Sashe 111
Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
…
Ko da Yashjub ya wuce ya bar Kausar, ciki ta shiga ta wuce bedroom ta fad’a bathroom domin ta watsa ruwa, tana mai jin wani sanyi da farin ciki kamar an yi mata bushara da gidan aljannah…plan A ya kammalu ba tare da wata matsala ba, yanzu saura plan B!tunda an yi sati biyu to ciki zai iya baiyyana kenan, gashi shima Yash d’in ya fara zuwa gida dama tanaso ayi komai a gaban sa ne, dan haka ta shirya akan gobe inshaaAllah dai dai lokacin da ta san yana zuwa za ta yi abunda ta shirya…
Tana wannan tunanin tana jin wani tsantsar farinciki hakanan ta kammala wankan ta ta fito d’aure da towel…
Sai da gabanta ya yanke ya fad’i da ta ga Yassir zaune a kan gado, idanunsa da fuskarsa sun yi jazur!!!
Ya tsoratata sannan yanayin sa ma ya tsoratata matuk’a..kamar mai jin tsoro haka nan ta k’arasa a hankali ta nemi guri ta zauna a gefensa tace”me ya faru?”
Ta yi masa tambayar a d’arare…
Sai da ya d’auki sama da minti d’aya tukunna ya juya ya zuba mata manyan idanunsa waenda suka yi jaaa yace”Kausar change of plans(shiri ya sauya)..ba za mu tsaya har ki haihu kafin Yashjub ya mutu ba, ya zamo dole ya mutu a yau!yanzu.”
Gabanta ne ya yanke ya fad’i, hankalinta ya yi masifar tashi, tashi d’aya yawun bakinta ya k’afe…da mugun kyar ta samu ta ce”me ya faru?”
Cikin tashin hankali shima yace”kawai a matsayinki na partner ɗita a komai da komai ne ya sa na ga ya kamata in gaya miki ki sani!
Ki bari zan yi miki bayani, amma ba yanzu ba, sai in komai ya kammalu. dan a yanzu ba zan iya ba Kausar, Ina cikin masifa, ba zan iya dogon bayani ba.”
Ya fad’i hakan yana mai mik’ewa da shirin fita,da sauri itama ta mik’e ta sha gabansa ta tsaya cikin nemo kalamai da mugun kyar..ta samu ta haɗa tace”Yassir, kar ka yi abunda za ka tona mana asiri ka lalata komai, ka tsaya ka nutsu ka yayyafawa zuciyarka ruwan sanyi, ka fad’a mini me ya faru, mu samu mu san abunyi….dan Allah dan annabi.”
Ta k’arashe maganar kamar mai shirin fashewa da kuka.
Saida ya runtse fuskarsa cikin tafukan Hannayensa, ya murtsuka ya fesar da wani zazzafan huci!!!
Tukunna yace”Yaran Grenade sun turawa Yashjub message…
yanzunnan nima suka turo mini shaidar sun tura masa ɗin..
Na gani kuma na tabbatar da sun tura masa videos kala kala har da wanda nake kulla yarjejeniya da su, da wanda nake basu kud’i!! Da ragowar maganganu na da su! da muryata da komai ma duk sun tura masa ta watsapp Kausar! komai da kika sani duk wata shaida da za ta nuna nine duk sun tura.
A yanzu dai na san bai riga ya gani ba, dan na duba na ga baya online…..
Kausar kar ki ce mini a’a, ko kuma ki ce za ki kawo wata mafita ko shawarar, dan ya zama dole Yashjub ya mutu kafin ya ga sak’onnin nan ya bankad’a komai ya saka a kashe ni! Kisan wulak’anci, cikin rashin gata.”
Karkarwa jikin Kausar ya d’auka…..ganin yana shirin fita yasa ta sake tare hanya tace”Yassir kar ka je garin kashe sa a kamaka!”
Wannan karon cikin tsananin b’acin rai yace”wai ba kya fahimtata ne???duk bayanin da na yi miki ba kya ji na ne?? An riga an tura masa ko na yi yunk’urin kashe sa ko ban yi yunk’urin kashe sa ba zai ga komai kuma idan ya gani aka kamani to kashe ni za a yi!
Dan haka gara in yi yunk’urin da fatan samun nasara a samu ya mutu, akan in zauna ban yi komai ba ni in mutu!”
Jikinta yana wani irin karkarwa tace”Yassir idan kuma suka turawa Daddy fa?shima binsa za ka yi ka kashe sa?ina ji maka tsoro kar ka je garin hanzari tsoro da fargaba kwab’armu ta yi ruwa!
Ka duba fa ka ga yadda kwata kwata plan d’inmu bai yi aiki a kan Daddy ba, dan sam bai ji haushin Yashjub ba, sannan ba mu riga mun ce cikin nan nasa bane ba ya ji ya sani!
Akwai abubuwa da yawa a gabanmu da ya kamata mu yi, kar ka lalata komai ka saka mana fullstop, dan idan aka kamaka komai ya zo k’arshe…misali yanzu ka je garin sauri a kamaka me kake tunani?,komai fa ya lalace mana kenan!
amma idan muka nustu muka yi tunani za mu samu maf…”
Cikin tarar numfashinta yace”idan na tunkaresa ba a kama ni ba kuma fa?sannan idan muka yi slow aka kama ni?”
“Yassir a irin wannan situation d’in mutum have to assume the worst!!!
saboda Ana so ka shirya kare kanka ka shirya mafita ka san abun yi idan komai ya rincab’e,ba fa a abu sama ta ka!”.
Abun nan da ya faru ni a wajena da tunanina gyarasa abune mai sauƙi!!
kar ka rikita kanka ta kwab’a komai ka lalata komai..a ganina dan sun tura masa tsaff za su iya gogewa tunda watsapp ne..Yassir kud’i fa aka basu suka karb’a suka yi maka aiki tun a karon farko!
Iyakar abunda za ka yi yanzu shine ka k’ara musu kud’i, wallahi in ka ƙara musu ɗin ni na san tashi d’aya za su manta da wani Grenade su bi ta watsapp d’in su goge, tunda kace ba ya online, ni kuma daga nan har zuwa dare ba zan bashi kwanciyar hankalin da zai hau watsapp d’in ba ma!.
Ai yana cikin gidan nan har yanzu, dan yanzu ma ta window Ina wanka sai da na hango motarsa a fake dam haka bai tafi ba har yanzu..so kawai ka jira ka zuba mini ido ka ga yadda zan yi da shi..
Sannan ka nutsu dan Allah!!kashe mutum yana da buk’atar plan da shiri,ko kaza za a yanka sai an wasa wuk’a an tanadi ruwa ballantana mutum d’an adam!
Ba ka da plan, ba ka da komai, tashi d’aya kace za ka kashesa a rana d’aya!! wallahi ba ni da tantama hakan ba mai yiwuwa ba ne ba, kuma sai an kamaka!kwanakin baya da ka yi yunk’urin hakan da tsararren plans har biyu ya mutu???sai yanzu a cikin rana d’aya ne kake son miracle ya (mu’ujiza ta) faru?”.
Shiruu Yassir yayi, yana mai fitar da huci kafin chan ya rungumeta cikin huci yace”I love you Kausar, na gode da kika wayar mini da kai,tabbas maganar ki gaskiyace…amma duk abunda kike shiryawa ki yi da wurwuri, saboda inaga masallaci kawai ya tafi daga nan zai wuce…”
“Okay bari in saka kayana”
Kawai tace, daga haka ta nufi closet d’inta ta zaro doguwar riga ta saka ta zare towel d’in ko undies da mai bata buk’ata ba haka nan ta wuce drawer ta d’auko turaren da tunda cikin ya shigeta ta tsani warinsa ta fesa a tafin Hannunta ta runtse da sauri dan tashi d’aya ta ji amai ya taho mata…Tana fara shiri Yassir ma ya fara waya da mutanen, ta san ba shi da enough kud’i yanzu shiyasa k’asa k’asa tace masa”ko nawa suka ce ya yarda za ta cika masa”
Daga haka ta saka Kai ta fice daga d’akin, tana jin
mugun mugun haushinsa,a ko da yaushe idan ya yi yunk’urin kashe Yashjub ji take kamar ta kashe sa!.
Addu’ar ta d’aya Allah ya sa mutanen su yarda kar su basu matsala! ita kuma ko nawa suka ce za ta bayar, ba ta so wani matsala ya taso ta koina kafin a yi aurenta da Yash.
Tana sauk’a ta tarar da su gaba d’aya suna cin abinci, har da junior Wanda ya zamewa Yadira cingum, itanma kuma ba laifi ya siye zuciyarta zuwa yanzu, musamman ma da ta fahimci yanzu ya shiryu ba kamar da ba, gashi shi aka zab’a mata dan haka aka bata shawara kuma itama ta yarda ta amshe sa hannu bibbiyu. Sosai Kausar ta ji dad’in ganin kowa a ranta tace”perfect!”.
Ba ta ko kalli kowa ba, hakanan ta wuce ta nufi kitchen babu wanda ta gaisar har Hajiya Mama, shiyasa ita kuma Hajiya maman cikin fushi tace
“tunda kitchen d’in ba na Ubanki bane ba, ki dawo ki zo ki gaida mutane, kafin ki shige”.
Wani sassanyan murmushi Kausar ta yi, dama hakan ta ke so ta faru, dan haka kawai ta shige cikin kitchen d’in ba tare da ta ko juyo ba!..kuma kowa ya san sarai ta ji! dan lokacin da Hajiya Maman ma ta fara magana sai da Kausar ɗin ta ja ta tsaya, tana dasa aya kuma Kausar ta ci gaba da tafiya ta shige cikin kitchen d’in.
Hatta su Mommy sai da suka sha tsananin mamaki, Hajiya Mama kuwa dire cokalinta ta yi da k’arfi ta mik’e tsaye ta kalli Junior tace”finciko mini Yarinyar chan, ka kawo ta nan, right away!!.”
Mik’ewa ya yi ya nufi kitchen d’in ransa shima a b’ace saboda da ma a wuya yake da su ita da Yassir, ga kuma rashin kunyar da ta yi wa Hajiya mama shiyasa yana shiga ya fincikota kamar yadda Hajiya Maman ta buk’ata, da ita da plate d’in hannunta ya fito da ita, sai da ya kawota gaban Hajiya Mama tukunna ya cika mata hannu ta hanyar yin cilli da shi….juyawa ta yi ta shiga zabga masa wata uwar harara yayinda shima yake jifanta da wani irin kallo.
Cikin b’acin rai Hajiya Mama tace”ai ni za ki harara ba shi ba..jinin marasa kunya da tarbiyya kawai!!
Idan ana gaya muku gaskiya ana cewa ku yi abunda k’uda zai bi ku ƙi yi, yanzu ai ga irinta nan kin fara gani tun a duniya! yaadda fuskarki ta koma izina ce a gare ki, kamata ya yi ace kin fara gyara Hali da ke da iyayen naki.”