuwansa waenda suka yi jazir ya ce ”zan baki mintuna biyu kacal Munirat! ki fice ki bar mini side d’ina, idan kuma baki fita ba to wallahi zan baki mamaki….aikin banza!!!…
Ba ma fa ki kai yadda na yi zaton zan same ki ba amma kin bi kin wani d’aga mini hankali sai kace wadda kika ba ni ranki!”

Kallonsa kawai take yi jikinta yana wani Irin karkarwa kamar mazari, idanuwanta kuma suna zubda ruwa tamkar fanfo….maganganun cin mutunci da cin zarafi ya ci gaba da fad’o mata, dan haka kawai ta wuce shi ta nufi k’ofa tun kafin ya sa zuciyarta ta buga!!!
Har ta fice bai daina magana ba, sai da ya tabbatar da ta yi nisa tukunna ya yi tsaki ya fad’a bathroom……
..
Washegari da sassafe ta rubuto masa doguwar wasik’a mai ƙunshe da tsinuwa da Allah ya Isa kalakala, sannan ta had’o masa da makullayensa da duk wasu gifts da ya tab’a bata, ta kai side d’insa ta ajjiye….
Tabbas Yassir ya koya mata darasi a rayuwa, kuma ya cuceta har gaban abada, amma ba komai ya je zai gani……

Da safe Dr ya sallami Manubiya, dan jikin nata Alhamdulillah, sai d’an abunda ba a rasa ba.

Direct gida Yash ya kaita bayan ya tsaya ya siya musu abinci a hanya…sai da suka yi wanka suka ci abinci suka huta tukunna ya ce “bara ya je ya d’auko mata Jidda da Muhsin su taya ta zama, kafin ya je ya d’auko mata gwaggwo mai aiki.”
A take kuwa farin ciki ya wanzu a fuskarta, murmushi kawai ya yi yai kissing forehead d’inta ya fice bayan ya tabbatar ba ta buk’atar komai.

Ko da ya je Inna ta so ta hana su Jiddan zuwa dan ta san halin k’annensa da mahaifiyarsa, kar zuwan nasu ya zamo case amma sai Baba ya ce”ba komai, su je kawai”
Dan a duniyar nan Baba bai ga alfarmar da Yashjub zai nema a wajensa ya k’i yi masa ba muddin bai fi k’arfin sa ba.
Hadda Siyama aka taho, dan a lokacin ita da anty Umma sun je duba Baba Yash d’in ya je,
hakanan ita da su Ya Nafi’u waenda suka zo da makullan gida suka ta yi masa godiya suma..Anty umma ta na saka masa albarka…..

Sai da ya kai su gida yace”su d’ebi kaya”dan a cewarsa “kwana za su yi”tukunna suka kama hanyar nndc quaters. Ba sa so su yi jayayya da shi,shiyasa kawai suka ce masa to suka d’ebo kayan amma sun san ko da ace suna son kwanan ma su Inna ba za su bari ba….

Yana hanya Najeeb ya kirasa ya ce masa yana k’ofar gidansa, dan haka ya ce”ya basa 5 minutes yanzu zai k’araso shima inshaaAllah”.

Suna isa tsabar saurin da Siyama take yi ko gama parking Yash bai yi da kyau ba ta fito da saurinta ta nufi entrance..ta ci sa’a kuwa dan Manubiya tana k’asa dama tana jiransu…murnar ganinsu da oyoyo d’in da Manubiyan ta tsaya yi ne ya sa ba ta samu ta shige d’aki ba har Najeeb d’in ya shigo shi da Yashjub.Allah ya so da ma Manubiya da hijab d’inta dan ba ta dad’e da idar da sallar azahar ba.

Sama suka nufa Yayinda shi da Najeeb suka zauna a nan k’asan….ba k’aramin tausayi Najeeb ya bawa Yashjub ba dan ya fahimci komai kuma ya lura ko kallonsa Siyama ba ta son yi, dan haka ya gama shirya yadda zai yi ya samu ya ceto rayuwar Abokinsa saboda in banda tsantsar so da k’aunar Siyama babu abunda yake hangowa a tartare da shi….

Siyama da Jidda har ma da Manubiyan ne suka sauk’o suka yi musu fried rice da coslo mai d’an karen dad’i, itakam Manubiya kafin a gama ta jigata dan wani irin amai da zazzab’i take ji gashi aman ya k’i fitowa……

Ana gama cin abinci Yashjub ya kira Manubiya yace “ta turo masa Siyama”
Da d’an mamaki Najeeb ya kallesa, sai kuma ya yi shiru kawai ya ci gaba da tunanin da tun d’azu yake ta yi dan ko da suka zauna ma Yash d’in ne yake ta magana.

Cikin nutsuwarta ta k’arasa cikin parlourn inda suke ta sake gaida Yash tukunna ta zauna a kan one seater da ya yi mata nuni yace “ta zauna”
Kamar ba za ta kula Najeeb ba, sai kuma kawai tace”Ina wuni”
Saida ya sauk’e ajiyar zuciya tukunna yace”Alhamdulillah,kwana biyu…”

Ta san jan magana yake so
,shiyasa kawai ta sharesa.

Shiru parlourn ya d’auka kafin ta ji muryar Yash ta d’ira a dodon kunnuwanta, ta inda kansa tsaye yana shiga cewa ”Siyama mai yasa ba kya kula Abokina? Ki ke ta bashi wahala..ko kwata-kwata ba kya son shi ne?”

Nauyi tambayar ta yi mata gashi ba ta yi tsammaninta hakan ba..shiyasa ta sunkuyar da kanta ta yi shiruu ta gagara cewa komai.

Jan numfashi Yashjub ya yi, kafin yace
“A da ban yi niyyar saka muku Baki ba, amma naga abu har wajen 4 months ya k’i gyaruwa sai gara mini Aboki kike yi, shi kuma na san ba hak’ura zai yi ba!”
“Na san watak’il a kan Ya’isha ne kuka samu sab’ani da shi…wanda ko baki auri Najeeb ba na san ba zai auri Ya’isha ba, tunda ba sonta yake yi yanzu ba, kinga an yi biyu babu kenan.
Kasancewar ni ɗanuwa ne ga Ya’isha ba shi zai sa in k’i bin bayan gaskiya ba,Maganar gaskiya Ya’isha ita ta yi neglecting Najeeb ta yi sakaci da alaƙarsu har ya zo ya had’u dake kuma na san kin san negligence (sakaci) ya kan kashe har aure ma ba wai iyaka soyayya ba….”

“Wannan itace gaskiyar maganar Ya’isha da Najeeb, dan haka zaɓi ya rage gareki, amma ni dai ina baki shawarar ki saurari Najeeb ki auresa, saboda na san yana son ki tsakani da Allah, kuma Najeeb yana da kirki, hankali sannan shi ɗin mutumin kirki ne.”

Shiruu parlourn ya d’auka kafin Yash ya mik’e ya ce “Bari na baku guri…”daga haka ya wuce chan sama d’akinsa.

A hankali Najeeb ya mik’e ya k’arasa ya zauna a gefenta kan three seater da ta ke a zaune yace “Wanne dalili kuma yanzu kike buƙata Siyama da zan ci gaba da azabtar da zuciyata?
Na garu haka, dan Allah ki ji k’aina….”

Shiruu ta yi ta kasa cewa komai kafin tace”zan yi tunani akai”

Wani sanyin farin ciki ne ya lullub’e Najeeb a hankali yace”sai an ja mini rai kenan yanzun ma..”

Murmushin da yaga ta d’an yi ne ya sa ya ji kamar an tsunduma sa a aljannah dan haka a fili ya ce”Alhamdulillah”
“Yanzu ko zuwa anjima idan na zo za ki fito kuma za ki kulani ko???”

Dariya ta yi wannan karon ta d’aga masa kai alamun”eh”sai kuma ta mik’e da sauri ta haye sama….dama chan tana son Najeeb kawai tana jiran wanda zai ba ta kwakkwaran dalilin da zai sanya ta auresa dan ba shi kad’ai ba ita kanta ta garu..yanzu kuwa da ta ji komai ta fahimci komai InshaaAllah za ta rufe ido ta goge babin Ya’isha daga rayuwarsu…

Ko da su Manubiya suka ji labarin a take suka goya mata baya d’ari bisa d’ari, suna ta murna suka kira Aisha aka sanar mata, itama kuwa ta ji dad’in batun matuk’a….

Najeeb kam farin cikin da yake a ciki ya k’i b’oyuwa…Tana wucewa ya kira Yash yace masa “zai tafi”
Yana sauk’owa ya kallesa yace”har kun gama?”

Jinjina kai ya yi kafin ya mik’e yace”Yash Ya’isha kar ta zamo silar…”
Dariya ya ga Yash d’in ya fara kafin yace”Najeeb if I were in your shoes (inda ace nine a matsayinka) to da da gudu zan bar sisternka fa in zab’i Manubiya, na san menene so!”

Sai kuma ya yi tapping shoulder d’insa ya ce”laifin Ya’isha ne,na dad’e da fahimtar hakan,kar ka damu!”

Ganin still Najeeb d’in bai sake ba yasa cikin zolaya yace”Allah ya sa nan da next week mu je mu yi gaisuwar iyaye”
Da sauri Najeeb ya ce”Ameen”
Dariya Yash ya yi yace”an zo
wajen da za ka yi magana kenan…..”
“You are welcome”
Daga haka suka fad’a zancen case d’in estate d’insa…wanda akwai haske sosai dan ana ta samun ci gaba,soon inshaaAllah suna ganin za a kamo culprit d’in(mai laifin)…..
Chapter 88 · 0% Book details