← Book details Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 48 OF 152

Sashe 48

Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Fincikota Yusra ta yi da dukkan k’arfinta daga gaban Ummi,
Ummi ta yi mamakin yadda Munirat ta zabgawa Yusran mari dan ba ta yi tunanin wannan ƙarfin halin daga Munirat d’inba…..
..
A chan sama kuwa, tun d’azu da Baba larai ta cewa Mommy “ba su yi komai a gidan Yash ba suka dawo”shikenan Mommyn ta koma kamar robot, dukda Baba Laran ta kawo sabon plan amman sam ita gani take tunda basu yi wanchan na farkon ba shikenan ta shiga uku!da farko ta ɗan nutsu hankalinta ya kwanta kamar kuma wata wadda aka kunno tashi ɗaya sai ta sake burkicewa! Bayan ta yi dogon nazari….
Har ila yau, ganin hakan ya sanya Baba Larai ta zaunar da ita, bayan abubuwan da aka yi wa Yash ɗin itama Manu ba a barta hakan ba, dan a take Baba Laran ta yiyyi abunta ta gama tukunna ta bawa Mommyn tabbacin ta kunce mata jini…amma ko gezau! tashin hankalin da mommy ta ke a ciki bai ragu ba!
Ta dai ce mata to ne kawai amma masifar da take a ciki ba kaɗan bace ba….ji take kamar za ta mutu dan
so take ma ta yi kuka amman sam hawayen sun gagara fitowa daga cikin idanunta. Tana a wannan halin ne kuma ta je ta yi wa Kausar bayanin dawowar Manubiya da Yash cikin gidan tukunna a samu a yi komai, aikuwa a take sai kausar ɗin ta ƙarasa hautsina ta!!…dan a tunanin Mommy Kausar za ta yi murna da hakan amman sai ta ga sab’anin hakan, dan tashi d’aya Kausar d’in ta birkice ta shiga ce mata
”Ashe ma bata da burin raba auren Yash da Manu kenan, tunda har ba za ta iya korarta a wanchan gidan ba har sai an kuma d’aukar lokaci an barta ta dawo nan, kafin nan ma wataƙila ta dawo da ciki!! shikenan komai ya lalace mata, dan ta san indai Manu ta samu ciki to ta gama cin riba a kansu……ita kawai ta lura ja mata rai suke yi suna yi mata wayo, dan haka yanzu kawai abunda Mommy za ta yi mata shine ta kira Yash a yanzu ta ce masa ya saki Manubiya idan kuma yaƙi sakinta to ta ce masa za ta tsine masa!!!
Indai har Mommy ta yi hakan to ta yarda ba raina mata hankali suke yi ba, idan kuma bata kira Yash ba wallahi sai ta bar gidan a yau kuma ba zata sake ganinta ba!”

Hankalin Mommy idan ya yi dubu tou ya tashi, ta san idan ta yi hakan tabbas Yash zai saki Manubiya amman ko hauka takeyi ba za ta tab’a yin hakan ba saboda ta san yin hakan kamar ta kashe relationship d’inta da Yashjub da Daddy ne, dan kowa bak’in ta zai gani kuma ita kanta Kausar d’in muddin hakan ta faru to Yash ba zai tab’a yarda ya aureta ba har abada, hatta su Yasira ta san sai bak’in jininta ya shafesu, watak’il ma ya tartara kayansa ya tafi ya koma uk ya zauna a chan shikenan ba za a sake ganinsa ba har abada, kuma wataƙilan suna nan su basu sani ba shi kuma ya lallaɓa ya maida manubiyan….

Shiyasa ta fara k’ok’arin fahimtar da Kausar d’in cikin lallami.

Ganin hakan ya sanya Kausar ta wuceta da sauri tana wani Irin kuka ta d’auki wayarta da makullin mota ta fice da gudu, gudun ma kar Mommyn ta yi yunk’urin tsaida ita, a ranta ta gama yanke decision ‘wallahi sai ta bar gidan, a yau!.’

Dai-dai nan ne kuma Munirat ta zabgawa Yusra mari, suna shirin rufar mata suka ga Kausar ta sauk’o da mugun gudu tana kuka Mommy ma wadda ta biyo ta tana kiran sunanta tana hawaye sharr kamar an kunna famfo.

Da sauri Yassira ta k’arasa bakin main door ta tsaya dan taga nan Kausar d’in ta nufa.

durk’ushewa Kausar ta yi a daidai gaban Yasira tace”Yasira dan girman Allah ki matsa in fita, idan na ci gaba da zama a cikin gidan nan mutuwa zan yi, ba zan tab’a iya zama a gida d’aya da Yash da Manubiya suna tare ni kuma ina kallonsu a gefe ba…..yanzu haka ma baki san ya nake ji ba, na san suna chan tare! Duk da haka na yi k’ok’ari na danne kaina amman naga Mommy so take yi sai na mutu tukunna za ta kyaleni”….
muryarta ce ta sark’e sakamokon numfashinta da ya d’auke, dan haka ta kasa ci gaba da magana ta shiga kokawar janyo numfashinnata .

A hankali Yassira ta durk’usa a wajen k’asa k’asa tace “Kausar kar ki yi disgracing kanki(kar ki kunyatakanki), kalli
yadda su Ummi su ke kallon….”

Cikin tsananin fushi tace
“Disgrace my foot!(ina ruwan abun kunya)
Su kalla mana!ina ruwana? so kike in yi ƙarya da munafuncin ban damu ba bayan kowa idan ya ganni ya san Ina cikin tashin hankali, kuma na kasa, kuma kun kasa yi min maganin matsalata?…akwai disgrace (abun kunya) da rashin gatan da ya fi wanda nake a ciki??”

Ahankali Yasira ta janyota ta shiga rarrashinta.
Kamar Kausar d’in zata mutu tace “Ina ta k’ok’arin ganin na yi picking pieces of myself na yi haƙuri na daure amman shine
kuma duk da haka wai Mommy
saboda ba ita ta haifeni ba
ta zo tana ce min wai Manubiya za ta dawo nan!
Wanne irin rashin adalci ne wannan?.Ba ku ma da shirin korarta kwana kusa kenan sannan ta ya zan iya zama ta dawo nan Ina kallonsu tare a waje d’aya a d’aki d’aya da Yash!?”

Ganin yadda su Yahanasu suka zuba musu ido ne yasa Yasira tace”calm down mana Kausar(ki huce haka mana Kausar ki kwantar da hankalinki), ki zo mu je….”
Fincikewa Kausar d’in ta yi cikin tsananin fushi
tace “Stop telling me to calm down!
(Ku daina ce min in kwantar da hankalina)
tun yaushe kuke cemin in kwantar da hankslinnnawa in yi shiru za ku san abunyi amman har yau shiru???inda ace ke ce ko su Yusra na san da tuni Mommy ta uzzurawa Baba larai an yi an wuce wajen…….”

Da sauri Mommy da Baba larai suka k’arasa inda take k’asa k’asa suka shiga yi mata magana amman inaa kamar zuga Kausar ake yi, gashi sai d’aga murya take yi tana ta yi musu b’aramb’atama.

Takaici ne ya rufe Yassira
ga Munirat Ummi da Yahanasu sun tsura musu ido, shiyasa ba ta san lokacin da tace “Useless munafukai kawai!kun wani tsaya kun tsurawa mutane ido”

Yahanasu ta ji zafin zagin amman sai ta danne ta saki dariya kafin tace”Ku fa kuka ce kar mu yi bacci yau,ko ba kune kukace kar wadda ta bar parlourn nan tsakanin mu nida Munirat ba!?”

Cikin fushi Yassira ta k’arasa inda take ta tsaya a daff da ita
tace” Yahanasu ki kiyayeni!
Wallahi ki kiyayeni!.
Mara Imani mara tausayi kawai!na tabbatar baƙin cikin da ki ka ga Kausar a ciki ne yasanya ki farin ciki da dariya haka, muguwa azzaluma!”

Murmushi Yahanasu ta yi kafin tace”Sam ba abunda ya saka ni dariya ba kennan, farin cikin ganin yadda kuka fara tonawa kanku asiri ne yasanya ni dariya Yassira, ramin k’arya ai dama k’urarre ne!”

Cikin fushi Yasmeen ta matso ta ce “I have said enough Yaha” kafin tace “Da ke da Ummi da Munirat ku wuce ku bawa mutane waje.

Tun zagin da Yasira ta yi musu dama Munirat ta zo k’arshen wuya, Ummi kuwa ji ta yi da ta sani da tuni ta yi sama abunta…cikin b’acin rai Munirat ta ce”Saboda kar mu ji more of your dirty secret?(ƙarin munanan surranku?)
Wai ni Yasmeen wa kuka haifa a cikin mu ne? ni ko Yahanasu ko Ummi? dan naga yadda kuke yi mana magana kamar irin kun samu ya’yan cikin ku d’innan”
Ta fad’i hakan tana matsowa daff da su.

Yassira a k’ufule take
shiyasa tashi d’aya ta rufe Munirat da wani irin mahaukacin duka, kamar
jira Yasmeen take itama ta sa hannu dama ta tsani Yarinyar,
haka Yusra itama dama a wuya take tun marin da ta yi mata!…
Hatta Ya’isha da Yadira shiga sukayi sukai mata rubdugu.

Yahanasu da Ummi ne suka fara k’ok’arin kwatar Munirat, ba tare da tantama ba su Yasmeen suka fincikosu dama haushin Yahanasu suke ji, shiyasa suka fi rufar mata suka fi laftarta, itama Ummi sai da suka kai mata duka a Kai suka kaita har k’asa.

Dai dai nan Daddy ya fara sauk’owa k’asan sakamokon hayaniyar da ya jiyo.
Wata mahaukaciyar tsawa ya daka musu wadda ta sa suka d’an tsaya, sai da suka d’ago suka had’a idanu da shi tukunna suka ja da baya suna huciii, har Mommy wadda ta matso kwatar Yahanasu.

Duk yadda Ummi ta so kasa daurewa ta yi, ba ta san lokacin da hawaye suka fara sintiri akan kumatunta ba…..wajen Ummin Daddy ya fara zuwa, ya d’an shafa inda ya ga Yassira ta kai mata duka akai, wajen har ya d’an yi jaaa.

Tashi d’aya idanuwansa suka yi jazir ya juya ga Yassira
tana shirin yin magana ya fara kimarta, hatta Yasmeen da Yusra saida suka karb’i
rabon su amman su sun samu sun zille dan Yassirar ya rik’e, ita ta fi
fusatashi.
dama Ummi ba ta dad’e da gama faiyyace masa abunda suka aikata a gidan Yash da gidansu Manubiya ba…tashi d’aya daga jin zancenta ya fahimci ashe k’arya suka shirga masa d’azun da suka dawo, shiyasa dama yana jin haushin su akan hakan yanzu kuma ya ga wannan shirme da aika aikar da suka yi, shiyasa ya fusata ba kad’an ba.

BULAMA ✍️
0903 441 3252
*MANNUBIYA*
*Book 2*
*page 21*

Abunda bai tab’a yi ba kenan
Wato ‘dukan y’ayansa’.
Shi da kansa yana jin zafin dukan nasu da yake yi a halin yanzu amman kuma ya zama dole a taka musu burki, dan tabbas abun nasu ya zarce misali…..

Waya Mommy ta karb’a a Hannun Yadira wadda ta b’uya a bayanta, tashi d’aya Mommyn ta danna kiran Yassir, dan sun gagara kwatar Yassira a hannun Daddy.
Yana d’auka tace
“dan Allah Yassir ka yi maza ka zo yanzunna.”
Chapter 48 · 0% Book details